Showing 180001 words to 183000 words out of 194226 words

Chapter 61 - GURBIN IDO COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

12 Dec 2024

26152

goshin dai,ya kamata anni taji wannan labarin" kunya ce ta kamata sosai,saitayi qasa da kanta tana goge hawayen da batasan sun zubo ba

"Ayi haquri yallabai,kada na kasa hada ido da anni" ta fada tana miqewa don yi masa rakiya.

Tun ranar da baaba tabawa ta tafi gidan ta koma 'yar kallo,hakanan ta dinga kame kanta waje daya,saboda gaba daya ja'afar din ya kunce mata tunani,ashe haka yake?,ashe lumbu lumbu ne?,wata irin wutar soyayya ke tashi cikin gidan,saidai cikin salo da ban sha'awa da kuma qayatarwa,ya dauki kulawar maimunatu gaba daya ya aza a wuyansa,abinda baaba tabawa kawai keyi kula da gidan da kuma girki.

Ta fannin maimunatu kuwa sai yanzu tasan meye ainihin ma'anar gata,gata mai sunan gata,tako ina lelenta akeyi,umma sa'adah nayi,su fareeda cousins dinta sunayi,anni nayi ammi da amma nayi,tsohuwa hajja nayi,umma sa'adah nayi,abbanta nayi,ga kuma afrah dinta data qeqashe taqi komawa makaranta,sai day abbuu ya maidata,wanda a yanzun itama ta koma ce masa abbuu,ya samu cikakkiyar lafiya ya kuma koma kan ayyukansa kamar daa,ya murmure fes dashi kamar babu wata jarrabawa data taba samunsa,a yanzun abu daya ya ragewa hajja shine ya qara aure,shi kuwa gani yake bazai samu mace kamar hauwa'u da shatunsa ba.

Ko yaya maimunatu ta motsa sai a kawo mata caffa,tako.ina gata da kulawa take samu,hatta su laila kaman zaayi musu haihuwar jikan fari,kusan ranaku d'ai d'aikune basa zuwan mata a yini ana hira,haka afrah itama fashin kwana daya ko biyu take,ba abinda maimunatu keyi saidai taci abinda ranta keso tasha abinda ranta keso,duk da cikin yazo mata da laulayi sosai,amma tana samun sauqi saboda akwai masu debe mata kewa.

Saidai fa duk yadda gidan yakai ga mutane,da zarar oga captain ja'afar ya dawo zai dauke abarsa ya wuce sassansa da ita,hidimarta kuma ta koma wuyansa,ita kanta maimunatu qorafi take masa ya dinga hutawa yaji da aikin office kawai amma yakance

"Da da hali zan ajjiye komai ne,nayita rainon cikin nan har sai randa kika haihu zan sake fita na barki" idan kun sake ganin maimunatu yana cikin gidan saidai idan wata muhimmiyar fita ce ta kamashi.

Tako ta ina babu abinda zata cewa rayuwa sai godiyar Allah,cikin dare daya Allah Almusawwiru ya canza mata rayuwarta gaba daya,bata da wani sauran qunci ko kuma damuwa kwata kwata,saidai lokaci lokaci takanyi tunanin inna furera,ko yaya take ciki?,me takeyi a halin yanzu,da gaske bata sonta don bata taba waiwayar inda take ba.

Abinda bata sani ba shine,inna fureran ta hadu da ibtila'i,bata da lafiya ta fita wani private asibiti da aka bude jikin rugarsu,bayan ta gama fadi tashin neman adreshin maimunatu har gembu amma kowa ya hanata,daga bisani kuma ta samu adress din,saidai har garin gombe ta shigo amma ta bace,tayita yawon neman gidan bata samu ba,qarshe ta hadu da 'yan damfara suka karbe sauran 'yan kudadenta,sai bara tayi ta hado kudin motar dawowa gida.bayan taje asibitin an gama dubata likitan yace

"Akwai wani aiki da mukeson bawa.mutane,aiki ne da yanzu yanzu zaki zama.shahararriyar attajira idan kinso" a yanzu ba abinda inna furera keso kamar wannan kalmar ta zata zama me kudi, kowacce hanyace tana jin zata iya binta,don haka tace

"Ko meye likita zanyi,zanyi wlh"

"Ba wani abu bane mai wahala,jini zamu diba leda biyu,zamu biyaki naira miliyan talatin" jin yawan kudin ya sanyata zamowa qasa,sai gata dabas zaune a qasa tana raba idanu,fillo yaji kudi sama ta ka ba tare daya siyar da kasanarsa ba😝😝😜

"Shin da gaske kake likkita?"

