Showing 108001 words to 111000 words out of 194226 words

Chapter 37 - GURBIN IDO COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

12 Dec 2024

26177

zungurarsa da magana ganin baice komai ba,dai dai sanda hafsat ke fitowa a kitchen din dauke da kwanukan abinci,gabanta yadan fadi,tana son jin qarashe zancen,kada dai ace ciki gareta

"Alhmdlh" ya amsa a taqaice

"Inaga kamar ya kamata tabawa ta dawo hakanan,dama tamin magana kan tanason tahowa" baiso annin ta fadi hakan ba yanzu,ko ba komai yana samun abinci kwana biyu yaci ya qoshi hankali kwance,ya rage zuwa eatery neman abinda zaici

"Ba laifi" ya amsawa anni,dai dai sanda ta iso wajen,ta fara ajjiyewa jabir,sannan ta qaraso inda ja'afar din yake,cikin salo ta duqa tana ajje masa nasa abincin,wanda zubin data masa ma daban yake,in a stylish way ta shirya salad din dake saman abincin.

Hannu ta miqawa amna

"Taho daddy ya samu yaci abinci ko?" Kafada ts maqale tana kallonta

"Ahaf.....wannan 'yar wulaqancin fa sai wanda ta zaba,wuce ciki abinki" batas anni tafada haka ba,taso zama ne a wajen taci gaba da jin hirarrakinsu,ta kuma morewa kallon ja'afar din,don yau din wani kyau yayi na musamman,kayan sunyi matuqar karbarsa.

Dakin dake opposition da dakin ta shige,ta zare key din dake jikin qofar tana leqensu ta jiki,abun haushin duk yadda ta tsara masa abincin bata wani ga yaci komai ba a ciki,hasalima amna taga ta sanya cokali tana cin abinta,ruwan kawai taga ya dauka yasha,shima ba mai yawa ba.

Ana sallar la'asar daga masallaci gida ya wuce bayan sunyi sallama dasu anni,already dama yayi kiran driver,don haka kafin su idar ma ya iso,ya daukeshi suka wuce,yana mota yana tunanin amnan,duk sanda yazo gidan sai yarinyar tayi attempting din binsa amma tilas take sawa yace mata a'ah,to yau ka harda kukanta,abinda yasa kenan yayi deciding next month ya dauketa su danyi yawo kadan,koda zuwa lagos ne,yasan hakan zai mata dadi,zai kuma debe mata kewa.

Samansa ya wuce direct,ya bude dakin yana kallonsa,gaba daya it's not in order,komai na dakin bai masa yadda yakeso ba,sai ya koma da baya ya bude daya bedroom din nasa ya sauka a can,kayan jikinsa ya sauya kawai zuwa wata farar jallabiyya ta maza mai sulbi da kuma wide neck,ya hada dukka aikin dake kansa wanda a qa'ida yau zaiyishi a office,amma yau din juma'ar qarshen wata ne,yana basu hutu yawanci duk qarshen wata,musamman idan akwai raguwar aiki sosai a lokacin.

Har zai zauna ya fasa,saboda cikinsa da yaji yana buqatar sanya masa wani abu,sannan kuma yanason jin ya hannun nata,don ya tabbatar a yadda yaji anni na masa magana a kanta yau,tabbas idan wani abu ya faru kai tsaye ma zata iya cewa shine ya qonata.

A nutse yake saukowa daga stairs din,duk inda ya gifta sassanyan qamshinsa yana biye dashi,rigar ta masa kyau ta sake maidashi cikakken mutum mai cikar kamala zati da kuma haiba.

Da tattausar sallama a bakinsa ya shiga falon,baba tabawan ce kadai xaune tana kallo,tana yi kuma tana duba girkinta dake kitchen,duk da abincin ma yau kusan ita daya taci na safen har na ranan,ta rasa wanne irin bacci maimunatun takeyi.

Cikin fara'a ta amsa sallamar tasa ta kuma yi masa maraba,ya tambayeta hannun nata

"Wallahi manya ban sani ba,tunda ta shiga ta kwanta bansan ma bacci take ba sai daga baya" baice komai ba ya miqe,hannunsa cikin aljihun rigarsa,ya nufa dakin nata.

