Showing 138001 words to 141000 words out of 194226 words
cikin tsakiyar dakin tana nufar toilet dinsa,idanunta take wulwulgawa cikin dakin,komai na dakin taji yana burgeta,komai cikin tsafta,babu datti ko qura,saidai kuma ba'a shirye wasu abubuwan suke ba kamar yadda aka san dakin mace.
Duk kyau da girman dakin da kuma tsadajjen marbles da aka saka masa an mamaye kusan fiye da rabinsa da wani tattausan carfet mai daukan sanyin acn dake kadawa cikin dakin kamar yanayin hunturu,kalolin dakin gaba daya dusty pink and beige color ne,sassanyar kalar da babu hayaniya a ciki,kama daga curtains zuwa komai ma na amfanin ciki,ta wuce toilet din tana kallon katafariyar walk in closet dinsa dake cike da himilin sutturu,kai zaka tsammaci ba'a nan qasar bane,da alama wadanda suka tsarata sun qware sosai a aikinsu.
A toilet ma bata yima kanta qauron kallo ba,a nutse take bin toilet din da kallo,kamar ba muhallin wanka ba,tuna abinda ke gabanta da kuma wanda ke jiranta yasa ta qara gaba zuwa jacuzzi bathtub,ta hada ruwa dai dai da ra'ayinta sannan ta koma gaban wani oval shape glass sink dake da wata qaraman drower a qasa,gaba daya kayan amfaninsa ne a ciki kana hangosu tarwai kamar ruwa bai taba wajen,kama daga brush toothpaste sponge da tarin shower gel masu tsadan gaske,sai kayan shaving nasa,clippers da sauransu.
Wadda ke a bude ta dauka tare da sponge din dake wajen data tabbatar dashi yake amfani,lumshe idanuwanta tayi sanda qamshinta da dumin ruwan ya hadu waje daya,sai taji kamar kada ta gama wankan,sosai qamshin ya burgeta ya kuma zauna mata a kwanyarta.
Rarraba idanu ta shiga yi data tuna bata ko shigo da kayan da zata canza ba,hakanan bazata iya maida rigar data cire din ba,ta koyi wata irin tsafta da gayu na daban,bata da wani sauran zabi,dole ta matsa jerin fararen towels din dake maqale a wata silver hanger ta cira daya,tun kafin ta raba shi a jikinta qamshinsa yayi mata maraba,ba kasafai ta fiya son cudanya da duk abinda ke qamshinsa ba,sai ta maida ta dauko wani,saidai.shima din dai sammakal,ganin tana bata lokaci yasa dole ta daurash cike da fargaba,bata manta waccar ranar ba da towel din yaso zamewa daga jikinta,Allah ya taimaketa batayi me gaba daya a gabansa ba,sai ta sake dauko wani ta lullube kanta sannan ta fito.
Da amna ta fara cin karo,zaune kan sleeper sofan dake gaban gadon da game a hannunta,bisa dukkan sabuwa ce yau din ta fara amfani da ita,sam ta mance da yarinyar,dazun tana ina sanda suke magana?,Allah yasa bata a wajen.
Kai ta daga tana duban maimunatu dake riqe da towel din dake kanta wanda ke shirin zamewa
"Anty moon,ga kayanki" duban inda ta nuna matan tayi,sai ta gyada kai,ta qarasa gaban mirror dinsa.
Kaman madubin mace,cike da kayan shafa designers amma irin na maza,bata da sauran xabi,hakanan ta bude mayukansa ta shafa na shafawa,duk amna anyi shuru an nutsu an sami game,sannan ta dawo tana daga kayan da amnan tace nata ne.
Tana duba kayan pant da breezier dinta suka fado daga tsakiya,sai ta fidda idanu cikin mamaki,ta daga kai tana duban amna
"Amna....waye ya daukomin kaya?"
"Daddy ne,nina rakashi" wata irin kunya ce ta kamata kamar zata nutse a wajen,musamman da taji suna fidda qamshin musk,saita qanqamesu kamar ta fasa kuka, knocking da taji anyi ya sata kwashe kayan da sauri,ta kuma koma toilet ta sakasu,tana sake jajantawa kanta,shikam baiji kunyarta ba?, dakinta ma ya shiga kenan?,bayan wannan dame dame ya gani nata?,Allah yasa baiga wani abu na kunya ba a dakin.
