Showing 6001 words to 9000 words out of 66967 words
take waige waige ya fito ya jingina jikin motar ya harde hannunsa a qirjinsa tana juyowa suka hada ido yana sakar Mata wani ni'imtaccen murmushi gabanta ne ya fadi ta qaqaro murmushin qarfin hali ta tako ta tsaya a gabansa tace “yau a gari daga Ina haka hala dai daurin aure kazo?" Lumshe idonsa yayi ya bude gabansa shima na faduwa yace “wlh takanas dominki nazo"
Murmushin fuskarta ta dauke ta zuba masa ido tace “takanas domin ni kazo?" Jinjina Kai yayi da izzarsa ya bude Mata mota ta shiga ta zauna shima ya zauna yana kallonta da qananun lumsassun kyawawan idanunsa yace “takanas domin nazo na ganki naga lfyrki nazo Bestienmu ya karatu?" Numfashi ta sauke tace “babu sauqi wlh karatun medicine akwai wuya nadama nakeyi da na karbi ra'ayin Bestie na da bansha wahalar nan ba"
Hannunsa yakai ya kamo hannunta yace “meye wahalarsa" janye hannunta tayi tace “coursis din suna bani wahala" murmushi yayi yace “kinsan me?" Girgiza masa Kai tayi yaja numfashi ya kawar da kansa yace “akwai wani Abu da nakeji a Raina Amma ki jira lkc idan yazo zan fada Miki am bestie dinki tana gaisheki tace na tambayeki yaushe zakizo?" Kallon da yake Mata duk ya takurata ta kasa sakewa tace “zamuyi hutun brain zan dawo azare idan na dawo zanzo" dagowa yayi ya dubeta yace “gobe zamu tafi Abuja Amma zamuyi waya Koda yake ni zanke dawowa duk sati saboda Mai martaba" Jinjina Kai tayi tace “ok babu damuwa mun mayi waya dai da ita dazu Amma ka gaisheta" tana fadin haka ta bude motar zata fita ya riqo hannunta kawai ya janyota da gayya ta fado cinyarsa tayi saurin janyewa ya rintse idonsa yanajin wani sabon salon nau'in masifa yana shigarsa yace “ashhhh" kallonsa tayi da sauri. yayi murmushi tare da sakin hannunta ya daga Mata gira yace “kije ki huta abinki"
_Please share_
_More comments_
_More typing_
*_Ummuh Hairan_*
[1/2, 8:59 AM] Mrs AA Fansah: *_My Bestie's Husband_*
*_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
*_Free book_*
*_5-6_*
_Kullum saina fada wannan book din Free ne comment kawai nake buqata OUM HAIRAN PALACE 1 Bakwa comments wlh daga wannan page din idan baa gyaraba zan daina yimuku post kwake gani a moqota Ina gdy OUM HAIRAN PALACE 2 inayinku Allah yabar qauna kuci gaba da zuba comments nikuma zanci gaba dayi muku typing._
Kallonsa takeyi cikin tsananin ta'ajibi tace “me hakan yake nufi?" Bude idanunsa yayi da suka kada sukayi red ya motsa dan qaramin bakinsa tare da qanqantar da qananun idanunsa yace “like feels...." Gabanta yabada wani ras ta cije lebe tare da bude motar ta fita shima ya fito yana gyara hularsa ya bude but din har tayi masa nisa ya Kira wasu samari da suke qoqarin giftashi ya nemi alfarmarsu suka daukar Masa kayan suka bita jin alamun ana bintane yasata tsayawa ta juyo kawai sai ta ganshi sauke da kaya niqi² ta dan bata fuska tace “meyesa kake haka bana buqatar qarin komai Mr Ja'afar Wakil Ina da komai enough...." Saukar hannunsa a bakinta ne yasata daga qwayar idonta ta zubashu cikin nasa shima nata idon yake kallo ya qara yalwata murmushinsa dimple dinsa ya lotsa farar fatarsa ta fulanin azare da ta hadu da hutu sai glowing takeyi yace “duk abinda nayi niyya baa dakatar dani Ja'afar Wakil baison sorry please baison...."
