Showing 156001 words to 159000 words out of 194226 words
ya santa haka,sai yayi kamar bashi yayi maganar ba,yaci gaba da wanke mata wajen,har ya gama tas ya bata pain killer.
"Abar girkin nan haka,nidai na yafe" ya fada yana rufe akwatin,sannan ya miqe tsaye,ya qarasa gaban gas din ya kasheshi,ta bishi da kallo,tana son gaya masa ya barta zata iya ta qarasa,amma sai ya tsaya gabanta yana bata hannunsa,dole ta miqa masa nata,ya jata jikinsa suka fice a kitchen din.
Duk yadda yaso dauriya daren ranar ya kasa,dole ya sake kai kansa gareta,saidai yadda ta dinga masa kuka cike da tsoro yasa ya haqura,ya sanyata a qirjinsa yana sauke ajiyar zuciya kamar zai shide,shi da ita dukka sun dauki dogon lokaci kowannensu baiyi bacci ba,saidai duk da haka ta rigashi yin baccin.
^^^^^^^^^Washegari kasa hada idanu tayi dashi,ko sau daya bata yarsa qwayar idonta ta shiga tasa ba,daren jiyan ba qaramin murzuwa tayi a hannunsa ba,duk da baikai ga gaci ba amma jikinta ko ina ciwo yake mata,har cinyoyinta ma basu tsira ba.
A haka ta dinga zuba idanu taji yayi mata zancan ta shirya komawa makaranta amma shuru,ko kadan shima bai sake tunawa da wata maganar makaranta ba,yana shiryawa zai fita gaida su amman wayar anni ta riskeshi,tace yazo shi da maimunatun takeson gani,amsa mata yayi da to,don bai kawo komai cikin ransa ba,gefe daya tun jiya zuciyarsa ke cike da mamakin unaisa?,ina taje?,ita dai ba qaramar yarinya ba bare ace bata tayi ko kuma an saceta,hakanan baiyi da ita zata fita zuwa ko ina ba,saidai duk da haka zaisa a bincika masa ko gida ta tafi.
Sanda yace ma maimunatu ta shirya zasu gidan muraran farincikinta ya gaza boyuwa,nan da nan ta buda kayanta na lefe,ta hada kaya sosai da zata kaima su annin da sunan tsaraba,ana zaune a mota yaga fitowarta,idanunsa suka dinga yawo a kanta saboda mugun kyan da tayi masa,yana zaune harta qaraso,sai ya bude murfin motar,ya zuro qafafunsa waje,ya kama hannunta ya jata zuwa ciki,bata musa ba tabi bayansa cikin fargabar kada dai yace an fasa zuwan,tuni ta narke fuska idanuwanta suka fara tara ruwan hawaye.
Closet dinta ya bude,ya fidda wasu kayan daban,sannan ya fara ware na jikin ta,hannunsa ta riqe gam tana dubansa,sai ya girgiza mata kai sannan ya zare hannunta.
Shi ya sake shiryata tsaf,ya isa da ita gaban mudubin yana tsaye a bayanta,dukkansu shi da ita suke kallon mudubin,ya sakar mata tattausan murmushi yana duban qwayar idanuwanta,yaso ya rage kyau da kaifin kwalliyar data yine,shi yasa ya shiryata da kansa,amma kuma ya gaza yin hakan,wani kyau na daban ta sakeyi.
Da wani irin zafin nama ya juyo da ita suna fuskantar juna,don har ta tsorata tana dubansa,hannunta saman kafadarsa, idanuwansa ya sauke kan jajayen lips dinta,wanda koda bata saka mishi jambaki ba iya man lebe ya wadatar ya fidda kyansa,miyansa ya tsinke,ya hadiye wani abu ta maqoshinsa,sannan yakai bakinsa saman nata a hankali yana lashe lips din nata hade da wani zafafan kisses.
Sai da ya gama kashe mata jiki gaba daya sannan ya dauke bakinsa yana sauke numfashi a hankali,sakinta yayi sai tayi taga taga kamar zata fadi saboda rashin qwarin jikinta,da sauri ya tallafe ta yana kallonta,a karon farko yaga yadda tayi laushi,don har ta cikin idanuwanta hakan sun nuna,sai ya ajjiyeta gefan gado sannan ya wuce toilet dinta a hankali.
