Showing 21001 words to 24000 words out of 243403 words
tsuma zuchiyar mai sauraro har barchi yayi awon gaba da ita.
Yola Nigeria
A hankali Inna ta waro idon ta wani haske ne ya kashe mata ido da sauri ta runtse su
sake buɗewa ido tayi a hankali, bin in da take kwance da kallo take sai wani jujjuya ido take sama, karaf idon ta ya sauka kan yaya Bello dake tsaye a Kanta ya harɗe hannu a kirji yana kallon ta, chike da mamaki tace "bello kai ne? Ina ne nan kuma? Waye ya kawoni? Ajiyar zuchiya yaya bello ya sauke tare da saukar da hannun sa kasa ya kariso in da take kwanche ya zauna a gefen ta burman nata ya fara magana "eh goggo habiba nine, nan kuma wajen mai magani ne, kuma ni na kawoki" yun kurawa tayi zata tashi amma ta kasa komawa tayi ta kwanta "yanzu Bello duk irin takurawa rayuwan ku da nayi bai sa kaki taimako na ba" "aa goggo habiba ki daina faɗin haka ko ba komai uwa ɗaya uba ɗaya kuke da Bappan mu kuma ni duk abun da nakeyi inayin sane dan Allah ba dan wani ba" kuka mai tsuma rai Inna ta fashe dashi chikin kuka take faɗin "Allah mai iko dan Allah Bello ku ya femin "goggo habiba kiyi shiru kinga yanzu kina chikin chiwo ni na yafe miki duniya da lahira Allah ya yafe mana tare" Shiru sukayi sai kuka kasa kasa Inna take, yaya Bello na rarrashin ta.
KANO
slowly zulaihat dake kwanche saman sofa ta tada kai da chinyar Aunty Amarya ta buɗe ido, da murna Aunty amarya ta fara faɗin "alhamdulliah alhamdulliah Allah mun godema ta farfaɗo" Ammi dake zaune a gefe guda ta taso ta nufo wajen tana faɗin "masha Allah" dogon tsaki Aunty amarya taja kafin tace "karki zo nan munafuka ba duk ɗan ki bane yaja ai wlh da ya kashe yar mutane zai gane kurenshi" shiru Ammi tayi ta dakata da nufar tasu da take, Ummi dake zaune saman sofa mai zaman mutun 1 ta mike ta kama hannun Ammi ba tare da tayi magana ba suka fice daga ɗakin sukayi part nasu.
Washegari Uk
Kwanche Lamrat take kan gado ta tada kai da chinyar yaya Yusuf sai kuka take,
Da kyar yaya Yusuf ya iya shawo kan ta ta dai na kuka kwata kwata taki chin abinci ita dai dole ya mai data wajen Ammin ta tun da kasheta yake sonyi, "my baby kiyi hakuri na miki alkawari ba zan sake miki hakan da zafi ba" waro ido waje Lamrat tayi chike da jin haushi tace "au daman yaya Yusuf zaka sake yimin hakan kenan? "My baby dole na sake yi maki mana idan ban miki ba taya zamuyi mu samu baby's" "nifa yaya Yusuf bana son baby's ɗin na hakura kawai ka mai dani wajen Ammi na" "haba my baby idan na mai daki wajen Ammi ni kuma fa dawaye zan zauna kenan? "Ka zauna kai kaɗai mana ai daman kai kaɗai kake zaune ba da ni ba "to shike nan tun da haka kika che yanzu dai zan mai daki wajen Ammi ni kuma sai na samo wata baby na Aura ta aifamin baby's masu kyau" kuka mai karfi Lamrat ta fashe dashi a razane yaya Yusuf yace "my baby lfy kukan me kuma kike "ni yaya Yusuf ka kaini wajen Aunty hiyana ta wlh ni yanzu bana son ka tun da dai wata mata zaka aura" dariya mai karfine ya kwache masa, dariya yake sosai har da rike chiki, ganin yana mata dariya ne yasa ta kara sautin kukan ta sosai, ba shiri ya dakata da dariyan da yake "sorry my baby tuba nake ni ai ke kaɗai kin ishe ni ba ruwa na da wata mace ni kam wasa