Showing 162001 words to 165000 words out of 194226 words

Chapter 55 - GURBIN IDO COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

12 Dec 2024

26197

tura baki tayi tana bata fuska,sai ya waiwayo ya nufota gaba daya,idanunta na rufe sai ji tayi an dagata,abinda ya sanyata ware manyan idanuwanta a kansa wadanda suka qara haske

"Ni ke nake kallo,kuma nakeso nayita kallo,jeki hadomin coffee" ya fada yans kallon light blue silk sleeping dress din jikinta,sai ya duqa a hankali yayi kissing qirjinta yana yaye mata duvet din,kana ya kama.hannuwanta ya taimaka mata ta sauko ta zura soft slipper dinta dake gaban gadon,yana tsaye yana kallonta har ta fice.

Numfashi ya zuqa ya fesar,wai dama haka kakejin wanda kakeso a zuciyarka?,yadda yakeji yanzun a kanta,bai taba din abu cikin zuciyarsa kwatankwacin hakan ba,qarasawa yayi ya gama shiryawa,sanann ya zura silk pyjamas dinsa navy blue,qirar kamfanin laurent.

Saman bed sofa ya koma ya zauna yana duba wayarsa, zuciyarsa cike fal da mamakin unaisa,baya son zarginta kan bin mazan banza,saboda yana tausayin mahaifinta,to amma kuma jikinsa yana yin sanyi idan ya tuna a inda ya fara ganinta,sannan kuma binciken da yasa aka masa ya nuna ita da wani ne suka koma,ya sake samun tabbacin hakan ta go and come ticket data siya,dama can ta shirya komawar kenan ba da sanin kowa ba?,zai zuba idanu yaga lokacin dawowarta.

Bayan ta kawo masa coffee din sai ya tsirar mata qananun aikin da dole tayita kai kawo,yayi relaxing jikin sofa yana qare mata kallo ta cikin sleeping dress din nata,har sai daya gamsu don kansa,sannan a zuwanta na qarshe lokacin ya kammala abinda yakeyi ta kawo masa turare,sai ya hade turaren da hannunta ya dorata saman cinyarsa.

Hannu yasa a tausashe ya fara zame mata rigar,wanda santsinta yasa ta fara fita ba wani wahala,sai tayi rau rau da idanu tana dubansa

"Sanyi nakeji"

"Kina da bargon da yafi wannan dumi.... you know what?, sleeping dress amfaninsu a wajen kadai kafin lokacin kwanciya barci ne,bana buqatarsu daga sanda zaki kwanta,i only need your skin,i really enjoy body contact" ya qarasa maganar cikin tsakiyar kunnuwanta,har sai data damqe hannuwanta waje guda tana rintse idanunta.


°°°°°°°°°Karfe uku da mintuna na yammacin washegari cikin makarantar tayi musu,bayan ya gama nuqu nuqunsa fes,kamar ma bazata koma din ba sannan ya baro office da kansa ya karba key ya daukota,bayan anni ta kirashi ta gaya masa,zata turo hisham ya dauketa ya kaita.

Fuska ya bata sosai,yana jin wani mugun kishi yana maqare masa wuya,yama rasa amsar da zai bawa annin

"Saiki shirya kayan tafiya asibiti jiyyarsa indai ya sake yazomin gida da sunan daukarta" haba ta kama,dariya nason qwace mata amma ta maze

"Iyyeee,dan nan?,dan daba ka zama,to wallahi ahir dinka da furta ta'addanci"

"Me kikeso ne nayi anni?,dole saikin qure haqurina......is okay,i love maimunatu......inason maimunatu,ina sonta......ina sonta,banason kowa ya rabeta please,karki qara wannan maganar anni, maimunatu tawa ce....." Girma maganganuna nasa suka yiwa anni,taji tsoron kada ya baro babbar magana,tasan halinsa duk randa ya cika ya fara fidda abinda ke cikinsa baya ji baya gani,don haka ta dakatar dashi da sauri

"Kai arcannn,yi ta kanka yaro,bani zaka gayawa wannan zancan banzan ba,nidai a maidamin yarinya makaranta ehe" da sauri ta datse kiran,sai ya sauke wayar daga kunnensa cikin wata kasala kamar wanda aka yiwa dukan tsiya,yabi wayar da kallo yana murmushi kawai,yasan maganin annin,daga yau shima zai nuna mata dan zamani ne shi,tunda so take ta qure haqurinsa.