A hankali ya tura qofar ya sanya jikinsa,kamar ko yaushe dakin gauraye da madaidaiciyar iska dake cakude da qamshi iri iri wanda ya bada wani scent na musamman,kasancewar yamma tayi dakin ya rage hasken dake akwai,yaci gaba da takawa zuwa inda yake hangenta a cure waje daya,saidai hasken wayar daketa aiki ta haske fuskarta sosai.

Gab da kanta amma ta bayanta,idanunsa suka sauka tun daga dogayen qafafunta dake harde waje guda,saidai kuma taba motsasu a hankali duk bayan wasu sakanni,da alama mafarki takeyi,don haka take dan motsa hannayenta ma,yawo yaci gaba dayi da idanunsa,yadda take kwancen sai yakega.kamar kwanciyar tata batai dai dai ba,sosai qugunta ya fita ta cikin rigar,sai ya dauke idanunsa da sauri ya saukesu kan screen din wayar.

Minti daya kacal ya tuna film din,one of the best dramas nashi,ya akayi ta nemoshi take kuma kalla?,hannunsa ya sanya ya zare earpiece din dake kunnenta ya maida a nashi kunnen idanunsa still suna kan wayar,lallausan murmushi ya qwace masa,abinda ya qarawa fuskarsa wani mugun kyau,abinda ba kasafai yake faruwa dashi ba kenan,ya tuna scene din,ya tuna wajen,murmushin yaqi daukewa daga fuskarsa,,ya tayar masa da wani tsohon memory da kuma wani sweet moment,sai yaji yana da sha'awan sake kallon drama din,ya duqa a hankali ta saman kanta da zummar dauko wayar ya kashe mata,abinda yasa yayi mata kamad rumfa a saman kanta.

Juyi tayi cikin hanzari tana sakin wata qaramar qara,abinda yasa ta bugeshi,ya kuma fada saman kanta saboda unexpected ta bugeshin,baiyi tsammanin zata motsa ha a sannan,qamqam ta riqeshi,tana tsamamnin cikin mafarkinta ne,saboda shine cikin mafarkin,ta kuma sake gasgata mafarkin takeyi jinsa a jikinta qamshinsa yana shiga qofofin hancinta.

A nutse ya zube idanunsa saman sleepy face dinta,karon farko da sukayi kusanci mai zurfi a tsakaninsu irin haka,har suna musayar numfashi,wanda yake fita da tare da qamshin jikkunansu,yayi gab da ita qwarai,kamar me shirin kissing lips dinta,sosai shagwababbiyar fuskarta ke shiga idanuwansa har yana ganin qananun gashin dake qasan hancinta wadanda suka sanya wajen danyi duhu kadan,cikakkiyar girarta da ta kusa hadewa da 'yaruwarta,siraran labbanta da suke dauke da wasu irin Pink lips masu daukan hankali.

Wani abu ne ya motsa zuciyarsa,har sai daya saki wasu irin tagwayen numfashi guda biyu a jejjere kamar mai sheshsheqar kuka,yanason zame kansa data zagaye hannayenta dashi saidai ya fuskanci mafarki take,kamar ma kuka kuka,saboda yadda shagwababiyar fuskartan nan ta narke gaba daya,ci gaba yayi da kallonta,a hankali murmushi ya soma maye gurbin yanayin kukanta,ya zubawa dan qaramin bakinta daya soma motsawa idanu

"Kayi haquri......."
"Yaa hisham" sunan ya fita can qasa,shi kansa motsi da dan qaramin fitar sautinta yabi ya fahimci me take cewa,mamaki ya cikashi,hisham?,hisham kuma take kira cikin mafarkinta?,for what reason?,fuskarta yaci gaba da kalla nasa yanayin na sauyawa ba tare daya sani ba,a hankali fuskarta ta koma normal mode na masu bacci,da alama ta gama mafarkin da takeyi kenan,sai ya zame hannunta daya nutse a qeyarsa cikin lallausar sumarsa,ya miqe tsaye yana ci gaba da kallonta bayan ya goye hannunsa a qirjinsa,kiran sunan hisham da tayi ya dawo masa,yadan rufe idanunsa sannan ya sake budewa,wani abu yaji yadan taba ransa,sai ya miqa hannu ya jawo hannunta dake boye a gefanta,zugi ya ratsa tsakiyar baccinta,abinda ya sanyata farkawa kenan.

