Showing 39001 words to 42000 words out of 194226 words

Chapter 14 - GURBIN IDO COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

12 Dec 2024

26153

ta fito wajen ya fara cika da mutane,mafi akasarinsu ma'aikatan gidan ne maza da mata,kowa na mata sannu da zuwa tare da qoqarin nuna kulawarsa a gareta,abinda zai nuna maka irin girma matsayi da kuma muhimmancin da take dashi.

Waiwayawa tayi ga maimunatu wadda ke rabe bayan murfin motar da suka fito a ciki,cikin tsoro,kamar xaka ce mata ket ta zura da gudu,sannan ta dubi daya daga cikin ma'aikatan,babba ce aqalla zatayi shekara arba'in da takwas,kuma da alama ita din ta hannun daman anni ce nesa ba kusa ba

"Tabawa riqo min baquwar nan ki shiga min da ita ta qofar baya" ta fadawa tabawan qasa qasa,gyada kanta tayi sannan ta juya inda anni tayi mata ishara,tunda tayi mata magana ta haka tasan cewa wala'alla abune na sirri bataso kowa da kowa ya sani.

Murmushi tabawa ta sake mata sannan ta kama hannunta,ko ba komai maimunatun taji ta sake da tabawa farat daya,saboda yadda ta kama hannunta babu kyama ko alamun kyara ko kuma tsangawa,tana biye da ita har sanda duka bulla wani tangamemen falo,falo ne daya wadata da dukkan nau'in kayan alatu na rayuwa,rukunin kujeru biyu ne a cikinsa saboda girmansa,kowanne color dinsu daban,akwai qofofi a ciki dake nuna alamun dakunan bacci ne,sai wata gajerar siririyar hanya wadda kitchen yake a ciki.

Kitchen ta wuce da ita,wanda maimunatu ga bishi da kallo cike da mamaki,farat daya ta gane kitchen ne,duk da na ainihin gidansu na gembu bai kama koda qafar wannan ba

"Tsaya ina zuwa" tabawa ta fada sannan ta juya ta fita,bata yi koda minti daya cikakke ba ta dawo,tana murmushi ta dubi maimunatu

"Kiyi haquri ko,na barki a tsaye,muje na nuna miki dakinki" kai ta gyada kawai tana maida mata martanin murmushinta,a salube kuma tabi bayanta.

Dakin yafi kusa da kitchen din gidan,don shi daya ne area din,babban dakine da aka shimfideshi da tiles marbles baqaqe masu dishi dishin light blue a jikinsa,yana dauke da babban gado madubu da wardrobe ta jikin bango,gurin ajjiye takalma,da manya bedside guda biyu masu dauke da bedside lamp,tun daga curtains zuwa dan qaramin carpet din dake malale a gaban gadon duka light blue ne,abinda ya qarawa dakin haske da kuma kyau.

"Anni tace nan ne dakinki,ki zauna ki huta sosai,sannan ki fadi abinda kikeso kici,ga bandaki can koda wata buqata zata kamaki,tace zata kiraki idan ta gama" kai maimunatu ta gyada,jikinta a sanyaye,tana ganin kamar taxo inda bai cancanci tayi rayuwa dasu ba,tako ina mutanen nan sunfi qarfinta sun kuma wuce tunaninta,yanzu wannan dakin shi za'a bata a matsayin dakin kwananta?,ita a wa?.

"Me zakici?" Tabawa ta sake maimaitawa idanunta akan maimunatu tana nazarinta,da sassanyar muryarta tace

"Ba komai,banajin yunwa,bamu dade da cin abinci ba" gaskiyarta kuma ta fada,cikinta ya riga da ya zama mara space sosai da bazai iya daukan wani abincin ba bayan awanni biyu,yunwa ta zamar mata jiki

"Shikenan,amma idan kinji kina da buqata,ga waya can ki daga ki kira kitchen,za'a kawo miki duk abinda kike buqata" kai kawai ta sake gyadawa bawai don ta fahimci yadda zatayi kiran ba,sai taga tabawan ta qarasa wajen da qullin kayanta suke tana niyyar dauka

"Kaya na ne" daga kai tayi ta dubeta,murmushi tayi mata sannan tace

"Anni ce ta bada umarnin a daukesu,za'a kawo miki wasu kayan da xakiyi amfani dasu" bata son rabuwa da kayan,kayan suna d matuqar amfani da kuma tarihi a wajenta

"Don Allah ki cewa anni tabarmin su,ina so" fasa dukan tayi,sai ta amsa mata da to,ta juya ta fita a dakin sannan taja mata qofar ta rufe

A nutse ta gama qarewa dakin kallo kusfa kusfa,daga nan inda take zaune tana iya jiyo maganganun mutane sama sama,saidai kuma bata iya rabewa da abinda suke fada.

