Showing 45001 words to 48000 words out of 194226 words

Chapter 16 - GURBIN IDO COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

12 Dec 2024

26154

dasu JJ suka basa nan,sun huta da ciwon bakinta.

Idanun dr marwan dake a wajen ya sanyashi miqewa yana sake shafa qeyarsa hadi da cewa

"Allah ya baki haquri"

"O'o'o'o,na kusa yiwa tufkar hanci ai"

"Fitarmin da briefcase din nan,ka cewa muslimu ya tada motar gani nan fitowa" cewar dr marwan,sai haisam ya qarasa ya dauka jakar ya musu sallama ya fice,amma tana masa addu'ar Allah ya tsare.

Kusan idan da sabo amma ta saba raka dr koda a gaban anni ne,idan ma bata je ba zata ce ita ta tashi taje,don haka yanzun ma ta tako masa har zuwa farfajiyar dake sassan annin

"Da gaske wannan karon anni ta tada wannan rigimar kan yaran nan,gaba dayansu so take a kauda su" rausayar da aki amma tayi

"Eh banga laifinta ba,tunda abinda ya kamata kenan dama ayi,kowannensu ya kamata zuwa yanxu ace bashi kadai bane"

"Musamman ja'afar da yake da buqatuwa ta kowanne bangare" dr ya fada don yasan daya daga cikin abubuwan da amma ke kwana dashi ta tashi dashi ne a cikin ranta,amma kuma yakana da kara ya sanya bata nunawa ko a fuska,amma shi din sau tari yasha jinta cikin tsakiyar dare tana kaiwa Allah kukanta akan matsalar yaron nasu,ya sani dole abun zai tabata sosai ya kuma dameta kamar kowacce irin uwa.

Kamar yadda ya zata din kuwa fuskarta ta dan sauya daga yadda take a daxun,hakan yasa cikin kulawa ya bata dukka hankalinsa

"A wannan lokaci muna saka rai da fatan samun warwarewar komai,bake daya ba bani kadai ba,kusan duk wanda ke cikin gidan nan ya damu da lamarin,amma kuma addu'ar bawa mumini bata faduwa qasa banza" kai amma ta gyada cike da gamsuwa,koda yaushe shi din mutun ne da yake da qoqarin ganin ya kwantar mata da hankali kan dukkan wani lamari,bawai iya na ja'afar kadai bama

"Idan na dawo akwai maganar da xamu tattauna,duk da ban sani ba wala'alla anni ta shaida miki kafin na dawo din"

"Allah ya tsare hanya,a adawo lafiya"

"Ameen een,zan samu dambun nan kuwa?" Ya fada yana murmushi,cikin nata murmushin ta amsa masa

"Ka cika cikakken bafulatani kai din,zaka samu in sha Allah" da haka yana dariya ya juya ya fice,ita kuma ta koma ciki tana murmushin itama,wani sashen na zuciyarta kuma ya lula ga tunanin dan nata,wanda ta kwashe wasu kwanaki bataji muryarsa ba,abinda a shekarun baya bata saba da hakan daga gareshi ba,komai cunkushewar aiki baya iya tsallake wuni guda baiyi kiranta ba,qaddarar data afkawa rayuwarsa tasa komai ya canza.

****************

Cikin sati guda rak maimunatu ta gama fahimtar abubuwa masu dama tattare da family din anni kuma familyn dr marwan khalid akko,ba shakka duk tubalin iyalin da nagartaccen uba ma'abocin ilimin addini da kuma aiki dashi ya samar dashi zaka sameshi ya banbamta da sauran ahali ta fuskoki da dama,kowanne mutum cikin gidan yana rayuwa bisa kyakkyawar tarbiyya da suka samu daga mahaifansu,mutane ne masu fahimta gami da sauqin kai da daukar kansu ba komai ba,duk da tarin dukiya da kuma arziqi da Allah ya yiwa mahaifinsu,akwai haduwar jini tsakanin maimunatu da 'yammatan,babu wanda ke nuna mata qyamata ko wani mummunan hali da zai sanya taji babu dadi cikin ranta.

Gida ne da baya rabo da baqi 'yan uwa family kuma jinin marigayi khalid akko mahaifi gasu dr marwan,mutanen gidan suna da son baqi da son ganin wani baquwar fuska yazo musu,abinda yasa suka kasance masu son jama'a.

