Showing 45001 words to 48000 words out of 66967 words
da lura da qasashen turawa da larabawa sunfi harkokinsu da dare,
Wani shagon siyayya suka shiga ya lodo Mata kayan sanyi suka fito ya sake biyawa wani gurin ya siya musu hot coffee sannan suka nufi masauki suka fara sabuwar rayuwa dakanta ta fahimci Ashe sunso suyi ganganci subarshi ya taho shikadai itama da take mace yanayin azabar sanyin yana sata shiga yanayi bare shi namiji lafiyayye dole ya buqaci dumin mace a jikinsa aikuwa tanacin ubanta babu qarya danma yañada tausayi idan yaga ta shiga yanayi yakan qyaleta.
Satinsu biyar a qasar Mexico ta fara rashin lfy ta gaske da farko ya zaci weather dince ta dameta ya rinqa lodo mata kayan sanyi yana siyo Mata duk wani nau'in abinci da zaisa ta rage jin sanyi Amma daga bisani saiya fahimci ita sanyin ma takeso batada aiki sai kwanciya a qasa shan ice da sauran abubuwan sanyi ga rashin cin abinci sai tayi kwana uku bataci abinci ba saidai ice ki jus sosai ya shiga damuwa,
To yauma tun safe ya fice sha'anonin daya kawosa qasar ya matsu ya gama su tafi shi tunaninsa duk wannan yanayin ne yasata shiga ha'ula'iYana wajen harkokinsa yaji hankalinsa yayo wajenta ya dauki wayarsa ya kirata bugu kusan biyar bata dagaba abin ya tsumashi dole ya ajiye komai ya nufo hotel din da sauri ya haura saman ya bude dakin ya shiga bata parlourn hakan yasashi fara kiranta Amma Shiru bude qofar dakin yayi gabansa ya yanke ya fadi hangota da yayi kwance a qasa a sume bakinta sai fitar da kumfa yakeyi,
Da mugun gudu ya qarasa gareta ya ciccibota jikinsa yana Kiran sunanta a gigice yana jijjigata cikin tashin hankalin dabai taba shigaba, dagata yayi cak ya fito waje da gudu da ita ya nufi emergency care din cikin asibitin suna ganinsa suka tareta aka dorata a gadon tura marasa lfy suka shiga da ita wani daki suka dorata a gado tare da jorner Mata na'urori shikuma sai danna qirjinta yakeyi, jinyeshi likitocin sukayi duk da kasancewar bangarensa ne tashin hankalin da yake ciki bazai barshi ya bata taimakon da take buqata ba,
Duk wani taimako na gaggawa Saida suka gama batashi ta fara sauke numfashi sukayi ajiyar zuciya tare da likitocin dashi ya matso yana zana musu irin sign din da ciwon ya fara bayarwa kafin ta kwanta hakan yasasu fara bincikarta cikin saa kuwa bincikensu ya nuna musu ai shigar ciki ke gareta na wata daya da awanni goma sha daya.
Wani ihu Ja'afar ya saki tare da yiwa Allah godiya ya rungumeta sai hawaye sharr ya sumbaceta yace “ni...Ni dama nasan aurena dake akai wani Abu me qarfi Allah baya hada lamarinsa a banza Allah na gde maka daka azurtani da samun qaruwa da mace mafi soyuwa a Raina Allah ka kareminsu ka tsareminsu daga sharrin duk wani abinqi" sake matseta yayi a jikinsa hawaye ya kwaranyo mata tun dirarsa ya tasheta taja ajiyar zuciya tare da qara gasqata girman Ubangiji tabbas Allah buwayi ne gagara misali burin Ni'imah kenan da anyi aurenta da Ja'afar ta samu ciki ta haifi Lil Prince Ashe ba haka Allah ya shirya ba ita da bata taba zataba bare ta kawo ita qaddara ta zaba a lissafin da likitan yayi ma ranar farko daya Santa mace ranar cikin ya shiga tabbas girman buwayar Allah abar jinjinawa ce.
Dagota yayi jikinsa cikin sanyin murya yace “har yanzu bakya sona Rafi'ah meyesa kika kasa koyawa zuciyarki son mijinki me sonki da qaunarki uban yayanki Ja'afar haba Rafi'ah me nayi Miki da kika kasa yafemin ne" rungumeshi tayi ta saki wani Kuma me ciwo tace “ni...nifa ba sonka ne banayi ba inajin tsoron Hajiya ta gane da gaske inada cikinka a jikina JM kasheni zatayi bata qaunata...."