Minti.biyu kawai ya fito yana goge fuskarsa,ya miqa mata hannunsa ta dora nata a kai sannan suka fice zuwa motar,cikinsu ba wanda ya sake cewa komai.
Yau kai tsaye sassan abbi suka fara dira,saboda khadim da suka hadu dashi yace amma da ammi duka suna can,tamkar ta nutse haka maimunatu ta dinga ji,sai take ganin kamar kowa yana karanto komai daga jikinta.
A matuqar kunyace ta gaida abbi sannan ammi,amma tana bedroom din abbin tana gyara masa gami da hada masa ruwan wanka,sai data fito ta gansu,sai ta shaidaws abbin ta gama tana qarasowa cikin falon.
Yau fuskarta dauke da wani irin murmushi da farinciki,ta qaraso tana amsa gaisuwar maimunatu gami da sanya hannunta dukka ta dagota,sai kawai ta rungumeta
"Ashe ke din jinin sa'adatu ce maimunatu?,na jima jikina yana bani kamar na sanki,kamar nasan wani da yake da.nasaba dake,ashe diyar matar dan uwana ce ke, alhamdulillah" ta qarashe maganar tana maimaita hamdalarta,yayin da kunya suka yiwa maimunatu qawanya.
Shiko jabir yana zaune qafafunsa harde da juna yana kallonsu,wani farinciki yana ratsashi,shaheeda ta tafi ga wata shaheedan,komai da yake qiyastawa na shaheeda wanda yayi missing nasa ya sameshi a wajen maimunatu,harma abinda ita din bata dashi.
Su laila nata kai kawo suna son samu space suyi hirar yaushe gamo da maimunatun amma kowacce idan ta shigo sai ta wayance da wani abun ta fice ganin ja'afar na wajen,sai da amma ta cikata da kayan ciye ciye a sassanta,amma ta kasa cin komai saboda kunyar amman da takeji
"Maimunatu,diyata ce ke yanzu ba surukata ba, maimakon ki sake sakin jikinki sai kuma ki sake dararewa?" Matsowa gaba kadan ja'afar din yayi,ya buda dukkan abinda amman ta ajjiye ya zuba mata,kafin ma ya gama amma ta miqe ta matsa a wajen.
Shanyayyun idanuwansa ya sauke mata
"Ko sau daya ban taba ganin kinci abincin kirki ba.....oya matso muci" ya fada murya can qasa,narkewa tayi kaman zata saki kuka,a shagwabe tace
"Nafa qoshi" idonsa ya lumshe yana cije labbansa,tana kasheshi.....har baisan iyakar illar da take masa ba idan tayi wannan shagwabar tata,tana jefashi a wani yanayi,har yana jin kamar bazai iya jurewa ba.
Kaman baiji me tace ba ya matso ya dauki spoon ya saka musu a ciki,ya tsareta kuma da idanunsa,dole ta dauka ta fara motsa abincin kafin takai bakinta,a spoon na biyu kuwa hannunta ya kama yakai bakinsa,idanu a waje tayi galala tana kallonsa,bayajin kunya ko tsoron kada wani ya shigo?,saidai shi ko a jikinsa,ci gaba yayi da tauna abincin,yana jin yana masa dadi a baki fiye da kullum,ko don da hannunta ta ciyar dashi?.
Wasa wasa sai gashi sunci abincin shi da ita ba laifi,shigowar anty maama yasa suka fara wucewa sassan anni ita da ita,kafin ya bisu a baya.
A nutse anni tayi mata kyakkyawan kallo guda daya,a take kuma ta fahimci komai ya kankama
"Anzo wajen,haka dama nakeso,zakaci qaniyanka" ta fada a ranta,tana amsa gaisuwa maimunatu,wadda ta duqa gabanta tana duban qafan annin data sake motsawa da ciwo,sannu take mata,tana jin ciwon annin yana taba ranta, tsohuwar nada kima da martaba a wajenta,sai ta karba man da take shafawar taci gaba da shafa mata,annin na tayata murnar na haduwarsu da sa'ade,da kuma maida zancan yadda abun ya kasance,anty maama na saka musu baki,itama har cikin ranta tana jin dadin kasancewar hakan
"Ni kaina na jima ina ganin yanayinta da anty sa'adah da fareeda,musamman fareeda,muryoyinsu kusan daya ne,duk sanda naji muryarta sai na tuna dasu,ashe jini daya ne"
"Ikon Allah kenan,ga abinda kaketa nema ashe yana kusa da kai baka sani ba" anni ta fada rana jin zuciyarta na mata dadi,abu daya ya ragewa maimunatu a yanzun shine bayyanar mahaifinta,wanda shima ta fara shirya yadda zata tunkari ja'afar da maganar,don ya kamata ayi wani abu a kai, lokaci yana dada ja.