nake" "ni dai yaya Yusuf ka kaini wajen Aunty hiyana tun jiya fa ban ganta ba"tana magana tana shesshekar kuka "to kiyi shiru idan kina son zuwa wajen su nima yanzu zanje na shirya na je wajen aiki sai karfe 2 na rana zamu dawo sai mu kai ku wajen shopping dan ku zabi kayan da kuke bukata" "to nayi shiru ka kai Ni" mikewa yayi batare da ya sake magana ba ya kwantar da kanta a saman gadon ya sauko kasa ya shiga dressing room jim kaɗan ya fito hannun sa ɗauke da jallabiya baki ya dawo kan gadon ɗagota yayi ya zura mata jallabiyar san nan ya miƙe ya ɗauke ta chak ya nufi waje da ita, a babban palon kasa ya samu su Zahra gaba ɗayan su suna zaune suna hira hiyana ce kaɗai bata wajen, saman sofa mai zaman mutun 3 ya direta chike da jin kunya lamrat ta fara gai da Zahra, shi ko juyawa yayi chikin sauri Zahra na gai da shima bai bi ta kan taba ya haye sama.
Da sallam hiyana ta shiga betroom ɗin Bgs sanye take chikin doguwar hijabi har kasa fari tas, hannun ta ɗauke da katon trey mai ɗauke da kayan breakfast nashi, tsaye yake gaban mirrow sanye da uniform na sojoji yana kokarin ɗaure gashin kansa ta baya, kasa kasa hiyana ke satar kallon sa ba karamin kyau kayan suka masa ba kamar dan shi akayi su, sai wani fitinannen kamshin da yake zubawa kamar anyi ɓarin turare ajikin sa, sosai take shakar kamshin turaren nashi
table ɗin tsakiyar ɗakin ta nufa da niyyar ajiye masa abincin, turus ta tsaya ganin abincin da ta kawo masa jiya da daddare ma ko taɓawa bai yi ba, shiru ta tsaya tana tunani shin na ajiye masa breakfast ɗin ko zai chi ne ko kuma dai na haɗa har da na jiyan na mayar kitchen tun da ba zai chi ba, tayi nisa chikin tunanin da take, sai ganinshi tayi ya wucheta ya nufi kofar fita, chikin sauri ta tsugun na kasa murya na rawa tace "ina kwana yaya prince" ko kallon in da take bai yiba ya fice daga ɗakin, shiru tayi ta kasa miƙewa dan ji tayi gaba ɗaya jikin ta ya mutu, yanzu ya zatayi da abincin nan, da ƙyar ta miƙe ta fice daga ɗakin ta mai da breakfast ɗin kitchen san nan ta dawo ta ɗauki na jiyan ma ta mai da kitchen chike da ɓachin rai ta koma ɗaki ta kwanta
Misali karfe 2pm gaba ɗayan su suna zaune a palon kasa suna hira wayar Zahra dake hannun Lamrat ya fara ringing, chikin sauri Lamrat ta miƙawa Zahra wayar, ansa Zahra tayi ganin sunan Aunty farida ne ya bayyana a kan screen ɗin yasa ta yin picking da sauri ta sanya wayar a hand-free dan su hiyana su gaisa da ita gaba ɗaya, daga ɗayan ɓangaren Aunty farida tace "Auta ykk? Ya Uk? "Aunty farida muna lfy ya junior? "Junior yana lfy ina Hiyana? "Gatanan Zahra tayi maganar tana miƙawa hiyana wayar, chikin sanyin murya hiyana ta fara magana
"Aunty farida ina wuni" "lfy lau my Hiyana ykk y mijinki? "Muna lfy ya junior" "yanzu dai bar zanchen wani junior mu fiskanchi abun dake gaban mu, kinga yanzu mijin ki yayi blocked ɗina, waro ido waje Hiyana tayi "yau Aunty farida ke da kanki yaya prince yayi blocked? "Eh my Hiyana nima na sha ruwan mamaki amma wan nan duk bashine matsalar ba kinaji kyalesa idan ya huche zai buɗe Ni, yanzu dai kina yin abubuwan da na tsara miki ne? ko kuma dai kin chigaba da zama shiru shiru "Aa Aunty farida inayi jiya ma na kai masa abinchi yau ma