Showing 189001 words to 192000 words out of 194226 words
gefe kuma saman kujerun da aka tanada a farfajiyar dai,sa'ad ne zaune riqe da tab dinsa shi daya yana faman dannawa,kamar mahaifinsa,shi ko da yaushe ba mai hayaniya bane,hakanan ba mai son damu bane,yafi ganewa zaman shuru,rashin son hayaniyarsa ya sanyashi baro hall din,ya gwammace surutai da maganganunsu nasim akan qarar amsa kuwwar hall din.
Daga gefe asim ne yake musu tafi yana biye da waqar da gajee keyi musu,shikam kusan halinsu daya da as'ad din,ba ruwansa,dan wasa ne,ya dauko kawunsa uncle JB kamar yadda suke ce masa.
Idanuwanta ta maida kan gajee,gaba daya ta canza shekaru biyar kenan da suka shude,tun bayan mutuwar inna furera wadda ta rasu saboda lalacewar qodarta guda daya data tabu,dayar kuma an yanke an dauke,bayan ta rasun gajee data auri saurayin ta bayan ta gama zuba rashin kunya da diban albarka kan shi takeso,wata biyu kacal ya ajjiye mata saki cikin dare suka kada shanunsu suka qara gaba,haka ta dawo gida cike da nadama da darasin rayuwa,rasuwar inna furera ta sanyata tattara ya nata ya nata ta koma gembu,saboda tana ganin babanta bazai yarda ta zauna dashi ba,tuni ya qara aurensa,kuma amaryarsa ta riqe laulo da kyau,tunda dama matsalarsa kadance,kuma zuwanta sai yasa yaron ya daidaita,bayan ta koma wajen inno mahaifiyar furera wadda tuni ta makance sai zaman yaqi yiwuwa,kaf 'yan uwan furera da suka fito ciki daya aka rasa me riqeta,hakanan ta dawo gidansu.
Da farko.jauro yace bazai zauna da ita ba,amma amaryarsa ta tsaya tsayin daka kan nan din gidan uban gajee ne,bata da inda yafi nan,haka ya haqura,dama kuma shima ba yayi hakane don tauna tsakuwa don aya taji tsoro.
Zamansu lafiya lau,gaba daya gajee ta canza,saidai tun dawowarta babu wanda ya nuna sha'awar aurenta,don kowa yasan yadda abubuwa suka kaya,har wasu na mata qazafin cuta mai karya garkuwar jiki,tayi kuka ta sake dadawa,ta kuma ji yadda sharri da qazafi yake,ashe haka maimunatu keji duk sanda suka jefeta da kalmar mayya?,ko barauniya?.
Lokacin da maimunatu tazo garin yiwa yuuma ta'aziyyar rasuwar baffa labaran taga gaaje sai taji hankalinta ya gaza kwanciya,zuciyarta kuma ta kasa samun nutsuwa,daga bisani tabi shawarar da wani gefen na zuciyarta take bata,domin cikar dan adam ya zamana me yafiya,saidai ba lallai ne ko kuma tilas zuciya ta manta nau'in azaba ko cutarwar da wani dan adam yayi mata.
Kasa tsaiwa ta saurareta gaaje tayi,saboda tsananin kunya nadama da kuma dana sani,sai data saka akayi mata tara tara,sannan ta tsaya ta saurareta cikin matsanancin kuka
"Bazan iya hada muhalli dake ba maimunatu,iya girman cutarwar da mukayi da yafiyar da kika mana ma kawai ta isa,kiyi tafiyarki kici gaba da rayuwarki cikin farinciki,ki barni naci gaba da karbar sakamakon abinda na shuka" maganar gaaje ta sake karyar mata da gwiwa,sai taji hawaye kawai yana sauko mata,meye rana ko ribar cutar da dan adam?,indai kyautatawa riba ce ga rayuwa tabbas zata kyautatama gaje,baa saka sharri da sharri,da wannan tayi magana da jauro,wanda shima da farko yace ta barta kawai a haka har Alllah ya sake fidda mata miji,saidai daga baya titi matar daya aura ta saka baki gaaje ta biyo maimunatu,wannan shine asalin zamansu tare,gaba daya rayuwar gaaje ta sauya,idan ka ga yadda ta canza kai baka ce ita bace, maimunatu bata barta da duhun jahilci ba,ta maidata islamiyya ta manya,saida ta sauke ta kuma iya litattafai da dama,wanda wasunsu a wajen maimunatu take daukan karatun,tana musu karatun ne ita dasu as'ad duk dare na litafin hadith da kuma fiqhu,gaajen bata da sha'awar karatun boko sam,don tace iya na addini ya isheta rayuwar duniya,gaba daya ta tashi daga gajen ta koma barira(asalin sunanta),saidai gajen bata bace ba a bakinsu.
