Showing 78001 words to 81000 words out of 194226 words
taba haduwa da yarinyar ba,basu taba gamuwa ba,ko yaya take?,tana ina yanzu oho?,taja wata qwafa kamar zata cire harshenta sanda zuciyata ta raya mata ace dai taje ta sameta tare dashi.
Har tsakiyar zuciyarta falon nasa ya tafi da ita,akwai wani yanayi na musamma tattare dashi,taci gaba da takawa a hankali ta nufi bedroom dinsa kai tsaye,saidai kuma kamar yasan wani zaya shigo masa,yana shiga kafin ya shiga wanka ya murza key,tana taba handle din ta gane hakan,dole ta koma saman kujerun alfarma dake falon,ta zauna ta dora qafa daya saman daya bayan ta kunna tafkekiyar tv dake falon,takuma canza tasha zuwa mbc Bollywood,ta samu kuwa suna wani film me kyau,saita maida hankalinta a kai,yayin da wani sashe na zuciyarta kuma yaketa wassafa mata yadda zai tarbeta,duk da tasa a ranta ba zata samu tarba me kyau dari bisa dari ba.
Cikin jallabiyya Morocco's male abaya me ruwan gold mai gajera hannu ya shirya bayan ya fito daga wankan,duk da baici abinci ba amma sam baya jin yunwa,muryar amna yakeson ji,yayin da wani sashe na zuciyarsa kuma a yau yake cike da kewar shaheedansa,ya feshe jikinsa da lallausan turaransa bayan ya gama gyara sumarsa dake samun gyara na musamman,ya dauki wayarsa ya danna kiran number ammansa.
Bugu biyu aka daga,salma ce,ta shaida masa amman tana wajen abbi,sai ya nema ta hadashi da amna,ta kuwa hadasun,yarinyar ta dinga masa hira sosai,abinda yasa ya samu relief daga abinda yakeji kenan,yadan sake shima yana tayata.
Ya kusa minti talatin tare da ita,ya samu sauqi sosai cikin ransa,harma ya samu qwarin gwiwan jin son shan coffee,don haka ya diba takardun da zai duba da system dinsa ya nufi falon.
Janye idanunta tayi daga fuskar tv din tana sakin murmushi,jarumin film din yana mata mugun yanayi da J dinta,yadda ya iya soyayya ta tabbatar J zai iya finsa,saidai shawo kansa da qwato hankalinsa abune mai wahala ta sani kuma,dai dai sanda take shirin sake maida idanunta ga film din,sai suka sauka ga babban hoton shaheeda dake rataye cikin falon,zuba ma kyakkyawar fuskarta idanu tayi,murmushin da take a cikin hoton tajiyana tabata,sake waiwaya tayi wani sashe still hotonta ne ita da twins dinta amna da amra,daga daha bangaren kuma shi da ita ne,sunyi masifar kyau cikin qananun kaya,karon farko data fara ganin wani abu me kama da murmushi saman fuskarsa,yana rungume da ita ta baya,da gani ba'a qasar nan aka dauko hoton ba,yana sanye da uniform da matuqan jirgin sama,kyau iya kyau yayishi,uniform din sun karbeshi matuqa da gaske,hoton ya fusgi hankalinta,ya kuma saka kishin shaheeda mai yawa cikin ranta,har sai data miqe ta isa ga hoton dake can wani kusurwa na falon,ta tsaya a gabansa tana sake qare musu kallo.
Da farko daya fito bai lura da ita ba,sai daya kusa isa inda ya ajjiye na'urar hada coffe dinsa take,yadan tsaya kadan,kamar zai magana sai ya fasa,ya isa inda coffee maker din yake,ya soma hada abinsa,saidai abun mamakin har ya hada ya dawo ya zauna saman kujera bata ankara da wanzuwarsa,abunda yayi masifar bashi haushi,saidai zaiga iya gudun ruwanta da nata qwaqwqwafin da kuma sanya idon.
Hannu ta sanya zata daga hoton don ganin date din jiki sosai
"Don't dare touch it" ya fada da kakkausar muryar data ankarar da ita yana wajen,tadan zabura kadan tana juyowa,idanunta suka sauka akansa, sipping coffee dinsa yake hankali kwance,idanunsa kan tv din daya sauya tasha zuwa ta news,kai baka ce da ita yake magana ba.