"Hajiya ba wasa a maganar nan,jinin muna kaiwa ana taimakawa marasa qarfi a cikin gari,saboda ku fulani kun fisu lafiya da yawan jini saboda yanayin abincinku da nasu ba daya bane"

"Aradu likkita ko yanzu ina iya kwanciya ka diba" ta fada jikinta na mazari,don har ta gama hango kudaden da abinda zatayi dasu idan sun samu,lallai magauta da maqiya ganin bayanta ba yanzu ba,ita din me sa'a ce,tayi musu shalll.....
11/27/22, 07:04 - Buhainat: 83

Murmushin nasara likitan ya saki,yau da alama ranar sa'arsa ce

"Babu damuwa hajiya,zamu baki daki ki kwanciyarki kita baccinki,basai kin koma gida ba bare ki gayawa kowa,ana gama diba zaasa miki kudinki a jaka a baki ki tafi dashi a sirrance saboda gudun barayi da 'yan sane,aidai kinsan miliyan talatin ba qananun kudi bane ko?" Kai ta jinjina

"Qwarai kuwa likkita,ai sai na samo.masu tayin irga inajin"

"Yauwa to" hankalinta kwance aka bata daki lafiyayye tayi kwanciyarta tana sheqa baccin,tasan gidanta babu kowa sai laulo,gaje kuwa batace ga inda taje ba,jauro kuwa tuni ya sawwaqe mata dama saki guda,saboda yadda tayi silar yawace yawacen gajee,gashi taqi saituwa,hidimar aurensa yake kawai yana fatan zuwan sabuwar amaryarsa ta daidata gidan da yaran,don yasanta tsayayya ce sosai akan tarbiyya.

Daga wannan baccin dai inna furera sai tashi tayi ta tsinci kanta ajeji cikin matsanancin ciwo,da qyar cikin masu wucewa cikin dare suka ganota suka daukota zuwa cikin gari,ciwo yayi ciwo har 'yan uwanta daga gembu sukazo,qarshe aka.kaita babban asibiti.

Sakamakon bincike ya nuna qodarta guda daya aka cire,dayar kuma ba cikakkiyar lafiya ne da ita ba,haka taci gaba da rayuwa cikin ciwo,idan ka kallo cikinta kamar zai fashe.

Duka wannan labarin sai da yuuma tazo take gayawa umma sa'adah,yuman tace

"Azabar cin dukiyar marainiyar nan kadai bazai barta ba,hala wutar data ciwa cikinta na dukiyar maraya Allah ya fara azabtar da ita tun gidan duniya"

"Haka Allah yake lamarinsa,shi hakki ai yanzu tun a duniya Allah yake sakayyarsa basai anje kiyama ba" umma sa'ada tana fada,sosai maimunatu taji tausayinsu daga ita har gajee,amma data fara maganar ma umma sa'adah cewa tayi

"Akul na sake jin maganar wadan nan mutanen daga bakinki,ki fuskanci rayuwarki,banda Allah ya qwaceki da tuni har yanzu kina hannunta,baasan ma a wanne hali zaki kasance ba".


°°°°°°°°°°A hankali ta soma bude idanunta,tana jin yadda yake shafar gefan fuskarta a hankali cikin taushi,kafin ta gama.bude idanuwan nata murmushi ya mamaye fuskarta,ta san mutum daya ne ke da wannan aikin,wanda salon tashin da zai mata daga bacci ya banbanta dana kowa.

Tarrr ta bude idanuwanta akan fuskar sa dake faman kallonta kamar zai cinyeta

"Yaushe ka shigo?" Sai daya langabar dakai gefe sannan ya amsa

"Kina can duniyar baccin,baby na ya daukemin ke,na zama abun tausayi,baccin nan ya fara yawa angel" ya fada yana sake shafar fuskarta data yi masa kyau sosai,a tausashe ta riqe hannunsa,a yanzun burinta shine ta samu lafiya ta shiga hidimta masa,tana tuna dramer dinsu da anni shekaran jiya da tayi maganar wai ya maidata makaranta,baima iya amsawa annin ba

"Ke maimunatu namiji baida tabbas,idan kika zauna zakiga zaunau,ya maidaki makarnatar daya zaba miki ki qarasa karatunki,koba komai kin tsira da kwalinki" anni ta fada saidai can qasan ranta bata nufin abinda ta fada din
"ki qyaleshi don Allah anni,na haqura da makarantar Allah" baki ta kama kamar gaske ta zabga salati

"Iyeee,ja'afaru?,yaushe ka iskantamin 'ya?"

