Showing 165001 words to 168000 words out of 194226 words

Chapter 56 - GURBIN IDO COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

12 Dec 2024

26175

daya da ita a bakin aikinka,koma da ita inda ka daukota" cikin rawar jiki da kuma matuqar tsoron rasa aikinsa ya janye akwatin zuwa baya,bai kuma sake bi takan maganar unaisa dake cewa karya fitar mata da kaya ya qaraso mata da ita ciki.

Wani kallo me cike da qasqanci da kuma qyama ya jefeta dashi,zallar kwarjinin da yake dashi ya daketa,gaba daya sai tayi collapse,har ya qaraso bakin sassan nata da ta zura key da nufin budewa,ya sanya hannunsa ya zare key din ya jefa a aljihunsa ya kewayeta ya fice abinsa ba tare daya ce mata uffan ba.

Sai daya kira dukka ma'aikatan gidan yaja kunnen kowannensu kan kada wani a cikinsu ya kuskura ta sashi abu yayi mata,koda ja mata luggage dinta ne,yaja musu kunne da kakkausar murya kam duk wanda yayi hakan a bakin aikinsa,cikin bin umarni kowa ya amsa mishi,tare da tabbatarwa kansu ba zasuyi wannan gangancin ba,a yanzun samun gidan aiki me cike da kyautatawa da bayan salary dinsu harda allowance ake basu abu ne mai matuqar wahala,bai tsaya sauraren rantse rantse da ban haqurinsu ba ya shige mota ya bawa drivern umarni su fice a gidan.

Ranshi ya baci sosai,amma tun kafin yakai office ya tattara damuwarta ya watsar,abu daya ne ya sani cewa ko sama da qasa zata hadu bazai taba iya zama da ita ba,bazai furta mata komai ba,amma dole takai kanta gida ta kuma gaya musu daga inda take,ta bakinta komai zai fita yana nan yana zuba idanu.

A bakin office dinsa ya tarar da jabir yana jiransa,gaba yayi yana qoqarin shiga tare da fadin

"I come late,am sorry" ya dauki uzuri,sabida ba dabi'arsa bace saba alqawari da lokacin zuwa aiki,binsa da kallo jabir yayi yana qoqarin karantar yanayinsa,gaba daya ja'afar din ya wani sukurkuce a 'yan kwanakin,duk da yadda yake nuna qarfin hali,anya zai jure?,bazai tayashi baiwa anni haquri ba ta sauka daga kujerar naqin data hau ba?.

Koda ya sameshi a office din bashi lokaci yayi,sai da yaga ya dan nutsu sannan suka gaisa,ya miqa masa takardun ya koma ya jingina da makarin kujerar da yake kai yana kallon ja'afar din duba na kai tsaye.
11/24/22, 23:35 - Buhainat: 75

Jan files din da jabir din ya tura masa gabansa yayi ya fara budesu yana dubawa,tun baiyi nisa ba ya rufesu yana duban jabir din

"Wannan ya akayi haka?" Gyara zamansa yayi

"Kai za'a tambaya malam ja'afar,tunda dai duka sanya hannunka ne a ciki,Allah yasa banyi gaggawar yin nawa sign din ba,da asara zamu tafka ba 'yar kadan ba" shuru yayi ya sake budawa yana kuma dubawa

"Duka cikin satin nan nutsuwarka ba'a jikinka take ba why?" Rufewar ya sakeyi yana sauke ajiyar zuciya,ya hade yatsuntsa waje daya,sai kuma ya sake warasu yana shafa sumarsa

"I'm not in a good mood jabir,anni tanason tayimin abinda zai sa na sake ajiye aikina gaba daya,very soon kuwa,idan ba haka ba zanyi ta shirme ne kawai" danne dariyarsa jabir yayi ya gyara zamansa

"Tun farko laifinka ne J,ba yadda ba'ayi dakai ba kada ka kaita boarding amma kaqi,duk abinda babba ya hango yaro bazai taba hangoshi ba"

"I made a mistake,what is the solution?" Shuru kadan jabir yayi sannan yace

"Yanzun dai kome zakayi anni zata gane setup ne kawai,so ka qara haquri ina ganin,zuwa sanda zasu gama exams su dawo gida hutu,daga nan sai kasan me zaka.shirya da zai hanata komawar" kai ja'afar ya fara girgizawa

"No... gaskiya,I can't wait until they finish the exam,lokacin yayi tsaho"

"Okay,shikenan,do your worst......amma kasan anni dai"

"Wait.....wai ita kemin zaman auren?"