Sanda ta tsaya a gaban madubi ita kanta tayi mamakin yadda kayan suka karbeta,suka dace da fatarta,a gurguje ta shirya,ta sanya takalmanta ta kuma yi rolling silk vail din dake mahadin kayan,take ta qara wani kwarjini sosai,saidai gaba daya ranta a jagule yake,hakanan akwai raguwar fara'a sosai daga kan fuskarta,sam sam bata shirya yin wata tafiya ba,musamman ma ace dashi,bugu da qari ma tana ji da tsoron kada tafiyar ta shiga qarewae hutunsu a koma makaranta banda ita,batason tayi missing koda kwana daya ne,amma a yadda taga ya dauki abun serious bata da wanin sauran zabi.
Yana tsaka da waya suka fito ita da amna,gaba daya ilahirin jikinta qamshin turaren yake,turare ne daya ajjiyeshi ya daina amfani dashi,saboda yadda yake kashe masa jiki da zuciya,ta wani glass dake jikin space din da aka maqala babban plasma din ya hangota,duk da bai juyo ba amma yana ganinta tarwai,sai ya lumshe idanunsa sannan ya sake budesu,yana ci gaba da qare mata kallo ta glass din ba tare data sani ba,har suka iso inda yake bai juyo ba bare yayi alamun ya gansu,saidai duk wani taku nata akan idanunsa ta saukeshi,kusantowarsa wajen d qamshin turaren sai ya fara raba masa hankali,da coolness din nan nasa dake bayyana kansa wasu lokutan yace
"I will call you later" ya zame wayar daga kunnensa ya jefata a aljihu,ya kuma bita da hannuwansa da yake yawan sanyasu a aljihun,sannan ya waiwayo.
Yawun bakinsa ne ya kusa daukewa,gaba daya kallon daya mata ta glass din gaibu ne,yanzun yake ganin ainihin zallar reality,inda ace ita ya bawa damar dauko kayan zaice tayi da biyu ne,saidai da kansa ya dauko saboda favourite color dinsa kenan,sai gashi sun mata wani mugun kyau fiye da tsammaninsa.
Idanunsa ya aza bisa fuskarta,baby face dinta a hade babu sauran fara'a,idan ma ya kula da kyau ta sake tsuke dan qaramin bakinta data zizarawa man lebe daya sanyashi yake qyalli,sai yadan rage kaifin kallon da yake mata,ya maida dubansa kan agogon hannunsa,ko bai magana ba tasan qorafi zaiyi kan ta bata musu lokaci,ta zaci zai amsa,sai taga ya kama hannun amna sunyi gaba,dole tabi bayansa.
Ta zaci zai bata dama ta koma sashenta ta kintsashi ko ta dauko abunda take da buqata,amma sai taga baice komai da ita ba,hakanan ta bishi kamar zatayi hawaye,wannan mulkin kama karya ne da kuma qarfa qarfa,ai ba ita daya bace a gidan,me yasa bazai dauka unaisa su wuce ba?, Da wannan mitar da take tayi can qasan ranta ta qarasa motar,ta kama daya side din ta bude murfin ta shige.
Har suka isa airport bata ce ko uffan ba,yana ankare da hakan,haka kawai ya samu kansa da monitoring mood dinta,wanda shi kansa baisan dalilin hakan ba.
Sosai take kallon tsarin airport din,karon farko a rayuwarta abinda ko kusa bata taba kawowa zuciyarta zai faru a rayuwarta ba,saidai tayi qoqarin kame kanta,bata wani zarme da yawa ba,tana bin komai da lura,sai kuma abinda taga sunyi sannan,hakan ya sanya batayi wani abu daga kwafsa ba,dama kuma a idanu batayi zubin wadda zaka tsammaci ba sananniya bace a fagen,duba da jibga jibgan motocin da suka yima ja'afar din rakiya bisa jagorancin shugaban ma'aikata na kamfanin nasa.