"Yo ai gaskiya ce,banda abinki hajiya anni,ta yaya matar aure da ciki ruqu qui ruqu qui zata wani dinga tafiya boko?,ta zauna tayi bautar aure shine gaba"

"To ai shikenan,duk qoqarin da nake kun watsan qasa a ido?,ya maisheki mara ta ido ko?" Anni ta fada tana tafa hannu,sai a sannan kunya ta kama maimunatu,ta miqe da sauri tana boye dariya tana ficewa a dakin

"Bi a hankali!" Suka hada baki wajen fada kowa yana zabura saboda yadda ta kusan yin tuntube wajen fitar.

Ashe ja'afar din na labe yana jiranta,tana qarasa fitowa kuwa ya dauketa cak yana dariya

"Well done,yau kin biyani,gwara da anni yau tayi ta kanta" dariya maimunatu ta shiga qyalqyalawa

"Wato yau itace tayi ta kanta din kenan?,to babu ruwana"

"Da gaske nake data sake tada maganar zan fito mata kaina tsaye,ko kuma na daukeki mu bace cikin duniya,kinga babu me takuramu" rungumeshi tayi tana dariya

"Ba inda zamu,zamu rayu cikin aminci da yardar Allah cikin ahalinmu".

"Me kike tunani?"ya fada yana shafar gashinta, murmushi ta sake
"Anni"
"The great rigimammiyar kaka" dariya maimunatu ta sake

"Maza ta jika" hannu ya bata yana murmushi

"Taso muje,abbi ne yazo dubaki" ido ta fidda

"Abbi kuma?,ta yaya zan iya kallonsa don Allah hubby"

"Am here for you,ba komai,ai shima.uba ne" tanata doddojewa da jin kunyar abbin haka ya rakata ta kuskure bakinta ya zura mata hijab suka fito.

Cikin kunya ta sulale gabansa tana gaidashi,mutum ne mai cikakken sanin addini dana zamani,don haka bashi da wata damuwa,ya amsa mata a sake yana tambayar jikin nata,daga bisani ta fita ta basu waje shida ja'afar din


"Tunda kacemin zaka samu lokaci banji kace komai ba,ni na samar maka lokacin,na shaidama minister zuwanka,yau basai gobe ba kaje ku sasanta ka dawo da ita,itama ta zauna a dakinta kamar 'yar uwarta" kansa a qasa,gaba daya abbi ya yanke masa hanzarinsa,to amma bazai iya musa masa ba,ya amsa masa da to,yana mamakin dattako irin na abbin,bayan duka tarin aibun daya gani a kanta amma bai bashi qofar rabuwa da ita ba.

Sanda ya koma dakin bayan ya raka abbi ya wuce yayi qoqarin danne dukka damuwarsa don kada hankalin maimunatu ya tashi,saidai wayam ya rasata a dakin,ya dinga lalubenta bai sameta a ko ina ba sai a kitchen, tayi zaune tana lodar abinci baba tabawa tana qara mata,sai yayi tsaye rungume da hannuwansa yana kallonta yana murmushi,baba tabawan ce ta fara ganinsa,sai tayi murmushi

"Sannu da zuwa manya,qaraso ciki mana"

"Baba ke kike sake shagwaba diyar nan taki, abincin nan da take ci dole ta qara nauyi" murmushi tayi

"Ba dole ba,ai haka mukeso,alamun samun lafiya kenan"

"Gaskiya ne" ya amsa yana sakin qaramin murmushi yana takowa zuwa inda take zaunen,baba tabawa kuma ta ajjiye serving spoon din hannunta tana bar musu kitchen din,don yanzu haka take musu.

Yadda take taunar abinda ke cikin plate din ya burgeshi,saboda yadda dan qaramin bakinta yake juyawa,tsigar jikinsa ta zuba,ya matsa kadan sannan a hankali ya riqe fuskarta ya hade bakinsu waje daya.

Sai daya tsotse dukka labban nata da sauran maiqon dake kai,tuni plate din hannunta ya yafi yayi nasa waje,abinda yake ciki ya watse,dauke kansa yayi a hankali yana maida numfashi,shi da ita suna kallon farantin dake watse a qasa,tabe baki tayi kamar zata saki kuka tana duban yadda dan waken yayi d'ai d'ai,dubansa ya maida kanta

"Meye wannan?"