Rufe Mata baki yayi da nasa ya lumshe qananun idanunsa itama ta lumshe nata sun jima a haka kafin su saki bakin juna yaja numfashi yace “bandamu da kowa ya tayani sonki ba nidai inasonki Kuma nine zan rayu dake matata ki cire kowa a ranki don Allah ki manta da kowa kinji?" Dagansa Kai tayi yayi murmushi yace “bari nayiwa Hajiya Innah albishir nasan zata tayamu farin ciki" da sallama ya fara wayar suka gaisa yace “wlh tananan da sauqi muna asibiti ma batada lfy Lil Prince yana wahalar da ita" dariya yayi yace “aa Innata kawai dai na fadane ko Prince ko Princess duka Wanda Allah yabani Ina murna" sun jima suna waya tanayi masa fadan rage zafin zuciya me ciki batason yawan fada da fushi hakan yana dabi'antuwa ga yaron dake cikinta idan San samune ma zaifi su yawaita karatun qur'ani hakan zaiyi tasiri wajen halittar yaro zai dabi'antu da hakan sosai.
Godiya yayi Mata ya miqawa Rafi'ah wayar a kunyace suka gaisa tayi Mata fatan alkhairi suka aje wayar ya sake Kiran qaninsa Jamal ya fada masa amaryarsa tanada ciki steel ya sake Kiran Muhseen ya sanar dashi kafin dai wani lkc mgnr cikin ta cika wannan family Hajiya Fatsum itace qarshen Kira dake taji lbrn gurin Jamal saitaqi daga wayar sai text ya tura Mata tayi tsaki tace _“tsiyar zanwa fatan alkhairi?"_ tura Masa tayi ya duba sosai zuciyarsa na tafasa cije lips dinsa yayi yace “tsiya! tsiya!!" Numfashi ya sauke ya miqe ya fita bai jimaba ya dawo yana kallonta tayi qasa da kanta yayi ajiyar zuciya kallonta kawai yana kwashe masa damuwar da yake ciki zama yayi a gabanta yace “bansan me bebie na yakeso ba a fadamin na tafi ns Nemo" Lumshe idonta tayi tace “Abbansa yake feel....."
_More comments_
_More typing_
*_Ummuh Hairan_*
*_37-38_*
_____________________________
_____________________________
Abin ya bashi dariya sosai yayi abarsa ta zuba masa ido yayi qiba sosai ya qara haske abinka da farin mutum ta sauke ajiyar zuciya tanajin wani yanayi game dashi, batayi aune ba taji ya dagota cak ya dauketa kamar babie ya sunkuyo da kansa daidai fuskarta ya sauke Mata kiss me zafi yaja numfashi yace “bansan me zanyi ki gane irin farin cikin da nake cikiba Rafi'ah inason babien nan na cikinki tabbas shine asalin raba gardama ga duk me hankali yasan cewa zafin rabo shine ya rinqa azalzalar zuciyata Saida na mallakeki sonki da sha'awar kasancewa dake suka hanani duba kowace irin alaqa tabbas inajin cewa da wani qaddara ta gifta dana kasa samunki da zanyi Miki fyade Kuma zaki samu ciki to sai Allah ya dubi kyawun niyyata ya qadarta zamowarki matata mace mafi daraja aguna"
Lumshe idonta tayi yayi murmushi tare da direta a gadon yace “inasonki Rafi'ah kema kinasona?" Rufe idonta tayi da hannunta tana dariya shima dariya yayi ya miqe yace “har yanzu nakasa samun wannan kalmar kina Sona ya gagareki furtawa ko?"
Ficewa yayi ta miqe ta shiga bathroom tayo alwala ta dawo tana duba alqibla ya shigo da kaya a Hannunsa ajewa yayi yana kallonta ta tayar da sallar bayan ta idar ya matsa gabanta ya fito da kayan daya shigo dasu tarkacen ciye ciyene ya rinqa bata wanda zata iyaci ta karba Wanda bazata iyaba ta kawar dakai da haka saida ta qoshi sannan ya qyaleta.