Kusan dukka jama'ar gidan ba mazauna bane,idan ka cire matan gidan da anni,kusan zamansu a gidan kadanne ne idan ba weekends ba,hakan yasa ta fara sabawa da anni sosai da kuma amma,duk da cewa har yanzun bata sake sosai dasu ba,musamman amma da hakanan take jin nauyinta,tafi sakewa dasu laila.

Bisa shawarar tabawa anni ta daga qafa,ta kuma fasa kiran ja'afar kamar yadda ta tsara,abinda ya karkatar da hankalin annin tasa aka maida maimunatu islamiyya cikin satin,tabawa kuma ta qara da cewa

"Ina ganin haj anni,me zai hana a maidata boko ma?,tunda rannan naji suna hira da laila,da alama meson karatu ce,kuma hakan shine dai dai,ta yadda babu yadda za'ayi babban mutum ya raina zabinki" murmushi anni tayi

"Haka maganarki take,amma kuma tabawa,inaso ne yayi mata hidima da kansa,ya raineta da kansa,ya kuma san ciwonta,ta yadda kome zaije yazo bazaiyi wasarere da ita ba,banqi shawararki ba,amma zan samar mata wanda zai dinga zuwa gida yana dora mata karatun bokon,har zuwa lokacin da zan fara aiwatar da abubuwan dana tsara,idan yaso shi da kansa ya samar mata duk makarantar da yaga dama,ya kuma cire kudinsa ya biya,hakan nakega sai yafi" kai tabawa ya gyada,lallai ta hangi dabaru masu yawa kan wannan shirin na anni,fatansu dai shine Allah ya tabbatar da alkhairi,ya shige gaba akan dukka lamarin.

Cikin satin maimunatu ta zama cikakkiyar daliba ta kuma saje da iyalan gidan dr marwan,islamiyya dake layi na biyu dake bayan gidansu,ranar da zata fara zuwa din laila natsaye falon anni hanunta dauke da qur'aninta tana tisa haddar da zata bayar a yau din,maimunatun ta fito sanye da Egyptian hijab dinta har qasa dinkin kalar blue black.

"Wow....ma sha Allah" laila ta fada tana murmushi,idanunta bisa fuskar bafulatana maimunatu,fuskar da zuwa yanzu ta sake washewa,ta fara fresh da ita saboda samun canjin weather da kuma zama waje daya gami da sauyin cima dama makwanci

"Kinga yadda kayan sukayi matuqar karbarki kuwa maimunatu?,kamar don ke aka zaba kalar?" Murmushin nan nata me sanyi ta sakarwa laila,wanda kusan shi ta fiyi yi fiye data yi magana.

Sai data leqa anni dake dakinta tayi mata sallama,sannan suka fito suka rankaya ita da hafsa da laila din da nadiya,fa'iza da rahama sun rigasu yin gaba,don dama ba kasafai suke jerawa dasu ba.

Abinda ke bata mamaki yadda duk sanda zasu islamiyyan da qafa suke takawa,duk da cewa idan da sunso jikinsu zasu iya bin motar gidan ya qarasa dasu,amma sam basu damu ba tafiyarsu suke,babu wani girman kai ko jin cewa ubansu wani ne,ko kuma sun fito ne daga babban gida.

*************

Zaune take cikin qawataccen falon anni,wanda ya wadata da tsafta da kuma qamshi ta ko ina,falon da a yanzu yake qarqashin kulawar maimunatu da bata bari koda tsinke ya sauka a kansa,ita daya ce qwal a falon,sanye take da wani milk high waist skirt na material mai santsi,sai rigarsa ta chiffon material milk color mai torches na brown,fatarta ta sake wani irin haske da kyau,ta kuma yi luwai luwai,duba daya zaka yi mata kasan cews tabbas ta samu nutsuwar zuciya da kuma ruhi a watanni ukun data shafe cikin gidan,saman kanta baby hijab ne da bata rabo dashi ruwan madara kalar skert din jikinta,wanda ya zame daga gaban kanta,ya bayyana lallausar sumar dake kwance daga gaba,kai baka ce akanta akwai manya kalba data roqi laila tayi mata ba,wansa lailan taso taqi matan,saboda sunyi sunyi ta bisu suje saloon da suka tsara zuwa a ranar saboda shirye shiryen bikin da suke a dangin ammi amaryar dr marwan kenan amma maimunatun ta qiya,ba kasafai take zarmewa da kuma zaqewa cikin lamuransu ba,don har yanzu bata saki jiki dasu yadda suke so ba,bawai don tans musu mummunar fahimta ko kuma zato ba,a'ah.....saidai ita din a koda yaushe tafi ganewa tsaiwa iya matsayinta,kada rayuwar ta rudeta ta kuma sanyata mantawa wacece ita.