Gashi dai ya kashe motar,amma kuma bai bude motar ba,saima kwantar da seat din motar da yayi ya kashingida bayansa yana qare mata kallo,idanunsa a lullumshe kamar zai cinyeta,yana jin yadda zuciyarsa ke harbawa.

Jira taketa yi taji yace ta fita din amma shuru,daga inda take zaune ta hangi su afra sunyo arean riqe da qur'ani,da alama islamiyya zasu wuce,sai taji kewar karatun ta sake kamata,tana so ko iya yau a fara karatun da ita ta rage wasu kwanakin da tayi missing.

Har sukazo suka gifta su basu ankara da ita ba,suna ta hirarsu su ukun,saita dauke kanta zuwa gareshi,cikin sa'a suka hada ido

"Zan iya tafiya?" Kai ya girgiza mata alamun a'ah,sai ta shagwabe fuskarta as usual,wannan karon harda tabe siraran labbanta,ji yayi kamar ta saukar masa dafi a jikinsa

"My moon" ya kirata da wani.lallausan sauti,kamar wanda ya tashi a barci,daga kai tayi ta dubeshi,saiya miqa mata hannunsa ya mata sihn din tazo,ido ta fidda tana kallon gaban motar dake da farin glass,kowa zai iya hangosu,bata dauke idanunta ba taga coloured glass ya maye gurbin farin,kafin ta maida dubanta kansa ya fincikota ta fado kansa gaba daya.

Riqon tsauri yayi mata sosai,ya dinga aike mata da kisses kota ina,cikin wani irin zazzafan shauqi,ba inda bai kai harshensa a fuskarta zuwa wuyanta ba,cikin qanqanin lokaci dukka suka fita hayyacinsu,tuni ya zare hijab din jikinta yayi nasa waje

"I love you angel......i love you my moon.....i love you diyammm" shine abinda yake iya fada kawai cikin rarrabewar sauti,jikinsa na rawa.

Dan bugun motar da akayi yasa shi tsayawa cak,wasu dalibai ne da sukazo wucewa suna hira daya ta daki motar suka wuce abinsu,sakinta yayi a hankali ta sulale daga jikinsa ta koma seat dinta tana dunqulewa waje daya,yayin da shi kuma ya dora hannunsa cikin sumarsa yana yamutsata sosai idanuwansa a rufe bugun zuciyarsa nata tsere da sauri da sauri.
11/24/22, 23:35 - Buhainat: 74

Sun jima a hakan kafin ya bude idanunsa a hankali,sannan ya miqe ya zauna yana kallon cotton din yadinsa fari qal daya ya mutse,ya fara maida button na rigarsa,sannan ya duqa qasan motar a hankali ya lalubo hijabinta ya matsa a tausashe ya miqa mata,bata iya hada ido dashi ba,ta miqa hannu ta amsa ta zura,sai daya tabbatar ta saka sannan ya dage coloured glass din da ya sauke din,ya sanya hannu ba tare da yace komai ba ya buda murfin motar,ya zagaya ya bude mata,ta zura qafafunta a hankali ta fito.

A gaba ya sanyata yana biye da ita kamar wani bodyguard dinta har zuwa office din da ake shigar da dawowar dalibi a register,ya cike komai ya kuma ce kada a sake barin kowa yazo daukanta,sai yazo da kansa ko kuma ya bada umarnin a dauketan,cikin ma'aikatan su suka daukar mata jakankunanta,cike taf da kaya fiye da yadda ta saba zuwa dasu,kamar zata bude qaramin provision.

Tana takawa a hankali zuwa dakunan kwanansu amma tana jin idanunsa cikin jikinta,ta tabbatar yana tsaye yana kallonta,saidai bata waiwaya ba har ta qule.

Nannuyar ajiyar zuciya ya sauke,yana jin kamar an cire zuciyarsa an wurgata can nesa dashi,sai ya waiwaya jiki a mace ya buda motar tasa ya tadata yabar cikin makarantar yana jin duk wani farinciki da yayi saura a zuciyarsa yana raguwa.