Likitan ya Kira yabasu sallama suka fito tana kwance a jikinsa suka shiga dakinsu suna shiga ta fada gado duk jikinta batajin qarfinsa shikuma ya fada wanka lkcn daya fito har tayi bacci ya dubi agogo 10:30pm ajiyar zuciya yayi ya haye gadon ya janyota jikinsa ya matseta yana shafa bayanta zuwa mazaunanta ta sauke ajiyar zuciya tare da bude idonta Dora bakinsa yayi saman idon nata yace.
“ke kikace babie na ni yake buqata" turo baki tayi tace “aa nifa wasa nakeyi maka banajin feel naka..." Rufe mata baki yayi yace “ni inaji" daga haka Bai qara bata damar mgn ba ya kashe musu fitila sosai ya sanyata nishadi salonsa yana tsaya Mata arai bata iya bijire Masa dadine me ratsa kwanya yake bata itama tana tayashi Saida suka samu nutsuwa sosai sannan sukayi wanka suka kwanta.
Wayarsa da tun farko fara harkokinsu take ruri ya dauka ganin number Ni'imah yasashi tsaki kawai ya sata a silent ya koma ya kwanta ya sake rungume matarsa wayarta ce itama ta fara ruri gashi ya hanata tashi bacci ne ya sakeyin dama dasu Basu suka tashiba sai asuba sukayi sallah suka sake kwanciya 11:00am suka tashi sukayi break ya fice ita Kuma ta danyi abinda zata iya ta sake kwanciya tare da janyo wayarta.
Missed calls tagani sunfi hamsin ta fara dubawa kusan duk na Ni'imah ne tayi murmushi tare da latsa layin Kira daya ta daga tace “sai yanzu kikaga damar daga wayar tawa?" Murmushi tayi tace “wlh kinsan dake ba zaman kaina nakeyi ba lkcn da kika Kira Ina tare da mijina shiyasa..." Wata dariya Ni'imah tayi tace “kaji fah masu miji mijine dake ko farka da akaga dama aka baki aronsa to bari kiji na fada Miki wani abu dole idan Mai fili yazo me trader ya dauke abarsa domin kuwa shi kansa yasan bazaiyi jayayya dame contenar ba to kamar hakane tsakanin ni dake nice me Ja'afar nice matarsa ta farko saboda haka shidin nawane ko kina da ja?"
Rafi'ah bataso kulata ba Amma idan ta barta haka tabbas zata siyawa kanta raini numfashi ta sauke tace “tabbas hakane kece matarsa ta farko bazaa taba canzawa tuwo suna ba saidai kinyi zuqu baki tsaya a iyakar matsayinki ba kinaso ki shiga nawa bawai Ina fada Miki bane dominsa aa Ina fada Miki ne domin ki kiyaye harshenki Ni'imah Ja'afar nawane zuciyarsa da ruhinsa dukka mallakinane domin ni aka haliccesa ki riqe wannan aranki akwai ranar da zaki maimaita dakank....."
Katseta tayi da cewa “hhhhh taqamarki waike kinyi ciki ko lallai yarinya to bari kiji wlh sai naso zaki haifesa banza sakarya yar fashin miji kawai"..... Qit ta kashe wayar murmushi kawai Rafi'ah tayi tace “shashasha kawai" Kiran Anti Raziqa tabi tana dagawa tace “uwar hudu tun jiya nake kiranki baki dagawa saraki ne ya hanaki ko?" Murmushi tayi tace “aa a silent na sata sai yau dana danji qwari naketa bin Kira kema ya fada Miki kenan"Sun jima suna waya sukayi sallama ta sake Kiran ta Ammi itama dai murnar samun cikin tayi Mata kunya kamar ta nutse Ja'afar bashida kunya duk ya gama bazata a duniya yanzu kowa yasan meye sukayi har suka samu cikin, sosai Ammi tayi Mata nasiha akan ta qara kwantar da hankalinta su zauna lafiya da mijinta da abokiyar zamantasannan tace abbanta yana gaisheta shima jiya bayan Ja'afar ya kirashi ya fada masa ya kirata Bai sameta ba, a kunyace suka gama wayar bata qara tsinkewa da lamarin Ja'afar ba Saida wata wayar ta shigo ta daga tare da sallama jin muryar babban mutum ya amsa yasata shan jinin jikinta,
Gaisheshi tayi ya amsa da muryar Isa ya jima sannan ya sake jan numfashi yace “Sannu Rafi'atuh dama haka Allah yake ikonsa Allah ya rabaku lfy yabaki lfyr shayarwa da tarbiyya Allah ya tsareku da tsarewarsa jiya magaji yake fadamin na kirashi ban sameshi ba idan yazo kice nace munason takwara idan namiji ne idan macece Kuma to munason princess dinmu ta zama tayi halin uwarsu Innah saboda haka munason asa Mata Nana Hafsatu" itadai a kunyace take amsawa sosai Mai martaba yayi musu addu'a sukayi sallama Saida ya aje wayar sannan ta kashe tata cike da mamaki Ja'afar yawucce tunaninta.