Wani mugun kyau yayi mata,sai ta dinga jin inama ace zai rungumeta,ko ita ya bata wannan damar?,qoqarin dai daita kanta tayi,sannan ta fara takowa cikin salo na canjin tafiya zuwa inda yake zaune
"Welcome home" ta fada tana sakar masa murmushi,saidai kuma abun haushin,baiko kalleta ba bare ya fahimci kwainanen da takeyi,hasalima tambaya ce ta biyo baya
"Who gave you permission to enter my room?" Tambayar data sanyata yin sak,kafin kuma ta saki murmushi tana ci gaba da takowa
"am your spouse fa,mene ne a ciki?" ta fada tana isowa dab dashi,shirinta shine ta zauna daura dashi din.
Idanun nan nasa masu matuqar nauyi da kwarjini ya daga ya watsa mata su,abinda ya sanyata tsaiwa ta kuma kama kanta,bata sake gigin yunqurin zama kusa dashi ba yadda taso a baya,kamar bai shirya yin magana ba,saidai zuciyarsa tana gaya masa,ita kadai ce a yanzu zata zame masa damuwa cikin gidan baiyi wasa ba,itakam waccan bashi da damuwa da ita ya tabbatar,don ya gama da babinta,unaisan ke kallon kanta a ta cika macen da zata kutso kai tayi tarayya dashi cikin rayuwarsa,abu mafi wahala da tsada da diya mace ke nema ko ta samu daga wajensa,yana jin komai nasa kebantacce ne na musamman
"Am warning you for the second time,stay away from me,banason kutse cikin al'amurana,Live your life,I live mine,banason kutse cikin al'amurana,ki kiyaye" ya fada da sautin dake nuna gargadi mai qarfin gaske.
Har cikin zuciyarta maganganunsa suka soketa,tanason ta maida masa raddi amma kuma ya mata kwarjinin da ko bakinta ta kasa motsawa
"Am saying in respect, get out of my room" ya fada with his husky voice.
Jikinta a sanyaye ta fara takawa zuwa bakin qofa,gefan ranta a quntace,sai ya ajjiye cup din idanunsa na sauka kan tray din data ajjiye,ya janyo wata qaramar dawer daga jikin kujerarsa,wadda ba kowa ne zai kula da ita ba,ya ciro kudi kusan adadin wanda ya baiwa maimunatu ya dora mata a kai,sannan yace
"Dawo ki dauke kayanki" cak ta tsaya,kamar ba zata dawo din ba saboda yadda qwalla ke neman cika mata ido,to amma ba zata iya tafiyar ba,saboda yadda muryarsa ke iya canza duk wani nufi naki,ta dawo ta dauka din kamar yadda yace sannan ta fice.
Cup din ya dangwarar a wajen,yana furzar da iska daga bakinsa,shi kansa yana jin baiyi dai dai ba,amma kuma hakan shine dai dai a wajensa,gwara tun wuri kowacce a cikinsu tasan cewa bata da gurbin zama cikin rayuwarsa,yafi kyau ya nesanta kansa dasu akan ya sake musu su sanya ransu a kansa.
Tun a falonta ta watsar da komai suka tarwatse sukayi nasu waje,ita kuma tayi daki da sauri tana sakin kuka,wayarta ta laluba,ta kuma kira anty talatu,kukantanya daga mata hankali sosai,don da qyar ta iya ta mata bayanin abinda ya faru.
Murmushi anty talatun ta sake,alamun hankalinta a kwance yake
"Hmmmm,yaro man kaza,ke haka kike unaisa?,baki da haquri?,ga shegen gaggawa?,daga fara wasan saiki saare?,waya gaya miki abu mai daraja da tsada yana samuwa ta sauqi haka?,in just a minutes amma kin gaza?,haka zaki nunawa kishiyar taki har ta fuskanci kema kin kasa?,to kiyita kukan,idan kin gama kya kirani na fada miki abinda zan gaya miki" sai ta kashe wayarta,itama bata sake kiran nata ba,sai data gama kukan nata,ta kuma huce sannan tayi kiran nata.