Dai dai lokacin da yayi sallama ya shigo,kamar kowanne lokacin idanuwansa suna kan maimunatu,duk inda zaya shiga ita yake fara gani,muddin tana waje.
Qasan carfet yau din ya zauna,dab da anni da kuma maimunatu da jikinta yayi week tun shigowarsa,batason yayi wani abu da zai bata kunya a gaban anni,don haka tana gama shafawan ta ajjiye man ta matsa daga wajen.
Gaida annin ya fara yi yana mata sannu da jiki,ta amsa tana dubansa,kafin ta dauke kai tace
"Sannunku da hanya matafiya,ya gajiyar tafiya"
"Alhamdulillah" ya amsa mata hankalinshi kwance,kamar bai fahimci da gatse tayi maganar ba
"To ma sha Allah,ba wata doguwar magana bace,dama so nake na gaya maka,da Allah kayi da jiki ka maida yarinyar mutane makaranta,tunda dai amana na dauko,kai kuma alqawari ka dauka,to ya kamata ka sauke" ya manta rabon da yaji gabansa ya fadi sai yau,yadan lumshe idanuwansa sannan ya budesu yana duban anni
"Wacce makaranta?" Dubansa take saboda yadda taga zai raina mata hankali
"Makarantar da ubanka marwanu ya bude" dauke kansa yayi daga inda take,yasan anni,zata fadi fiye da haka ma,don haka ya fito mata shima a ja'afar dinsa sak
"Na cireta anni,wata zan canza mata"
"Dalili?" Ta tambayeshi harda riqe qugu tana qare masa kallo
"Kawai" ya amsata yana sassauta daurin agogon dake hannunsa,don a take yaji kamar ya matseshi ma.
"To uban maryamu,to billhuwallazi la'ilaha illa anta baka isa ba,uban kuturu ma yayi kadan ballantana na makaho,kaiiii ja'afaru,kayi ta kanka wallahi,bakasan wace maryamu ba hala,mu zaka mayar qananun mutane?,wanne irin zabine baa baka ba amma ka kafe can zaka kaita?,shine zaka tsire cireta a makaranta kanason yi mata walagigi da karatu?,to kayi qarya ka kwana da yunwa" boyayyar ajiyar zuciya ya saki,yana jin cewa ya shiga uku yau,tijarar anni ta dira a kansa
"Lemme explain you mana anni....."
"Lamma ma taci qaniyarta,kayi ta kanka fa,idan hausa hausa idan fillanci fillanci" hannunsa yasa ya dafe goshinsa da kyau,anni bata da kyau idan ta tubure,gashi jabir baya kusa ballantana ya tayashi,shi kuma bai iya daukan hayaniya da yawa ba har haka
"Relax.....relax,ba daina karatu zatayi ba,inaso ta koma day ne,i mean jeka ka dawo"
"Baka isa bafa,ita ka fara zaba mata ita zata ci gaba da zuwa,idan kaga ta daina saidai idan itace tace bata so....." Maida dubanta tayi ga maimunatu dake zaune,tayi shuru yana sauraren dambarwar tasu
"Ke maimunatu.....kinason komawa makarantarki......ko kin zabi dadi miji ya sauya miki wadda yaga dama?"....
11/24/22, 23:35 - Buhainat: 72
Tambayar da annin tayi mata gaba daya sai taji ta daburce,daga ita har ja'afar din sun zuba mata idanu,kowa yanason ta dauki zabinsa,bai taba tsintar kansa cikin fargabar jiran fitar amsa daga wani waje ba irin yau,koda aiki da kasuwancinsa da yake daukansa da muhimmanci bai fiya damuwa da rashin samuwar wani abu ba,idan yayi duk abinda ya dace yana ci gaba da harkokinsa ne ya barwa Allah zabinsa.
