Showing 24001 words to 27000 words out of 66967 words
zaunar da ita tayi tace “ya akayi haka Rafi'ah garin yaya har kika bashi dama ya tura gda Abba ya amsa har suka karbi kudinsa bayan kinsan mijin aminiyarkine"
Tsayar da kukanta tayi tace “kina zarginane aunty Raziqa yaushe na zama maci Amana da zan yarda da wannan hargitsin hatsin barar wlh bantaba bawa Ja'afar dama ba komai nasa iko yake gwadamin banasonsa Amma yace dole ne ma nasoshi Ni Kuma tsanarsa nakeji"
Shiru sukayi na dogon lkc kafin aunty Raziqa tace “Hmmm! To Allah ya kyauta Amma akwai qura Wakil family basuda sauqi akan qudurinsu tare mukayi karatu da Karimah qanwarsace babansu daya itama haka take indai tace tanason abu ta saita sameshi kiyi addu'a kawai Allah yasa hakan shine yafi alkhairi sannan kisa a ranki miji yafi qawa duk kuwa girman shaquwarku to wacce shaquwa ma ta rage ai babu ita tunda namiji ya shiga tsakiyarku kishine zaku fafatashi na mutuwa wannan shi ake Kira ranar biyan buqata rai ba abakin komai yakeba qanwata bazan zugaki kici amanar aminiyarki ba Amma idan ya dage ki hqr ki karbeshi dama wani lkcn ana samun haka garashi ma aurenki zaiyi wasu lalacewa sukeyi a titi yaqine yake tunkaroki qarfinki bazai qwaceki ba sai taimakon Ubangiji da samun yardar mijinki...."
Kuka takeyi sosai itakuma Aunty Raziqa ta dage nasiha take Mata da nuna Mata ba kanta aka faraba a fakaice take kwadaita Mata son auren Ja'afar Wakil hardai ta samu tayi shiru da kukan Amma qasan zuciyarta ciwo yakeyi Mata lamarin Ja'afar tsoro yake bata tayaya ma zata iya kallon idon Ni'imah tace Mata mijinta zata aura? wannan tunanin bai barta ba bacci ya dauketa bata tashi ba sai bayan azahar tana tashi ta shiga tayi wanka tayi sallah ta dade cikin sujjadarta tana roqon Allah kada ya tabbatar da wannan kwadon tuwon alkamar bama zai cuwu ba.
Tana idarwa aunty Raziqa ta shigo tace “kizo to kinsha bacci ko?" Miqewa tayi ta gyara fuskarta kasancewar kwalliya ta zauna a jikinta ko batayi ba kamar tayine takowa tayi tanajin gabanta na faduwa kawar da idonta tayi daga kansa a fili tace “maye kawai" abin mamaki batasan yaji ba sai taji yace “tukunna ma sai ranar da komai ya kammala zaki tabbatar da ni asalin mayene akanki don wlh nayi Miki alqawarin tun daga yatsanki har qofa ta qarshe ta gashinki saina lashe"
Juyawa tayi ta kalli inda su anti Raziqa suke lunch taga hankalinsu ba akansu yakeba kafin ta dawo da nutsuwarta taji ya rungumeta ta baya ya sanya hannunsa ya dago habarta qamshin turarensa ya sakar Mata da wata kasala me qarfi ya dago habarta ya dora bakinsa saman nata suka lumshe idonsu a tare tare da sauke ajiyar zuciya ya dora hannunsa saman qirjinta batare da ya kamaba daya na kan mararta daya na qirjinta ga bakinsa cikin nasa"
Wai Ashe bashi kadai bane kawai sai haske tagani a cikin idanunta dake lumshe suka bude da sauri kawai sai taji gurin ya dauki tafi Muhseen ne da wani camera man, janyewa tayi da sauri ya sake janyota ta fada a hannunsa nanma Saida suka qara haskasu sannan camera man din ya fice Muhseen ya kalli JM yace “maye kawai" dariya ya kwashe da ita Yana sakinta abinda bata taba gani a fuskarsa ba ta kalleshi taji qirjinta yabada wani dam ta dauke Kai ta zauna cikin tsananin jin kunya.