********Cikin kwanakin ya maida kansa busy qwarai da gaske,duk wani tunani nasa da kulawarsa na ga companies dinsa dake nan gombe kano da kuma lagos,kusan tun daga ranar yama mance dasu cikin lissafin rayuwarsa,basu kuma sake haduwa da kowacce a cikinsu ba,kamar yadda suma kowacce rayuwa take a sassanta ba tare da 'yar uwarta ba,duk da cewa sau tari maimunatu takanyi kamar ta leqa su gaisa da unaisan,amma kuma sai taji tsoron yin hakan,musamman idan ta tuna da me gidan kansa
"Qila itama irin halinsa ne da ita" abinda zuciyarta take raya mata kenan,saita juya ta koma.
Daga gidan dr marwan ake kawo musu abinci kullum,safe rana dare babu gajiyawa,kullum maimunatun ke amsa,ta kuma barshi saman dining na main parlor na gidan idan ta diba yadda zai mata,wanda yawanci ma idan ta diba na rana ita shike kai mata har dare,bata sake neman wani kalar abincin.
Ba kasafai yake dawowa gidan da wuri ba,yakan kai tara ko goma,kuma daya dawo ya haye samansa yake rufewa,idan ba wani babban uzuri ba baya saukowa sai washegari,takwas na safe ya fice sabgoginsa,saidai lokaci lokaci yakan sauko ya duba cikin gidan ko akwai wata matsala,sai ya tabbatar da babu wani abu da ake buqata sannan ya sake komawa,a hakan suka kwashi sati biyu cur,a ranar suka tashi shuru babu saqon abinci,dama kuma maimunatu ta tsammaci hakan,don haka qarfe sha daya saura bayan tayi wanka,ta danyi gyare gyarenta cikin daki wanda basu da yawa,tayi wanka ta shirya kanta cikin wata army green din atamfa me maroon din ado saita fita zuwa kitchen don samawa kanta abinda zata saka a bakinta.
Ruwan tea ta dora,ta kuma hada kayan qamshi kamar yadda ta koya daga wajen baba tabawa,sannan ta juya ta laluba dankali ta debo bayan ta kwashe wadanda suka lalace saboda kwanakin da suka dan dauka ba'ayi amfani dasu ba,ta dauko qwai guda biyu ta fara aikinsu.
Tana aikin tana kuma tunane tunane,abinda ya zame mata jiki,a zaman kwanakin da tayi cikin gidan,zaman kadaici,da za'a irga adadin tunanin da tayi zata tashi wani dan qaramin littafi,ta saqa burika masu yawa da takeson cimmawa a rayuwarta,wadanda bata da tabbas din wanzuwarsu,tunda dai bataga hanya ko qofar da hakan zata kasance ba,nan din tana wani zama ne kwatankwacin zaman mutumin da aka kai prison.
Bata dauki lokaci ba,ta gama komai,tuntuni ta juyr tea din a flask,dankalin kuma ta zuba akwando don ya tsane,ta matsa gaba tana neman plate da zata xuba,tana ta kokwanton ma zata iya cinyeshi kuwa.
A dan hanzarce ta turo qofar kitchen din saboda wata mahaukaciyar yunwa dake sakadar cikinta,ta duba saman dining inda kullum take tadda abinci ta diba ba tare data damu da wanda ke girkawa ba.
Motsinta ya sanya maimunatu dake dauko plate dakatawa ta waiwayo,idanunsu suka hadu waje guda lokaci guda,lokaci na farko kenan da kowacce taga 'yar uwarta,kuma kowacce a cikinsu jikinta ya bata.