Sai data bude ta kuma rufe idanunta sau uku don son tabbatar da cewa yanzun ma mafarki ne ko ido biyu,yaji alamun ta farka amma kuma baiko daga kansa ga dubeta,yana dai nazarin hannun nata ne,sai daya tabbatar batayi ko alamin tashi ba sannan ya sake mata hannun,a hankali kuma ya aza mata idanunsa masu nauyi da suka tilastata janye nata,ya basar ya kuma motsa kaman zai fita sai kuma ya dakata

"Karki qara kwanciya bakiyi addu'a ba,that's why kuke rubbing mafarkai" yana kaiwa nan ya taka sannu a hankali ya fice.

Idanunta ta waro waje tana bin hanyar daya wuce da kallo bayan ta tabbatar da fitarsa,kada dai yana tsaye ta gama mafarkin da tayi yanzu,saita cusa kanta tsakiyar pillow tana son tuna me da meye ya faru cikin mafarkin,tsahon minti kusan biyar kafin ta sake daga kanta da sauri ta kalli agogo

"Kai" ta fada da sauri tana wantsalowa daga gadon,ganin lokacin salla ya qwace mata sarai.
11/24/22, 23:25 - Buhainat: 49

A kasalance yabar sashen nata zuwa nasa,gaba daya ta sakarwa jikinsa wata irin kasala,ya rasa dalilin da ya sanya duk sanda incident irin haka zai faru tsakaninsu sai haka ta kasance.

Sam bai kula da wanzuwar mutum a wajen ba,har ya kama stairs zai hau yaji an kirayi sunansa a tausashe,sai ya tsaya cak,ya kuma waiwaya a hankali.

Unaisa ce tsaye,sanye da wata fatar gown,kanta babu dankwali sai qaramin vail data yafa a kanta me shara shara,idanunta a kansa,tana dubansa cikin wani irin kallo wanda ya nuna yadda tayi laushi har cikin idanunta,qasan ranta tana jin wani irin qaunarsa tana fusgarta,zuwa yanzu takai maqura,hakanam tana jin haqurinta yana neman gazawa,tayi iya matuqar qoqari a irin yadda ta saba rayuwarta,sai ta sake sassauta fuskarta tana fatan ya duneta da idanun tausayi,bata taba kawowa cewa izzarsa miskilancinsa da kuma jin kansa sunkai har haka ba,tayi tunanin a kurkusa zata tagi da imaninsa kamar yadda yake tafiya da imanin duk wani da namiji,fara takowa tayi a hankali,yana biye da ita da idanu,har zuwa sanda yaga tana shirin wuce iyakar da yakega ya kamata ta tsaya

"Stop there" ya fada da muryarnan tasa dake dauke d wani irin amo,ba zato babu kuma tsammani sai jinta yayi ta fada jikinsa gaba daya,ta kuma sanaya hannunta ta qanqameshi da kyau idanunta yana tara qwalla.

"Meye haka?, what's this?" Ya fada yana yunqurin tureta daga jikinsa,saidai hakan bai samu ba saboda yadda ta sake cukuikuyeshi tana fadin

"Na gaji.....na gaji,am going to kill my self indai ba zaka saurareni ba" furucin nata yayi masa banbarakwai sosai atsakiyan kansa,diyar musulmi ke zance aikata ta'addanci a karan kanta?,bawai don ya damu ko kima ya tsorata da furucinta ba yace

"Okay,okay......sakeni tukunna" kamar ba zata sakeshin ba sai kuma ta sakeshi,ta kuma ja da baya tana dauke qananun qwallar fuskarta,hannyensa ya shiga yarfewa kamar wanda wani abun qi ya tabawa fata,fuskarsa ya sake hadewa ya tsare gida sosai yana dubanta

"Am all ears" ya fada yana goye hannuwansa a qirji,idanunta tadan watsa bangaren sasan maimunatu,ta yaya zatayi irin wannan maganar dashi a waje.irin wannan,by mistake yarinyar tazo guftawa ta jisu?,ta tabbatar idan haka ta faru ajinta ya gaba zubewa a idanunta har abada

"Am not comfortable here......i need privacy" kamar bazai amsata ba,sai kuma ya juya ya soma takawa zuwa saman a nutse cikin takunsan nan na daban,ta bishi da kallo tana jin wani abu yana tsarga mata,kafin daga bisani ta soma bin bayansa,tana qiyasta irin kalmomin da zatayi amfani dasu wajen ganin tasha kansa.