Nan ta yini zaune waya ta ko Ina yimata akeyi hatta Hajiya Kaltume Saida ta kirata tayi Mata fatan alkhairi kowa a gidan murna yakeyi zasu fara samun jikan da namiji Lil Prince zaizo qasan zuciyar Kaltume baqin cikine fal duk qudurinta ya rushe idan har ta kuskura tayi saken da Ja'afar ya fara haihuwa shikenan mulki zai koma gurin Zuri'ar Fatsum sukuma sun tashi a tutar babu kenan, tashi tayi tana kaiwa da komowa tabbas dole tayi wani Abu akan Wannan lamari dole zataja Rafi'ah a jikinta ta hakane zata samu cikar burinta Ja'afar ya jima yana bata barkono ya jima yana cizon zuciyarta idan tabarshi yashata bisillah ta cutu batada hanyar ramawa saita hanyar raba tsakaninsa da Rafi'ah domin ta fahimci duk duniya babu abinda yake qauna kamarta Rafi'ah itace jarrabarsa ita kadaice zaa taba duniyarsa ta girgiza.
Murmushi tayi tace “Kulsum matanadar makirci Ja'afar lkcn daukar fansa yayi tabbas zaka gane ka tabani" mayafinta ta dauka ta fita ta shiga bangaren bayi ta Kira jakadiya tayi Mata ihsani tace Mata lallai yau tanason ganin Mai martaba, dariya jakadiya tayi tace “ai kin biya uwar dakina jeki jirani yanzu zan dawo da sakamako" murmushi Hajiya Kaltume tayi ta koma ta zauna tana karkada qafa awa daya bata cika ba saiga Jakadiya Indo tana rawa tana juyi tace.
“Anyi nasara uwar dakina ki shirya kije kawai" tafawa sukayi tace “ki jirani gobe zamu tattauna dole wannan aikin sai kin shigo ciki so nake na tarwatsawa Magaji farin cikinsa gabadaya na hanashi samun nutsuwa a duniya kamar yanda ya hanani amaryarsa tanada ciki nasan kin samu lbr don jiya yini akayi ana celebrating a gdannan zanyi duk me yuwuwa na zuge Mai martaba yasashi dawo da ita amaryar gidannan ta hakane zan samu damar janta jikina so nake nayi amfani da ita wajen ganin bayan mijinta"
Jinjina Kai Jakadiya Indo tayi tace “zaki iya uwar dakina Amma fah ance yarinyar batada sabo naji suna fada"
Murmushi Hajiya Kaltume tayi tace “babu ruwanki da rashin sabonta ki bari na gama aikina sai na baki naki kedai kiyi qoqari kiga kina nadomin abinda waccan makirar take ciki idan nasan abinda suke shiryawa shine nima zanyi amfani da hakan nayi nawa cikin sirri" Jinjina Kai Jakadiya tayi sukayi sallama ta tafi.
Itakuma ta fara shirin tafiya gurin me Mai martabaBayan ta gama komai ta hada masa zobo me dadi da sanyi ta nufi turakarsa sai zuba qamshi takeyi ta qwanqwasa yayi Mata iso ta shiga yana zaune saman sallaya yana lazumi ta samu guri gefensa ta zauna ya dubeta ta sunkuyar dakai yayi murmushi ya ajiye carbin ya dubeta yace “Uwar gida saqonku ya ishemu dazu ta wajen su Jakadiya muna fatan dai lfy?"
