Showing 159001 words to 162000 words out of 194226 words

Chapter 54 - GURBIN IDO COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

12 Dec 2024

26163

ainihin falon gidan,idanuwanta suka ci karo da hotunan shaheeda dana amna da amra,tamkar tana raye,sai taji zuciyarta na karyewa a hankali,tausayin amna yana tsirga mata,jikinta yayi sanyi sosai,dan adam ba'a bakin komai yake ba,kamar zaka kirata ta amsa,kamar zata tashi taci gaba da rayuwa a gidanta.

Wani sashe na daban suka bulla,kallo daya tayi ma sashen tasan bangaren mai gida ne,falo biyu suka ratsa sannan suka isa ga makeken bedroom dinsa.

Aljannar duniya shi yafi dacewa a kirasa,komai yana nan a muhallinsa fes dashi,hatta da ac din dakin a kunne take tana aikinta,ana kula da gidan sosai,don akwai amintattunsa da yake sanyawa duk bayan kwana biyu su shiga su gyara har bedroom din

"Ki zauna ina zuwa" ya fada yana wani shan qamshi,sannan ya fice yana jan qofar dakin.

Sai data gama qarewa dakin kallo tsaf sannan ta taka zuwa saman sofa bed din ta zauna,idanuwanta suna qarewa dakin kallo,very neat and clean,idanunta suka sauka kan tarin takardun sake saman gadon gefe guda,tayi mamaki don dakin fes yake,su kadai ne a wajen,batasan ya akayi ba ta miqa hannu ta debosu ta fara dubawa.

Hotunan shaheeda 'yan biyunta da kuma ja'afar dinne,sunyi masifar kyau,ahali me kyau da daukan hankali,tana kalla tana sake jin wani abu yana tabata a zuciyarta game dashi,yadda ta ganshi cikin hoton ya gaya mata he's nice and friendly to his family,daga hoto na qarshe sai wani dan littafi dake dauke da sunan my dairy.

A hankali ta soma buda shafin farko,a nan ta gane na shaheeda ne,sai taci gaba da budewa tana karantawa,tun batayi nisa ba ta fuskanci duka akan ja'afar tayi littafin sanda tana raye,da farko ya zame mata kamar novel,ta dinga karantawa yana debe mata kewa da kuma sakata murmushi,halayensa abinda yafiso da wanda bayaso,yadda fushinsa da walwalarsa take

"He's arrogant and very annoyed person sometimes,but hes the best husband i know in the planet" murmushi ya kubcewa maimunatu,sai taji kamar gata ga shaheeda take gaya mata hakan,girarta ta dage

"Na shaida hakan" ta fada a fili,sannan taci gaba da bin rubutun tana fahimtar kowanne zance da yake ciki,daga bisani kuma labarin ya fara tabata,har zuwa sanda tayi rubutun ta na qarshe,wanda akan amna da amra tayi.

Kasa riqe kanta tayi,kuka ya subuce mata sosai,ba abinda take tunawa sai daadarta da kuma abbanta,tausayin amna kuma na sake sarqafar zuciyarta,qaunar yarinyar na sake shiga zuciyarta.

Sai da kukan ya lafa mata,duk da hawayen baibar sauka ba sannan ta daga kanta tana maido da littafin shafin da shaheedan ke bayyana halaye da dabi'un ja'afar din,ta dora hannunta a kai tana sake maimaita wajen.

Ko kusa bataji motsi ko alamun shigowar sa ba,har sai da taji ya sauke wata ajiyar zuciya mai qarfi,ta daga kanta da sauri tana dubansa,shima ita yake kalla,idanuwansa sun kada sun canza kala,da alama wani abu ya taba zuciyarsa sosai.