Shiru yayi yanaci gaba da kallon qwayar idonta ta sauke numfashi qamshin turaren hannunsa yana ratsa hancinta ta sanya hannunta ta dauke nashi inda matasan suka ajiye Mata kayan a daidai qafarta ya zaro kudi me auki ya Basu sukayi godiya suka tafi jan hannunta yayi yayi kissing nashi ya juya da sauri yabar gurin ya barta da sanyayyiyar gwiwa mamakin lamarin mijin aminiyar tata takeyi gabadayansa ta kasa gane inda ya dosa tun ranar dinner take tuhumar kanta me wasu abubuwan da ya rinqayi suke nufi amma ta kasa ganewa,
Tabe baki tayi ta debi kayan ta shiga ciki zama tayi a bakin gadonta ta fara bude kayan daidai lkcn da Nina wata abokiyar karatunta ta shigo ta zauna a kusa da ita tace “kay Hajiya ta kina wanke garori fah wannan hadadden guy din fah Ina kika samoshi?" Tsuke fuska tayi tace “ke banson iskancinki fah mijin Bestie nane wlh" zaro ido Nina tayi tace.
“What wanne irin mijin aminiyarki me ya kawoshi gurinki?" Yarfa hannu tayi tare da tabe baki tace “nims bansani ba wlh nayi tunanin daurin aure yazo ko wani Abu amma na tambayeshi yace takanas danni yazo"
Jinjina Kai Nina tayi tace “na dade Ina kallonku fah ni wlh na dauka saurayinki ne Amma gsky akwai alamun tambaya a cikin kallonsa gareki Kuma fah shi namiji bayada tunani wani lkcn lissafinsu na abinda yayi musune basa lissafin meye zaiyi daidai da tunanin dan' adam nifa na hango wani Abu a qwayar idonsa Pretty anya bazaki dakatar dashi ba"
Numfashi taja ta sauke tace “ni kaina yasani a compus inata tunanin abubuwa mabambamta Amma idan na tuna wayeshi kuma na tuna alaqar dake tsakanina da matarsa da irin soyayyar da sukayi ta one month before aurensu sai na qaryata zuciyata nakan dauki abubuwansa a matsayin son farantawa bestie na tunda yasan cewa bata da farin cikin da ya wucce taganni cikin farin ciki wannan dalilin yasa nake qaryata mind dina Nina Ja'afar Wakil bazai aikata abinda zuqatanmu suke fadi mana ba kawai dai shidin haka yake meson damuwa da damuwar wani" a kusan tare suka sauke numfashi Nina tace “Uhm to! Da wannan don wannan Amma dai gsky kiyi takatsantsan Rafi'ah ni na hango abinda ke baki hango ba" da wannan suka fara duba kayan tayi murmushi tace “gashi kuwa ya iya siyayyar Mata bari na Kira Bestie na nasata tayi masa gdy" saurin dakatar da ita Nina tayi tace “idan kikayi haka zaki iyafa sosa zuciyarta kinsan ita batada qashi" harara ta galla Mata tace “ashema ba Bestie din nawa bace ai bazataji ko ta kawo komai ba kuma bari kiji"
Wayarta ta fito da ita ta latsa number Ni'imah bugu biyu ta daga tace “My Bestie yanzu sweet yake cemin yazo ya kawo miki ziyarar bazata" ajiyar zuciya ta sauke tace “eh wlh yanzu bai dade da tafiya ba kawai sai naga Kira unexpected na daga yace nazo na sameshi a two park Ina zuwa naganshi naji dadi sosai sai naji kamar ke nagani"
Murmushi tayi tace “inanan inata fama da tunaninki sai yanzu na samu nutsuwa gashi zamu wucce Abuja baki dawo ba" jikinta ne yayi sanyi taja numfashi tace “kiyi hqr Bestie kina Raina banzaci zan dade hakaba a school so kinsan karatun namu sai a hankali Amma nayi Miki alqawarin indai na dawo hutun section zanzo har Abujan nayi Miki sati guda" wani ihu Ni'imah tayi tace “amma dakin burgeni kinsan me?" Girgiza Kai tayi tace “aa saikin fada" dariya tayi tace “sweet ya dameni da mgnrki kullum sai ya tambayeni wai bakida tsayayyen saurayine da bazakiyi aure ba idan nace masa bakya kula samarin ne sai yacemin Wai to ko bakida lfyne nace masa qalau kike ya Kuma cemin Kuma idan kika samu mijin zakiyi sure Niko nace masa to ko yana cikine wannan tambaya haka"
Duk da gaban Rafi'ah Saida ya fadi Amma hakan be hanata qaqalo dariya ba tace kukam da abin dariya kuke kinsan kema bazai yuwu bane shiyasa kike fadar haka yanzu dai duk ba wannan ba yaushe zaki haifamin baby?" Dariya tambayar tabawa Ni'imah tace “wlh kinada abin dariya Bestie to ni yanzu yazaayi na sani abinda bani zanbawa kaina ba kuma ma yaushe akayi bikin har yanzu banyi cikakken 2 mouths ba har zaku dameni da maganar beby"
Hakadai sukayita wayarsu gwanin dadi a qarshe sukayi sallama kowacce ta ajiye Nina ta dubi Rafi'ah tace wato amintarku tana burgeni amma ga bisa dukkan alamu yanayin danagani yau da Kuma kalaman Bestie dinki yana nuna cewa lkcn katsewar wannan amintar yazo Rafi'ah mijin qawarki sonki yakeyi da gaske ko ki yarda ko karki yarda duk kalamansa na qaunane...."