Numfashi ta sauke tana duban dakin nasu,tayi missing nasa,saidai yadda ta dauka zatayi farinciki da da dawowa cikinsa sai ta lalubi hakan cikin zuciyarta ta rasa,hasalima wani mutuwar jiki takeji da kasala,sai ta zauna bakin gadon ayman,ta zare socks din qafarta da takalminta ta wuce toilet ta daura alwala.

Sallar la'asar tayi,tana son binsu masallaci amma kuma batason garin murnar nan tasu suyi mata tarere,don haka sai ta bude jakankunanta,ta fara fidda kayanta tana shiryawa.

Kafin wani lokaci ta gama shirya komai yadda ya dace,ta sake kintsa musu dakin,wanka take som yi amma ta kasa,sai ta koma ta kwanta gadon afrah tana jin wata lafiyayyar gajiya tana bin jiki da gabobinta,haka kawai takejin zuciyarta duka babu dadi,walwala da dokin dawowa makarantar duka sun kau,ta lumshe idanuwanta,abun mamaki sai tunaninsa ya soma mamayarta,ta fara hangen fuskarsa a mabanbantan lokutan da suka kasance tare dashi.

Ganin lokaci na tafiya kuma ta gaza hasala komai sai ta yunqura ta miqe tana duban dan qaramin agogonsu dake jikin bango,wanda afra ce ta maqala musu,tace hajjanta wato kakarta ce ta bata shi,yau kamar sun dan gota lokacin dawowarsu,ta miqe ta shiga dube duben dakin babu abinci,kuma yunwa take dan ji,duk da taci abinci kafin su fito,don takeaway ya mata na musamman da abinda taji ranta yana so.

Babu sauran abinci a cikin dakin,da alama ma basu dafa komai ba,a kitchen suka karba abinci,sai ta zari hijabinta har qas ta zura ta sanya slippers ta fito,tana tuna maganar da ja'afar ya gaya mata sanda suna kan hanya,hannunsa na cikin nata

"Please ki kularmin da kanki,ki adanamin kanki da kyau,don babu yadda zanyi ne da anni,kamar uwa take a wajena,banda ita abbi da amma babu wanda ya isa yayimin wannan hukuncin na yarda dashi,zan iya mutuwa wallahi angel......ina da kishi sosai.... please take care of yourself".

Ajiyar zuciya ta saki ta qarasa shiga kitchen din,mama's dinsu dake musu girki dukka ta samesu suna nan,kowacce cikin fara'a ta soma mata maraba,ita kuma tana gaidasu cikin matuqar girmamawa,suna son maimunatun sosai saboda yadda take martabasu,ba kamar wasu daliban da suke ganin sun fito daga gidan gata ba,ana.biya musu school fees almost one million naira so babu me takurasu

"Munata jajjabin rashin dawowarki,sai afra tace ai kunyi tafiya ne keda 'yan gidanku"

"Eh wallahi mama"

"To madalla,an dawo lpy ko?"

"Lafiya lau mama,zan samu abinci kuwa?"

"Eh akwai na rana da akayi,bari na duba miki" ta fada tana buda babbar tukunyar,ta deba mata cikin plate maimunatun ta karba tayi mata godiya kamar yadda ta saba tana cewa

"Idan kun tashi aiki mama kiyimin magana,sai ku karbi tsarabarku" kusan hada baki sukayi wajen mata godiya,indai kyauta ne maimunatun ba daga nan ba,ta juya ta fice da abincin a hannunta.

Sam bata kula da tahowarsu ba,gab da zata isa dakinsu taji an saki ihu,kafin ta waiwayo taji an rungumeta tsam ta bata,ayman da fatima kuma suka zagayo ta gabanta suna riqe da hannunta gam,wanda saura kadan abincin hannunta ya kife a qasa

"Daga ina?,saukar yaushe?,wai mu zakiwa suprise moon?,kin barmu gaba daya makarantar babu dadi?" Murmushi ta sake musu,ita jikinta gaba daya babu wani cikakken qwari

"To sakeni afreen,afwa,wacce tambaya zan amsa miki a ciki?"