A hankali tayi yinqurin hade littafin ta rufe,bakinta yana fadin

"Am sorry,kayi haquri" tausasan hannayensa yasa ya riqe hannunta ya dakatar dasu daga qoqarin rufewar da takeyi,sannan ya zare littafin yana duba saqonni wajen da yaga tana karantawa,sake daga kansa yayi ya kalleta,sai ya zame shima ya zauna kusa da ita sosai har jikkunansu na gogar na juna,ya kuma sanya littafin atsakiyan su,kamar masu bitar karatun jarabawa,yatsansa tabi da kallo zuwa wajen da ya dorasu

_bana jin a duniya za'a sake samun wata macen da zata soshi ta kula dashi kamar yadda nake sonshi_ abinda paragraph din ta qunsa kenan,tana kaiwa nan ta tada kanta tana kallonsa,shima sai ya sanya qwayar idanunsa a tata,suka shiga kallon kallo,a hankali ya maida littafin ya rufe,ya aje a gefansa,sannan ya kama fuskarta ya saka a tafin hannunsa,ya hade fuskokinsu waje daya,suka fara musayar numfashi.

Shuru ya ratsa a tsakaninsu,ba komai dakin sai qarar ac dake kadawa da kuma qananun motsi daga harabar gidan

"Wataqila an gama samun macen da zata soni ko?" Ya yiwa maimunatu tambayar da batasan amsarta ba,sai tayi shuru tana saurarensa,sai kuma ya zame fuskarsa a hankali,ya kama hannunta ya dora saman qirjinsa,ya danne hannun nata da tafin hannunsa.

Wasu abubuwa ne suka bi ta jininta zuwa gangar jiki da qwaqwalwarta,jikinta ya saki tsigar jikinta ta zuba,duk sanda jikinsu zai hadu sai taji zubawae tsigar jikinta

"Bansan yadda zan canza kaina ba wajen daukan duk abinda zuciyata ta gamsu da ta soshi da mugun muhimmanci ba,na rasa shaheeda,amma bansani ba ko zan samu maimoon?" Ya qare tanbayar yana ritsata da kallonsa.

Gaba daya taji wani rauni ya cikata,karon farko da tausayinsa ya mamayeta,ko bai gaya mata ba tasan zuciyarsa na cikin wani yanayi na kwashe kayan da yau akayi bayan wasu shekaru,tasha jin labarin yadda ya hana a taba komai din,amma yau karon farko babu shiri ya yarda,sai ta buda bakinta a hankali zatayi magana.

Tsoron jin negative answer daga bakinta ya sanyashi hanata cewa komai,sai kawai ya riqe fuskarta gam,ya kuma kai bakinsa ya hade da nata.

Da dukka zafin da yakeji a zuciya da gangar jikinsa yayi amfani ya soma sauke mata hot kisses,kafin daga bisani yanayinsa ya sauya,tsiminsa da yaketa qoqarin dannewa ya motsa masa,sai kawai labari ya canza,wasan ya sauya salo,kwanyarsa ta fara barin wancan tunanin izuwa wata kyakkyawa kuma ni'imtacciyar duniya.

Kamar wancan lokacin ta karba saqon yadda ya kamata,har ta kasa aiwatar da komai,saidai kuma sanda yayi yunqurin isa waccar duniyar da yake muradi da kuma marari sai ta shiga tsoro razani da fargaba,amma yayi nisan da baisan me take fada ba,fatansa kawai ya dangane da inda ya hara din.
11/24/22, 23:35 - Buhainat: 73

Kamar wancan karon,wannan karon ma ta dandana kudarta,duk da bai qarasa gamuwarsu ta farko ba amma taji a jikinta,harshi kansa yayi tunanin anya ya gama bude hanyar wancan karon kuwa?,rashin ganin jini yasa ya fahimci wancan karon ya kammala aikin nasa,wataqila ita din irin matan da sai a hankali suke gama samuwa ne.

Wannan lokacinma shi yayi barnarsa ya kuma shiga gyara,hawaye kawai takeyi tana jin yadda yaketa bata haquri gami da jero mata sannu,can qasan ranta tana mamakin yadda duk sanda hakan ta faru yake zama wani iri,kamar wanda ya aikata mummunan laifi,saida data tuna dabi'ar tausayi da shaheeda ta zayyanar akansa,sai mamakin nata ya ragu.

Yadda ya dinga kula da ita yasa ta sassauta qananun kukan da take masa,zazzabi yaso rufeta yau din ma,amma kuma ya hana afkuwan hakan ta hanyar bata paracetamol,ya kuma lullubeta a qirjinsa kamar first night dinsu,suka sha baccinsu sosai bayan sun hada azahar da la'asar data riskesu a farkon lokacin shigar mukhatarin la'asar din.