Jitayi yace “eh ka fada dama ka samu ko matata mijinki mayene ko?" Harara ta galla masa ya sake kwashewa da dariya yace “zanga ranar da zaa daina hararata nikam yanzu ya zakiyi dani fadamin abinda kike shiryawa game da aurenmu?" Daukan cup din lemo tayi takai bakinta ya matso ya zauna kusa da ita ya dauko abincin ya diba yakai bakinsa ya sake diba yakai Mata ta janye yace “kada ki wahalar da shari'a kotu batason gardama ki karba kawai idan kinqi kuwa kinsanni yanzu zan baki charge"
Ga mamakinsa sai yaga tana neman bare Masa baki yayi saurin saita kansa duk wani annurin farin ciki dake fuskarsa ya dauke yace “Ansha fama Ashe ba banzaba kafiyar ma gado kikayi Abba koro mutane yayi da kudin aurena naje har kasuwa na sameshi yayimin kaca² baa taba cimin mutunci kamar Wanda akayimin a sanadin aurenki ba Dad ma babu abinda Bai nuna masa ba yaqi amsawa qarshe dai sai Dad ne yayiwa Mai martaba jagora sukakai kudin Darazau gidan Baba Hudu kayy yau Baba Hudu ya gamamin komai a duniyar nan wlh dattijon arziqi cewa yayi tunda abin yazo da haka kawai a daura inyaso nanda 1 mouth din ayi biki zancen da nakeyi Miki Mai martaba da waziri da sauran wakilaina Basu baro Darazau ba Saida suka tabbatar da igiyar aurena ta hau kanki...."
Miqewa tayi a gigice yayi saurin riqeta yace “meye hakan?" Kawai sai yaga ta sulale qasa jikinta ya dauki tsuma haqoranta suna haduwa ya matsa kusa da ita kafin yakai ta dauki cups din dake gabanta ta jefeshi dashi a goshi ji kakeyi qwal take jini ya balle masa ya dafe gurin da sauri ya dago ya kalleta kawai sai gani yayi ta fizgi wuqar dake jikin kankana ya kuwa kwaso gudu ya riqeta suka rinqa kokawa tans kuka me gunji tana Kiran sunansa tana cewa “ka qyaleni Ja'afar ka qyaleni na kashe kaina na huta wlh banasonka na tsaneka na tsani kaina Ja'afar meyesa rayuwa tayimin haka meye nayiwa duniya da batamin adalci wlh saina kashe kaina bazan taba karbarka a miji ba"
Duk qarfinsa sai gashi ta watsar dashi a qasa ya sake tashi daidai lkcn da Abba ya shigo gdan ganin yanda aka taru akan autar tasa rai biyar sun kasa riqeta sai kuka takeyi tana ihu tana rantsuwar saita kashe kanta yayi mugun tashin hankalinsa dama abinda yake tsoro kenan yasanta yasan batada control indai akakai hqrnta qarshe kafin ya ida qarasawa ta zubar da Ja'afar Muhseen Naseer Raziqa da Musa camera man daqyar Ja'afar ya qwace wuqar duk ta yankeshi da ita a hannu,
Kwasa tayi da gudu ta nufi kitchen Abba ya daga murya ya qwala Mata Kira sai ta zube a gurin tanabin kowa da kallo ta sake sakin kuka me ciwo ta fada jikin Abba daya tsugunna a gabanta yara Rashid ya riqota ta lafe a jikinsu tana sake shigewa jikinsu tana kuka me tafasa zuciya tace.
“Allah ya isana wlh Abba bazan taba yafewa Baba Hudu ba me nayi masa me na tsare masa da zai dauramin aure da wannan tsinannen maci Amanar Abba kace ya sakeni wlh zan kashe kaina Kona kasheshi banasonsa na tsaneshi tsana ta gaske wayyoh Abba zuciyata qirjina Abba wayyoh rayuwata wayyoh Bestie na meyesa kika dauko mana jarfa ya yanke mana igiyar zumunci saboda cikar burinsa.....
Bata gama rufe bakinta ba sukaji an banko qofar da qarfi dagowar da zasuyi sukaga Ni'imah ce da gudun bala'i ta nufi Rafi'ah da wuqa a hannunta tsirara tana kuka itama gabadaya parlourn sukayi kanta suka tareta batakai ga qarasawa ga Rafi'ah tayi tayi ta qwace ta kasa sai ta sake sakin kuka tana cewa.
“Ashe munafukace ke maci amana mijina kikeso bansani ba Rafi'ah me nayi Miki a rayuwarmu ta 21 year's kika zabi yimin wannan sakayyar mijina Rafi'ah Allah ya Isa tsakanina dake kin cutar dani kin yaudareni kullum alkhairinki nake fada bantaba ganin sharrinki ba Ashe ke naki sharrin
yafi na kowacce mace a duniya na rantse da Allah indai Ina raye kamar yanda kika yankemin farin ciki saina yanke Miki naki keda farin ciki har abad....."