Kusan ita ke taya baaba tabawa aikace aikacen gida da rainon yara,duk da maimunatu da baaban sunso hanata amma tace wannan kadai take ganin zatayi ta sakawa maimunatu,ta kuma shafe munanan abubuwan da suka aikata mata ita da innarta wadda har yau nema mata gafara takeyi.
Abu guda ke damun maimunatu,shekara goma sha uku kenan da auren ita maimunatun,amma babu zancan aure wajen gaaje,yanzun haka su asad shekarunsu sha biyu kenan,takanyi murmushi kawai duk sanda aka mata zancan aure.
Ana haka himu ya bayyana a matsayin ma'aiki a qarqashin dr marwan,gaskiyarsa jajircewarsa da riqon amanarsa ya sama masa matsayi wajen dr,randa suka fara haduwa da maimunatu kamar bai taba saninta ba,duk da sun gaisa cikin mutunci,shima yayi aure amma sun rabu da matar sai yaransa guda biyu dake hannun daadarsa,wadda nauyin kulawarta take wuyansa tun bayan rasuwar mahaifinsu baffa labaran.
Yana yawan zuwa saboda yuuma data dawo gidan wajen anni,burin annin kenan na shekara da shekaru sai yanzu Allah yayi sanadin mutuwa,sanin alaqarsa da yuuma ya qara masa matsayi a wajen dr marwan,ya sake jansa a jiki,tare da matsayin da yake samun albashi da kyau.
Kuka sosai daadarsa ta dinga yi sanda taga abinda Allah ya yiwa himunta,ya samu rufin asirin da kai tsaye zaa kirashi da mai kudi a yankinsu,duka ta dalilin yuuma da maimunatu,mutanen da bata kallonsu a baya a matsayin wasu abubuwa masu daraja.
Yuuma ce ta bashi shawarar idan ya gama gininsa ya nema aure,ya kuma dauko daada ta dawo nan,amma kunya tasa daada tace ba zata iya zama kusa dasu ba,batasan da wanne ido zata kalli anni ba,hakan ma da suke ci susha daga alfarmarsu ba tare da sunyi duba da dabi'arta ba godiya take musu.
To shima himun tsoron zabar matar aure yake a yanzun,don baiji dadin aurensa na fari ba,duk da sauqinta zabin daada ne,yuuma dai nata bashi shawari tare da jan hankalinsa akai.
To gaurayen marasa auren nada yawa,cikin ikon Allah hankalin maimunatu afrah da anni ya karkata akan yiwuwar hada yuuma da abbuuun maimunatun aure,suka kuma gabatarwa da abbi wato dr marwan
"Na dade ina qiyasta hakan a raina,saboda dacewa da sukayi da junansu,zan jarraba,Allah yasa a dace,Allah kuma ya sanya alkhairinsa da albarkarsa a ciki".
Cikin ikon Allah kuwa dukkaninsu suka bada hadin kai,abun ba qaramin dadi ya yiwa su maimunatu ba,hadi kuwa yayi albarka,cikin wata qudurar ubangiji isa tsarki da kuma buwayarsa saiga yuuma da ciki,abunda ya girgiza tunanin kowa,yuuma da ciki?,ita kanta ba qaramin girgiza tayi ba,ta kuma qaryata har sai da laulayi ya kankama
"Allahu akhbar,Allah buwayin sarki,duk zaman nan ashe rabon yana ta wani waje daban yana jiranki ramatu?" Anni ta fada tana qwallar farinciki,ita kanta yuuma kuka ta dinga yi sosai,kafin daga bisani kuma ta dinga jin kunya,takan kalli kanta,taga yadda shekaru suka fara tarar mata amma wai ciki gareta?.
Ta fannin hajja kuwa kamar ta zuba ruwa a qasa tasha
"Allah mun gode maka,ashe abubukar akwai sauran qwanka a duniya" shiko abbu fadin irin farinciki daya samu kansa ma bata baki ne,haka ya dinga bawa yuuma kulawa dai dai da shekarunsu,cikin girma da kulawa,har Allah yasa ta haife abinda yake cikinta ta hanyar CS da akayi mata,aka samu yaro namiji wanda kai tsaye abbuu ya sanya mata sunan mahaifinta ita yuuma din,yace shi 'yan uwansa sun saka sunan nasa mahaifin,wannan ya isar masa,itakam gwara a bar mata abinda zata dinga tunawa.