Bayan an gama checking luggage dinsu suka amsa boarding pass sannan suke wuce gates,wannan karon amna ta dawo hannunta,dukka passingers ne dake jiran tashin jirginsu daga gomben zuwa Lagos,cikin kujerun dake wajen ta hangi jabir da fa'eemansa,tana kwance sosai ajikinsa,da alama wani abu yake nuna mata cikin waya.
Yaga jabir din amma baiyi ya ganshi din ba ganinsu tare da fatiman,miskilancin ya motsa,muryar amna tana kiran sunansa yasa ya ankara da shigowarsu wajen,da sauri fatiman ta gyara zamanta abinda ya bawa jabir daman tashi yana sanya wayar a aljihu,yayin da fatima ta budewa amna hannunta,akwai sabo tsakaninsu saboda tana da son yara fatiman,don haka ta nufeta, maimunatu ta bi bayanta,sai taji ta fara sakewa,don da alama da fatiman zasu wuce gaba daya.
*_To masu karatu, honeymoon za'a je ne ko yawon bude ido?,meye zai faru?,😂,nidai bana ce ba,ku biyoni mu qarasa bin qwaqwafin labarin tare daku_*
11/24/22, 23:35 - Buhainat: 64
Da murmushi suka dubi juna ita da fatiman,ta bata hannu sukayi musabaha sannan suka fara gaisawa,fatima na matsa mata gefenta ta zauna,amna na saman qafafunta.
Cikin mintunan da sukayi suna jiran lokacin tashinsu ta sake sabawa sosai da fatima,kamar su dauki shekaru tare,tana da sauqin qai da kuma yawan hira,ta dauki maimunatu kamar mate dinta,duk da ta bata aqalla shekaru uku,don ita ta rufa shekara ashirin,wannan yasa maimunatu ta sake sosai,suka shiga hira da fatiman,suna baiwa juna labarin makaranta,duk da fatiman ta gama secondary school,yanzun haka tana 200level ne.
Tare da fatiman suka shiga jirgin,sai itama ta duba jikin boarding pass dinta kamar yadda taga fatima tayi ta laluba seat number dinta.
A hankali take dubawa har ta iso gurin,tuni daya kujerar wadda ita ke bakin window me ita yana zaune akai,saita juya tana duban inda su fatima ke zaune,ita da amna ne seat number dinsu daya, jabir kuma da ja'afar wadanda seats daya ne suka rabasu,batasan tsarin jirgi ba,tunda ba sabawa tayi da shiga ba,don haka ta zame qaraman jakar dake kafadarta ta zauna saman kujerar bakinta dauke da bismillah.
A hankali ya waiwayo yana dubanta,matashin saurayine wanda duka duka bazai wuce shekara ashirin da bakwai ba,kana kallonsa zakasan wayewa da hutu sun ratsashi,unexpected ya ganta a kusa dashi,sai ya tashi ya zauna sosai idanuwansa a kanta,duk yadda yaso basarwa amma ya gaza,cikin muryarsa dake nuna zallan iyayi yace
"Sannu 'yammata" a hankali ta waiwaya ta kalleshi,sai ta dauke kanta tayi gyaran murya kawai ba tare da tace komai ba, shima sai yayi shurun,amma kuma lokaci lokaci yana waiwayowa ya kalleta,saidai ta basar,ta kuma tsuke fuskarta da kyau,kamar yadda ko sau daya bata waiwaya ta dubeshi ba.
Tunda ta zauna a seat dinta ya fuskanci wanda yake abokin xamanta hankalinsa ya gaza kwanciya,kunnuwansa naga jabir ne dake ta masa bayanin wasu receipt da suka biya kudin wasu clearance a wajen custom's,saidai dukka hankalinsa yana kanta.
A hankali yaji kamar ana matsa zuciyarsa sanda ya fahimci saurayin yana yawan juyawa yana kallonta,ya dinga qoqarin dannewa da kuma kauda hankalinsa amma sai ya gaza,agogon hannunsa ya daga ya kalla,akwai awa kusan biyu a gaba kafin jirginsu ya sauka a lagos,sai yaja wani dogon tsaki,abinda yaja hankalin jabir kenan,sai a sannan ya fahimci bama fahimtar bayanin nasa yake ba,yakai idanuwansa inda ja'afar din ke kallo,sai a lokacin ya gane abinda ke faruwa,cikin taqaitaccen lokaci jabir ya qare masa kallo,hatta zamansa bai zauna properly ba,kamar wanda taushin kujerar bai masa ba,amma da alama duka bai fuskanci hakan ba shi.