Qasa tayi da kanta ta tsiyaya lemon a Kofi ta miqa Masa ya karba tayi farr da ido tace “lfy ranka ya dade kawai dai inason ganawa dakai ne saboda an kwana biyu baa zauna ba balle a shawarci juna" shanye zobon yayi yace “wannan gaskiya ne Kaltume to ai kudin ne kun fiye rigima shiyasa muka rabu daku" dariya tayi tace “to ranka ya dade ai baayi haka ba tunda Allah yabaku amanarmu ai sai kunyi hqr damu"
Murmushi yayi yace “hakane Allah ya qara Mana hqr" Hira sosai ta barke tsakaninsu inda cikin hirar ta lura duk Rabin maganarsa akan cikin da matar Magaji ta samu ne ba wani dadin hirar takeji ba Amma haka ta rinqa daurewa tana nuna masa dokinta akan cikin nandanan zuciyarsa tayi wasai saboda duk Wanda ya nuna yanason cikin jikin amaryar dannasa dadi yakeji, Nan ta samu dama tace “am dama Mai martaba nikam idan ka bani dama na kawo mana wata shawara Mana" dubanta yayi yace.
“To kaltume muna sauraronku" numfashi taja tace “duba da yanayin auren Yarannan Rafi'ah da Ja'afar da Kuma quruciya ni sai nake ganin tunda muna raye baikamata abarsu a gefe ita dashi suyi rainon cikin nan ba yakamata manya su shiga ciki domin zatafi samun kulawa ita da jikanmu dake cikinta" Jinjina Kai Mai martaba yayi yace “gaskiyane" sake qass tayi dakai tace “Me zai hana ya dawo da ita cikin gdannan idanma bazai bari taje wani bangaren cikin gidan ba tayi boffiɗonta acan ba to ta zauna a bangarensa na cikin gidannan kaga yafi kusa Kuma zatafi samun kulawa fiye da can da suke daga ita saishi dai kishiyar tata Kuma ba zaman lfy sukeyi ba kullum cikin fada suke saboda ita Ni'imah gani takeyi Rafi'ah taci amanarta to kaga ba wani kulawa zata samu ba kuma ma Koda zaman lfyr ai dukkansu yarane ba tabayi sukayi ba ita haihuwa irin wannan sammatsi gareta Allah shine me karewa saidai sa idon yanada amfani gaya"
Shiru Mai martaba yayi yana nazarin kalamanta can ya dago yace “kinyi tunani me kyau zamu duba sosai" da wannan suka shiga tattaunawa akan abinda ya shafi cikin gida tana qara tura Masa ra'ayin dawo da Rafi'ah cikin gdan.
Bangare Ni'imah kuwa tunda ta samu lbrn tabbatar cikin Rafi'ah ta tashi hankalinta ita da uwarta da surukarta babu dare babu Rana suna yason bin bokaye duk bokaye sun kasa sama musu mafita sai guda dayane yayi hobbasan yi musu alqawarin yiwa Ja'afar din kiranye ya dawo gida idan har ya dawo zai sauka a bangaren Ni'imah to duk abinda ta bashi zaici wannan karon ba asiri zasuyi ba tsafi ne Amma sai Ni'imah ta yarda an zuqi jininta zaa hada laqani dashi.
Wa'iyazubillah Allah kayi mana tsari da shirka, aikuwa haka tabada hannunta bokan na dutsen shadan ya zuqi jininta ya hada da wani qarin magani yace taje tayi turaren gabanta dashi ta tabbatar ya kusanceta to daga haka ksda ta qara komai zataga zuwan da zowar Amma kafin turaren ta gauraya ruwan rubutun daya Bata da abinci ko lemo ta bawa Ja'afar din yaci.
*_MEXICO_*
Yau laraba ce a Maxico 21/3/ wanda yayi daidai da watannin uku a Mexico suna parlour a zube tana kwance saman jikinsa yana shafa cikinta da ya dan fara dago mararta yanajin dadi sosai Wai shima ya kusa zama Dad murmushi yayi yanajin qauna da tausayinta yanda cikin nasa ke wahalar da ita yace “ina tausaya Miki Bestie babie na yana wahalar dake over" lumshe idonta tayi tace “ni baka wani tausayina bayan baka dagamin qafa"
Rufe Mata baki yayi ya dagata ya shiga da ita ciki yace “ok haka kikace" Nan fa suka rinqa kokawa daqyar yakaita kasa yaja musu bargo yana Mata dariya yace “sabida Kinga jiya na qyaleki shine kika samu bakin mgn" da turje turjen da komai ya rabata da komai sukayi komai ta miqe tana mita ta shiga bathroom tayi wanka shikuma bacci ya daukeshi bayan ta fito ta sanya kayanta itama ta kwanta ta fara bacci taji ya zabura ya miqe da sauri itama miqewa tayi taganshi riqe da kansa yana furta “a'uzubillahi