Tsawa Ja'afar ya daka Mata ta juya kansa yayo kanta yana huci ya shaqota yace “da nace kada ki fito shine Saida kika fito to daganan ki wucce gdanku...." Saurin katseshi Abba yayi da cewa “haba kaikuma mema ka fara gani da har zaka fara yanke hukunci Ja'afar aj bakaga komai ba tunda haka ka zaba gasunan duka matanka ne kalmata ta qare tunda abinda Allah ya hukunta ya riga ya faru Abu daya da zan fada maka shine, yata Rafi'ah batada hayaniya zuciyarta a tsarkake take idan ta gyaru Kaine idan ta lalace Kaine bazan taba baka itaba tunda baka Isa da gidanka ba ka gama danan sannan saika dawo nan..."
Yana fadin haka ya figi hannun Rafi'ah suka fice sakin Ni'imah Ja'afar yayi yabisu yana Kiran Abba shiko ko sauraronsa baiyi ba ya cilla yarsa a mota yaja suka fice shima motar ya dauka a guje yabisu sun rigashi zuwa suna zuwa Abba yace da megadi kar yabarshi ya shigo, aikuwa yin duniya magiyar duniya mado megadi ya hanashi shiga gdan komawa yayi cikin mota ya buga kansa da sitiyari zuciyarsa na tafasa baiyi aune ba saiji yayi glass din motarsa ya tarwatse ya dago da sauri tare da budewa ya fita daidai lkcn da glass din ya tarwatse ya zubawa Ni'imah ido kawai sai yaji ta bashi dariya ma ya tsare Napep ya shiga ya fada masa inda zaa kaishi da gudu ta biyo sahun tana cewa “ka saukeshi wlh cikin biyu saidai ya zabi daya azzalumi macuci mayaudari maci Amana..."
_Kaina ya kulle da wannan chakwakiya bazan iya dogon typing ba Sun bani ciwon Kai sai nasha paracetamol_
_Vote_
_Comments_
_Share_
_Please_
*_Ummuh Hairan_*
[1/5, 7:31 PM] Mrs AA Fansah: I think you'd like this story: "MY BESTIE'S HUSBAND" by realfauzahtasiu on Wattpad https://my.w.tt/DZncHfSZNcb
*_My Bestie's Husband_*
*_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
*_Dedicated to Real Smasher_*
_Ina gdy da kulawarki gareni Allah ya qara ilimi me amfani😍_
*_19-20_*
____________________________
____________________________
Tunda suka dawo gidan mutanen gdan suka hadu a kanta suna aikin rarrashinta yin duniya taqiyin Shiru Koda tayi niyyar yin shirun idan ta tuna da furucin aminiyar tata ta Kuma tuna da cewa yanzu fah da ita da aminiyarta duka sunan matan mutum daya suke amsawa sai taji sabon kuka ya qwace Mata qarshen qarshema zazzabi ne ya rufeta ba qaramin artabu sukayi da Abba ba sannan ta daina furta zata kashe kanta yajata yakaita daki kamar wata qaramar beby ya kwantar da ita ya rinqa bubbuga bayanta har bacci ya dauketa sannan ya tashi ya fita.
Dakinsa ya shiga ya Kira wayar Dad ya daga suka gaisa yace “Haba Sabo meyesa kayimin haka don Allah banji dadiba wlh duk da na matsu naga Rafi'ah ta fitar da miji Amma ai ba irin wannan matsuwar da zaa kasa duba alaqa ba yanzu ga abinda wannan auren ya janyo daga ita har Ni'imah babu me hayyaci ita tanata kukan bataso saita kashe kanta kota kashe Ja'afar ita Kuma Ni'imah tana zargin da sahalewarta akayi wannan auren Sabo wannan bayyananniyar cin amanace fa da kowa zai shaida...."