Rafi'ah akwai zuciya batasan sanda ta Kai hanu ta bige bakin Nina ba tace “ke mahaukaciya ce bakida lissafi to ai abune da bazai taba yuwuwa ba kema kin sani kamar yanda Allah ya haramtamin auren mijin Raziqa yayata da muke uwa daya uba daya matuqar tana raye nikuma na haramtawa kaina Koda bata raye to haka mijin Bestie ya haramta gareni har gaban abada don Allah ki dainayi mana wannan mugun fatan mudai wannan qaddarar bazata ratso ksnmu ba"
Miqewa Nina tayi tace “karki yarda yanzu nsn gaba kadan Zaki gasqatani bana magana saina samu madafa" tsaki Rafi'ah taja dogo tace “bakinki ya sari sabon danyen kashi yar neman bala'i" tashi tayi ta fara shirya kayan daya kawo Mata a loccar ta bayan ta gama ta shiga wanka tana bathroom din taji wayarta na ring Saida ta fito ta dauka dake batayi saving number ba bata gane ba tayi sallama da sanyin muryarta
Amsawa yayi tare da cewa “Bestienmu na tafi da tunaninki kamar bakiji dadin zuwana ba ko?" Dariya tayi tace “kayy My Bestie's husband ya zaayi nace banji dadin ziyararka ba kawai dai naso ace da Bestie kukazo ne ins fatan kaje gida lfy" ajiyar zuciya yayi saukar muryarta na saukar masa da kasala yace “normal wlh wanka ma zanyi na kwanta kina bawa zuciyata aiki"
Shiru tayi tana tunanin kalmarsa kafin ta gama yace “don Allah tambayarki nakesonyi Rafi'ah please kada ki fadamin ba daidai ba shin meye yasa bakison kula samari?*
Dif tayi na tsayin lkc har saida ya maimata kalmarsa sannan ta sauke numfashi tace.
Bafa wani abu bane kawai har yanzu mutuwar yassar bata sakeni bane nakasa samun madadinsa a duniya" murmushi yayi me sauti yace “idan kika samu wanda yafishi zakiyi aure?" Tambayar tayi Mata bambarakwai tace “kamar yafa?" Fasali yaja yace “kinsan shi aure Allah ne yakeyinsa akwai wani abokina da ya ganki ya nunamin yanada interested akanki so shiyasa nakeson tabbatar da yardarki kafin na bashi number ki" daqyar ta bude baki tace “amma...." Katseta yayi da cewa “amma me baki shirya aure ba ko baki aminta da zan iyayi Miki zabin abinda yafi daidai daidai da rayuwarki ba? Rafi'ah kiyi Believe cewa komai yana faruwa ne bisa yarda da buwayar Ubangiji idan yaga damar yuwuwar Abu abune me sauqi kiga ya yuwu nidai roqona ki kwantar da hankalinki ki toshe kunnenki ki tsayar da ra'ayinki kinji?"