Daga can bangaren anni kuwa sannu da zuwa jikokinta suke ta shigowa sunayi mata,duk da cewa ba kasafai take wannan wasan dasu ba,amma kuma su din basu qyaleta ba,duk da zafin da take dashi.

Fitowar annin kenan daga wanka bayan ta fito tana zaune a qasa,ta miqe qafafunta da sukayi mata nauyi da kuma tsami saboda zaman mota,man zafi take qoqarin shafawa tabawa ta shigo dakin,dauke da wani qaramin flask din silver da cup guda daya,gefe ta zauna anni ta daga kai ta dubeta

"Sannu tabawa"

"Yauwa hajiya anni" ta amsa mata tana murmushi tare da qoqarin bude flask din ta zuba mata abinda yake ciki,dan yamutsa fuska tayi

"Dakata mana tabawa,yaa daga dawowata zaku hau duramin magani?,ba wani abu me galmi galmi sai magani kamar bugagga?" Dan danne dariyarta tabawa tayi,ita din ba baquwar hutsun anni bace,ta riga data saba da hakan tsahon shekara goma sha

"Ammi ce tace shi xa'a fada baki"

"Ta rasa abun arziqin da zata yimin sai wannan?"

"Abu me galmi galmin yana hanya ai anni,ita da kanta ta karba girkin abinda zakici idan zaki dawo,yanzu haka a kitchen na barta" sai a sannan annin ta saki fuska

"Allah sarkiAishatu,badai qoqari ba....ba daga nan ba" ta fadi tana miqa hannu tare da karbar maganin da tabawa ta zuba matan tana kurba a hankali,ita kanta tana son maganin,saboda yana saurin warware mata gajiya daga jikinta.

Kurba uku tayi aka turo qofar dakin hadi da sallama,matashiya ce sanye da rigar material da aka yiwa budadden dinki,kanta yane da mayafi plain daya dace sosai da kayan jikin nata,tabawa ce ta amsa sallamar tata tana dubanta

"Ina kika shiga tun dazu ga aikinki can an dade da gamashi?" Sai data zauna gefan gadon annin ta yage mayafin kanta sannan tace

"Bari kawai baba tabawa,ai na baje zanci dadi kawai aka kirani daga makaranta nazo ga lecturernmu da yace bazai samu shigo ba ya shigo,mugu ne mutumin nan na qarshe,shi yasa ba shiri na tashi na tafi"

Murmushi tayi

"Ai gashi can a ajjiye"

"Yauwa baaba tabawa.....godiya nake" waiwayawa tayi zuwa ga anni tana murmushi

"Anninmu ta mutunci......barka da sauka,kun dawo lafiya?"

"Lafiya garas na dawo,gashi ma kin ganewa idonki?" Dariyar dake cin salma ta danne,don tasan anni na ciki da ita,domin kuwa ita ya khalid(shine babban jika a wajen anni ta danta na biyu me bin dr marwan)yace ta shirya ta rakata amma ta kawo nata uzurin bata je ba

"Amma nafi kowa jin dadi a gidan nan,Allah da bakya nan duka gidan babu dadi,ai bansan yau zaku dawo ba don munafurci laila bata gayamin ba,da na saka an siyo miki nama a wani suya sport nan bayanmu me shegen dadin tsiya......"

"Ke.....kiyi ta kanki,wato ga kuriya ko?,to ta Allah ba taki ba,bana so" fuska tadanyi qoqarin canzawa,duk a qoqarinta nason gamsar da anni duk da dariyar daketa taso mata,saboda tana da buqata wajen yayansu ja'afar,kuma ta tabbatar da zarar annin ta saka baki anyi an gama

"Allah anni da gaske nake,kar kiso kiji yadda duk naji......"