Basu tashi ba sai bayan magrib,ya sake wanka sannan ya hada mata itama,yace zaije yayi sallah ya dawo,haka ya fita yana waigenta kamar zata bace masa.

A inda ya barta a nan ya dawo ya taddata zaune,qarasowa yayi

"Lokacin sallah fa" idanunta fal da qwalla tace

"Bazan iya tashi ba....waj....wajen akwai zafi" sumar kansa ya shafa da kyau yana fadin
"oh sorry" ya tako a hankali zuwa inda take din,tsugunnawa yayi a gabanta kamar me shirin yin kneel down,ya kuma kama kunnuwansa da hannayensa guda biyun

"Laifin abban amna ne,a yafe masa" nauyi sosai ya aza mata ganin yadda ya zube a gabanta,sai ta boye kanta a kafadarta,tana jin ba zata iya hada ido dashi ba

"Yes,na gaji da ganin amna a haka,she needs a sister...."

"Na yafe" ta furta da sauri don kada yaci gaba da fadin maganar da fadin maganar da bazata iya dauka ba,murmushinsa dake bata mamaki da kuma jan hankalinta ya qwace masa,sai ya faki idanuwanta yayi wuf da ita sai bandaki.

Yanzun ma shi ke tayata,duk da yadda take noqewa,kusan dai shima sabon wanka ya sake sannan suka dawo dakin,ya saka kayansa da sauri saboda jun bell tana kadawa ya fita ya barta a wajen bayan ya nuna mata inda zata samu kayan sawa.

Dukka side din sabbabin suturu ne na mata,ta fidda guda ta saka,tana jin jikinta ya mata dama dama,sannan ta janyo wayarta data hanga qasan gado ta kunna,low battery ta nuna mata ta sake mutuwa da kanta,saita matsa gefan gadon ta sanya mata charge ta koma ta tada sallah.

Har ta idar bai shigo ba,wannan ya bata damar kunna wayarta,umna sa'adatu ce a ranta,so take taji muryarta,tana gama kunnawa kuwa kiranta ya shigo,ta saki murmushi tana dagawa

"Diyam dita.....ina kika shiga yau duka wayarki a kashe?,na kira ammanku tacemin dazu kuka bar gidan,yanzu nake shirin insa driver ya kawoni gidan naki naga ko lafiya,hankalina naji ya tashi" murmushin jin nauyinta ta saki,ta rasa me zata ce mata,wacce amsa zata bata,Allah ya taimaketa dabara ta fado mata

"Wayar ne charge dinta ya qare,ban kuma kula ba sai yanzu"

"To alhmdlh" hira suka dan taba kadan,kasancewar ba wani sabo bane mai yawa tsakaninsu ba abun tattaunawa sosai,ta tambayi su fareeda,sai ta miqawa su faridan waya,suka gaisa,umma sa'aden ta karba wayar tace zatayi sallah zata sake kiranta.

Tana sauke wayar yana shigowa,bakinsa dauke da daddadar sallama,sai ya tuna mata zamansu na johannesburg,yadda ya iya rera karatun qur'ani kamar wani baqin balarabe,muryarsa nada dadin ainun,sau tari da sautin karatun qur'aninsa bacci yake sake saceta,tana son muryarsa a guraren guda biyu,yayin karatun qur'ani da kuma sanda yake sallama.

Samun zuciyarta tayi da wani irin bugawa,ta lumshe idanunta tana amsa masa sallamar,qarasowa yayi ya zauna daga bakin gadon yana fuskantarta sosai,sai ya miqa mata hannunsa ya mata alama kan ta taso,murya can qasa kamar yadda ya saba yi mata magana yace

"Zo muji jikin naki"a nutse ta miqe tana isa gabansa,shirin zamewa ta zauna tayi sai ya janyota ta fada jikinsa,yayi mata masauki akan cinyarsa.