Katseshi yayi da cewa “meyesa zaka tsuke tunaninka ka rinqa tunani irin na Mata Alh Nuhu Ni dama na dade da fahimtar hakan zata faru Ja'afar yanason Rafi'ah tunkan ya auri Ni'imah da an qara jinkiri baayi gaggawar hada aurensa da Ni'imah ba qila da Rafi'ah zaigani ya zaba to Amma Allah ya hukunta dukkansu matansa ne saboda haka muyi Shiru kawai mu karbi abinda Allah ya zartar Ni'imah ai ba ita tayi kantaba naji duk haukan da taje tayi muku wlh akan lamarin nan zan iya cin mutuncinta indai bata nutsu ta fahimci abinda ke gabanta ba bandama shirme irin nasu na Mata da yaje ya dauko Mata bare ta girgijeta ai gara ya auri aminiyartata babu wani cin amana a auren sunnah dukkansu matansa ne haka Allahu ya tsara to mubi kawai muyi Shiru"
Sosai Alh Sabo ya rinqa tausar Abba da kafa masa hujjoji hardai ya rusuna ya karbi abin tare dayi musu fatan alkhairi Amma yana Jinjina yanda zaman zai kasance shi tausayin ma Ja'afar din yakeyi har gara Ni'imah qila ta tausu ta dadi Amma Rafi'ah tanada wuyar sha'ani akan abinda ta yarda aranta ba daidai bane"
Bangaren angon Ja'afar kuwa da Ni'imah tunda yaje gida ya haye samansa yanada dan qaramin clinic a cikin bangarensa ya fara dressing din hannunsa ya yanku sosai amma baiji haushi ba saima murmushi da yayi yace “zan saitaki ne Rafi'ah wahalar dama zamowarki tawa tunda kin zama ai asiri ya rufu" yana wanke ciwon yana cije lebe har ya gama ya koma ya kwanta yanajin zugin hydrogen din ya jima a kwance sannan yaji alamun shigowarta saman ta hau ta kalli qofar a rufe ganin hakan yasata fara dukan qofar da dukkannin qarfinta tana cewa.
“Tunaninku zakuci amanata ku hutane qarya kake Ja'afar Wakil tabbas baka fara shiga damuwa ba wlh ka zubar da farin cikinka tunda kaci amanata macuci mayaudari maci Amana azzalumi, Ashe dama abinda yasa kullum bakada Hira saita Rafi'ah kenan Ashe da gaskene saqon da aka taba turomin cewa kullum sai anganka a makarantarsu ka dauketa ni Ina tunanin saboda nine macuci Ashe kanka kake ginawa to wlh dole ayi dayan biyu dole ka saki daya cikinmu domin baa fada daya sarki biyu Ja'afar ka budemin ka fadamin laifin da nayi maka da zakayimin wannan sakayyar...."
Yanajinta yayi Mata banza tayi bugun duniya yaqi budewa zagin duniya tayi masa ya shareta saboda dama ya shiryawa zuwan wannan lkcn baizaci ma haukan nata zai tsaya iyanan ba a yanda ko a Hira take nuna masa ita zata iyayin komai akan kishiya, yanajinta ta gaji ta zube a gurin taci gaba da kukanta tana cewa “Allah dama mafarki nakeyi na bude idona naga ba gaske bane Allah ka mayarmin dashi tunani na shaidan Allah bazan daukaba wlh kasan bazan daukaba bazan iya zama da Bestie na matsayin kishiya ba Allah ka kashe wannan azzalumin Ja'afar na huta Allah ka hada hardani nikam na shiga ukuna Allah...."
Maganganu takeyi kamar zararriya yanajinta yaqi budewa saboda shi kansa zuciyarsa a cunkushe take bada damuwar Ni'imah ba aa damuwar halin da Rafi'ah take ciki shine yake addabarsa gashi Kiran duniya yayi taqi dagawa ya tura Mata saqo taqi replying dabara ce ta fado masa ya Kira number Ammi don dama tun ranar data kirashi tayi masa warning yayi saving ring biyu ta daga da sallamarta ya amsa tare da cewa “Ammi barka da Rana" jin muryarsa yasata hadiyar wani takaici Amma dake dattijuwa ce saita dake tace “lfy Ja'afar ya gdan"
Shiru tadan ratsa kafin ya ja numfashi yace “inata Kiran wayarta taqi dagawa Ammi Allah yasadai lfy?" Iska ta furzar tace “yo wanne lfy Ja'afar dama kanasonta da lfy ne ai da sauqi ma da bata hadiyi zuciya ba tanacan tana fama da zazzabi" miqewa yayi zaune yace “ya Salam bari nazo na dubata" yana fadin haka ya kashe wayar ya tashi shi kansa idan zaa dubashi din so yake bai Saba da tashin hankali ba shi tashin hankali fitar dashi a hayyaci yakeyi.