Gimtse dariyar dake son qwace masa yayi,ya buda baki zaiyi magana dai dai lokacin ja'afar din ya dunqule hannunsa ya buga a hannun kujerar da yake kai
"It can't" ya fadi yana miqewa zumbur,ya taka a hankali ya fito daga inda yake ya nufi wajensu.
Cikinsu ba wanda yasan da wanzuwar tasa a wajen,dai dai sanda saurayin ke qoqarin miqa mata tissue ganin ta rufe bakinta atishawa nason fita,ido hudu sukayi da ja'afar dake tsaye a kansu,ya goye hannuwansa a qirjinsa ya zuba masa wannan idanun nasa dake saurin ladabtar da kowa,wasu kibiyoyi da baisan suna fita a idanunsa ba nata spark.
Sosai kallon da yake masa ya dakeshi ya kuma yi masa kwarjini,sai ya janye tissue din bakinsa na subucewa da cewa
"Lafiya?" Cikin fargaba tare da tunanin qila matar aure ce kenan,tunanin da baizo ransa ba sai a lokacin,maganar da yayin tasa maimunatu daga kanta,suka hada ido,sai ya mata inkiyar ta tashi,yayi gaba,ta miqe tana sake saqala jakarta ta biyo bayansa.
Kafin su iso jabir har ya miqe yabar mususeat din,dariya kaman zata kasheshi,ya koma inda ta taso din,saidai koda hakan shima ya taya J dinsa kishin da yaketa qaryata kansa bashi yakeyi ba,ya dubi matashin
"Ku dinga hankali da matan mutane" ya fada yana jifansa da wani kallo me kama da harara,don shi din dama yafi ja'afar magana.
Shi daya ya dinga quncin rai,yaja tsaki yafi a qirga,ita dai bata dashi komai ba,har awannin da suka rage musu ya cika jirgi yayi landing a lagos cunkus dakin tsumma.
Motar kamfaninsa ta nan lagos ce tazo daukarsu wadda aka tanadar masa saboda irin haka dama sauran mamyan baqi da sukeyi daga qasashen waje abokan kasuwancinsu,already jabir ya musu booking na dakuna a daya daga cikin five star hotels,wanda kuma yafi kusa da inda sukazo duba ayyukansu,ciki da falo ya kamawa su ja'afar saboda amna,shi da fatinsa kuma single room.
To tun saukarsu lagos basu samu zama sosai ba,idan motar company tazo ta saukesu tun safe sai dare,wannan ya bawa su maimunatu damar yawo sosai cikin garin lagos,jabir yasa wata motar daga company musamman take zuwa duk sanda suka gama shirinsu ta daukesu tayita zagayawa dasu guraren shaqawatawa kala daban daban,ya tura musu enough kudi ta account din fatima,ga kuma bandir da J ya ajjiye mata itama,basu da wata matsala ta komai,duk yadda maimunatun tayi tsammanin ba zataji dadin tafiyar ba sai abun yazo mata akasin hakan,taji dadin garin fiye da zatonta,sunyi yawo sosai,hakanan fatima ta musu siyayya mai yawan gaske,musamman maimunatu da batazo da wasu kayan ba,saidai kuma ita fatiman kusan duka qananun kaya ne siyayyar nata,sai sakakku da zata iya fita dasu cikin gari,don haka maimunatu ta ware kowanne jaka daban,wandancan da takejin ba zata iya fita dasu ba,da kuma wadanda zata iya sakawa.