"Dan wake nane fa?,kaga abinda kayimin" ta fadi a mugun narke,da alama qiris take jira ta saki kuka,murmushi ya saki yana dan take yatsunta da nashi

"Yanzu tsakani da Allah ni na zubar miki?,ba ke kika zubar da kayanki ba?, mene abun dadi a nan ma fulawa ne ko da menen?,kaman bama" baisan hakan daya fada tunzurata yayi ba,kawai saita sake masa kuka

"Ragowarshi kenan fa,Allah saika sakemin wani" ta fada tana hawaye daya na bin daya

"Bari na kira baaba tab....."

"A'ah" ta fada da sauri tana maqale kafada

"Ni kaine zaka yimin" hannu ya dora saman kansa yana dubanta,sai kuma dariya ta kubce masa

"Bansan ta yadda akeyi ba" kafin ta amsa baaba tabawa tayi sallama ta shigo ajjiye flask din abincin ta

"Subhanallah me ya faru?" Ta tambaya,tana kuka tana gaya mata ja'afar ne ya zubda mata dan wake,kuma tace ya sake mata wani yace zai kirata

"Ikon Allah.....sai haquri manya,yanayin nata cikin kenan,yanzu kiyi haquri na sake miki wani"

"Shi zaimin Allah,shi ya barar min"

"Jeki baaba zanyi" ya fada yana tattare hannuwan rigarsa

"An shiga uku toh....." Baba tabawa ta fada taba riqe baki tare da dafe kai,wannan rigimar bata taba ganinta wajen maimunatu ba sai yau,itakam ba zata iya kallon babban mutum mai matsayi da kima kamar ja'afar ya gwaggwafe yana dan wake ba,sai ta fice daga kitchen din tana cewa

"Allah ya sawwaqa".

Cikin lokaci qalilan ya fuskanci dan waken nan fa bazai yiwu ba,ga maimunatu ta kasa ta tsare,asalima hira ta koma tana masa ko a jikinta,jira take ya.kammala taci,shuru yayi sai kuma ya kashe gas din,kafin tace komai juyo ya dauketa cak,sai ta dubeshi

"Baka gama ba fa"

"Babban son of beans zan baki,zo muje kiji" ya fada dukka jikinsa yana amsawa,gaba daya ta canza masa,cikin ba qaramin qara mata daraja da martabar da mace ke samu a auratayya yayi ba,duk da dama maimunatun yayi imani da ta dabance,sosai madarar shanu ta ratsata tun tana qaramarta.

Ko acan babbar bedroom din shagwabe masa tayi,tanata qwallar shagwaba shi kuma yana biye mata,a sannan kaga yadda lallabarta kamar qwai sam ba zaka ce shine wannan Captain J din ba,matuqin jirgin sama,kuma babban dan kasuwa,maabocin izza miskilanci shan qamshi da jin kai ba,gaba daya ya sukurkuce maimunatu,wani lokaci har tsoro yake bata.

Tare sukayi wanka kamar yadda ya saba mata,yakan gaya mata sunnah ne mai qarfi yin wanka tare da iyali,saita koma jikin kujera ta takure kamar wata 'yar mage,don tun dazun tace masa tana jin sanyi.

Binsa take da kallo sanda yake taho wa wajenta dauke da wasu fararen socks masu taushi,yayi mata kyau sosai,kayan daya sanya din sun amsheshi ba kadan ba,ko yaushe sake fresh yake da kyau,ko ba'a gaya maka ba hankalinsa a kwance yake.

A hankali ya duqa gabanta idanunsa cikin nata,farare sol din qafafunta ya kama ya soma zura mata safar,har ya gama tana kallonsa,sai yasa hannu yaja kumatun ta

"Wai duk yunwar dan waken ce?,kada ki cinyeni angel" murmushin ta saki tana lumshe idanu,tuni ya bata abinda yafi dan wake,a hankali tace

"Idan na cinyeka kuma wa zan kama?,kawai ka yimin kyau ne,so nake na haifo baby me kama da kai" dan fuska ya bata cikin salon tsokana

"Baby ko babies?,biyu ko uku nakeso,kuma masu kama dake ni nakeso" kafada ta maqale tana murmushi