Ajiyar zuciya maimunatu ta saki,yadda gaaje kewa yaran kawai zai gaya maka zallar shaquwa dake a tsakaninsu,tausayinta yana cikata,shekarunsu sun fara turawa,a qalla yanzun dukkansu suna neman shekara talatin da hudu zuwa da biyar,so ya kamata ace ta ajjiye itama zuri'ar da zata tuna da ita ko bayan ranta.
"Ummeee" nasim wanda ya fara hangota a cikinsu ya fada da qarfi yana wara hannayensa gami da qoqarin gangarowa zuwa wajenta,abinda yaja hankalin sauran kenan,asad ya ajjye tab din hannunsa ya taso a nutse ya karba hand bag dinta yana cewa
"Sannu ummee,amma an gama ko?" Dubansa tayi da murmushi bayan ta duqa ta dauki nasim
"Ka gaji kenan?" Shafa kansa yayi kamar wani babba
"Hayaniya....hadisan da kika kara mana shekaran jiya da daddare naketa qoqarin haddacewa,so gurin ba dadin zama na kasa riqewa" murmushi tayi tana duba hannun nasma dake nuna mata wai ya baci da qasa
"Mun gama sai tafiya gida" ta fada tana sauke dubanta ga gaaje
"Antyn yara,basu barkima kin shiga ciki ba bare kiji duka abinda aka tattauna" murmushi tayi
"Na jiyo wasu abubuwan ta nan....."
"To Allah yasa mu amfana"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu" gaaje ta amsa,sai maimunatun ta fara takawa a hankali tana cewa da as'ad ha hado kan yaran gaba daya anty barira ta huta
"Amma gidan yuuma zamu tafi ko?,kwana biyu bamuje ba" da murmushi maimunatu ta kalleta
"Zaki fake da haka dai ki gudu,aikin saba duk sanda daddy zai dawo a tafiya saiki tarkata kansu ku gudu da sunan ziyara" murmushi tayi mata
"Aiba laifi bane,sai sunfi barinki kin sake kin hadawa daddy hankalinki waje daya" murmushi kawai maimunatu tayi,gaajenta ta canza,ta yadda kullum mamaki take sakeyi.
"Ki bari ya iso,kuyi masa sannu da zuwa,sai na tambayar muku zuwan tunda gobe ba school,an shiga hutun makaranta"
"To shikenan" ta amsawa maimunatun,tana takawa zuwa inda motar ke girke tana jiransu,asad ne kawai a ciki.
lafiyayyar motar suka shige gaba dayansu driver yaja,yaran sunata hirarrakinsu,kowa na fadin sautun daya bawa captain J din,a haka suka dauki hanya.
Sai da suka biya ta wani babban guri,ta karba saqonta a wajen sannan suka isa gida,a gaggaucw ta fita a motar ta barsu da gaajen,yau ko rabiyar fadan da sukanyi sanda zasu fita a mota na "kin takani" bata tsaya bi ta kansu ba, mayafinta ma dashi ta wuce kitchen din.
_ZAFAFA BIYAR_
_ZAFAFA BIYAR_
_ZAFAFA BIYAR_
_ASSALAMU ALAIKUM JAMA'AR KWARAI MASOYA MABIYA, KUMA MAKARANTA ZAFAFA BIYAR..._
_ALBISHIRIN KU... INA MASU JIRAN *COMPLETED DOCUMENTS NA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR DA AKA KAMMALA WANNAN KARON* ?_
_KU MATSO.. DOMIN JIRAN DA KUKE YA KARE... LITTATTAFAN NA ZAFAFA SUN KAMMALU DAGA FARKO ZUWA KARSHE CIKIN FARASHI MAI RAHUSA..._
_GA MASU TAMBAYA.... ZAFAFAN DAI GA SU KAMAR HAKA_
_*FARHATAL QALB* (NA NANA HAFSAT MSS XOXO) NERA 400_
_*GURBIN IDO* (NA SAFIYYAH HUGUMA)NERA 400_
_*SANADIN LABARINA* (NA HAFSATU RANO)NERA 400_
_*INAYAH _RIBA BIYU* (NA MAMUH GEE)NERA 400_
_*BABU SO* (NA BILLYN ABDULL)NERA 400_
*_DUKA COMPLETED DOCUMENTS DIN AKAN NERA DUBU BIYU 2K (2,000)_*