"A'ah,amma ita tayi maka auren" ya fada yana dariyar tsokana,sai akwai ja'afar din ya saki murmushi ba tare daya shirya ba yaja gajeran tsaki sannan a fili yace

"Rabbish rahli sadry,wa yassir ly amry" sai ya dauka correction fluid ya bude ya soma gyara inda yake da kuskure yana gyarawa,jabir na zaune suna tattaunawa akan kasuwancinsu.

Haka kawai ya samu kansa da yawo saman titi bayan an tashi daga office,jabir da ya dauko ya rakashi aka masa gyaran fuska ya dubeshi

"Ka yiwa Allah ka kaini gida,na gaji da wannan ragaitar,kada fa'eema ta dauka wani gun na wuce tayi fushi dani" harara ya waigo ya watsa masa,sai ya qarawa motar wuta

"Ni da kuka hada baki da anni kuka maida tawa makarantar kwana wato na mutu kenan?" Dariya sosai ya sake

"Wa ya isa ya daukar maka mata ya kaita can?,kai kakai kanka" shuru ya kasa na wasu mintuna sannan ya sauke ajiyar zuciya

"Abu daya zai hanani daukota yanzun,wannan aikin da nakeyi a kanta,amma da zarar ya kammala na daukota daga makarantar to ta fito kenan,ba ruwana da wata anni" dariya ya kuma yi,sai kuma ya katse yana cewa

"Niko kamar naji kace unaisa bata nan?,ina ta tafi?" Ajiyar zuciya ya sauke hade da wata zazzafar iska daga bakinsa,ba boye boye tsakaninsu da jabir,a nutse ya gaya masa komai.

Shuru jabir din yayi abun yana kadashi,magana ta Allah bazaiso ja'afar dinsa ya hada jini da unaisa ko ya riqeta amatsayin matar aure ba,shi kansa tun randa ya fara ganinta ya gane fuskarta,yayi shuru ne baice komai ba saboda baisan me Allah ya shirya ba,sannan kuma ma babu kyau mutumin da yayi tuba na gaskiya ka tona asirinsa,ashe da sauran rina a kaba.

Shawara ya bashi ta hankali,wadda ta kusan zuwa daya da abinda ja'afar din ya yanke,saidai shi yace ya sanar da abbi abinda ake ciki

"Ka qyaleta,idan baka iya kama barawo ba sai barawo ya kamaka,da kanta zata fadi me tayi da inda taje,idan tana taqamar gata sai gatan ya qwaceta" har suka isa gidan jabir din suna tattauna batun.

Babu yadda baiyi dashi ya shigo ciki suci abinci ba amma yace aah,ya kunna motarsa ya qara gaba,dama yasan mawuyacine ya shigo din.

Samun kansa yayi da kasa komawa gidan,saboda yasan idan ya koma din ma bawai zama zai iyayi ba,gaba daya both gidajen guda biyu babu wanda yake masa dadi,yaja tsaki yafi a qirga a saman titi,kafin ya yanke ya tafi gidansu kawai ko zai rage tsahon dare a can.

Ganin lokacin sallar magrib ya kusa sai ya sanyashi zama saman motar abinsa ba tare daga shiga cikin gidan ba bayan ya faka motar a parking lot na gidan,ya fidda wayarsa ya soma dannawa,kusan babu wanda yasan ya shigo idan banda ma'aikatan gidan.

Bai rufa minti ashirin ba aka sake hon,mai gadin ya tashi ya sake budewa,sau daya ya daga kai ya kalli motar,sai ya maida kansa yaci gaba da danna wayarsa,motar hisham ce,ta gangaro gefansa tayi parking.

