Showing 126001 words to 129000 words out of 194226 words
zai qare
wajen ne kawai zai bata soyayya da martabar
kowa aure a cikin sa'anninsa.
tsohuwar matarsa takai,zata tsallake shingen
tsakaninta dashi,itama zata kai wani bigire da
wannan lokaci?,unaisa ya bawa kansa da
kuma bashi mamaki kenan,ya zubawa qofar
saman nasa,duk taku daya tana yinsa ne da
idanu qwaqwalwarsa nason tuno masa waye
da take da tabbacin tsallakewarta zuwa nan
zuciyarsa na canzawa,tun ba yau ba yasan
da kuma bedroom dinsa ya qure temperature
Dai dai lokacin da unaisa ke takowa zuwa
matsa ya diba remote na dukka acn dake falo
dinsa ya nufi qofar kawai kai tsaye,ya mance cewa babu riga a jikinsa.
cikin dabara ta turo qirjinta zuwa gaba tana
aure,don haka daga uya sleeping dress da ta
dabi'a irin tasu,uw uba ma ya taba yin
yana mata duban baki da wayo,yayin da ita
kuma ke masa duban so da kuma
a gwiwa ba ta sakar masa murmushi,sannan
kaman dai tazo da sa'arta kenan?,batayi qasa
saka a jikinta take tsaye kuma a gabansa ya
sha'awa........
karkacewa cikin kwarkwasa.
Mutuwar tsaye tayi sanda sukayi arba
dashi,idanunta qur bisa fuskarsa zuwa
isa ya gaya masa me take nufi?
qirjinsa,wani abu ya soma zagaya jikinta,lallai
Koda bata ce komai ba shi din ba yaro bane
"Zanyi maganinki" ya ayyana hakan a ransa
bai,ya kuma karanci mabanbantan hali da
qarami,dai dai gwargwado yasan mata ciki da.
End of book
11/24/22, 23:25 - Buhainat: BABU SO
Chapter 58
58
........Hanunta take ɗagawa daƙyar tana kai masa ƙananun duka, ya fara ƴar dariya da ƙoƙarin riƙe hannayen nata. Duk yanda yaso su koma barci hakan ya gagara, dan ƙorafinta na zafi da raki ya gagara tsayawa. Ga zazzaɓi mai zafi dake ƙara rufeta bayan sauka ya kamata yayi tunda tasha magani. Dole ya tashi zaune da ita a jikinsa yana ƙoƙarin son su haɗa ido amma taƙi yarda. Bai damu da hakan ba, dan yasan kunya dole ce. Shi kansa wani nauyi yakeji amma yana ta ƙoƙarin ganin ya fuske abinsa..
“Faɗamin miye matsalarki kuma Noorii na?”.
Shiru ta kasa bashi amsa, sai ƙoƙarin son kauda kanta kuma take yaƙi bata dama. Dole ta buɗe baki muryarta a ɗashe irin ta wanda yaci kuka ya more, dan ko fita batayi da ƙyau. “Inajin zafi mai raɗaɗi, dan ALLAH ka kiramin Mamie ko ka kaini wajenta”.
A ransa yace, (Ko ɗaya a ciki bazaki samu ba) a zahiri kam wayarsa ya ɗauka zuciyarsa na masa kaikawo akan waya dace ya kira. Har yai dailing number Dr Jamal sai kuma ya katse, text message ya tura masa. mintuna kaɗan kuwa sai ga kiransa. Kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya ɗaga da miƙewa ya fice a ɗakin.
“Malam ba kirana nace kayi ba, Nurse daka aminta da ita nace ka turamin”.
Dr Jamal yay murmushi da shafa kai daga can, “Oh to ai ko asibitin ban fitaba shiyyasa nace bara na kiraka naji waye babu lafiya?”. Jimm yay na wasu ƴan sakkani, sai kuma ya furzar da huci a hankali ya furta “Juwairiyya!”.
“Ayya ALLAH ya bata lafiya, mizai hana ka kaita asibiti kawai sai mu haɗu, dan gaskiya a iya hasashena ban san wace Nurse zan tura maka ba indai irin wadda nasan zaka buƙata ce. Amma Dr Bilkisu na tabbatar ta iso yanzu zatafi kulawa da ita da sanin matsalarta kai tsaye inma mune baka son mu duba maka ita..”
“Kai ka sani”.
Ya bashi amsa a taƙaice da yanke wayar. Daga can Dr Jamal yay ƴar dariya da ajiye wayar ƙasan zuciyarsa na masa kaikawo amma yana turewa dan yayi alƙawarin mantawa da ita, zai cigaba da mata kallone kawai irin na ƙanwa kuma matar amininsa insha ALLAHU.
