Showing 51001 words to 54000 words out of 66967 words
bata ikon juyawa mijinta baya a kowanne hali, saida Rana ta fito sannan ta kwanta takuwa Jima tana bacci ba ita ta tashi ba sai 12:00pm wanka tayi ta shirya cikin wata baqar doguwar riga ta zura hijjab dinta qato sannan ta dauki wayarta har yanzu gabanta faduwa yakeyi tayi Bismillah ta Kira lambar JM Kira daya ya daga muryarsa wasai yace.
“Maman Twins kin tashi lfy?" Murmushi tayi ta sanyaya muryarta tace “har naji sanyin dadi ya ratsa zuciyata dana tabbatar da cewa Daddyn twins ya tashi lfy" dariya yayi ya dubi Ni'imah da ta wani hade rai yace “tun jiya zuciyata tana gurinku keda BBY na yar'uwarki ta riqeni ta hanani zuwa naganku" abinka da kishi da bashi da kadan sai taji zuciyarta ta sosu dake tana da wayo sai tayi murmushinta da tasan yana kashe Masa jiki tace.
“Allah Sarki mijina nasan muna qasan ruhinka kada ka damu kabata lkc sosai ai ta cancanta am dama nace idan babu damuwa inason shiga cikin gida mu gaisa jiya duk sun shigo harda Hajiya Babba" gabansa ne ya fadi yace “hajiya babba kuma? Me tace Miki?" Ajiyar zuciya tayi tace “babu komai kawai dai ta kawomin agwaluma ne Best Kai dan gatane kowa tattalin unborn dinka yakeyi"
Ajiyar numfashi yayi yace “ok kije Amma ki kula da kanki nifa don Mai martaba ya dage ne hankalina bai kwanta da zamanki a gidannan ba Rafi'atuh zuciyata taqi nutsuwa" fasali taja ita kanta bataji tata zuciyar ta yarda ba Amma saboda burinta kullum qarfafa masa gwiwa sai tace “karka damu insha Allahu zamu kasance cikin tsaro da kariyar Ubangiji" wani gwauron numfashi yaja yace “banajinki Amma ki jirani ganinan zanzo saina rakaki ko Ina"
Yana fadin haka ya miqe ya fice yabar Ni'imah da sakakken baki cike da mamaki mota ya shiga zuciyarsa na ayyana Masa abubuwa da yawa game da Rafi'ah yana murmushi gabadaya jinsa yake kamar Wanda ya rasa wani bangare na jikinsa iyakar kwana biyu da yayi ba tare da ita ba musamman daren jiya daya kasa rintsawa tunda yake baitabajin irin yanayin daya kasance jiyan ba wani bangare na zuciyarsa yayi masa nauyi yanajin wani Abu daya kasa tantancewa idan ya rufe idonsa Rafi'ansa yake hangowa cikin wani yanayi na tashin hankali hakanan zai zabura ya miqe ya sake kwanciya sai ya ganta dauke da wani kyakkyawan farin yaro me kama dashi cikin wata rijiya me zurfi ga wani duhu yana mamaye rijiyar tun yana jiyo ihunsu da salatinta tana Kiran sunansa har yakar da yadaina ganinsu da jinsu gashi an Tara mutane anyi anyi à daukosu ankasa shikuma sai hanqoron binsu yakeyi Hajiya Fatsum da Ni'imah sun daddaure shi wani abin haushi ya kasa qwacewa sai hanqoro yake da ihu Amma ya kasa samun mafita
Can nesa ya hango Hajiya Kaltume ta nufo rijiyar gadan² da wani ice yanaci da wuta ta cilla a ciki inda kafin ya dira qasa ita Kuma Hajiya Innah tayi tsalle ta fada rijiyar ta cafo itacen tayo sama dashi ta jefi sarqar da aka daureshi da ita take sarqar ta tsinke ya kwace da gudu ya nufi rijiyar..... A daidai nan ya farka yayo alwala ya tada sallah domin mafarkin ya tsoratashi firgigit yayi saboda horn din da yaji anata doka Masa dubawa yayi yaga ashe tsayawa yayi a tsakiyar titi numfashi ya sauke yaja motar ya qara gaba.
Shiga fadar sarkin qofar bangaren nasa ya bude Masa ya shiga yayi parking ya bude motar ya fito taka qafar da zaiyi yaji kansa ya sara gabansa ya yanke ya fadi take yaji zuciyarsa tana tafasa “ Innanillahi wa innah ilaihirraji'un" ya rinqa karantawa har ya murda qofar ya shiga ko Ina na gdan qamshi yakeyi yanason Rafi'ah komai da yakeso a cikin watanni hudun ta gama karanceshi tsaf baiji fitowarta ba saiji yayi ta rungumeshi ta baya tana yar qaramar dariyarta me sanyashi nutsuwa tace “Ur are welcome My life...." Ajiyar zuciya yayi yana shaqar qamshinta ya juyota yayi kissing kumatunta yace “inasonki fatan kina lfy" qasa tayi da kanta tace “ina lfy kamar Kai" kalmar ta bashi dariya yace “haba yarinya da wannan dumar da ta fara girma a tumbinki zakiyi lfy kamar tawa?"