Sosai abbi dake zaune gefan hisham din yadan kafe ja'afar da ido wanda.baima san waye da waye a cikin motar ba

"Miskili kafi mahaukaci ban haushi" abbaya fada yana murmushi yana duban fuskar ja'afar din,kallonsa hisham yayi shima yana taya abbi murmushin,ya karanci kamar akwai damuwa akan fuskarsa,amma ba wanda zai iya buda baki ya gayawa,yasan bazai wuce case dinsa da anni ba,ko kuma unaisa da yau minister ya kirashi ya gaya masa cewa ya turo ta gida ba tare da sunsan meye ya faru ba,bude murfin motar abbi yayi yana cewa hisham ya biyo shi da jakarsa.

Yana ganin abbi din ya ajjiye wayarsa ya duro daga bayan motar ya tako inda yake cikin girmamawa yana masa sannu da zuwa

"Yauwa ja'afar,ya gida ya iyali?"

"Alhmdlh abbi" ya fada yana shafa kansa

"To masha Allah,bari na shiga ciki na fito sai mu wuce masallaci tare ko?"

"Okay abbi" ya amsa masa,zuwa sannan hisham ya qaraso,ya miqa masa hannu sukayi musabaha yana gaida yayan nashi,sannan suka rankaya ciki suka barshi a wajen.

Babu jimawa abbi ya fito da alwalarsa,tuni shima yayi tasa a bayan gidan suka wuce masallacin.

Bayan an idar a hanyar dawowarsu abbin yake tambayarsa

"Me yarinyar nan unaisa tayi maka manya?,abun kuma har yayi girman da zaka turata gida?" Abbin ya fada a tausashe,duk da tsauri da zafinsa amma yana sauqin kai da kuma saurin fahimtar al'amura

"Abbi,tafi kowa sanin abinda tayi,ita ya kamata ta gaya musu da bakinta" kai ya girgixa

"Yanzun ai ni nake tanbayarka bawai su ba,me tayi maka,ka gayamin ko mene ne,sai asan yadda zq'a gyara abun" kai ya girgiza

"Abbi.....banajin zai gyaru"

"Meye wanda bazai gyaru ba?" A nutse ya gaya masa dukka wani abu daya taba sani a baya akan unaisan,da kuma abinda ya farun yanzu da binciken da yayi da hujjojin da ya samu.

Sosai abbin ya kadu,don bai taba kawowa yarinyar haka ba,duk yadda suke takatsantsan wajen samawa 'ya'yansu maza da mata abokan rayuwa na gari,amma duk da hakan bai nunawa ja'afar din ba sai yace

"Ka barni da kaina zan sake bincike"

"To abbi" ya fada hankalinsa a kwance,tunda dai ya sani,koda abbin din zaiyi binciken zai binciko kwatankwacin abinda shi ya samu ne koma wanda ya fishi.

Zuciyarsa ce ta dinga raya masa ya yiwa abbi zancan maimunatu,sai kuma yaga bazai iya ba,don haka ya share batun,yasan dai akwai lokacin daya dibama koma meye anni ta shirya.

Sassan amma suka wuce shida abbin din gaba daya,saboda yace yunwa yakeji,yau da wuri zaici abincin darensa,baya wasa da girkin amman,saboda yadda ta qware sosai wajen sarrafa abinci,tarin masu aiki ko sarauta ko arziqin da take dashi baisa ta sako abincin mijinta ba hannun yara ko masu aiki,har yau har kwanan gobe ita keyi,saidai a tayata.

Amma na shirya musu abinci suna fira sama sama,bayan ta gama itama sai ta samu kanta da zama a cikinsu,abinda ba kasafai takeyinsa ba,duk da ita bacin abincin take ba,tana ta dai serving dinsu ne,daga baya saiga hisham ya shigo shima yayi joining dinsu, khadim ma sai gashi,da yake sau tari sai ya baro abincin ammi ya taho wajen amma ci,duk da itama ammin gwana ce,amma shi dan dakin amma ne.

