Showing 66001 words to 66967 words out of 66967 words
na sha biyar ne aka kirashi a waya ake fada masa anga gawar Rafi'ah da danta a jejin Dambuwa daga tsaye ya yanke jiki ya fadi shine har yau Bai qara lfy ba.
Jamal ne ya biyosa yake jinyarsa kwanansa ashirin yaji sauqi sauqi aikuwa a ranar ya turawa da Ni'imah saqon sakinta uku harda qarawa da cewa “dama Ina zaune dakene arziqin Rafi'ah tunda na rasata kema dole kibarni nayi rayuwata ni kadai ki nemi miji kiyi aure Ja'afar na Rafi'ah ne ta mutu ta barni zan jira ranar mutuwata mu hade da ita a darussalam" wannan saqo ya rikita Ni'imah ta rinqa kwarara ihu an dauka na iskanci ne Ashe qaiqayine ya dawo kan masheqiya tun ana daukan abin yanzu anjima har Abu ya tatura ta fara surutan tonan asirin kansu tashin hankalin da kowa ya shiga ba kadan bane aka rinqa Allah wadarai da halinsu.
Daqyar Abba ya rarrashi daddy Ni'imah ta koma gdansa Yana tur da Allah wadarai da halinta ita da uwarta aka rinqayi mata magani amma Babu sauqi Abu sai gaba yakeyi dole sai daki aka ware Mata aka rinqa Kiran malamai sunsyi Mata ruqiyya aljani kuwa yaci laya akan bazai barta ba tunda Rafi'ah tafi qarfinsa ai dama Saida sukayi sharadi shi baya zama hakanan batare da ya kada wani juji ba sukace sunji sun gani saboda haka Babu inda zashi Abu kamar wasa Abu sai gaba yakeyi takai tana tsigar gashin jikinta da kanta tana cinyewa kusan shekararta guda a haka sannan aka samu daqyar wani malami ya rabasu Amma me yana barinta ya koma kan Hajiya Fatsum.
Tashin hankali Ashe ga inda ake hauka can tuburan rawa da juyi takeyi tana yagar jikinta tunda akayi katari ta falle daga gdan sarautar har yau baaji duriyarta ba, inda Ni'imah take cikin tsananin nadama mabayyaniya son zuciya da zugar jahilan iyaye takaita ta baro gashi tayi uku babu babu mijin da take hauka akanshi babu aminiyarta babu auren Kuma babu mutunci da qima saima tarin tsana da qyamata da take fuskanta gurin mutane.
Tazamo kamar mujiya gurin dangi da mutanen gari daga ita har uwarta babu me musu dariyar rahama saidai habaici da shagube wannan abu nasata kukan tashin hankali takan dade tana tunano rayuwarsu ta baya da Bestienta da irin alqawuran da suka rinqa yiwa juna takanyi nadama tare da tambayar kanta meyesa tayi kaza meyasa ta yarda aka zugata tayi kaza ina zataga Bestienta da gaske Bestienta ta mutu ta sanadin mugun abinda sukayi Mata?
Tana tuna haka saita qara rushewa da kuka itace asalin asararriya mara gatan rahama data shiga tsakanin ma'aurata ta zamo silar sanyasu baqin ciki tabbas ta Debi kaya me yawan da batada me sauke mata, gabadayanta tayi sanyi bata iya komai sai kuka takan tuna a baya idan ta shiga mawuyacin hali Rafi'ah ke Bata shawara yanzu babu Rafi'ah waye zai bata shawara takanji dama hqr tayi da Ja'afar tun a farkon farawa kafin ya aureta data gane qawarta yakeso tabarshi ya auri aminiyartata da yanzu duk hakan bata faru ba Amma son kanta yasata qin gane kuskurenta Saida ta aikata kuskuren daya zarta kuskure.
********
A bangaren Rafi'ah kuwa shaquwa qara shiga tsakaninta takeyi da Jamal dole tasa ya hqr da mgnr soyayya ya dauketa kawai matsayin qawa mamaki yakanyi da wasu abubuwa da takeyi daya shafi harkokin lfy yakance Mata a Ina tayi karatun medicine sai kawai yaga ta fashe da kuka tace “tabbas nayi karatu Jamal Kuma mijina ma babban likita ne Amma na kasa tuna wani Abu daya shafeshi ko ya shafeni Jamal mijina fitaccen mutun ne fah Ina tuna kamar ya mutu kamar Bai mutu ba" bayason yawan furta masa mijinta mijinta da takeyi shiyasa yake basar da zancen ya aunata a abubuwa da yawa sai yaga ta wucce tunaninsa.
Yau tun safe yake tunanin meye yakamata yayi Mata Wanda zataji dadi, murmushi yayi yayi ya gama ayyukansa ya Isa gidansu tana harabar gidan tana wasa da danta Bari'ah daketa faman laulayi na gefe tanashan lemun tsami ya shigo ta tsaya da buga ball din yayi parking ya fito Mahir ya nufeshi da sauri yana kiran “Abba oyoyo" daukan yaron yayi yana cillashi sama ya zauna suka gaisa da Bari'ah ya dubi Rafi'ah yace “maman dana inason mgn dake" tsuke fuska tayi yayi murmushi yace “banan na nufaba hajjaju am ko kinada intereste akan aiki?" Saurin kallonsa tayi sai Kuma tayi dariya shima dariyar yayi yace “akwai sabon asibitin da Yaya Ja'afar ya bude anan jikin pharmacy dinmu Rafi'ah Memorial Hospital so muna buqatar ma'aikata shine nake ganin kamar kinada rawar takawa idan babu damuwa zan baki gurbi a asibitin kema kya rinqa rage kewa Amma me kika gani?"
Wani ihu tayi ta rungumeshi tana dariya shima dariyar yayi yace “kinqi aurena Kuma kina susutani meye yasa Anya kinamin adalci" nandanan ta hadiye murnarta tace “bazaa aureka badin ni ta mijina ce shishi kadai" kawar da zancen yayi yace “zan gama Miki komai ranar litinin ki fara zuwa aiki kawai" sosai taji dadi Kuma tayi masa godiya har ya miqe tace “amma Jamal banida takarduna a hannuna da mijina ya tashi mutuwa dasu ya mutu" dariya sukayi duka yace “bazan baki inda zakike aiki me wahala ba saboda gudun shirme ni inaji ma a lab zan barki" dariya sukayi ya kalleta yayi murmushi ya shiga mota ya tafi.
Binsa tayi da kallo Bari'ah tace “yana bani tausayi sosai Rafi'ah yaqi hqr da wahalta Miki ke Kuma kinqi hqr ki karbeshi don Allah ki bashi dama ko yayane" ajiyar zuciya tayi ta zauna tana matsa Mata qafa tace “uwar biyu bazaki gane ba ne kawai Allah bazan iya hada soyayyar wani data Abu Mahir ba ki barni kawai" sanin idan ta cika mgn fushi zatayi da ita yasata yin Shiru kawai sukaci gaba da hirarsu tna bayyana jin dadinta da aikin da Jamal yabata wannan kenan.
_Comments_
_Share_
_Voting_
*_Ummuh Hairan_*