Dagansa Kai tayi tana shafa mararsa yanajin wani irin yanayi ta dago ta dubeshi ya wani lumshe ido tace “zuciyar Rafi'ah da alama kanajin yunwa me kakeson ci na sama maka banson zaman gwarzon maza da yunw...." Bata qarasa ba ya hade bakinsu guri daya suka zube a kujera tasan yau ta ballowa kanta ruwa da alamun dama kadan yake jira daqyar ta qwaci kanta shima Saida ya samu nutsuwa tayi luf a jikinsa son mijinta takeji a hankali yana mamaye duk wani gurbi na qiyayyarsa na baya Ashe takusa ta cuci kanta da ta yarda son farin cikin wata ya hanata karbar nata farin cikin.
Dagota yayi yace “me kike tunani?" Murmushi tayi tace “son mijina nake fasaltawa a zuciyata nakasa gane yanayin girmansa da matsayinsa na yarda na mutu dakai mijina kaifa?" Farin cikine ya cika masa ruhi ya rungumeta yace “na dade da yarda da hakan Rafi'ah tun kafin kisoni nasoki Kuma zan mutu da soyayyarki" luf tayi a jikinsa sun jima a haka Bai zaci zata sake magana ba yaji tace “kayimin uzuri a duk lkcn da na bata maka mijina bazan taba furta ko aikata abinda zai taba farin cikinka a halin Ina sani ba" sanyi jikinsa yayi ya sunsuna sumarta yace “Insha Allah" miqewa tayi tana takansa rawa yayi murmushi komanta dabanne ya dagata cak suka shiga ciki wanka yayi ita ta qara gyara jikinta ya fito ya canza kaya suka fita bangaren Hajiya kaltume suka shiga tana parlon tana ganinsu ta miqe tana washe baki tace “tun dazu naso zuwa naga lfyrki Dije tace baki tashi ba to sannu kinji yarnan Magaji meyesa baka kirani nazo mun gaisa ba me ciki batason yawo balle ita da ba lfy ce ta isheta ba" dadi yaji sosai a ransa ya zauna yace “hakane Hajiya shima motsa jikin yana da amfani" zama tayi suka gaisa ta miqe tace “bari na kawo miki wani Abu nasan jikalle na zai soshi"
Kitchen ta shiga bata jima ba ta fito dauke da wata kula ta bude wata lafiyayyiyar gurasa ce ta alkama da aka mulketa da Zuma sai kunun tsamiya sai zuba qamshi yakeyi" kwantar da kanta tayi a jikinsa ya dago kanta yaga yanda take hadiyar yawu sukayi dariya shida Hajiya Kaltume yace “ta koma kamar mayya komai tagani tanaso tunda mukaje Mexico take sani barnar kudi a Rana sai tace tanason abu kusan kala talatin"
Zaro ido tayi sukayi dari dukansu Hajiya Kaltume ta kirawo Jakadiya Indo tace “ki dauki wannan kayan ki kai bangaren magaji" gdy Rafi'ah tayi Hajiya Kaltume tayi murmushi tace “Ah haba babu komai ai dole mu kula dake haqqi ne akanmu am don Allah Ja'afar duk abinda ya faru baya a manta dashi ya wucce har abada Rafi'ah duk abinda kikeso ki aiko a karba Miki bani da wani amfani sai hidimarku"
Jinjina Kai Ja'afar yayi yanajin dadi a ransa idan aka nuna anason Rafi'ah da cikin jikinta ji yàke kamar yayiwa mutum kyautar duniya, miqewa yayi ya kamo hannunta yace “bari mu qarasa ciki mun gode da kulawa" fita sukayi tanata zubawa Rafi'ah sannu" suna fita ta kwashe da dariya tace “zakuci ubanku waikai ne Mata ita Kuma me ciki har wani godiya kakemin kamar ka mantani nice dai Ummu kursumu yar mage baki dadin goyo sai baqin naci har wani proud akeyi Wai batada sabo tunda ta samu kwadayayyen ciki ai dole ta saba dani zan shekara yi Mata hidima domin Rana daya tak yahudu tuba babu hhhhhhhh" ta qara kwashewa da dariya.