kuma na kai masa" "good my Hiyana abu na gaba da zan faɗa miki ya kamata ki rage tsoronsa kuma na faɗa miki ki daina sanya manya manyan hijaban nan da kike sanya wan kina jina ko? Zan sanya yaya Khalid ya sai muku waya gaba ɗayan ku dan mu rinƙa waya sosai kinji ko? Hiyana zatayi magana sukaji diran motochi su Bgs a chikin gidan alamun sun dawo daga wajen Aiki, chikin ruɗu hiyana tace "Aunty farida gasu yaya prince sun dawo aikin" "good my hiyana yanzu yana shigowa ki bishi ɗaki nasan yana shiga ɗaki zai zauna saman sofa yaɗan huta to yana shiga ki bishi ki chire masa takalmi da socks kinji? Shiru Hiyana tayi tana tunanin ta yarda zata fara tunkaran Bgs har ta chire masa shoe "my Hiyana kimin alkawarin zaki min hakan kinji? "Aunty farida na miki alkawari zanyi tana magana wasu zafafan hawaye na bin kunchin ta, hannu Zahra tasa tana gege mata hawaye chike da tausayin ta, katse kiran tayi ta ajiye wayar a gefe ta rike hannun Zahra tanan kokarin fara magana kenan, sukaji takun tafiyar su Bgs nan take suka nitsu ɓoye fuska hiyana tayi chikin chinyoyin ta dan hawayen nata sunki tsayuwa kuma bata son su yaya Yusuf suga tana kuka.
Bgs ne a gaba ya shigo kafin Zahra ta ɗaga masa gaisuwa ma ya haye sama abun sa, miƙewa Hiyana tayi chikin sauri ta bi bayan sa, a tare su Khalid suka shigo gaba ɗayan su suka baje a palon kowa ya zauna kusa da matar sa, chike da so da kauna suke gaisawa da juna "ke Amrat tashi kije ɗaki ki ɗauko min laptop di na" chewar yaya Fahad, da gudu Amrat ta miƙe ta haye sama
A ɓangaren hiyana kuwa
Tana zuwa bakin kofar ɗakin yaya prince ta tsaya ta goge hawayen ta, san nan ta shiga ɗakin da sallama yana zaune saman sofa mai zaman mutun 2 ya ɗan jingina da jikin sofan ya lumshe ido, a nitse ta tako zuwa gaban sa jikin ta har rawa yake, ta sungunna, ta kai hannunta kan takalmin sa, da kyar ta ita sai ta hannun ta ya dai na rawa, igiyar ta kalman tafara kwanchewa, da kyar ta iya ɗan ɗaga kafar tasa ta zame ta kalmin haka ta zame ɗayar ma, ɗan ɗaga kafar wandon nasa sama tayi ta kama bakin safar kafar tasa ta zame ta a hankali, zubawa kafar tasa ido tayi, ba karamin kyau dogayen yatsun kafan sa suka mata ba, ga wani bakin lallausan gashi a kwanche a kan yatsun, farchen (kunba) kafar sa farare tas sai kyalli suke bata san lokachin da ta kai hannun sa saman yatsun nashi ta shafuso su ba wani gigitachen mari ya sakar mata a kumatu wadda yasa ta mikewa tsaye ba shiri tare da fasa wani razanannen ihu chikin tsawa yace "get out" a guje ta fice daga ɗakin ta nufi nata
Tana shiga ɗakin ta ta chire hijabin jikin ta, ta sanya karfi ta yagashi gida uku chikin sauri ta ɗauko face Mark ta sanya a fuskar ta ɗaukan hijabin nata tayi ta taka saman gadon ta ta ɗaura hijabin a jikin Ac tanayi tana kuka mai suma rai, daure hijabin nata tayi sosai chikin kuka tace "banga anfanin rayuwata ba wlh Bappa ya rasu Inna ta rasu diyana ta ɓata yaya prince da yake matsayin mijina ya tsane ni to me kuma ya ragemin sosai ta gyara face Mark dake fuskantar ta yadda zatayi saurin mutuwa kar numfashi ta ya fita ɗaure wuyar ta tayi da kyau san nan ta sauka daga kan gadon kafar ta na lilo a tsakiya sai karkarwa take ta zaro blue eyes nata waje sosai saboda shake wuyar ta da hijabin yayi,