Suna isa tsakar falon idanuwanta na sake sauka ga hotunan shaheeda,yadda ta tsani mutuwarta haka ta tsani bude idanu taga wadan nan hotunan,asalima tana kishinsu fiye da yadda take jin kishin maimunatu,tunda a yanzun maimunatu bata tsare mata komai ba,bata ma.kallonta a matsayin matsala gareta,saidai tana jin haushin amsa sunan matar mijinta da tayi,harara ta jefi hoton dashi,wanda ja'afar dake qoqarin ganin ya saurareta idanunsa suka shaida masa hakan,wani abu me kama da mamaki ya saukar masa

"Harara?,for what?" Maida idanunsa yayi ga sassan da hoton shaheeda ke maqale,dai dai sanda ya dauke dubansa zuwa ga unaisa,itama dai dai sannan ya dauke idanunta zuwa kansa,sai suka hada idanu,kamar an zare wani abu daga zuciyarta taji,bataso ya ganta ba,amma ita ba wannan ne damuwarta ba,damuwarta ta fidda wadda ke cikin hoton daga zuciyarsa gaba daya,kamar yadda ta five a filin duniya,ita kuma ta maye gurbinta

"Uhmm.....go on" takowa ta soma yi tana sake nufoshi,ta dora dukkan wani yanayi da zai baka tausayi a kan fuskarta,saidai tana zuwa gab dashi ya sake dakatar da ita

"Don't do it" ya fada calmly gami da yi mata nuni da hannu kan yana saurarenta,bata da wani zabi illa fashewa da kuka harda sheshsheqa,abinda ya bashi mamaki ganin cewa shi din bai aikata mata komai ba,fuska ya hade sosai yana dubanta,sai kuma ya kau da kai yana jan tsaki can qasan ransa

"Bansan meye laifi na,ban kuma san me na aikata maka ba,don kawai nace ina sonka ja'afar?,ta yaya da hakkina a kanka tsahon shekara kusan guda ka takemin kamar bakasan da wannan ba"

"Anzo wajen" ya fada a ransa yana jin tana sake ficewa daga ransa,ta yaya yarinya mai cikakkiyar kunya da nutsuwa zata iya duban idanun da namiji.....duk da kasancewarsa mijinta,amma a matsayin budurwa ta gaya masa hakan?,well.....batayi laifi ba,tunda hakkinta ne kamar yadda ta fada din,amma bayajin koda danneshi akayi zai iya aikatawa,hes not in the mood gaba daya,bayajin wani feelings a yanzu a kanta ko dis.

Kujerar dake daura dashi ya qarasa ya zauna a hannun kujerar,yaci gaba da dubanta hankali kwance sanda taketa kukanta tana sake qara ma kukan salo a fatan da take na samun nasara a kansa,can qasan zuciyarsa yake qissima ta yadda zai raba kansa da wannan matsalar.....eh.....matsala mana,zuwa yanzun yana jin unaisan ta zame masa matsala,babu abinda take haifar masa banda kwasarwa kansa zunubi,bayan yana da tabbacin abune mai wahala ya iya karbarta cikin rayuwarsa,zuciyarsa wata irin zuciya ce mai wahalar sha'ani


"I already told you,zamanmu abu ne mai wahala da ban hango yiwuwarsa,ni am ready to dismissed you,the choice is yours.....karki sake tara ta da irin wannan shirmen" daga haka ya miqe ya nufi bedroom dinsa,ta yunqura zata bishi,saidai ko kafin ta isa ya maida qofansa ya rufe,ta daga hannu kamar zatayi knocking sai ta sauke,ta fahimci wasu daga cikin halaye da kuma dabi'unsa,idan ta sake tayi knocking masa qofa,batasan me zai biyo baya ba,sai ta juya da gudu gudu tana sauka daga stairs din kuka yana kufce mata,ta gaji gaskiya,ta kuma kai maqura,tana jin ta iso geji,batason kuma ta bata dukkan wani tanadi da tayi masa,zata dauki mataki na gaba itama da takeji har cikin ranta da zuciyarta shine dai dai.


°°°°°°°Ta tabbatar idan har ta zauna a wajen baba tabawa babu abinda zai hanata cewa taje takai masa abincin dare,wannan shine worst abu da zata sanyata,bata jin zata iya hada idanu ko muhalli dashi,gaba daya ya ajema ranta da zuciyarta wani abu,wani irin nauyi da kwarjininsa daya qaru cikin idanunta,gefe guda wani abu me kama da haushinsa da take ji,gaba daya halayyarsa batayi mata ba,hisham ya fishi sauqin kai kirki fara'a da iya mu'amala da mutane,komai nasa cikin tsumewa da tsare gida?.