Shawarar Jamal ta masa, dan haka ya taimakawa Anaam daketa hawaye har yanzu ta shirya, shima dai a gurguje yay nasa shirin. Duk yanda yaso tai taku daga bedroom zuwa waje ta kasa, ko bedroom ɗin ta kasa iya ƙarasa fitowa zafi kawai take ambata tana hawaye, gashi duk ta langaɓe masa kamar mara ƙashi a jiki. Dole ya ɗauketa gaba ɗayanta ya fito.....
★Ranta fes ta tashi yau kamar yanda ta kwanta sakamakon jin ƙwarin gwiwa daga sirrin su aunty Safarah. Gaba ɗaya cikin yaƙini da imanin maganin da suka batan yayi aiki take. Tana idar da salla cike da karsashi ta shiga kitchen da kanta haɗa breakfast. Hakan ba ƙaramin mamaki ya bama maman Abu ba. Sai dai bata iya cewa komai ba dan ta fahimci uwar ɗakin nata tana a farin ciki, tasan kuma yana da nasaba ne da abinda taga tanayi jiya. Sai taji inama zata fahimceta kuma ta isa ta bata shawara akan abinda take kallo ba komaiba. Taji sanda su aunty Safarah ke tabbatar mata maganin matane suka bata, ita kuma ta aminta da hakan saboda bata da ilimin banbancewa, ta sani Fadwa nada rawar kai da ɗagawa, dan duk wanda ya kwana ya tashi a gidansu yasan ita ɗin boss ce musamman akan ƴan aiki, to amma kuma duk da kasancewarta a haka ɗin bata taɓa tunanin ganinta da wani mugun hali da ya zarta waɗannan ɗin ba, tanaji a ranta kuma da wani zai fahimtar da ita abinda su aunty malika suka bata nada banbanci da maganin mata ƙila bazatai amfani dashi ba duk da bata san zuciyarta ba dai.
Tana aikin gyaran sashen nata ita kuma tana haɗa breakfast mai rai da lafiya a kuma nutse, dan dama dai shiriritarta da son jiki ke hanata yi ɗin a yanda ya kamata bawai dan bata iya ba. Cikin ƙanƙanin lokaci ƙamshi ya gauraye ko'ina, cike da nishaɗi ta kammala ta koma bedroom ta gyara jikinta. A yau zata kawo duk wani iskanci da jiji da kan Anaam a gidan nan, dan babban burinta tai gaba ta barta da mijinta salin alin.
Ƙarfe takwas da wasu ƴan mintuna ta nufi sashensa dan tasan ya tashi zuwa yanzu, shi ba ma'abocin barcin safe baneba ma, amma a yanzu tunda yana gida ba aiki zai fitaba tasan ko yaya zai ɗan kwanta.....
Fitowar Fadwa yayi dai-dai da fitowarsa ɗauke da Anaam daga sashenta. Babu shiri taja birki ƙirjinta na dukan tara-tara bama uku ba, shi sam baimaganta ba dan hankalinsa gaba ɗaya ya tafine ga kallon Anaam yana murmushi, saboda tsokanarta yake akan raguwace ita tana tuttura masa baki da kauda fuskarta gefe. Anaam ɗin kam sarai ta ganta, duk da halin da take ciki hakan bai hanata ganin wannan wata dama bace, ada taƙi yarda ta riƙesa, a yanzu kam saita saƙalo hannayenta a wuyansa duk biyu tana sake sakin kuka da cusa kanta a ƙirjinsa. Shiko da bai san dalilin yin hakan ba sai ya ɗan manna mata kiss a goshi da sakin siririyar dariya. A hankaki yake taku har zuwa wajen motar tasa, ya dureta ƙasa tare da jinginata da motar.
“Ina zuwa”.
Ya faɗa yana barin wajen, batace komai ba sai dai idanunta na satar kallon sashen da Fadwa dake binsu da kallo har yanzu kamar a birkice take. Da sauri Fadwa tai baya alamar bata buƙatar ya ganta, shima da yake ALLAH yasa hankalinsa ba wajen yake ba sai bai lura da ita ba ya wuce yanzu ma. Mintuna da basu fi uku ba ya sake fitowa hannunsa da key ɗin motarsa. Sake wucewa yay abinsa batare da yanzu ɗin ma ya ganta ba dai...