Ita kuwa anni fatanta daya maimunatun kar ta amince da tsarinsa,wannan din wata hanya ce da zata sake samar mata da kima da daraja a idanunsa,ya dandana yaji idan tana da muhimmanci cikin rayuwarsa,musamman yanzun da ya fara sanin ainihin ita din wacece.
Maimunatu kuwa zahirin gaskiya tana son makarantarta,saboda ta saba da ita,gasu afra da takejin kamar ba zata rabuwa dasu ba,kada ma afra taji labari,ko don ita kadai batajin zataso canjin makaranta
"Nafison wadda nakeyin yanzu" kamar an sauke masa guduma a kansa haka yaji
"Subhanallah" ya fada can qasan ransa,yana dauke idanuwansa daga kanta
"To kaji,saboda haka kada ka wuce gobe baka maidata ba,tun gabanin na hadaka da marwanu ya cimin qaniyarka,don ni din yanzu na fuskanci wani sabon raini kayimin" cak ya miqe daga zaman yana cusa hannunsa a aljihun wandonsa,wani bacin rai yaji yana ratsashi,bai taba tunanin zata iya zabar maganar anni akan tasa ba,baice komai ba ya fara takawa zai fice a falon
"Yauwa dakata.....iyayen marigayiya sunyi magana jiya akan debe kayan yarinyarsu za'ayi sadakarsu,na riga nace musu su sauraremu zuwa yau......ya kamata a fiddasu haka ayi mata sadaka Allah yakai mata ladan k...." Tun bata qarasa ba ya tari numfashinta
"Nan da one hour su sameni cikin gidan su dauki dukka abinda zasu dauka" ya taka yana barin falon,umma tabawa da anty maama suna binsa da kallon tausayi,sunsan anni,da biyu tayi hakan.
Umma tabawa ce ta sauke ajiyar zuciya
"Banda abin maimunatu,ke da zaki goyawa mijinki baya,saiki biyewa anni ku kware masa baya?"
"Har yaban tausayi,don Allah a sassautawa dan qanina" anty maama ta fada tana murmushi,su duka suna kallon maimunatu,kunya da nauyinsu ya sake cikata,maganar anni ta tsaida su
"Kunga,ke maryamu bakisan dawar garin ba,keko tabawa da kika sani bai kamata kice komai ba,ku bamu guri ni da ita" ta buqata daga garesu,sai suka miqe anty maama tana cewa suje kitchen baaba tabawan ta sake nuna mata kwabin alkubus irin na rannan,duk sadda tayi nata da qyar takesha,sai ya kusa cabe mata yayi nauyi.
"Maimunatu"anni ta kira sunanta a tausashe
"Na'am" ta amsa mata kanta har yanzu a qasa
"Allah yayi miki albarka,ya jiqan mahaifiyarki,ya bayyana mahaifinki,babu abinda zamu ce dake sai Allah ya kyauta qarshenki,bamu zaci dawowar ja'afar da sauri haka ba,sai gashi cikin tafiyar nan taku jabiru yana shaidan canjin da ya gani na tunkarar rayuwar ja'afar din ta sanadinki,ni kaina shaida ce,yana shigowa naga haka akan fuskarsa,banda wannan maganar dana masa wadda baiso nasan a yau din zamu jima dashi,xan kuma ga ainihin ja'afarunmu,amma babu komai,mun saba irin haka dashi,kema kada ki damu don ki goyi bayan hukuncina,dama haka naso,saboda ta hakane zaki gane girma da martabarki a ransa,karki damu da dukka fushinsa,ki bishi a hankali,zai sauko da kansa,bashi da riqo sosai musamman akan abinda yake so" kalmar abinda yake so din ta sanya maimunatu daga kai tana kallon anni,sai ta sake mata murmushin su na manya
"Eh,a yadda naga yanayin ja'afar,na tabbatar indai ba mutuwa ba babu abinda ya isa a yanzu ya rabashi dake,naji dadi hakan da ya zaman kece kika samu wannan gurbin,dama abinda naketa taraddadi,kada waccan ta qwace matsayin da naketa miki fatan samunsa,abu daya kawai nake gudu, wahalar da abokiyar zamanki zataci,ja'afaru ba irin mazan dake iya zama da mace biyu bane,saboda idan suka fara son abu suna fara sonshi da gaske ne,suna kuma miqa masa dukkan yarda soyayyarsu da kuma amannarsu,shi yasa tun farko naso marwanu ya qyale batunta,amma bazaiyiwu na tursasashi ba,dukkansu suna min biyayya akan dukka maganata,to ya kamata a qalla suma na dinga basu dama cikin rayuwarsa,ba fata nake ba,ba kuma baki nake ba,amma tabbas dole akwai abinda zai biyo baya,kedai kawai abinda zance dake,ki koma makaranta abinki,karki waiwayeshi ko sau daya" kai ta gyada tana jin gamsuwa da maganar anni,hawayen farinciki yana sauko mata,ta rasa da wanne irin harshe zata yiwa anni godiya,batasan girman soyayyarta gareta ba.