11/24/22, 23:25 - Buhainat: *HUGUMA*
34
*Arewabooks chapter 39*
https://arewabooks.com/chapter?id=63637876d52c9563f3289fda
_______________________________
Wani kallon qurilla me dauke da mamaki da kuma fargaba unaisa ke bin maimunatu dashi,zuciyarta na qiyasta mata wannan ce maimunatun?,wannan itace kishiyar tata?,yarinyar da duka duka bata wuce qanwarta ta uku biyu ba?,a qalla zata iya bata good five years,wannan zata kalla a matsayin kishiya?,no saidai ta dauketa tamkar 'yar aiki,amma kuma...... she's very beautiful,tana da wani irin kyau daya daki zuciyar unaisan,kyan da idan tace maimunatun ma 'yar aikinta ce ba shakka babu wanda zai yarda,don yarinta kam yarinya ce,amma batun tace 'yar aikinta ce ma bata taso ba,kyan yarinyar ya daketa,ya kuma tsole mata idanu tun daga kallon farko,abinda ya hanata sukuni,ko bayan data qarasa kitchen din tayi abinda zatayi ta fito,wanda gaba daya ruwan zafi ta iya dafawa ta juye a cup ta hada tea ta dauki five slices of bread ta hada dashi ta fita.
Ji tayi sam bata jin taste na tea din,sai ta aje ta dauki waya ta kira anty talatu,ta kuma rattaba mata komai
"Keba macace bace?,meye na daga hankalinki?" Ajiyar zuciya unaisa ta saki
"Ba zaki gane bane anty,ni da nake mace ma kyanta ya tabani,ina ga da namiji?" Murmushi me sauti ta sake
"Bakisan namiji ba kenan,shi kam idan zuciyarsa ta qyasa da abu babu ruwansa da kyansa ko muninsa,abu daya ne da zakiyi shine ki kama zuciyarsa da kyau ta duka hanyoyin da suka dace,ba da bakinki kike gayan tafi marigayiyar matarsa kyau ba?" Kai ta gyada kafin tace
"Haka ne anty"
"To amma me yasa wannan kyan bai sanya ya sota ba har yanzun zuciyarsa naga marigayiyar?" Tambayar da tun kafin ta amsawa kanta ita taji gamsuwa
"Exactly"
"Da kyau,abu daya ne yanzun zakiyi,ki tabbatar kawai yarinyar bata sake cikin gidan ba,duk yadda zakiyi ki nuna mata a qasanki take,matsayinku kuma ba daya bane,wanna zaisa ta kasa kallon kanta a matsayin cikakkiyar mace da har zata maida hankali wajen ganin tayi tarayya dake akan mijinku,sannan kinfinkowa sanin daga inda ta fito,bata da cikakkiyar wayewar da zaki kasa juyata yadda kikeso,cikin ruwan sanyi zata zame miki kamar qasqantacciyar 'yar aikin ba tare da ta ankara ba" dukka wadan nan maganganun na anty talatu dama wadanda suka biyo baya sunwa unaisa dadi,sai ta saki jikinta suka sha hirarsu,tana sake bata haske game da wasu abubuwan.
Cikin zuwan da yakanyi gida wasu lokutan idan ya tashi a aiki da wuri anni tace ya kawo unaisa da maimunatu su gaida surukansu,hikimar hakan kuwa,tayi ne don taga kamun ludayinsa da kuma yadda su din suke zaune,don tun daga washegarin randa aka kaisu ba wani dan gidan daya sake komawa gidan nasa.
Baya buqatar magana da kowacce a cikinsu,baisan ta yadda zai sanar musu su shirya ba,don haka sai kawai ya sanya driver ya dauki laila yace ya kaita gidan su taho tare,shi kuma ya wuce aikinsa abinsa.
Kamar a mafarki maimunatu taga lailan,ta saki ihun murna ta rungume lailan duk da baqunta da rashin sakin jiki irin na maimunatun,sanda ko ta gaya mata inda zasun ji tayi kamar anyi mata bushara,sati na uku nason cikewa ko farfajiyar gidan bata qara leqawa ba tun randa sukazo tayi musu rakiya,nan da nan ta hau shiri,kafin ma unaisa ta gama laqai laqai dinta ita ta gama shiryawa,cikin wata jar atamfa data haskata sosai.
Duk inda maimunatun ta motsa laila na binta ne da ido,tayi wani fresh sosai,fatarta kamar babu abinda yake hawa,saidai kuma babu wata qiba ko murmurewa da tayi,kuma tana da tabbacin inda maimunatun ta qara qiba lallai zama zatayi abar kallo,don komai na jikinta ya soma cika da alamun girma da budurci tare da kwarjini na aure.