Yanda ya qarashe mgnr da sigar rarrashi yasata jan zuciya tace “ok na gde Mr Ja'afar Allah ya qara girma yaja kwanan me martaba" murmushi yayi ganin ya sameta da sauqi yace “yawwa koke fah kadafa ki dauki kalamai na na dazu kisasu a ranki tsokanace kawai Bestienmu ki huta sai anjima"
Dariya abin yabata a ranta tace “haba kokai fah Amma da ka fara fadarmin da gaba" sallar La'asar tayi ta fita zasuyi group discussion ita da abokan karatunta suka zauna sunata fama hankalinsu gabadaya ya tattara a discussion din saboda wani practical zasuyi me wahalar gaske sai shidda suka tashi mazan suka nufi nasu hostel din matan su uku Suma suka rankaya nasu suna tafe suna hirarsu yunwa takeji shiyasa tana zuwa ko wayarta data sanya a charger bata waiwaya ba ta nufi inda take girki ta kunna gass ta dafa indomie da taji ganyen alayyahu da albasa da kifin gongoni ta juye a flat ta dauko lemo cikin kayan daya kawo Mata ta zauna bayan ta dauko wayarta tanaci tana duba wayar saqonni ne guda uku.
Budewa ta farayi tana dubawa na farko sallama ce kawai na biyu ne akace “ina fatan kadaitacciyar halittar da Ubangiji ya samar da ita domin ni kadai tana cikin amincin buwayi gagara misali" na ukun Kuma wasu zafafan word ne da suke nuna irin halin da zuciya take ciki a halin da taga abin buqatarta amma ta rasa yanda zatayi ta furta masa, girgiza Kai tayi tanabin number da kallo baquwa ce a gurinta batada ita a contact dinta hakan yasa ta miqe kawai taje tayi alwala ta dawo tayi magrib bayan ta idar ta sake zaman azkar tananan zaune har isha tayi tayi addu'o'inta ta dauki wani littafi tana nazarinsa ba ita ta kwanta ba sai kusan biyu da rabi na dare kasancewar ta saba idan ta gama karatu takanyi nafila da karatun qur'ani tare da addu'o'i yawa yawan addu'arta tanayinta ne akan Allah ya tsareta daga rudin zamani da mutanen zamani Allah ya jarabceta da qaddarar da zata iya takance Allan daya dauki rayuwar abin qaunarta daidai lkcn da tafi buqatarshi ya musanya Mata da wanda yafishi alkhairi.
Wadannan sune manyan addu'o'inta saboda ita abinda ta sani Kuma ta dauka a ranta qarshen rayuwar jin dadin mace shine samun masoyi na gaske wanda tsanani da qunci ruwa da iska bashi sanyashi juya Mata baya, yana daya daga cikin dalilanta naqin kula samari saboda har yanzu tun bayan mutuwar Yassar bataga Wanda zai iyayi Mata sallamawar da Yassar yayi mataba bataga Wanda zai qaunaceta kamar yanda Yassar ya qaunaceta ba.
Lkcn da ta kwanta kamar koyaushe mafarkinta dai shine gatanan zaune tare da wani mutum jikinsa ke bayyana kyawunsa Amma fuskarsa ta kasa ganuwa a idanunta a gefe Kuma ga aminiyarta nan ta shigo da gudu da wuqa a hannunta tayo kanta wannan mutumin da bata ganin fuskarsa ya tashi ya dauketa da mari tare da janyeta daga inda take zaune inda ita Kuma Ni'imah ta daga wuqar ta sauketa a gefen cikin mutumin ya saki qara tare da sulalewa taga taga ya fadi tayi kansa da sauri tans kiransa fadi take “Beby ka tashi tashi Baby don Allah ka tashi...." Dakatawa tayi da mgnr jin saukar tsinin wuqar a nata cikin turtsetse da yake Shirin fitowa duniya kafin ta gama sulalewa taga itama Ni'imah ta daga wuqar ta cakawa cikinta
Daidai lkcn ta farka a firgice tare da dafe qirjinta da yake bugawa da qarfi tana addu'o'in neman tsari saboda wannan mafarkin kusan kullum sai tayishi “to Wai me wannan mummunan mafarkin yake nufi ne?" Ta tambayi kanta tare da fara kallon dakin daga ita sai Nina taja fasali ta koma ta juya wani bangaren ta kwanta tun daga wannan lkcn baccin ya qauracewa idonta ganin bazata samu damar komawa ba ta tashi ta sake dauro alwala dake ta kasance me yawan tsaiwar dare batajin gajiya wajen neman kusanci da ubangiji Rafi'ah tana cikin mutane masu neman kusanci da ubangiji ta duk wata hanya da tasan zats kusantasu.