"Ki rabawa aishatu da marwanu biyar biyar....."annin ta fada tana danqara mata daquwa,wanda babu shiri salma ta miqe ta zari jakarta tana cewa

"Allah ya baki haquri ya huci zuciyarki tsohuwa me ran qarfe" tayi waje,annin bata barta ba ta dora mata

"Sannan kada uban wanda ya sake saka tabawa aiki cikin gidan nan na gaya muku,ba me aikin kowa bace ehe......" Murmushi tabawan tayi bayan ficwwar salman

"Ba wani abu bane hajiya anni,koda aikin gidan nan duka zai dawo kaina indai zan iya zan yishi,keda iyalinki ai kunfi qarfin komai a wajena" kofin maganin ta ajjiye gefe

"Na sani,amma ace duk ma'aikatan dake gidan basu ishesu ba?,ubansu ya lalata su ya dauko masu aiki ya zube musu kamar ba diya mata ba da gobensu a gidan aure zata samesu?,kiga yarinya batasan ta zagi jikinta tayi aiki gidan aurenta ba?,shi yasa suke wayar gari qazamai,ko cikakken tuwo basu iya yiwa miji da zaici kamar ya cire yatsunsa ba......haka yaranmu na karkara suke?" Kai tabawa ta kada tana murmushi

"Sha wuya ne ai wadan nan" furucin na tabawa ya tuna mata da maimunatu

"Kwarai da gaske kuwa,kin tunamin ma,akwai maganar da nakeso muyi dake tabawa" anni ta fada tana gyara zama,tabawa bame aiki anni ke kallonta ba,yar uwa take kallonta kuma abokiyar shawara,bama ita daya ba,kusan duk wanda ya girma ya tashi a gidan kallon kaka yakewa tabawa,mutum ce ita me tsananin mutunci da kuma dattako,bata aikin komai ma cikin gidan,saidai idan anni na buqatar wani abun da sun riga sun saba tabawan kadai keyi,duk da akwai masu aiki sosai cikin gidan


"Kinga yarinyar dana sanya ki kaita ciki ai ko?"

"Qwarai kuwa haj anni" tabawa ta fada tana bawa anni dukka hankalinta

"Yarinyar kyakkyawa sosai,saidai akwai alamunrashin sukuni a tattare da ita da kuma wahala" kai anni ta gyada

"Bama alamu bane,akwaisu" a nutse ta bawa tabawa labarin maimunatu,tare da qudurinta a kanta,labarin da yayi matuqar sanyaya jikin tabawan,tare da saka mata tausayin maimunatu me yawa cikin ranta

"Kiyi nufin alkhairi sosai hajiya anni,kuma dama halinki wannan,Allah ya baki nasara akan hakan,yasan kuma iya bakin matsalar ce,yasa ta zamto masa haske cikin rayuwarsa"

"Ameen,ameen ya hayyu ya qayyumu"anni ta fada tana jin dadin yadda tabawa ta fuskanceta

"Amma kuma wani hanzari ba gudu ba.….."

"Uhmmm,ina jinki tabawa"

"Kinsan akwai matuqar banbanci da tazara me yawa tsakanin manya(sunan da takan kira ja'afar dashi,saboda sunan babban malamin da yaci,kuma wasu sukan kirashi da sunan) da ita yarinyar?,kinsan kuma hali da dabi'ar yaran zamani,musamman shi daya keta qasashe da dama,yaga kuma mata iri iri,inajin kamar idan akace za'a bashi yarinyar nan a haka zai zama da matsala" murmushi anni tayi

"A hakan zaa bashi ita ba kuma a hakan za'a bashi ba" cikin rashin fahimta tabawa ta kalli anni don bata gane hausar ba

"Abinda nake nufi shine,inaso ki kulamin da duk abinda zata ci ta kuma sha,nasan ba lallai a yanzu ta farat daya ta dauki cimarmu ta iya sakin jiki taci yadda ya kamata ba,sannan ki kulamin da tsaftarta ki jata a jiki a kiyi mata duk abinda ya kamata,sauran abubuwan zanyi magana da salamatu,abinda ya samu zuwa sanda zai zo gida shikenan,zan bashi ita a haka,shi nakeso ya qarasa rainonta,kinsan hikimar yin hakan?" Kai tabawa ta girgiza tana duban anni

"Inaso ne yasan ciwonta,yasan dadi da kuma wuyarta,yadda bazai riqeta sakwa sakwa ba,sa'annan inason ya ginata kan tsari da dabi'ar da yakeso,ya dabi'anceta a yadda yakeson matarsa ta kasance,hakan shi zai bada damar da zata shiga zuciyarsa fiye da marigaiya shahida,don shahida tazo da tarbiyyar ta da kuma dabi'unta ne daga gida,ita kuma wannan shi zai saitata a yadda yakeso,zata kasance ne kan tsarin da duk yaso" sosai tunani da hangen anni ya yiwa tabawa dai dai,kuma hikimarta tayi mata,ta sha alwashin lallai zata yiwa annin duk abinda ta buqata,don tana cikin mutane na gaba gaba da takejin ciwo da zafin yadda har yanzu suka kasa shawo kan matsalar manya,tana jinsa kamar danta,don tun yana qarami take a gidan,da ita akayi rainonsa.