A gaban idonta ya sake ɗaukar Anaam ya saka a mota, shima ya shiga suka fice gidan. Tai baya kamar zata faɗi maman Abu da itama komai ya faru akan idonta ta riƙota. “Hajiya dan ALLAH ki kwantar da hankalinki”. Maman Abu ta faɗa muryarta cike da damuwa itama. Da taimakonta Fadwa ta koma ciki, ta ɗakko mata ruwa amma sai ta hankaɗar da shi ya zube, wasu zafafan hawaye da sai yanzu suka sami damar fita a idanunsata suka shiga rige-rigen sauka a fuskarta. Maman Abu dai batai fushiba, takai zaune kusa da ƙafafunta a ɗarare ta sake faɗin, “Hajiya dan ALLAH karki ɗaga hankalinki, wannan kaɗanne daga halin maza idan suka ƙara aure. Amma inaga ki bincika kiji mike faruwa tukunna kamar zaifi. Koba komai kin jefa tsuntsu ɗaya da dutse biyu. Na farko dai zaki san mike faruwa, na biyu kuma zaiji kunyarki idan fitar bata da wata babban dalili da farar safiyar nan. Amma idan na shiga hurumin daba nawa ba kiyi haƙuri..”
Idanu Fadwa ta sake rumtsewa da ƙarfi zuciyarta na wani irin zafi da raɗaɗi, dan tabbas abinda Shareff yayi ya sake zuzuta zafin daya sauka mata lokaci guda, kishi ya rufe idonta ta kasa ji a ranta wata matsalace ta sakasu fita gidan da safen nan bawai lafiya ba.....
Waya ta ɗauka da sauri ta fara laluben layin aunty Safarah. Bata tsaya ko gaisuwa ba ta sakar mata kuka.
“Subahanallahi Fadwa lafiya kuwa?”.
“Aunty Wlhy maganin beyiba, yanzu fa da safen nan ya fito ɗauke da ita suna farin cikinsu da dariya suka bar gidan nan. Alhalin jiya babu wani kusanci makamancin hakan tattare dasu. Aunty na shiga uku idan hankalinsa ya koma kan yarinyar nan. Jiyafa taimin alwashin indai ya fara kasancewa da ita saina zama ƴar kallo....”
“Kinga nutsu ki saurareni Fadwa. A yanzu haka gani tare da Aunty (Gwaggo halima) kuma duk tana jinki, dama nazone zan amsa sako da zamuje wani waje saboda ke”.
Sunan maman ta fara kira cikin kuka, Gwaggo Halima da tun fara bayanin Fadwa wutar kanta ya ɗauke saboda shi babba duk inda yake babba sunansa, tuni zuciyarta ta hasko mata wani abu ya shiga tsakanin Shareff da Anaam kenan, dukan kokarinsu na hana faruwar hakan bai yuwuba kenan, taja numfashi. “Fadwa kinga nutsu kuka ba naki baneba. Karki damu damun bayanin komai na riga na sani domin ni na aiko su Safarah wajenki dama nace ne karsu faɗa miki. Yanzu ki jira zamu kiraki ina zuwa...”
Kafin tace wani abu aka yanke wayar, ta zube a bakin gado da sake fashewa da kuka mai cin rai....
_______
Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso asibitin, yanzu dai taso nuna jarumtar hanashi taɓata amma ina hakan bai yuwu ba. Dan taku biyu kacal ta nema zubewa tamkar ta fasa ihu dan zafi. Dole dai ya ƙaraso ya ɗauketa.
“Ni dai Yaya ka saukeni zan iya”.
Ta faɗa tana sharce hawayen dake ambaliya akan fuskarta saboda hango Dr Jamal dake nufosu alamar yasan da zuwan nasu.
Murmushi yay da kashe mata ido ɗaya “Da wannan tafiyar tonamin asirin ne zaki iya?”.
Idanunta ta rumtse kunyar duniya a kanta, dan gani take kowa zai iya sanin miya faru da ita ne. Da taimakon Dr Jamal suka sami ganin Dr Bilkisu a sahun farko. Ganin Anaam taƙi amsa tambaya ko guda ɗaya a gaban Shareff daya tsatstsareta da ido yasa Dr Bilkisu kallonsa da ɗan murmushi. “Alhaji Al-Mustapha ko zaka ɗan bamu wajene dan naga patient ɗin tawa kasancewarka tare damu ya hanata cewa komai”.