Amrat na fitowa daga ɗakin su rike da laptop ɗin yaya Fahad, daga ɗakin hiyana taji wani irin numfashi da take da sauri ta nufi ɗakin tana nura kofa taga hiyana na kokarin mutuwa dan gaba ɗaya har jikin ta ya fara saki, wani razanannen ihu Amrat ta saki wadda ya dira a dodon kunnen kowa dake gida, gaba ɗaya su Khalid suka miƙe a tare suka hauro dai dai lokacin Bgs ma ya fito daga ɗakin sa dan jin irin ihu da Amrat ta saki, kusan tare suka shiga ɗakin Hiyana.
Bgs na ganin halin da Hiyana ke chiki yaja wani dogon tsaki tare da karisawa chikin ɗakin da hannu ɗaya ya damki kafafunta tare da chire hijabin da ta ɗaure wuyarta ya sauko da ita kasa sai wani tangal tangal taka alamar ta jigata, wuyar ta ya damko ta bayan ya fara janta har suka fito waje, chike da bachin rai Khalid yace "haba Bgs menene haka? Bai bi ta kan kowa ba yayi waje da ita chikin bayan motar sa ya jefata ya shiga gidan gaba yau da kansa ya ja motar da gudu suka bar gidan, a razane Fahad yace "ina key ɗin ɗayar motar nan dole na bisu dan nasan halin yaya prince yanzu wani abun zai mata, tun kafin Fahad ya karisa maganar yaya Khalid ya shiga motar sa ya tayar da sauri Fahad da Ahmad suka shige chikin motar da gudu suka bi bayan Bgs
sai kuka su Zahra suke suna addu'ar Allah ya kuɓutar da hiyana daga hannun Bgs
Wajen saman wata gatuwar dutse dake zubar da ruwa kasa Bgs ya tsayar da mota fita yayi ya buɗe gidan baya ya damko wuyar Hiyana ya jata har zuwa bakin dutse kallon kasan dutse Hiyana tayi katuwar rafine awajen a tsorace ta dawo da kallon ta kan shi, so take ta chire face mark dake fuskantar ta masa magana amma kafin ta ɗago hannu ya daga mata tsawa chikin tsawa yace "ba mutuwa kike son yi ba to ga hanyar da zaki mutu chikin sauki, yana gama faɗin hakan yayi wurgi da ita kasan dutsen ya juya abun sa.....
Masu karatu Bgs fa ya buga min kai yau sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu naso na muku 2 page amma bani da charji shiyasa na muku long page Ashe karatu lfy azo a bani hot comments
NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖
*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇
*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)
*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)
*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)
*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)
💖The Talent Troupe Writer's 💖
*DUK ƘARFIN IZZATA*
💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*
Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai
Book 2
*Episode 9*
Uk
....wurgi yayi da ita kasan dutsen ya juya abun sa,ya shiga mota chike da tsanar hiyana ya ja motar da gudu ya bar wajen dai dai lokacin lokachin motar Khalid ya iso wajen yana kashe motar suka fito da sauri, a sukwane Fahad ya chiro wayar sa dake aljihun sa tare da balle agogon diamond dake hannun sa ya miƙawa yaya Khalid yayi tsalle ya faɗa kasan dutsen ya ce bi bayan hiyana, ta sauri yaya Ahmad ya karisa wajen yana kokarin faɗawa yaya Khalid ya riƙe sa yana faɗin "muje mu sauka kasan dutsen mu tare su a chan, a tare suka koma chikin mota yaya Khalid ya jasu juya kan motar yayi suka bar waje.