Hannunsa ya sanya ya shafi wuyanta,saita karyar da kai gefe tana jin tsigar jikinta na zubawa

"Thank God,babu zazzabin,ki qarasa shiryawa mu fita ki tattaka ko zaki sake warwarewa,amma inajin yau saidai mu kwana a nan ko?" Ido a narke ta dubeshi,sai yaji kamar ta watsa masa qanqara,yana masifar son shagwabar nan tata

"Uhmmm,kamar akwai magana a bakinki,say it.... Don't be shy" da gaske kunyar tashi takeji,sai ta boye kanta a kafadarsa sannan tace

"Bazan iya tafiya ba" har cikin b'argonsa yaji maganar,don sai da yaja numfashi sosai,maganar ta shiga kunnensa da yawa,kamar tana sane tayi hakan

"Zaki iya.....am by your side,i will support you" ya qarashe maganar yana dagata sosai.

Laffaya ya fidda mata a side din kayan dai data dauko,ta riqe masa ya daura mata,data kalli kanta sai taga kamar ba ita ba tsaye gaban mudubi

"Me yasa kika goyi bayan maganar anni akan tawa uhunnn?" Shuru tayi masa ba tare data iya amsashi ba

"Well,bakya tausayina....kuma bakya sona ko?" Salon da yayi maganar a narke yasa dole ta daga kanta tana duban fuskarsa ta cikin mudubin,gaba daya ya koma kalar tausayi,tana mamakin yadda yake komawa haka a gabanta,why?....me yasa ne?.

Jin shurun ya sake biyo baya sai ya zagayo da kansa ta kafadarta,a hankali ya sakar mata kiss a kuncinta,sannan ya dawo da baya cikin kunnenta ya rada mata wata magana data sanyata sandarewa,sai ta rufe idanunta,matsananciyar kunya tana yawo da ita,maganar kuma naci gaba da amsa kuwa a kunnen nata

"U are very sweet fiye da duk wani abu me zaqi a duniya" anya kuwa ba matsala ja'afar din ya samu ba?,ita maimunatu yake gayawa wadan nan kalaman?.

Zaune kawai sukayi cikin mota ya dinga wani slow driving da ita manyan tituna tana more kallonta,kusan awa daya sukayi a haka,sannan ya zarce da ita wani babban wajen cin abinci me shegen tsada,babu mamaki tunda dama waje ne na wane da wane,ya bata menu ta zaba duk abinda takeso,sai ta rasa me zata zaba din,tunda dai ita ba saba fita tayi gurare irin wannan ba,uwa uba ma kuma bata iya cin abinci cikin jama'a ba tunda ta taso

"Duk abinda aka kawo maka" haka tace masa,to ko da aka kawo dinma juya abincin kawai take,yana ankare da ita,ya fuskanci kunya ne da ita sosai da sosai,yana shirin mata magana wayarsa ta dauki tsuwwa,sai ya aje spoon din hannunsa ya daga wayar.

Sallama kawai yayi ya tsaya yana sauraren bayanan da ake masa

"How comes?" Ya fada fuskarsa na bayyanar da bacin rai,ya sakeyin shuru kafin ya sake cewa

"Okay,thanks".

Unaisa dubai taje?,an tabbatar kuma 'yan gidansu da suka tafi tare dukka sun dawo?,a ina ita din ta tsaya?,wannan itace tambayar da ya jefa ma kansa,ta yaya ma zata dauki qafa zuwa wata qasa bada izininsa ba?

"Have you finished?" Ya tambaya maimunatu,sai ta gyada masa kai,ya kira waiter din ya aje musu kudinsu kan plate din ya qara gaba kafin ya qaraso ma,yana riqe da hannunta.

Shuru suke cikin motar yana tuqi,hankalinsa yayi wani waje na daban,itama hanya take duba ganin still yanzun ma ba gida suka nufa ba,ba wata tafiya sukayi.mai tsaho ba suka shiga wata unguwa,basuyi nisa ba ya tsaya qofar wani gida ya danna hon mai gadin ya bude masa.

Parking lot na gidan ya tsaida motar,ya waiwayo yana dubanta da idanunsa dake cike fal da bacin rai

"Ki shiga ciki,only one hour" kai ta gyada,duk da bata gane ina bane,bata kuma fahimta ba sai data kutsa kai falon gidan sukayi ido hudu da fareeda.