Ido suka sake haɗawa da Anaam. Tai azamar janye nata da tura masa baki. Mikewa yay yana murmushi batare da yace komai ba ya fita. Ko'a bayan fitar tasa ma sai da Dr Bilkisu ta sha fama sannan Anaam ta amsa mata wasu daga cikin tambayoyin nata tana faman sinne kai, a yanda ta fahimci ta kasa zama da ƙyau tai hasashen abinda Anaam ɗin ke faman ɓoyewa. Batace komai ba ta taimaka mata zuwa gadon da suke duba marasa lafiya, ganin tana neman ɗage mata doguwar riga ta riƙe da sauri tana girgiza kanta...........✍
11/24/22, 23:25 - Buhainat: Chapter 59
59
.........Murmushi Dr Bilkisu tayi, cikin sigar lallashi tace, “Kiyi haƙuri dubawa kawai zanyi, dan idan yazam yaji miki ciwo ne ba'a ɗauki mataki ba nan gaba zaki iya fuskantar wata matsalar da ba'a fata. Gara tun yanzu yana a ɗanyensa a ɗauka mataki kinji ƙanwata. Badan Anaam taso ba ta bar Dr Bilkisu ta duba, dan sosai ta dinga lallaɓata da nuna mata illar rashin dubawar harta amince.
“Ya ALLAH”. Dr Bilkisu ta faɗa da sakin rigar Anaam ɗin takai hanunta saman goshi tana murzawa. Sosai ranta ya sosu, sai dai kuma ta fahimci matsalar daga jikin Anaam ɗinne. Amma duk da haka an nuna mata mazantaka da yawa da ƙawazuci.
A tsorace Anaam dake kallonta tace, “Doctor wajen ya daina aiki ko?”. Murmushin da babu niyya Dr Bilkisu ta saki, ta girgiza kanta da kallonta. “A'a bai daina aiki ba ƙanwata, kawai dai anyi ɓarna ne da alama angon naki tsohon tuzurune halan shiyyasa ya gagara binki a sannu. Gaskiya yayi miki ɓarna da yawa da dole sai anyi ɗinki”.
“Na shiga uku”.
Anaam ta faɗa tana fashewa da kuka. “A'a kinga kwantar da hankalinki baki shiga uku ba. Mata da yawa sunci karo da matsala fiye da taki ma a dalilin first night, ban san mike damun mazan ba da suke muku irin wannan zuwan haka, ko soyayyace ke ingizasu oho, koda yake suma iyaye akwai laifinsu, zaka kai yarinya buduwa gidan miji amma kaita tsumata da kayan mata. Sune suke saka gushewar hankalin mafi yawan mazan har su aikata mummunar ɓarna ga yarinya, a yanzu haka inada irin cases ɗin nan da yawa ga wata can ma kwana uku kenan da mata ɗinki har huɗu kaɗan ma ya rage ita mijin ya kasheta dan a sume aka kawo mana ita tana bleeding kamar mai haihuwa” (Iyaye wlhy da gaske matsalar nan tana cutar da yaranmu, maganar mai ɗinki da bleeding ɗin nan da nake muku ya faru a gaske ALLAH har kuka naima yarinyar, amma koda aka binciki mijin iya gaskiyarsa ya faɗa cewar ya fita hayyacinsa ta yanda ya gagara jin tausayinta balle tuna ita din virgin ce, koda yarinyar ma akaji ta bakinta daga baya akan ko tasha wani abu ne bata ɓoye ba ta sanar da irin kayan matan da aka dinga ɗirka mata har ji ta dingayi kamar ta jawo auren koma ta bashi kanta kafin a ɗaura. Ya ALLAH, iyaye mata a duba dan ALLAH a gyara, ƴarki budurwa ce bata san komai ba, koda ɗan kayan fruit kika gyarata da su zuma da mazarƙwaila sun wadatar ai, sai maganin sanyi da a kullum bana gajiya da tuna muku shine mafi muhimmanci kafin kikai ƴarki gidan aure ki tabbatar bata tare da imfection yafi maganin matar nan da za'a iya cutar miki da yarinya a dalilinsu. Dan mazan da yawa sukan kasa controling kansu ne harsu fatattaka miki yarinya a banza taje yoyon fitsari ya sameta. Dan waccan yarinyar da nake gaya muku sai da yakai ko fitsari bata iyayi da kanta saida taimakon robon fitsari tsahon wasu wattani. Shin riba akaci ko faɗuwa kenan🤦🏻?).
Kuka sosai Anaam ta dingayi har ba'ajin sautin muryarta a yayin da ake mata ɗinkin, tabbas ita din ragguwace bata wasa ba. Ko yaya abu ya sameta ta dinga raki ke nan balle wannan da ya zame mata makafin ajewa a tarihi dan bata taɓa riskar azaba makamancin hakanba. Shareff yasha tarin ALLAH ya isa da inda tarasu za'ai waje guda buhu-buhu zai ɗiba ya kaima Mommy ajiya saboda tarihi😝😆.