Komai dake tattare da maimunatu ya sauya,saidai har yanzun bata bar wasu dabi'u nata ba,saboda gudun manta asali da tushe,kamar yadda bata zubda ko cire duwatsun hannunta ba,hakanan kayan saqinta suna nan,tayi musu kyakkyawar ajiya,kamar yadda lokaci zuwa lokaci idan taji kewar gida ko dabbobinta,take sanyasu a jikinta ta wuni da abinta,su laila suyita tsokanarta,saidai ta bisu da murmushi kawai,kasancewar shine fiye da rabin amsar maganarta.

Yau din gidan babu yawaitar jama'a sosai,kusan dukka kowa ya fita sha'aninsa,'yan mata matan sun fita wankin kai,anni kuma yau tana daki a kwance,don kwanaki biyu kenan bata da dan jin dadi tana fama da mura,masu aikin dake sassanta kuwa suna kitchen,wasu kuma suna bangarensu suna hutawa,ammi ta fita unguwa itama,sunata shirye shirye da hidimar biki,acan sassan nasu sai amma kawai.

Yankam farce takeyi abinta da nail cutter,ta bada hankalinta sosai ga yankan,yayin da wani sashe na zuciyarta yayi nisa cikin zurfin tunani,yadda rayuwa ke gara mata,babu mahaifiya bakuma tasan inda mahaifinta yake ba,takan kalli su laila a matsayin 'yan gata gaba da baya,bawai gata na dukiya da daular da suke ciki ba,a'ah,gata na kasantuwarsu suna rayuwa gaban mahaifi mahaifiya kaka harma sa danginsu,sukan burgeta a yawancin lokuta,takanji inama ace tana da wannan gatan.

Takun tafiya da sauri da asauri da kuma sautin kukan qaramar yarinya cike da rigima ya sanyata daga kanta daga abinda takeyi,ta kuma maida dubanta ga qofar shigowa falon duk da labulayen alfarmar da suka kangeshi daga ganin wanda ke tahowa daga waje,jim kadan me kukan ta bayyana,ta bankada labulen tana shigowa da sauri kamar yadda ta taho.

Kyakkyawar yarinya ce ta gaske,wankan tarwada,kalar da dukka gidan mutum daya taga yana da ita,sanye da wata irin short sleeve gown mai azabar kyau,qafarta sanye da rufaffen takalmi na mata daya dace da kayan jikinta,kanta mai cike da suma me santsi da laushi kuma an masa wani irin gyara mai kyau da daukar hankali,an qawata shi da ribbons,hannunta daya dauke da wata qatuwar teddy da suka kusa yin kai daya,kai tsaye taci gaba da takowa cikin falon tana kuma kukanta,tare da rarraba idanu da alama akwai wanda take nema.

Da idanu maimunatu ta bita,kuka take yarinyar da gaske,hawaye shabe shabe kan fuskarta,hakanan kawai tausayinta ya tsirga mata,duk da batasan wacece ba,batasab me akayi mata ba,saita miqa hannu a tausashe ta riqo hannun yarinyar,abinda ya ankarar da ita kenan da wani a falon,ta waiwaya a hankali tana duban maimunatu.

Murmushi ta sakarwa yarinyar,duk da yadda taji idanun yarinyar har tsakiyar kanta,wasu irin idanu ne da uta masu kyau da daukan idanu,a hankali ta buda bakinta

"yaki,zoki gayamin wane ne?,me akayi miki" ta fadi da taushi cikin sigar lallashi,kai tsaye kuwa yarinyar ta soma takowa zuwa wajen maimuntun,batayi qasa a gwiwa ba ta dorata saman cinyarta kana ta jinginata da jikinta,take yarinyar ta narke jikin nata.