Doguwar riga yasa ya dauki key ya fice a hanya ya kira Muhseen yake sanar dashi ya daukeshu suka tafi daqyar megadi yabarsu shima Saida Ammi tayi masa mgn suka shiga sukayi parking Rashid dake fitowa yazo suka gaisa yayi masa ya hannu saboda yaga aika²r da qanwar tasa tayi, shine yayi musu jagora har parlourn baqi suka qara gaisawa ya dauki wayarsa ya kirayi Rafi'ah ta daga lkcn ta tashi tasha magani tayi salla yace “kizo ki sameni maza a parlourn baqi" bai jira cewarta ba ya kashe wayar ta kalli Ammi Ammi ta kawar dakai tace “
“Kidaibi a sannu kada ki zafafa kiyi biyu Babu ba mijin babu aminiyar ita rayuwa baduk abinda kakeso kake samu ba iyakar saninmu munayi Miki addu'ar samun miji na qwarai Kuma kema munsan kinayi tunda Allah shi ya zaba ya zaayi dama shi muka miqawa zabin Kuma yayi abinda ya dace"
Ficewa tayi tabarta da sassanyar gwiwa wasu hawaye suka zubo Mata wayar Yaya Rashid ce ta sake shigowa cikin kuka ta daga tace ”gag ganinan Yaya" miqewa tayi ta zari hijjab saboda sanyin da takeji ta fice ta sauka ta nufi parlourn baqin ta tura qofar ta shiga da sallamarta idanunsa na kanta suka amsa Yaya Rashid ya miqe shida Muhseen suka fice tare dajan qofar ya rage daga ita saishi ganin taja ta tsaya yasashi shareta yaci gaba da danna wayarsa kawai takaici yana cika masa ciki Wai kawai laifinsa don ya sota ya aureta ne take basa wannan ciwon kan jibi yanda ta wani tsaya masa aka kamar sa'anta.
Dagowa yayi ya dubeta tama kawar da kanta gefe daga facing dinsa idanunta ya balle da ruwan hawaye miqewa yayi a ransa yana dannan zuciyarsa dole ya koyi rarrashi don alamu sun nuna masa Kuma yaji a bakin Ni'imah amaryar tasa yar shagwaba ce a sangarce take kuka bayayi Mata wahala idan Kuma akaqi bata hqr sai tayini tanayi kamar wata qaramar yarinya shikuma gashi ba gwanin iya rarrashin mace ba to ta inama zai iya shida ko rakiyar zance baitabayi ba Saida yazo kansa Kuma itadin daya kamata su daidaita su fahimci juna taqi bashi hadinkai da tuni sun wucce babin kansu saidai suji da Ni'imah yar tujara, Hannunsa yakai ya kamo hannunta ta fincike kamar wacce akayiwa allura ta balle da bala'i tana nunashi tace “zan zagi babanka idan ka qara tabani mara zuciya kawai Wanda aka dafa zuciyar kare aka bashi ya ciny....."
Wata tsawa ya daka Mata me hade da ihu data sanyata ja da baya yayi saurin dukan qofar da qafarsa ya fara matsarta tana janyewa Saida sukaje qarshen dakin ya damqi wuyanta idanunsa sun kada sunyi jawur jikinsa sai rawa yakeyi ya bude bakinsa dake tsuma yace “bana umarni sau biyu wannan shine na uku ki rinqa sanin kalmar da zaki fadamin duk so bazan dauki raini da wulaqanci ba ni ba qasqantaccen bawa bane da zaki rinqa jana a qasa kamar karenki dole ne Rafi'ah dole kisoni kiyimin biyayya domin Ni nan mijinki ne ba yaronki ba kuma ba dan iska baneni nida kike ganina bana daukar raini raini ma a gurin macen da nakeso kawai don nace inasonta wlh idan kika bari kikakai zuciyata qarshe zan wahalar da ruhinki Rafi'ah zaki kasa samun jin dadi ta ko Ina ni a gurina zaki samu farin ciki to nima nema kike ki qureni"
Sakinta yayi ya koma ya zauna yana huci taja ajiyar zuciya me qarfi iya tsorata ta tsorata dashi ta shiga taitayinta guri ya nuna Mata a hassale yace “ki zauna naceee!" Da sauri ta zauna yaja numfashi ya sauke muryarsa ya sauko gabanta ya Kama hannunta yana murza cikin a hankali ya