Suna karisawa kasan dutse daga bakin rafin suka ga motar yaya Yusuf a wajen, kashe motar yaya Khalid yayi a tare suka fito suka nufi wajen da yaya Yusuf yayi parking motar sa, da mamaki suke bin motar da kallo, ga mota dai motar Yusuf ne amma baya chiki, ɗaga kai sukayi suka fara dube dube ta in da zasu ga Yusuf, amma basu ga ko mai kama da Shiba, almost 5mins suna tsaye sunyi shiru sai karan tsuntsaye da ke tashi da sautin zuban ruwa.
Chan suka hango Fahad saɓe da hiyana a saman kafaɗar sa yaya Yusuf na biye dasu a baya dukkan su sunjiƙe sharkaf ruwa sai zuba yake daga jikinsu, hiyana kuwa ko motsi bata yi, da sauri yaya Khalid da yaya Ahmad suka karisa wajen su, a hankali Fahad ya kwantar da hiyana a kasa ta gefen rafin, zuba mata ido sukayi, fiskar ta yi falau ta kara haske sosai
hannu Fahad yasa ya chire face mark dake fuskantar ta ba karamin razana sukayi da ganin yadda tayi haske sosai kamar babu jini a jiki ta, kasa kasa Fahad yace "daman haka kamannin fuskar ta yake? Ai wan nan ba in da ta bar yaya prince a kamanni, wlh tama fishi kyau" dogon tsaki yaya Khalid yaja chike da ɓachin rai ya fara magana "wai kai Fahad ta fuskar ta ma kake ko? Baka tunanin abun da Bgs ya mata bai kyau taba kashe ta fa yaso yayi ba dan Allah yasa muna nan ba" "No yaya Khalid wlh ni ina da tabbacin dan yaya prince yasan muna nan ne kuma yasan bazamu taɓa barin ta mutu ba shiyasa yayi hakan amma wlh da yasan babu kowa ba zai mata haka ba, ai shi ba mahaukaci bane, yasan me yake yi" da sauri yaya Yusuf ya karɓi zanchen da chewa "kana da gaskiya Fahad wlh idan Bgs yasan bamu nan ba zai yi kuskuren jefata chikin ruwan nan ba, tabbas yana da zuchiya kuma yana za zafin rai sosai kuma ya tsani mace amma ai shi ba mahaukaci bane ya san idan ya kuskura wani abi ya sami sister wlh Ammi zata iya tsine masa akan hakan, yana sane da duk abun da yake, inaga fa ya mata hakane domin gobe karta sake kwatan ta kashe kanta da kanta" chiki tsawa yaya Ahmad yace "dalla kuma mutane shiru koma me kusani idan da wan nan abun da yayi wa sister yazo da karan kwana da ta mutu ku ɗaga kan ku fa ku kalli daga in da ya jefota wlh idan da wata mai karamin zuchiyar ne tun kafin ta iso chikin ruwan nan zata mutu dan tsoro, than God sister iya suma tayi" chike da confidence yaya Khalid ya fara magana "kana da gaskiya Ahmad wlh ya zama dole yau mu gwadawa Bgs kuskuren sa ai dan yaga muna tsoran sa sosai ne shiyasa yake duk iskanchin da ya ga dama kuna gani fa yana jefata ya juya ya shiga mota abun sa da bamu zo da wuri bafa wlh mutuwa