"Duka" ta fada tana sakinta gami da zagayowa gabanta tana murmushi,sai kuma ta fidda idanunta waje gaba daya,ayman tayi caraf tace

"Kinga abinda na gani sis afreen?"

"Ko makaho ai dole ya gani....moon?,me captain yake baki?"

"Banason iskanci afreen,zaki fara ko?" Cikin qyalqyala dariyar farinciki tace

"Wallahi Allah am serious,kinga yadda kika qara fresh?,jikinki kamar jini zai diga?,don Allah bai saka miki dokar sanya niqaf ba?"

"Saidai ki bashi shawara 'yan wulaqanci.....mu qarasa daki don Allah" ta fadi saboda yunwa da gajiya da tsaiwar da tayi.

Cikin dakin suka bude sabuwar hira,gaba daya sun sakata gaba kan irin yadda ta qara kyau da kuma yi fresh da ita

"Wallahi honeymoon tayi kyau,Allah yasa an samo mana dan lagos to johannesburg" afra ta fada tana kwanciya saman gadonta tana dariya,har qasan ranta tana jin dadin canzawar aminiyar tata.

Duka maimunatu ta d'ana mata a bayanta tana cewa

"Mara kunya kawai,ni ba abinda ya shiga tsakanina dashi,ni da sauran kunyata"

"An fada a radio" ta amsa mata tana sake sheqewa sa dariya,dariyar ta baiwa maimunatu,sai kawai ta murmusa itama.

"Allah ko,inda nice ke banga abinda zaisa na dawo makaranta ba,kuma wai boarding tabdi" ayman ta fada tana duban maimunatu,idanu ta fidda

"Yaushe afreen ta bata ku da son aure?"

"Dan sunna yaqi sunna" ayman ta amsa mata tana dariya.

Anan sukayi sallar magariba da isha'i tare,don ko fita cin abinci basuyi ba tsabar hira,fatima ce taje kitchen ta karbo musu, maimunatu ta hada da tsarabar su mama fatiman ta kai musu.

Sai wajen goma na dare kowa yayi shirin kwanciya,saboda gobe suna da shiga lab qarfe takwas,malamin kuma yace duk wadda ya rigata shiga ba zata shiga ba,tasu tsarabar ta ware,dogayen riguna ne masu kyau irin daya,sosai sukayi murna kamar basu taba sawa ba,duk da kowacce a cikinsu tafi qarfin abin,amma hausawa sukace alkhairi dadi gareshi,koda kafi qarfin abun.

Ba'a rufa awa daya ba dakin ya dauki shuru,da alama bacci ya daukesu,sama ko qasa maimunatu ta nemi bacci a idanunta ta rasa,ta dinga juyi tana canza position da wajen kwanciya,saidai still dai kwanciyar babu dadi,ta dinga jan qananun tsaki,gadon ne babu dadi ko kuma katifar?,ko sauyin wajen kwana?,sai ta rasa amsar tambayar,can wani sashe na zuciyarta kuma yanata qoqarin danne abinda ke taso mata,tana ta qoqarin karyata zuciyar tata,yaushe ta sanshi?,yaushe sukayi sabon da zata ji babu dadi don babu shi a kusa?,kwata kwata sai kwanciyar taqi mata dadi,ta runtse idanunta da kyau tana qanqame filo a qirjinta,tana son tilastawa kanta yin baccin ala dole.

Maimakon baccin sai memories dinsu dashi ya dinga dawo mata,haka tayita ganin komai cikin idanunta,ta jima kafin ta samu idanuwanta suyi nauyi,a hankali bacci ya fara sauko mata.

Hannu ya miqa a hankali,ya rage hasken reading lamp din dake saman kyakkyawan zagayayyen table din da ya cikasu da takardu,sai ya koma da baya yayi relaxing yana shafa sumarsa gami da furzar da iska daga bakinsa,ya janyo a gogon dake gefansa a matuqar gajiye yana duba lokaci.

K'arfe biyu harda minto goma na dare,qaramin tsaki yaja ya maida agogon muhallinsa,bai taba ganin dare mai tsahon wannan ba tunda yake a rayuwarsa,ya tsammaci zaman da yayi a nan zai tsinciki kiran sallar asuba ne,saidai gaba daya lokacin ma kamar baya tafiya,kamar a tsaye yake cak.