"Dubamin ita tabawa,ki duba ma'ajiyar kayan nan da aka dinka wancan watan ki ciccire mata wadanda zasu yi mata dai dai,inason ta fito muci abinci da ita anjima kadan"

"To an gama haj anni" tabawa ta fada tana miqewa.

Tana shirin fita a dakin sallamarsa cikin muryar dake cike da tarin nutsuwa da kuma haske na ilimi da dattako ta ratsa falon,dr marwan ne,sanye yake da lafiyayyar shadda ruwan qasa dinkin babbar riga 'yar ciki da wandonta,kansa kuwa hula ce da ba'a iya hangota saboda fari qal din rawanin dake nade a kansa,idanunsa sanye yake da farin gilashi dake qara masa qarfin gani,akwai cikakken gemu a fuskarsa wanda furfura ta fara yiwa ado ta gauraya da baqin dake jiki.

A girmame tayi maaa sannu da shigowa sannan ta juya ta fita a dakin,shi kuma ya sanya kai dakin mahaifiyar tasa,bakinsa dauke da sallama.

Fuska a sake ta amsa sallamar tata,sannan ta janye qafafunta don ya samu wajen zama saman lallausan carpet din da take kai,don qasa ne wajen zamansa duk sanda yazo gaidata.

"Kun sha hanya anni" ya furta bayan sun gama gaisawa da tambayar mutanen data baro.

"Wlh marwanu,amma alhmdlh,gamu a gida"

"Mun godewa Allah" ya fada yana murmushi

"inata zuba idanu na zaci baku qaraso ba,har ina shirin kiran jibril"

"Mun iso marwanu,kana tare da baqi lokacin.....na iso da baquwar yarinya ma"

"Eh tabbas,muna tare da ministern ilimi ne,batun da nakeso mu tattauna kenan dake akai" kai ta jinjina

"Nima akwai batun da xamu tattauna din,amma kamar lokaci bazai bamu dama ba,naga an kusa sallar magariba,inaga idan aka idar da sallar isha'i sai mu zauna"

"Eh hakan yayi anni,Allah ya nuna mana"

"Ameen.....amma kunyi waya da jabiru ne?" Dan dubanta yayi

"Sai da ya sanar miki kenan?"

"Kana da wadda ta fini ne marwanu?" Qas yayi da kansa

"Babu anni,amma banason tashin hankalinki ne ko kadan"

"Ja'afaru rayuwata ne,Allah ne ya doramin qaunarsa cikin dukka jikokina,idan har an aka fara boyen matsalar ja'afar saboda kada na shiga damuwa to kuwa ba'a kyautamin ba,zanyi dukkanin me yiwuwa ne don naga rayuwar jaafar ta daidaita kamar yadda take a baya"

"In sha Allah ba zata sake faruwa ba,kuma maganar da nakeso muyi din tana da alaqa da jaafar din"

"Allah yasa alkhairi"

"Khairan in sha Allah" ya amsa mata
10/20/22, 08:13 - Buhainat: 16

Da sallama tabawa ta tura dakin,ta ajjiye ledar kayan hannunta fuskarta dauke da murmushi tana duban maimunatu

"Ki shiga kiyi wanka,ki canza kayan jikinki maimunatu ko?" Kai ta gyada mata,saidai ta maida dubanta ga jikinta,bata ga wani datti da zai sakata yin wanka ba,don yau din da safe Allah ya 'yantata,ta samu tayi wanka kafin su baro gida,kuma bataga wani aiki da tayi wanda ya bata mata jikinta ba,hasalima ta jima bata samu cikakken hutu da yanayi me kyau irin na yau ba

"Muje ko na nuna miki bayan gidan" abinda tabawa ta fada kenan bayan ta ajiiye wasu maya mayai saman madubi,sai kawai ta miqe tabi bayanta.