_YADDA ZAKU BIYA_
_IDAN BANKI NE_
_ACCOUNT NAME: HAFSAT UMAR KABIR_
_ACCOUNT NUMBER: 2270637070_
_BANK NAME : ZENITH BANK_
_SAI KU TURA SHEDAR BIYA TA: 07040727902_
11/30/22, 08:56 - Buhainat: _ZAFAFA BIYAR_
_ZAFAFA BIYAR_
_ZAFAFA BIYAR_
_ASSALAMU ALAIKUM JAMA'AR KWARAI MASOYA MABIYA, KUMA MAKARANTA ZAFAFA BIYAR..._
_ALBISHIRIN KU... INA MASU JIRAN *COMPLETED DOCUMENTS NA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR DA AKA KAMMALA WANNAN KARON* ?_
_KU MATSO.. DOMIN JIRAN DA KUKE YA KARE... LITTATTAFAN NA ZAFAFA SUN KAMMALU DAGA FARKO ZUWA KARSHE CIKIN FARASHI MAI RAHUSA..._
_GA MASU TAMBAYA.... ZAFAFAN DAI GA SU KAMAR HAKA_
_*FARHATAL QALB* (NA NANA HAFSAT MSS XOXO) NERA 400_
_*GURBIN IDO* (NA SAFIYYAH HUGUMA)NERA 400_
_*SANADIN LABARINA* (NA HAFSATU RANO)NERA 400_
_*INAYAH _RIBA BIYU* (NA MAMUH GEE)NERA 400_
_*BABU SO* (NA BILLYN ABDULL)NERA 400_
*_DUKA COMPLETED DOCUMENTS DIN AKAN NERA DUBU BIYU 2K (2,000)_*
_YADDA ZAKU BIYA_
_IDAN BANKI NE_
_ACCOUNT NAME: HAFSAT UMAR KABIR_
_ACCOUNT NUMBER: 2270637070_
_BANK NAME : ZENITH BANK_
_SAI KU TURA SHEDAR BIYA TA: 07040727902_
87
K'awataccen kitchen ne na wadanda suka samu duniya da kyau a hannunsu,iya tsaruwa ya tsaru,hakanan an wadatashi da dukkan wani nau'in kayan wuta,bedroom da kitchen dinta suna daya daga cikin muhallan da maimunatu bata wasa dasu,don duniyar gidan aurenta kenan,tana iya kashe ko nawa ne ta qawatasu,don faranta ran captain dinta.
Da sallama a bakinta ta shiga kitchen din a dan gagggauce,mutuniyar kirki baaba tabawa na tsaye tana aiki,yayin da yasira kuma ke zauna tana tayata suna hirarsu kadan kadan.
Da murmushi saman fuskarta ta waiwayo tana yiwa maimunatu sannu da zuwa,yayin da yasira ta miqe itama cikin girmamawa uwar gijiyar tata mai tsananin kirki da adalci itama tana mata barka da zuwa,gami da yunqurin karbar mayafinta da take qoqarin zarewa
"An karbo kambun andawo kenan?" Murmushi maimunatu tayi yana buda kwabin alkubus din da tayi kafin ta fita
"Mun dawo baaba,amma naso manyan naki yana kusa,shi yafi cancanta ya karba min" kai ta jinjina tana murmushi,yanayin soyayyarsu koda yaushe abar burgewa ce,kullum sake kusanci suke da juna
"Dake dashi din duk daya ne maimunatu,idan kaga zahra ai kaga wata,kema kuma kin cancanci ki karba,alkhairanki ga al'umma masu tarin yawa ne,Allah dai ya jiqan mahaifiyarki,ya raya miki zuriyarki,ya kuma qara danqon qauna tsakaninki da mai gidanki"
"Ameen baaba,na gode,Allah ya qara nisan kwana da lafiya me amfani"
"Ameen ameen" daga nan suka kama aikin gadan gadan,wanda kafin wani lokaci sunyi nisa a aikin.
Suna falo sunata hayaniyarsu,lokaci lokaci suna shigowa kitchen din,wannan ya kawo qarar wancan,wancan ya kawo qarar wannan,kasancewar gaaje ta fita islamiyya bayan dawowarsu,sai su kadai,asad dake ta aikin alqalanci ya gaji,shi kuwa as'ad dama ba kasafai yake kula fitinarsu ba,idan yayi magana daya biyu ana uku baka jiba jikinka ne zai gaya maka, maimunatu na yawan masa fada,shi yasa bai fiya zama cikinsu suna wannan shirmen ba.