Duk yadda garin ke mata dadi amma bata mance da lissafin lokacin komawarsu makaranta ba,sunyi waya da afrah itama tana sake tuna mata
"Allah ya nuna mana,amma bana gida ma,muna lagos,kuma banga alamun dawowarmu ba" dariya sosai afra ta sake
"Wannan abu yayi min dadi,tsuntsun soyayyar ya fara sauka kenan,honeymoon aka tafi ne?" Kamar tana gabanta saita saki harara
"A'ah milkmoon aka tafi,tare fa muka tafi da amna,harda su fatima"
"To sai me?,bikin magaji zai hana na magajiya ne?,amna ina ruwanta?,zatafi kowa son a bawa daddynta kulawa,fatima kuwa na tabbatar saidai ta tayaki,kuma nasan ba daki daya kuke ba,kidai zauna garin kallon ruwa kwado yayi miki qafa"
"Mtsweew,Allah ya shiryeki afrah,gwara hajja tayi miki aure ta huta"
"Wallahi ko gwara a aurar dani a huta,idan ba haka ba......."
"Ba'a kunne na zaki qarasa wannan zancan naki ba,ya girmi kunnuwana" saita datse wayar tana dariya.
A hankali ta aje wayar a gefanta
_ki tsaya dai kallon ruwa kwado yayi miki qafa_,wai me yasa kowa maganarsa kan ja'afar ne,kowa kusan abinda yake fadi mata kenan idan irin wannan zancan ya hadusu,sai ta sauke ajiyar zuciya,idanuwanta na hango mata kalar soyayyar jabir da fatima,wata irin soyayya me nuna zallar kulawa da kuma shaquwa,ita kanta abun yana burgeta,sau tari idan ya kirata bayan ya fita tunda yawancin lokutta suna tare,sai tayi kasaqe tana sauraren kalar hirarsu,ta fahimci ita kanta fatiman ta gano kalar zamansu,don wani lokaci ta taba cewa da ita
"Shi namiji da kike gani,babu abu mai sauqi wajen sarrafawa irinsa,sau tari dama suke nema ko jira ka basu,mijinki ko?,hmmmmmm,astagfirullah,soyayyarsu ta dabance,duk sanda suka tashi nunawa mace soyayya za'a sha mamaki,saidai suna da wani irin aji da kamewa,wanda zaisa ki gaza fahimtar inda suka dosa" ajiyar zuciya ta sauke tana gyara kwanciyar rub da cikin da tayi saman kujerun falon,amna na daki tana bacci,dama a ciki suke kwana ita da ita,shi ya canjesu a falon.
Qarar security na jikin qofar taji,kafin kuma ta ankara an murda handle din an turo qofar,sai ta daga kai da sauri don ganin wanda ya shigo din,saboda ta san wannan ba shine lokacin dawowarsu ba,zata iya cewa tun zuwansu tsahon kwanaki takwas yau,sau uku kawai suka hadu ita dashi,tana qunshe a daki sanda zai fita,kafin ya dawo ta tattare tayi kwanciyar barci abinta.
Tun kafin ya saki handle din idanunsa ke manne a kanta,wata gown ce a jikinta ta wani material maras nauyi,wannan yasa kwanciyar rub da cikin da tayi ya bayyana mazaunai da qugunta sosai.
A hankali idanuwansa suka kai kai,ya lumshe idanunsa tsigar jikinsa na zubawa,sai ya juya ya maida qofar ya rufeta,sannan ya soma takowa cikin dakin bakinsa dauke da sallama.
Tuni ta miqe ta zauna kanta a qasa tana wasa da yatsun hannunta,itakam dawowarsa a yanzun kamar takura ce a wajenta,dole saidai ta koma daki tayita zama
"Sannu da zuwa" ta fada a hankali tana miqewa tsaye duk da bataji ya amsa ba,taku biyu tayi taga ya babbake gaba daya hanyar wucewarta,idanuwansa a kanta,yau din kallonta tsakiyar idanuwanta yake kansa tsaye,ya karkatar da wuyansa gefe daya yana son hukuntata da idanun kamar yadda ya saba
"Am...zan zan wuce" ta fadi muryarta nadan rawa,saboda jiki da zuciyarta da taji sun fara amsawa
"Idan naqi fa?" Ya amsa mata yana hade fuskarsa,mamaki amsar da ya bata ta bata,sai ta dan tsuke bakinta kadan kafin ta sakeshi,idanuwansa suka kai kai,ya sake jin wani abu na sauka a dukka sassan jikinsa,yana kuma gauraya da