"Ban yarda ba,nafison me kama dakai gsky" ido ya zaro

"Angel......kina kallon kanki da kyau kuwa,kinsan yadda Allah ya tsara halittarki?,duk sanda na kalleki saina yima daada addu'a da fatan dawwama a aljanna data haifomin ke" murmushi tayi tana sake lumshe idanunta,farincikin samun miji d'aya da d'aya kamar ja'afar na sake kamata,bata da abinda zatace da anni itakam a rayuwa,ta gama mata komai data hadata da d'an jikan nan nata,wanda ya hada komai na rayuwa,ko a aljanna shine zabinta

"Ko baki qoshi bane naga kina wani kallona qasa qasa?" Ya fada cikin sigar tsokana yana kai hannuwansa saman qirjinta daya soma cika sosai saboda yanayin ciki,hannuwansa ta ture tana bata fuska hadi da turo baki

"Nifa yunwa nake ji Allah,a bani abinci ko kuma na cinyekan" tattausan murmushi ya saki yana dora kansa saman cinyarta ta tadda zai iya ganin fuskarta sosai

"Bana gajiya dake angel,bana gajiya da kasancewa tare dake,you are my world angel" a hankali ta dora tattausan lips dinta akan nasa,ta bashi wani hot kiss,sai ya lumshe ido yana fadin

"Wash Allah amma,zata kasheni" dariya ya bata sosai har tana qyalqyalawa,gami da sanya hannunta ta rufe fuskarta.

Babban hijab ya dauko mata yace suje taci abincin a wani wajen,daga nan tadan tattaka ta miqe qafart,hakan yayi mata,taji dadi sosai,don tunda ta kwanta ciwon bata fita ba.

Leqawa tayi ta gayawa baaba tabawa zasu fita,tayi musu adawo lafiya tana binsu da kallo,murmushi kwance akan fuskarta tana mamaki.lallai mata suna da wata babbar baiwa da daraja,mutum kamar ja'afar amma yarinya kamar maimunatu ta sukurkutashi,inda wani na waje aka baiwa wannan labarin zai qaryata,captain ja'afar a kitchen yana sakun dan wake(🤣🤣kadan daga aikin mata,munfi gaban haka,talaka ko mai kudi ko malami dukka a tafin hannun mata suke,Allah dai ya qara mana albarka da juriyar haquri da mazanmu,ya qara mana qauna da fahimtar juna a tsakaninmu,ameen)

A hanya yake gaya mata ya sama mata malama da zata dinga zuwa kullum,qarfe sha daya na safe zuwa biyu kullum suna karatu,muhimman subjects da take buqatar samu a waec neco da jamb dinta,in sha Allah karatunta bazaya tsaya ba.

Qwararriya ce sosai matar,hasalima hausa kadan kadan takeji,sunanta miss serah,sosai taji dadi, hankalinta kuma ya sake kwanciya,don yanzu babban burinta a yanzu shine ta zama full house wife,ta kyautata masa matuqa kamar yadda taga daadarta tanayi sanda take raye,gata da soyayyar da ja'afar ke nuna mata babu wani abu da zata saka masa dashi face nuna masa zallar soyayya da kulawa.

Wannan eatery din mai tsada daya saba zuwa ya kaita,yace yau sai ya qureta,ta zaba duk abinda takeso a kawo mata

"Zan baka mamaki"

"Haka nakeso" ya fada yana zube mata idanun nan nasa,ta kuwa zaba abinci kamar hauka, waitress din ta kalleshi

"Sir,total din fa da yawa" fuskarsa a dan daure kamar yadda ya saba zama boss dinsa duk sanda ya fito ya kalleta

"Kiyi aikinki kawai,ba ruwanki da abinda za'a charger"

"Ok sir" ta fada tana juyawa a ladabce,cikin zuciyarta tana jin inama ace itace maimunatu,tunda suka shigo idanunta yana kansu,wata irin madarar soyayya take gani suna zubarwa zallarta(haka dan adam yake,a duk sanda kaga wani ya zama wani,ko ya taka wani muqami,burinka kawai dama kaine shi?,shin kasan irin qayoyin daya taka ya wuce a hanya kafin ya iso bigiren da yake kai?,so duk wanda ya zama wani akwai qalubale taf daya haura kafin yakai tudun nasara,jajircewa haquri da juriya gaskiya da amana suke kai dan adam duk wani mataki a arayuwa,kamar yadda amanar maimunatu ta sake baiwa anni sha'awa wajen hada iri da ita).

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login