Bai waiwayi sassan anni ba sai da ya dawo daga sallar isha'i ya kusa wucewa gida,tasan ya shigo gidan sarai,kuma batayi mamakin rashin shigowarsa ba,sanda ya shiga tana zaune a falo tana shan damammiyar fura data sha sugar,don annin ba daga nan ba wajen shan zaqi,kanta ta daga ta dubeshi sannan ta tabe baki ta maida kanta ga abinda takeyi,ya samu hannun kujera ya zauna yana gaidata,a yatsine ta amsa masa,yadan zubawa tv ido sannan ya miqe

"Wannan sugar din da kike yawan sha fa yana yawa,shekarunki sun ja" dama jiransa take,saboda haushin qin shigo matan da baiyi ba,saboda ta saba anan yake sauka ko yaushe bayan ya gama gaisawa da kowa

"Kai arcannnn.......kayi ta kanka malami,mu jikinmu ba irin naku bane, sugar abin banza ba abinda zaiyi mana,haka zamu mutu ras da lafiyarmu in sha Allah,damu da mazanmu ba irinku bane,wanda sai mace ta shekare a gidansu su kasa yi mata ciki sabodq tsabar raggwanta" dole ya dora idanunsa akan fuskar anni,tirqashi😂, abun yazo harda gori?,ya tabbatar dashi take,shi takema gorin baima maimunatu ciki ba,don yasan itace tata,da ita ta damu.

Murmushin gefan baki ya saki yana cusa hannuwansa a aljihun wandonsa,shima bari yayi mata ta 'yan zamani

"Me kike ci na baka na zuba anni?,ba tsallaken shekara daya bane?,to itama za'a ciketa,ki rubuta ki ajjiye biyu xa'a baki ko uku,nex year mu sake maimaitawa" daga haka ya juya yana ficewa daga falon,sai ta bishi da kallo,tana jin sanyi qasan ranta tare da cewa

"Ameen ya hayyu ya qayyumu,'yan ameen su amsa ya rahman" can qasan ranta,amma a fili sai tace

"Ahhh waima,zamu gani".

Yana mota yana tuna matter dinsu da anni,sai kawai ya samu kansa da sakin murmushi,tare da imagining diyoyi daga wajen maimunatu,wanne irin kyau zasuyi?.

Duk guje gujensa yau dinma sai da yasha baqar wahala kafin ya samu bacci ya daukeshi
11/24/22, 23:35 - Buhainat: 76

A hankali ta rufe bangon littafin dake gabanta gami da sauke ajiyar zuciya,zuciyarta na wani irin karyewa da kuma samun rauni,a hankali ta zubawa wajen da afra suke zaune suna hira kallo,tun dazun suka ce mata ta bar karatun tazo tayi joining dinsu amma taqi,saboda bata da wani karsashi ko farincikin hirar,tunda ta dawo sati biyu cikin na uku zuciyarta a quntace take,ba wani walwala ko farinciki.

Wayarta ta zaro ta sake kallon fuskar wayar,cikin sarewa da gajiyawa ta dora wayar saman table din data aje littafin nata sannan ta zame ta kwantar da fuskarta saman table din,daga dawowarta zuwa yau batasan sau nawa ta duba fuskar wayarta ba,haka kawai taji tana tsimayin kira daga gareshi,saidai ko sau daya bai kirata din ba,tana ta sanya rai taji ance tazo gashi,duk da tasan ba bari ake azo ganin naka ba idan bada wani babban uzuri ko dalili ba,amma tata zuciyar nata shauqin jin hakan,saidai shuru,lumshe idanunta tayi tana jin yadda zuciyarta ke tabuwa,ba zata taba kiransa ko sau daya ba,sabida tayi alqawarin jan ajinta da mutuncinta,zata kuma cika burin anni in sha Allah


"Maimoon,lafiya?,me ya sameki?" Taji muryar afra saman kanta,sai ta bude idanunta da kyau a kan fuskar afran

"Me kike gani?"

"Kuka.....hawaye fa kike?" Bata yarda da zancan afra ba sai data sanya hannu ta shafi fuskar tata sannan taji danshinsu,abinda ya sake sanya zuciyarta karyewa,kawai sai ta saki kukanta sosai tana kifa kanta a table din.

Da sauri afrah taja kujera dab da ita ta zauna tana fadin

"Innalillahi,wai menene yake damunki maimoon?,meye matsalar?" Bata bata amsa ba,sai kawai tasa hannu ta zare wayarta dake gefe,tasan me zatayi mata.