Komai na cikin bandakin ta nuna mata tare da yi mata bayani,maimunatu na biye tabawan har ta gama nuna mata komai sannan tace

"Idan kin gama kin fito ki dannan nan ina daga falo,zan shigo na gyara miki kanki" kai kawai ta gyadamata,har ta fice tana tsaye tana bin toilet din da kallo.

Yadda ta nuna mata komai haka tayi amfani dashi,sai gashi ta dauki lokaci me tsaho tana wanke jikinta lungu da saqo,irin wankan da daadanta ta koya mata ta dinga yi a sanda take da gatanta.

Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana shaqar qamshin sabulun da tayi wanka dashi,ga wata iska tana ratsata tako ina,bata buda ledar da tabawa ta shigo da ita ba,sai ta zauna qasan tiles din tana qanqame da jikinta waje daya,saboda har wani sanyi sanyi takeji,ta kuma danna inda tace matan,a haka ta share wasu mintuna tana zaune.

Gajiya da zaman jira tabawa tayi,gashi anata kiraye kirayen sallar magariba,don haka ta dawo dakin,ta samu maimunatu zaune

"Ya kike zaune haka?baki kirani ba baki kuma saka kayan naki ba?" Qas tayi da kanta,tabawa ta karanci akwai baqunta sosai da kuma takura kai ga maimunatu,wataqila rayuwarta ta baya ce tayi tasiri sosai a kanta.

Kayan ta fidda mata harda half vest tace ta koma bandakin ta sanya tazo suyi gyaran kan.

Ta jima tana jujjuya kayan a hannunta,tamfar ba zata iya sanyasu ba,sai kuma ta tuna jiranta akeyi,abinda yasa ta budasu ta saka sannan ta daure kanta da dankwalin tayo waje,daf da zata fita ta hangi kanta ta wani dogon madubi da akayi cikin bandakin,harta gota ta dawo tana duba kanta.

Farat daya ta fara canzawa daga maimunatun bafulatanar riga,babu mudukajenta(kayan saqi) babu wuffije,babu komai na fulani tattare da ita sai duwatsun hannunta da na kunnenta,hakanan fatarta haskenta ya qaru koda ba'a gaya mata ba idanuwanta sun gaya mata hakan,sai ta soma takawa a hankali tana saqe saqe masu yawa cikin ranta.

"Babu ma wani datti me yawa akan naki ai" tabawa ta fada sanda maimunatu ta bude mata yalwatacciyar sumar kanta,tabbas babu datti,amma kuma tana da buqatar qyara,ita da kanta idan ta samu sarari take guzurin toka duk sanda taji kan nata ya dameta,ta tsaya daga bakin rafinsu sanda shanunta ke shan ruwa ta badeshi da toka ta wankeshi,saidai tana shan wahala qwarai,saboda wata irin suma Allah ya bata ga tsaho ga cika,babu mataimaki,a baya daadarta ke gyare mata shi fes,ta xauna duk tsahonsa ta bata lokaci ta zuba mata kitson fulani a bishi da wasu irin duwatsu nasu masu kyan gaske,duk randa zatayi mata irin wannan aikin wuni guda suke kashewa kafin a gama,amma fa duk wanda ya kalla kan sai ya kalla ya sake kalla ya kuma tanka,daadarta kadai ke iya mata wannan aikin,ita kanta duk randa ta wareshi ta wanke saidai ta cukuikuyeshi cikin dankwali ta maidashi yadda yake taci gaba da rayuwa dashi a haka,babu cikakkiyar taza bare ta samu kitson arziqi.

Tabawa batayi tsammanin aikin zai daukesu lokaci mai tsaho ba,sai gashi kafin ta gama wanke mata shi ta busar a hand Drayer sun dauki kusan awa biyu,har anni ta aiko laila.

Tsaye laila tayi tana fiddo idanu sanda ta shigo dakin

"La la laaaaa......maimunatu,dama haka kike da suma?,ma sha Allah,kice mu fulani kawai muka rako duniya,ga inda ainihin fulanin suke" murmushi kawai maimunatun tayi,kasancewarta bame yawan son magana ba,zama laila tayi tace tare zasu tafi,tana ta qarewa maimunatun kallo,cikin zuciyarta tana tadinta,yadda cikin awanni kadan kamanninta da kyawunta sun fara fita tun ba'aje ko ina ba.


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login