Karadinsu ya sanya umma sa'ade fitowa,murmushin fuskarta yaqi boyuwa,ta rasa inda zata tsoma maimunatu

"Amma kun shammaceni,ke dawa?"

"Shine ya kawoni" ta fada bayan ta rasa sunan da zata kirashi dashi,sai ta aike fareeda tace tace masa ya shigo,duk da ko a baya bai tana shigowa gidan ba,iyakarsa daga waje ne idan ya gama abinda zaiyi ya koma.

Ta samu bayanan,mai gadi ya shaida mata yana sauke baquwar yaja motar ya fita

"Ko kwana zakiyi?" Murmushi ta saki,itama zataso hakan inda zai barta,don ita yanzun tsoron kadaicewarsu ita dashi takeyi

"Baice hakan ba,inajin akwai inda zaije ya dawo" ta fada tana tuna mood din fuskarsa data gani tun a wajen cin abinci.

Dukansu suka hadu sai hirar tafi armashi,ta samu sunyi irin abincinsu nacan gida,don haka ta saki jiki sosai taci,sai data qoshi fareeda tana gyaran wajen umma sa'adah tace da ita

"Har yanzu babu labarin abbanki?" Cikin matuqar alhini da kuma kewarsa maimunatu tace

"Babu umma,Allah ma yasa yana raye" kai ta girgiza,cikin bata qwarin gwiwa tace

"In sha Allah yana raye,a yanzun ne zamuci gaba da addu'a da kuma nema,sannan shi kansa a yadda nasan shi a matsayin mutumin kirki,nasan duk inda yake hankalinsa yana kanku"

"Allah ameen" maimunatu tace tana sadda kanta,tana kuma tuna fuskar.mahaifin nata da har ta soma neman dusashe mata a ido.

Mintuna kadan ya qara a awa dayan ya dawo,ya aika ta fito,sai umma sa'ade tace ya shigo su gaisa mana,kememe ya qiya,don shi baya shiga gidan mutane haka kai tsaye,musamman idan mai gidan baya nan

"Ja'afar?,har yanzu haka yake kenan,banda abinsa nan din ai ba baqonsa bane,gidan babansa da mamarsa ce,muje na gaisa" umma sa'adah ta fada bayan ta hada ma maimunatu uban kaya,wai duka tsaraba ce aka ware mata nata,haka suka rakata mota niqi niqi.

Ko a hanya hannunsa na cikin tafin hannunta yana driving,yanata kuma amsa waya,batasan akan me yaketa wayar ba,amma kuma taji ya ambaci sunan unaisa kusan sau biyu,a haka suka isa gida yanata wayar.

A falo ta barshi ta shige daki,har ta gama shirin kwanciya ta kwanta bai shigo ba,bawai don tana saka ran zai shigo dakin ya kwana ba,sai tayi lamo tana jin gadon wayam,a sannan ne taji motsinsa,ya shigo riqe da wasu kaya,ya bude closet dinta ya zubasu,sannan ya shige toilet dinta.

Ya kusa minti talatin sannan ya bude ya fito,daure da bathrobe dinta,wanda ta tsaya masa iya qaurinsa saboda ya fita tsaho sosai,qamshinta dake manne jikin robe din yana ta shigar masa hanci.

Sassan da take kwance ya maida dubansa,sai suka hada ido tana satar kallonsa ta qasan duvet,da sauri ta runtse idanunta tayi kamar bashi take kalla ba,sai ya saki miskilin murmushin gefen bakin nan nasa,ya qarasa gaban mirror ya dauki lotion dinta,yana kallota ta cikin madubin

"Satar kallon nawa na meye kuma hajjaju?, just get up and look at your husband directly" kunya iya kunya ta kamata,saita shagwabe fuska ta kuma turo baki,ya hangota ta madubi,tsaiwa yayi cak da shafa man yana kallonta,yasan yanzu zata kasheshi da shagwabar tata

"Ni bakai nake kallo ba fa?" Sauke dukka hannuwansa yayi murmushi na subuce masa

"To wa kike kallo?" Sake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login