Ta Jima tana nafila takin tayi sujjada tana addu'a cikin larabcinta me dadi take roqon Allah ya juya wannan mafarki nata Wanda ya zame Mata na wajibi ya zama alkhairi ga rayuwarsu ita da bestie dinta ya bayyana Mata gaskiyar abinda ya dade yana nuna Mata a cikin baccinta samada shekara uku tun mutuwar Yassar ta fara wannan mummunan mafarkin da takasa dainawa har yanzu Kuma baya canzawa kullum iri daya takeyinsa gashi ta kasa fadawa kowa, abinda ta riqe a ranta kawai shine akwai wani Abu da zai faru a nan gaba Wanda ubangiji yake haskamata ta shiryawa zuwansa abbanta yasha fada Mata cewa mafarkin shirme baa riqeshi gabadaya dole sai an manta ko farkonsa ko qarshensa ko tsakiyarsa Kuma baa maimatashi in yatafi ya tafi kenan.
Kiran sallar asuba ne yasata ta qarayin kasaqe tana Kai kukanta gurin ubangiji yau zuciyarta ta gama karyewa da wannan mafarkin nata har kuka tayiwa ilahi tans roqonsa ya bayyana Mata koma menene tasanshi ko zuciyarta ta huta da tunanin menene, bayan tayi sallar asubarne ta koma ta kwanta tare da dauka wayarta abin mamaki dake a silent take sanyata idan zatayi karatu Kira 10 text 5 tagani duk da number daya guda biyu ne kawai bada itaba daya number Bestie dinta daya Kuma na Ja'afar ne tana tunanin wanne zatabi taji wani saqon ya shigo ta budeshi da sauri.
_“duk da nasamu lbrn cewa ke ma'abociyar tsaiwar darece Amma inayi Miki tuni da ki qara qaimi wajen kusanta kanki da ubangiji nima zanyi hakan duk da kasancewar inada iyali Amma bazanyi qasa a gwiwa ba zan raba lkc na uku kamar yanda ma'aiki ya kwadaitar damu zan bata daya zanyi bacci na huta a cikin lkcnta biyu zanyi amfani dasu wajen neman sahalewar ubangiji wajen mallakarki cikin sauqi"_
Murmushi tayi ta duba lkc 1:24:am yayi Mata wannan saqon ta sauke ajiyar zuciya tace “na gde" ta sake bude wani ya rubuta _"ina addu'a Ina qara samun qwarin gwiwar fitowa takarar neman wannan babbar kujera da zata zamomin fahari a duniya tabbas idan na samu Rafi'ah matsayin Mata nasan Allah ya gama yimin arziqin duniya ko iya hakama yabarni na gode masa"_
Dariya tayi tana toshe baki tace “au haba da gaske?" Sake bude wani tayi _“Iya wuya zan jure kowacce kalma daga bakin duniya domin cikar burina kedin ke nakeso Kuma ke na faraso Rafi'ah meyesa bakizomin a farkoba kikazo a qarshe?"_ murmushi tayi ta bude wani Wanda dagashi sai na qarshen ya rubuta _“indai na kasance ni dake bana iya yaqar zuciya My Raf inada naci akan duk abinda zuciyata ta aminta tanaso Ina fatan bazan dameki ba kuma bazaki qosa dani ba ni namiji ne na gaske inada naci My Wife....."_
Murmushi tayi ta bude na qarshen _“Hi Assalamu alaiki Qurrah ki shirya tarata yau zan kawo miki ziyara yau bazan iya barin Bauchi banganki ba"_ zaro ido tayi tare da miqewa zaune tace “nashiga uku aa wlh yau inada lecture tun safe har magrib banida Interval" miqewa tayi ta fada wanka ta shirya cikin doguwar riga me masifar kyau dayi rolling kusan shigarta kenan ta dan gyara fuskarta tasa lipstick ta dauki littafanta ta fice ta nufi hall din da zasuyi lecture din mamakine ya kusa sata faduwa batayi nisa da tafiyar ba ta fara hango Ja'afar Wakil tsaye jikin mota shida wata budurwa ta duba agogo 8:30am taka zuciya yanda ya kafeta da ido bata Isa ta wucce ba dole jikinta a sanyaye zuciyarta a jagule ta matsa gabansu tace “Mr Wakil lfy da sassafe haka azare da Bauchi da nisa Ina Bestie na?" Kallonta yake yakasa qiftawa ganin yanda yake kallonta yasata duba jikinta tace “lfy Mr Wakil?" Murmushin gefen baki yayi ya kalli yarinyar ta matso gabanta ta Kama hannunta tace “morning princess Aunty