Contact ta shiga ta fara laluben sunayen soyayya data sama wata contact,saidai babu ko daya a ciki data gani,haka ta haqura,ta sanya ainihin sunansa saiga number din ta fito,kallon maimunatu da batasan ma tanayi ba tayi taja qaramin tsaki,wai itakam yaushe zata bude zuciyarta ta yarda soyayya takeyi?,ta kuma gane ita ke wahalar da ita?,kawai saita canza sunan dake kan number zuwa honey bee,sannan kanta tsaye ta danna masa kira.

Dai dai lokacin yana kwance a wajen hutawa daya ware cikin office dinsa,tunda yazo yake zaune a wajen,ya gaza hassala komai,baisan me yake damunsa ba,gaba daya tunda ta tafi ta tafi da walwalarsa,hannunsa daya bisa fuskarsa,sai yaji shigowar kira wayarsa.

Har tayi ringing dinta ta katse bai dauka ba,ta sake shigowa ta kuma katsewa,ya shareta yana ci gaba da kwanciyarsa,har sai da yaji qishirwa,sannan ya miqe zaune ya jawo wayar yana son duba lokaci,don da wuri zai fita daga company din yau,saboda ya lura bazai iya aikata wani abun kirki ba.

Ganin miscall da number ta yasa ya tashi ya zauna sosai,bai zaci wayarsu na amfani ba a school,daga sama kuna tex ne

_ka kira pls yaa ja'afar,qawar maimoon ce_

Bai gama karantawa ba ya fita a saqon ya kira number din,yana jin yadda zuciyarsa ta tafi gaba daya ta kuma afu gason jin muryarta.

Da sauri afra ta duba kiran sannan ta dan matsa gefe kadan daga inda maimunatu ke zaune ta daga

"What's happening?" Ya tambaya kai tsaye,jin ba muryar maimunatun bace

"Kuka dai takeyi,na tambayeta taqi magana"

"Bata wayar" ya fada cikin jin wani tashin hankali yana shigarsa,meye ya sameta?,itace tambayar daya fara yiwa kansa.

"Yaa ja'afar ne" ta rada mata a hankali,kafin ta gama fuskantarta har ta nana mata wayar a kunne

"Angel" ya furta cikin wani irin taushi,da zuzzurfar muryarsa data aike mata da wasu saqonni lungu da saqo na jikinta karo daya,wani nauyi taji zuciyarta tayi,hawayenta kuma ya dauke cak,ta zuqi numfashi sosai tanason fesarwa amma kamar ya riqe

"Hello.....angel,my moon" ya sake fada very softly,wannan karon fidda numfashin tayi gaba daya,wanda ya zame mata kamar ajiyar zuciya mai sauti,batasan sanda tasa hannu ta dafe wayar sosai a kunnenta ba,har yanzu idanuwanta suna rufe tana sauraren saukar numfashin sa daga cikin wayar,da alama shima ta taba zuciyarsa sosai

"Say something mana angel,bazan iya jurewa ba,meye ya faru?"

"Zazzabi" ta fada muryarta a mugun narke,kuka mara sauti me dauke da hawaye yana kubce mata

"Ya salam......jirani gani nan zuwa" ya fada yana katse wayar gaba daya.

A gaggauce ya maida takalminsa ya kira PA yayi cigiyar key din motarsa,ya karba ya fice ba tare daya tsaya sauraren kowa ko kuma meeting dake gabansa awa daya mai zuwa ba.

Kasa motsawa tayi daga wajen,sai kunnuwanta suka shiga maimaito mata abinda yace

"Ta jirashi gashinan?,da gaske zuwan zaiyi??" Zuciyarta dai ta cika da wasi wasi,amma duk da haka sai tayi likimo taci gaba da kwanciya a wajen,har zuwa sanda ta tsinci muryar afra na kiranta irin kiran gaggawa,idanuwa kawai ta bude tana jiran isowarta

"Ana kiranki office din principal,yaa ja'afar ne yazo" batasan ta miqe da hanzari ba sai data ji kanta ya saara,ta dafe kanta da hannunta sannan ta dubi afra

"Muje ki rakani please" hannunta ta riqe tana murmushi,tanason tsokanarta amma kuma yanayinta yana nuna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login