Leqawa kawai tayi ta duba baba tabawan don tasan ta tashi kuma lafiya take,don ko ita tayi mamakin jimawar da tayi tana bacci

"Zan koma na kwanta baba,jikins yau banajin qwarinsa"

"Ashsha.....amma dai ba ciwon bane ko?,yana shirin dawowa ina shirin tattara komatsaina na koma inda nafi wayo?" Dubanta da kyau maimunatu tayi,gabanta ya fadi,sai taji an cire dukka sauran walwala daga zuciyarta,komawa tayi ta zauna a maimakon tashi da tayi dazun

"Tafiya kuma baba?" Kai ta gyada

"Eh,ai gwara na koma gida hakanan,tunda naga jikin naki ai yayi kyau,banda tsautsayin da ya faru yau ma ai da yau din a gida zan kwana" gaba daya jikinta ya gama mutuwa,batason tafiyar baban,saboda tasan ba komai bane zai faru sai zaman kadaici kara dadi,wanda a yanzun ta fara sabawa da rayuwa da mutane,daya daga cikin dalilan da ya sanya ko hutun makaranta bata fiya son ayi ba,banda tanason tazo taga anni wasu lokutan.

"Don Allah baba ki bari sai zuwa wani lokaci,ko kuma idan zan koma hutu,saura kwana ashirin gaba daya mu koma" kai ta girgiza

"Banda abinki maimunatu ta yaya zan zo cikin yara gotai gotai dani na zauna banda ma lalura ta rashin lafiyar?,ai gwara na tafi,kema kyafi sakewa kiyi bautar aurenki yadda ya kamata" daga qarshe ta shagwuba mata magana,wadda ta sanya bata sake cewa komai ba,sai tayi qas da kanta.

Bata sani ba ko kewar baban ta fara, yadda ta tsara guduwa daki batayi hakan ba,sai ta zauna suna fira sama sama,yayin da baban tayi amfani da wannan damar tana sake jan hankalin maimuntu a fakaice akan rayuwar auren nata.

Washegari gaba daya bata fito a daki da wuri ba,tana qiyasta lokacin da zai shigo gaida baba tabawa,ta kuwa qiyasta dai dai,don kuwa ya shigo gaida ita din,saidai a gurguje,don yana sauri zashi gida karbar kudin auren salma hafsa da kuma nadiya,harma da laila,sosai baba tabawa taji dadin labarin,bayan kuma maimunatu ta fito ta shaida mata.

Tun a waya ta kira laila tayi mata murna,saboda tasan yadda take son auren,don babu wanda ya zaci ma za'a karba harda nata,ta kuma dan tsokaneta,baba tabawa na zaune tana jinsu tana dariya,ko bayan ta gama wayar ma hirar familyn dr marwan din suka shiga,wanda duka baba tabawan ce ke bata labarin yawan zuri'ar khalidu akko,da kuma karamcin mutan gidan dr marwan din,wanda ita kanta maimunatu shaida ce,bata taba zaton a duniya akwai mutane irinsu ba,sun samu dukkan wata dama ta rayuwa,amma hakan baisanya sun wulaqanta kowa ba,ko kuma sun dauki kansu a wani abu ba.

***********Washegari tun safe maimunatu tana dakin baba tabawa,gaba daya yau din ranta babu dadi,tare sukayi abincin safe,baba tabawan ta dora na dare da wuri,saboda da yamma sukayi da driver zaizo ya dauketa,ko mai maimunatun takeyi cikin kasala da rashin dadin rai takeyinsa,tana jin inama ace zata iya hana baban tafiya,inama zata yarda suyi zamansu tare,saidai tasan hakan ba mai yiwuwa bane.

Suna gama girkin ta wuce dakinta,tayi wanka,sannan ta shirya cikin wata chiffon gown da aka fidda mata desin me kyau,ta bude sosai daga qasa,ta gyara kanta,ssnnan tayi rolling vail din da tazo dashi shima na plain chiffon mara ado a jiki,jikinta na fidda sassanyan qamshin turaren burberry london,bata saka komai a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login