Sai data tabbatar komai ya hau saiti sannan ta saki ajiyar zuciya tana duban agogon dake kitchen din,akwai sauran minti arba'in a gabanta,waiwayawa tayi ga yasira
"Nan da minti ashirin ko da biyar haka,don Allah ki kunna dukka burners din gidan nan a saka turaren wuta ko ina"
"To ranki ya dade,turaren wajen aisa?" Idanu ta fidda tana dubanta
"A yau din?,ai karkimin gangancin nan,turare idan bana hajiya na'ima ba banason kowanne a gidan nan"
"Gaskiya ne,na jima banji turare irin nata ba wallahi,kamar kyauta ake bata kayan hadin,komai a wadace kamar yayi.magana,rannan fa asad naga yana murza turaren a jikinsa,nace me ya hadaka da turaren icce?,wai qamshin turaren ne baya gajiya dashi" dariya dukkansu suka saka maimunatu ta fara takawa zuwa gaba tana cewa
"Kinsan qasan kwalaben iya ruwan turaren dake kwanciya ya isa azuba wani sabon turaren ya tsumu,kiyi a gida kiyi a kayan sawa gaba daya,gaskiya yanzun ban gane kowanne turare idan ba nata ba"
"Ai ta hadu wallahi matar" yasira ta sanya musu baki,don ita kanta tafi son maimunatun tace ta kunna turaren hajiya na'imar saboda yadda gidan ke daukan wani tattausan qamshi
(Tasted and trusted,ba biya tayi ayi mata talla ba,nayi hakanne don mata su amfana,saboda naga yadda yake zaunarwa da gidanki da jikinki qamshi,na tabbatar duk wadda tayi amfani dashi saita godemin,turaren wajenta shine turarena a yanzu,na bar amfani da turaren wutar kowa idan ba nata ba zaki iya tuntubarta ta wannan number (803 212 7953) if u are interested,idan kinji dadinsa kiyimin addu'a kawai).
Sai data fara komawa sassansa tayi masa barin turare sosai,ta duba lungu da saqo ta tabbatar komai yayi neat tun daga katafaren falonsa zuwa lafiyayyen bedroom dinsa,ta ajjye masa dukka siyayyar data yi masa kowanne abu a muhallinsa sannan ta wuce nata sassan.
Bedroom ne itama mai lafiya,wanda ya zamanka a ciki ya isa samar maka da nutsuwa, yadda aka shiryashi kadai ya isa gaya maka matar gidan tasan abinda takeyi,tasan kuma me ake kira da aure da kuma soyayyar miji,toilet dinta ta shiga ta fara shirya kanta.
Cikin minti talatin kacal komai ya zama ready,ba abinda jikinta ke fiddawa sai daddadan qamshin turaren hajiya na'ima mai taushi da sanyaya rai,cakude da wasu lausasan bidy mist.
Wani fitananniyar atamfa ta saka wadda aka yima wani zaunannen dinkin girma,da yayi masifar fidda haibarta da kuma kwarjininta,kallo daya idan kayi mata ba zakaso sauke dubanka daga gareta ba,don ita kanta data fito falo yaran binta da kallo suka dinga yi,duk da sun saba ganin irin hakan a tare da ita,amma kwalliyar yau din ta tafi dasu,gaaje ma sai data yi comment akai,saboda sosai gayun maimunatu ke burgeta.
Tana tsaka da musu fada akan rashin fita da abincin masu gadin gidan da wuri,sannan ta koma wajensu asim tana masa maganar yadda suka fidda dukka games dinsu suna bazasu a wajen qarar bude gate da shigowar motoci gidan suka baqunci kunnuwanta,sai ta lumshe idanu bugun zuciyarta yana sake daduwa,wanda ya tabbatar mata da dawowar masoyinta uban 'ya''yanta kuma rayuwarta gaba daya zuwa gareta,ta sauke wani siririn murmushi dake dauke da tarin saqonni daga zuciya har zuwa saman fuska.
Tana jin nasma da nasim na rige rigen fita zuwa gareshi,saidai ta tabbatar kafin su isa ya shigo,kusan haka al:adarsa take,duk sanda yadda suke sauri wajen ganin sun cimmasa sai ya rigasu,don shima a d'okance yake dawowa kuma a qagauce da son ganin iyalin nasa.
Kamar yadda ta zata kuwa a bakin qofar falon sukayi clashing da yaran,the handsome and adorable captain ja'afar marwan khalid akko,cikin wata shiga data bayyana zallar izza kyau kwarjini da kuma qasaitarsa,sassanyan matashi wanda yake kan ganiyar quruciya kyau da kuma arziqi,wanda ya dace da macen qwarai haziqa daya tamkar da dubu irin maimunatu,wadda a kowanne mataki na rayywarsa tana biye dashi tana kuma riqe hannuwansa zuwa kowanne mataki a rayuwa,nasara ko kuma akasinta.
"Assalamu alaikun warahmatullah" ita ya fara fada hancinsa yana shaqar masa qamshin da yafiso a duniya fiye da kowanne qamshi,zuciyarsa na masa wani irin motsi