Maida kansa yayi ya jinginar,ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa yana dan lilo kan kujerar da yake zaune,gaba daya ita ke masa yawo tsakanin idanuwa zuciya zuwa qirjinsa,sau biyu yana attempting kwanciya,amma idan yaje sai yaji ya gaza zaman bedroom din,memory din data bashi yammacin jiya zuwa dare ke dawo masa,sai ya miqe tsaye yana kwasar wayoyinsa gami da kashe fitilar gaba daya ya sake nufar bedroom din.

Sai daya shiga toilet ya daura alwala yayi bursh sannan ya dawo ya kashe qwayayen dakin ya nufa gadon,addu'ar bacci yayi yaja duvet yana rintse idanunsa gami da addu'ar Allah ya kawo masa bacci da wurwuri,saidai inaa,addu'arsa bata ciba,don gaba daya qamshin ta daya maqalewa pillow din data kwanta jiya akai shi kuma yau ya daukeshi yayi amfani dashi shi ya maqale masa a hanci,ya shiga tuna masa da ita gamida tada masa hankali.

Dogon tsaki yaja kamar zai cire harshensa,dukka anni ce taja masa,ta yaya za'ayi mutum da matarsa amaisheshi gauro?,don ya kaita boarding school a baya....ai ya aikata hakanne a sanda baisan daraja da kimarta ba,a yanzun kuwa duk duniya yafi kowa sanin martabarta,da wannan tunanin da kuma kewar ya dinga fama har ya samu baccin ya daukeshi.

°°°°°°°°sati guda kacal amma gaba dayansu kowa ya jikkata a jiki da zuciyarsa,tuni ya sallama cewa soyayyarta ce tayi masa mummunan kamu,irin kamun da yakejin labarinsa a labarai yake kuma qaryatawa,ashe da gaske haka ne?,komai yakeyi tana cikin tunani da zuciyarsa,sai ya fara samun cikas a ayyukansa na office,wasu abubuwan sai yayita mistake,sai jabir ya ankarar dashi,mamaki yanata shigan jabir,lallai gigitaccciyar soyayya ce ta kama ja'afar din

"Kaga masu abu da abunsu,malaman soyayya" ya fada a ransa yana sakin qaramin murmushi.

Yayin da bangaren maimunatu kuma taketa dojewa kan gajiyar tafiya ce ke luguiguitata sanda afra suke mata tsiyan ta faye zama cikin tunani,sannan bata baccin kirki cikin dare,ko tana kewan captain ne?.

Tun tana qaryatasu tare da basu uzurorinta har ta soma sallamawa itama,a hankali ta sake zama so silent,duk da bata yiwa su afrah miskilanci amma a yanzu kamar ta sauya musu su dinma,tafi kebewa ita kadai ta zauna shuru,wanda ba komai take ba illa tunani.

°°°°°°°°°Karfe tara na safiya ne,yana kwance bayan motarsa qiran ferrari,daga gidansa na government house road zuwa gidansa dake zuwa gidansa dake daya baro tun randa ya dauko maimunatun,bai sake komawa ba,koda ta koma makaranta ma a nan gidan yaci gaba da zama,a yanzun ya samu qwarin gwiwar zama a ciki tunda aka kwashe kayan shaheeda daga ciki,akwai takardun da yakeson debowa daga can gidan kafin ya wuce office.

Gaisawa sukayi da masu gadin gidan nasa,sannan ya wuce ciki da dan gaggawarsa yana gayawa driver din nasa kada ya kashe motar yana fitowa.

Bai jima ba ya dauko abinda zai dauko din ya fito,yana saukowa daga stairs din yana sake duba file din don tabbatar da cewa ya dauko komai a ciki da yake buqata.

"Ka kulamin da jaka karka karcemin ita fa" muryar da yaji kenan data samyashi dago kansa,ido hudu sukayi da unaisa,wadda ke takowa cikin gidan,sanye da wata irin mini gown da straight leg trouser,kusan rabin fuskarta mamaye da sun glasses,tana tauna chewing gum.

Cikin tsawa ya bawa mai gadin umarni

"Ina zaka da wannan jakar?"

"Ah....hajiya ce tace a kawo mata ciki"

"Kana qara taku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login