Dumin jikin yarinyar yasa maimunatun taba wuyata,da alama zazzabi kenan take,saita zagayo da kanta gefan fuskarta

"Waye ya tabaki?,waye ya sakaki kuka?" Ta sake tambayarta kanta tsaye,salon tambayar da alama ya taba zuciyar yarinyar,sai ta saki kuka sosai cikin sheshsheqa tana cewa

"Uncle hisham ne......."
"Ya isa,yi shuru,indai shine sai mun hukuntashi,ki daina kukan haka,kinji akwai dumi a jikinki kada ya sake qaruwa" maimunatu ta fada tana jin tausayinta ba tare da tasan dalilin hakan ba.

Qanqameta yarinyar tayi

"Ba za'a yimin allura ba?" Ta tambayi maimunatu tana duban idanunta,murmushi ta sakar mata tana shafa tattausan gashinta

"Babu wanda zai miki allura kinji" ta qarashe maganar tana jan yarinyar cikin jikinta sosai ta rungumeta,sai ta narke itama tana sassauta kukan gami da sakin ajiyar zuciya me qarfi,da alama abinda take buqata dama kenan,tunanin maimunatu yadan cilla wani waje jin yadda yarinyar tayi luf a jikinta tana sauke ajiyar zuciya,kamar tasan fuskar yarinyar a wayoyin al'ummar gidan,kamar tana ganin fuskarta a wajensu.


Tsakiyar tunanin da take aka daga labulen akayi sallama wadda ke cakude da sauti na dariya a tausashe,ta daga kanta a hakali tana amsa sallamar,idanunsu suka sarqe waje guda dame sallamar.
10/20/22, 08:13 - Buhainat: 18
Karo na uku kenan da ta taba ganinsa cikin gidan tun zuwanta,ba zata iya cewa ga ainihin sunansa ba,don babu abinda ya taba hadata dashi da ya wuce gaisuwa,daga nan take barin waje,tana da dabi'ar barin guri a duk sanda taga iyalin gidan sun hadu waje guda,har sai idan sun buqaci tayi zamanta.

Cikin tsarguwa ta janye idanunta daga cikin nasa tana sake gyara zamanta gami da jan skert dinta zuwa qasa sosai,duk da dama ya sauka din,shima nasa idanun ya dauke yana shigowa cikin gami da sassauta dariyarsa

"Ina yini" ta gaidashi idanunta nakan teddy din yarinyar data yar

"Lafiya lau.....anni na ciki ne?"

"Eh ta amsa masa a taqaice"

"Yimin kiranta idan ba damuwa" da to ta amsa masa tana yunqurin tashi tare da qoqarin ajjiye yarinyar,saidai fir taqi ta qanqame maimunatu da kyau,idanunta nakan hisham.

Qaramar dariya ya sake yana kallonta

"Duk ki gama guje gujen naki tsaf kuma azo ayi allurar,wannan zazzabin jikin naki ta yaya za'a barki dashi" kafada ta noqe tana sake tale baki da alama zata sake sakin wani sabon kukan ne

"Miqomin ita ki kiramin annin" gam ta sake riqe maimunatu tana cukuikuye dan qaramin hijab din jikinta,har sai da maimunatun tadan jashi kadan saboda jikinta daya dame

"Qyaleta,bari na kira maka ita a hakan" ta fada tana saba ta a kafada,sannan ta fara takawa a hankali zuwa gefan anni.

Da.kallo yadan bisu har suka bacewa ganinss,sai ya dauke idanunsa yana sakin boyayyar ajiyar zuciya,wannan shine karo na hudu daya ganta a gidan,baisan wacece ba,baisan kuma relation dinsu da ita ba,saidai akwai wani abu me fusgar hankali tattare da ita,bama kamar yanzun da sukayi kusa da juna ba kamar kwanakin da yake hangota daga nesa ba.