Ko awa daya cikakkiya ba'a rufa ba ya aiko khadim ta fito zasu tafi,sai ta narke fuska,bata zaci zaice yanzu yanzu ba daga zuwansu,wuni ta dauka zatayi a nan din,gashi ta fara jin dadin hira dasu laila.
Murmushi anni tayi,a qufule yake kenan da alama,abun yana mata dadi ita kuma sosai cikin ranta,hakan na sake nuna darajar maimunatu a wajensa,sai ta dubi maimunatu
"Tashi ki bishi ku tafi,zaki zo wataran ki wuni,karki damu" haka ta tashi jiki a sabule tana goge qananun qwalla,su fa'iza zasuyi mata rakiya anni ta hana kowa zuwa wajen,tace su barta ta fita ita daya.
Tunda ta shiga motar baice komai da ita ba,saidai tana jin yadda yake sauke numfashi da kuma ajiyar zuciya lokaci bayan lokaci hadi da fidda wata iska daga bakinsa,da alama ransa a bacen yake,duk sai taji babu dadi cikin ranta,amma kuma sai ta kama kanta,tunda dai me zata ce masa?,tun farko shi ya zaba matan kamar yadda anni tace,yanzun kuma ita kanta bataga kamatar biye ma tsarinsa haka kai tsaye ba ba tare da an dan latsashi ba,amma can qasan ranta sai takeji babu dadi sam,abinda ya dauke walwalarta itama gaba daya,amma sai ta maida dubanta ga titi tana kallon yadda suke wuce hanya.
Duk da ba sanin garin tayi sosai ba,amma ta fahimci kamar ba hanyar gida suka nufa ba,saidai bata tanka ba,tana dai kallon hanyar ne kawai.
Sau kusan uku yana satar kallonta,ya zaci zata nuna damuwa ko wani abu da yayi kama da haka,amma sai yaga kamar ma batasan me ya faru ba,abinda ya sake qular dashi,ya dinga hadiyar zuciya shi daya yana lumshe idanunsa hadi da budesu,matsa mai kyau yakeson mata amma kuma driver ke jan motar ba shi ba,wannan yasa ya qagu su isa gidan.
Da yake ba wata tazara tsakanin gidan nasu da government house road,nan da nan suka isa ainihin gidan nasa dake can,wanda a nan ya fara rayuwarsa da shaheeda.
Tun daga tsarin ginin katangar zaka san cewa ba qaramin gida bane,ba kuma ginin wasa aka yi masa ba,shi kansa yana kimanta gidan saboda ya qunshi abubuwan tarihi masu yawan gaske da suka shafi rayuwarsa a ciki,uwa uba da kudin aikin da yake mutuwar so a rayuwarsa ya ginashi,wato sanda yake a matsayin cikakken captain ja'afar marwan akko dinsa.
Tun a gate security suka fara miqa gaisuwa,yana amsa musu da hannu,saboda ba'a cikin yanayinsa yake ba,motar tasu ta sulala zuwa cikin katafariyar harabar gidan,sannan suka tsaya a parking lot.
Yana gaba tana biye dashi,idanuwanta suna kallon tsarin gidan,ginin turai zam,komai kuma yana nan a tsaftace a muhallinsa tamkar dan adam yana rayuwa a ciki.
Bata fahimci inda sukazo ba har sai da suka qaraso