Sosai ya dinga kaikawo dan yana iya jiyo kukanta da kiran Abie da Mamie da take famanyi, har da wasu a ALLAH ya saka matan da take ambata da ja masa ALLAH ya isa. Sosai hankalinsa a tashe yake dajin ɗunbin tausayinta da takaicin kansa. Da yanada damar dawo da ciwon jikinsa da yayi ko zai samu sassauci a zucyarsa, dan itaɗin wata abace mai daraja a zuciyarsa da baki ko alƙalami ƙaryarsa zanawa. Ita ke kukan amma tare suke raba raɗaɗin a zuciya. Koda aka kammala Dr Bilkisu tasa aka kaita wani ɗaki danta huta yana shigowa ta fashe da kuka wai bata son ganinsa Dr Bilkisu ta koresa. Duk da haushinsa da Dr Bilkisu keji kasa daurewa tai sai da tai dariya. “Tunda patient ɗina bata bukatar ganinka jeka abunka mun sallamaka Alhaji Al-Mustapha. Dan gaskiya kai mai laifine mai girma a wajenmu ɗin”.
“Gutun murmushi ya ɗanyi iya laɓɓa sai dai bai fitan ba. Ya jingina da bango hannayensa zube cikin aljihun wandonsa ya zuba mata idanu. Bargo taja ta rufe har fuskarta ita a dole bata buƙatar ganinsa ɗin dai. Dr Bilkisu ta janye daga kallonta tana ƙara sakin ƴar dariya itama. Inaga ka bata dama ta huce sai muyi magana a office”.
Kansa ya jinjina mata kawai. Ta juya ta fita. Cigaba yay da tsaiwa a wajen har bayan minti biyu da fitarta sannan yabi bayanta, har sannan kuma Anaam bata buɗe fuskar taba ɗin.
A office ɗin doctor batare data kallesa ba ta miƙa masa takardar data gama rubutu a jiki. “Taji ciwo ne, amma mun mata ɗinki. Na fahimci cewa ƙaramin jiki ALLAH ya bata, amma shekarunta sun kai ga hakan. Sai dai kuma yanayin halittarta tana buƙatar bi a sannu, domin masu irin yanayinta zakaga ko'a wajen haihuwa ana shan fama dasu matuƙa saboda jikinsu bashi da wani ƙwarin gaske, sauƙinta ma ita tanada wannan ƙaramin jikinne, da irin raɓo-raɓo ɗin nan take akwai matsala, hakan na nufin ko anan gaba za'a bita a hankali inba hakaba kullum zata dinga shan ɗinki kenan. A yanzu dai zan riƙeta anan gaskiya har zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ta samu nutsuwa yanda ya kamata saina baka ita da sharuɗɗa masu tsauri. Muna buƙatar waɗan nan drugs ɗin dana rubuta anan.”
“Uhhim”.
Kawai ya faɗa yana miƙewa. Dr Bilkisu ta bisa da kallon mamaki, irin miskilan mutanen nan na bata tsoro, sai sun tafka tsiya ka rasa ta inda zaka auna yaya ma sukai. Kiji fa ta gama masa bayani akan kuskurensa ya bita da ‘uhhim’ kawai tsabar miskilanci. Bai san ta ɗaga masa ƙafa bane kawai saboda Dr Jamal. Amma da yaga yanda ake ruwan masifa yau, duk da kwarjininsa shima ya taka rawar gani wajen cika mata ido ko fushinta ta gagara nuna masa akan fuskarta.
Pharmacy ɗin asibitin ya nufa domin sayo magungunan, sai da aka gama haɗawa zai ɗauka waya dan musu transfer yaji babu wayar a jikinsa, kansa ya dafe yana ambaton sunan ALLAH. Dole ya bar musu maganin akan zaije ya dawo. Ɗakin da take ya sake komawa, saboda yana son jin ko tana buƙatar wani abu. Samu yay tana barci a yanda ya suka barta, ya kai hannu ya yaye bargon data lulluɓe har kanta tare da kaiwa tsugunne gaban gadon. Duk da barci take kumburin idonta bai hana ya bayyana ba, ya saki murmushi yatsansa na kaiwa a saman idanun ya shafa, a hankali ya gangaro har saman fuskarta zuwa lips ɗinta. Yatsansa ya shiga zagayawa a kansu, kafin ya sake matsar da fuskarsa gab da tata murya ƙasa-ƙasa ya furta “Tabbas kin cika mai tsadar da tafi tsada