Saman lallausar dardumar dake dakin ta samu anni,tanata danne danne a wayar da ala dole ta karbeta,saboda ciwo baki na jikokinta,bata daga kanta ba,tadai amsa mata sallamar cikin kulawa saboda hankalinta na ga wayar,har sai da maimunatun da zuwa yanzu ta maida yarinyar bayanta ta shigo dakin gaba daya

"Wa nake gani a bayanki kamar amna?" Leqowa yarinyar tayi da kanta don anni ta tabbatar

"Ja'ira,sai yau Allah yayi suka dawo mana dake kenan?" Anni tafada tana dariya,koda bata sake cewa komai ba maimunatu ta gane wacece,yarinyar da kullum rana ba zata fito ta fadi cikin gidan wani bai ambaceta ba,taji yadda akasha gwagwagwa da kakanninta na wajen uwa kafin su yarda su dawo da ita,saboda ita kadai ce jikarsu,jikarma kuma ta wajen diyarsu mace qwaya daya tal da suka mallaka,taji kuma ance mamanta ta rasu,take tausayi da qaunar yarinyar ya sake saukar mata fiye da dazu,qaramarta da ita tasan dacin maraicin uwa?,ko ita dake da girmanta yaya takeji a ranta bare wannan,hukuncin Allah ne,ba yadda baya tsarawa,haka bawa zai karba a duk yadda yazo masa.

Kememe amna taqi sauka daga bayan maimunatu,duk yadda anni taso tazo gareta

"Yar nema,zamu hadu ne,wannan din kin santa ne?,daga zuwanki zaki dafewa diyar mutane?" Annin ta fada tana dungure mata kai,abinda yasa amnan ta sunne kai a bayan maimunatu ba tare data ce komai ba,maimunatu na jinsu tana tayasu da murmushi

"Yaa hisham ne yace nayi masa kiranki" ta fadi sunansa kamar yadda taji yaran gidan na fade

"Ya shigo mana,baisan dakin nawa bane da zai tattago ni ina fama da kaina?" Goye da amna ta fita a dakin don gaya masa saqon annin.

Waya yake dannawa,amma jin takunta yasa ya tsaya ta daga kansa yana dubanta,ta shaida masa abinda anni tace,har ya miqe kira ya shigo wayar tasa,sai yace

"Ina zuwa" yana duban fuskar wayar ya fice daga falon,dai dai lokacin da daya daga cikin ma'aikatan gidan me suna sha'awa ta shigo falon tana shaidawa maimunatu malaminta yazo

"To ina zuwa" ta amsa tana komawa wajen anni ta gaya mata abinda hisham din yace,taso aje mata amna amma yarinyar taqi,haka ta juya zuwa kitchen don kaita wajen tabawa,wadda dama ita ke rainonta amma sam wajen tabawan ma taqi zaman

"Haba uwar gijiyata,wannan zazzabin na jikinki da kin haqura kin zauna,bakya fita gurin shukokin can ba iska ta sake kadaki" fir taqi,saboda tana tsoron kada hisham din ya biyota nan yayi mata allurar da ya ambata din,haka maimunatu ta fita da ita inda ake mata karatun tana goye da ita,hannunta kuma riqe da litattafanta.

Tana cikin jikinta suna karatun,tana bala'in qaunar karatun nata,saboda.malamin ba qaramin qwarewa yayi ba da kuma sanin makamar koyarwa,cikin watanni uku kacal ta fara gogewa fiye da tsammaninta,duk da dama dai ta samu foundation me dan kyau ba laifi daga makarantar primary din da tayi a gembu.


Gab da magariba suka gama karatun kamar kullum,tana goye da amna da barci ke dibanta suka shiga cikin gidan,ta taras dasu laila duk sun dawo,sun sha qunshi da gyaran kai tubarkalla,kowacce cikinsu tana da suma dai dai gwargwado irin na fulani.

Duk yadda suke daukin amna tazo gurinsu taqi kowa,kowa da kalar wayon da zaiyi mata amma ta qiya,murmushi maimunatu ta sake,har fararen haqoranta suna fitowa

"Saiku haqura,yau dai kam ni ta zaba" sunata yiwa yarinyar tsiya ta wuce da ita dakinta ta kwantar da ita saman gadonta,zuwa lokacin bacci yayi awon gaba da ita.

Washegari amnan tana barci maimunatu ta wuce islamiyya,sanda ta farka bata ganta ba ta saka rigima,rarrashin duniya kowa yayi mata amma ta qiya,hatta da anni da amman da suke dasawa yau taqi,saboda sun bari hisham kafin ya fita aiki ya nata allura,basu samu lafiya ba sai da maimunatu ta dawo,da gudu ta taryeta kuwa tun daga bakin qofa,maimunatu ta dagata tana taba jikinta,ta samu zazzabin ya sauka,baki ta tura gaba cikin murya irin ta yaran da suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login