Sanda suka fito zasu wuce laila ta leqa yiwa unaisa magana,sai ta sameta bata ma shirya ba
"Kaina kemin ciwo,kice ina gaishesu,zan sanya lokaci sai mu shigo ji dashi" amsar data bawa laila haushi matuqa,ta kuma fito tana mita,wannan ai tsabar rainin wayo ne,ita dai mainunatu batace komai ba,daga bisani ma sai ta janyo mata hirar islamiyya,wadda takejin kewarta qwarai da gaske,tana jin inama za'a barta taci gaba da zuwa,tana jin rashin dadi kan yadda haddarta ta tsaya cak,duk da tana tilawa a gida.
Tsaki unaisa taja bayan jin tashin motarsu,me suka maidata ne?,ko sun manta matsayin ubanta a qasar nan,banda soyayyar da takewa J da ta yaya ma zata zauna a inda take yanzu?,ta yaya zata yarda ta hada kishi da wata bafulatanar ruga?,idan gaisuwar surukai ne ai basai ta hada kafada da 'yar qauyen yarinyar ba,cikin motocinta zata ja daya takai kanta gidan idan fa shirya gaishesun basai an mata jagora ko an tusata a gaba ba.
Sai data shiga ta gaida amma da ammi sannan ta yada zango wajen anni,annin na karance da maimunatun sarai duk da ita bata fahimta ba,ta kuma samu gamsuwar gabatarwa da ja'afar qudurinta,don haka sanda yazo washegari gidan,akaci sa'a safiya ce,saboda yau din da yunwa ya tashi,don jiya bai samu tsaiwa yaci abinci a inda ya saba tsaiwa cin abincin ba
"Makaranta nakeso ka dauki maimunatu da kanka ka sanyata" ta bashi umarni nakai tsaye idanunta a kansa sanda yake zaune gabanta amna na saman cinyarsa yana bare mata chocolate.
A hankali ya daga kansa zai kalleta,sai ya samu itama shi take kallo,ba tun yau ba,yasan anni sarai,yasan kuma tunda ta tada zancan nan akwai abinda ta taaka,kamar zaice wani abu sai kuma yace
"Ba damuwa" a taqaice,yadda yayi saurin amsawar ya bawa anni mamaki,ya kuma tabbatar mata akwai wata a qasa,kuma ruwa baya tsami banza,amma kuma zata zanya idanu taga me zai aikata
"Idan ka tashi ka hada mata da waya,don ya kamata ace tana waya da 'yan uwanta,bawai don ta taho ta taho kenan ba"
"To" ya sake cewa da ita
"Kiyi picking ledojin chocolates din ki biyoni mota zaki rakani unguwa" yace da amna bayan ya sauketa daga kan cinyarsa ya kuma miqe,ta sauka kuwa da sauri tana murna,ta hau tsincewar tana ta yiwa anni da ta bishi da kallo surutu,hankalinta bai kwanta ba,tasan halin ja'afar itama,wannan saurin amsawar da yayi ba'a banza ba,amma koma meye ya shirya yi,indai cutuwa ne ga maimunatun ba zata bari ba.
Shegen miskilanci gami da zurfin cikinsa yana nan har yanzu,yana da wannan nuna shakulaton bangaron kan abubuwan da yana sane dasu sarai,suna kuma cikin ruhi da zuciyarsa,amma sai yayi kamar bai damu ba,kamar baya ankare da abun,kuma kamar baya gani,saidai duk randa ya magantu ko ya dauki wani action akai kowa zaiyi mamakin hakan,wannan ya sanya anni ta sake sanyama ranta zata kula da komai da irin abinda zai biyo baya,ta sauke ajiyar zuciya tana hade hannayenta waje daya,fuskantar ja'afar ko yin gaba da gaba wajen saukeshi daga ra'ayinsa ya zuwa wani babban aiki ne da ba kowa zai iya shi ba,fatanta ubangiji ya dubesu,rayuwarsa ta sai saita,ya kuma riqe amanar yaran mutane kada suji kunya.
*********Kwanaki anni tayita qirgawa tana jiran taji yace wani abu,ko kuma ya tanka game da maganar da sukayi da ita,saida har ta gama irga kwanaki bakwai baice komai akan maganar ba.
A daren ranar ya koma gida da wuri kai tsaye daga wani gidan saukar