Bangaren Hajiya Innah suka shiga anan ya tafi yabarta saboda Hajiya Fatsum batanan anan ta kusan yini ita da Karimah qanwarsa yar wajen Hajiya Innah sunata hirarsu dake dama basufi sa'anni ba sai yammaci ta tafi bangarenta ta shiga hadimai sai hidimarsu sukeyi tayi wanka ta baje a qaramin parlour Dija ta kawo Mata kunun da gurasar tayi Bismillah taci tayi hani'an sauran tasa a freegde tayi alwala tayi sallar magrib ta kunna kallo anan yazo ya isheta shima yabiyeta sunata hirarsu abin da yakebashi tsoro da mamaki idan baya tare da ita sai kewa da tunaninta ya damesa Amma idan yazo sai ysji duk ya gundura duk wani motsi da zatayi maimakon birgeshi da yakeyi da yanzu haushi yake bashi,
Sai darema da sukaje kwanciya yini yayi yana feeling nata Amma yanzu sai yaji duk haushinta yakeji gashi shi baiga wani laifi da tayi masa ba balle yayi fada yaji dadi duk wani Abu da tasan zai sanyashi farin ciki shi takeyi, itakam batajin komai a ranta kawai dai yanayinss ne yake bata mamaki sai ya kwanta ya tashi ya sake kwanciya ya tashi Saida yayi haka sau uku tanajinsa batace komai ba taji ya miqe itama saita tashi ta rungume pillow a qirjinta yakai ya kawoya tsaya a gabanta yace “na rass meye yake damuna wani haushinki nakeji Rafi'ah Kuma wlh bakiyi min komai ba" Allah sarki sai kawai tayi murmushi ta miqe ta dauki qur'ani ta dawo ta rusuna ta miqa Masa yasa hannu ya karba tace “a duk lkcn da najini a irin wannan yanayin nakan bar duniya da abinda yake cikinta ta na koma ga Allah ta hanyar ambaton sunayensa tsarkaka da Kuma karanta zancensa me dadi da sawa zuciya haske mijina kaima kayi haka nasan zakaji sauqin abinda kakeji...."
Ajiye qur'ani yayi ya matso gabanta yana huci kamar wacce ta zagi uwarsa ya dago kanta kawai saiji tayi dauketa da Mari ya hankadata a gado ya hau bala'i yana cewa “wato saboda kin rainani harni zaki fadawa yanda zanyi idan Ina cikin yanayi ai ba duniya ce tayimin zafi ba kece kikayimin Kuma wama yace Miki banayin karatun qur'ani ko yau da asuba saida nayi nifa banson kirsa waike ta Allah to fadamin wanda yake bautar ubanki..." Fuuuu ya fice daga dakin yana cewa haba nima da jarabata in Banda qaddara ma mezanyi dake nifa baa hakicceni domin wahala ba ke kika rasa ba yar iskar da zata doramin hawan ruwa sakarya kawai" miqewa tayi da sauri ta leqa ta window jin tashin motarsa agogo ta duba 1:49am kawai saita dora hannu a ka ta rushe da kuka ita ba cin mutuncin ne ya bata Mata raiba aa fitarsa a wannan lkcn gashi gda basu kadai ba kowa da abinda zai fassara ta jima tana kuka ganin bazai kaita ba ta tashi tayi alwala ita ta rungumi qur'anin da aka mareta dominshi tana karatun tana hawaye tunda take baa taba wulaqantata irin wannan wulaqancin ba harda zagin ubanta wai JM da bakinsa yake ce Mata yar iska, sake rushewa tayi da kuka tare da daukar wayarta ta fara kiransa Kira daya tayi masa ya daga shassheqar kukanta yasashi saurin cewa “kinga don Allah kiyi Shiru wlh bazan iya kwana a gidannan ba zuciyata tafasa takeyi kaina kamar zai tarwatse Rafi'ah bansan meye yake damuna ba na kasa jurewa idan na cika takurawa cutuwa zanyi"........
_More Comments_
_More Typing_
*_41-42_*
_____________________________
_____________________________
Numfashi ta sauke tana qoqarin shanye kukanta tace “amma me nayi maka JM don Allah kayi hqr tun kafin ka fadamin laifina inasonka bazan iya jurewa wannan sauyin da kake neman wanzarwa tsakaninmu ba" numfashi shima ya sauke yace “calm down please ki kwanta ki huta babienmu nason hutu da safe zamuyi mgn"
Bata iya jayayya ba hakance tasata cikin sanyin murya tace “shikenan kayi bacci cikin aminci Allah ya tsaremin Kai" kashe wayar tayi ta koma ta takure a saman gadon tana saqe saqe ta rasa tuno abinda tayiwa mijin nasu kwanciya tayi tana shafa cikinta da ya fara motsi jiya ta sauke ajiyar zuciya tanajin qaunar abinda ke cikinta a wannan daren dai daga ita har Ja'afar babu wanda yayi bacci shima din daya fita bai iya nufar gidansa ba asibitinsa ya nufa yayi parking a mota ya qarasa kwana saida yayi sallar asubz sannan ya juyo ya dawo gidan sarautar, a fada ya tsaya akayi zaman fada dashi sannan ya shiga gidan tana kitchen sanda ya shigo ya shige ciki yayi wanka ya canza kaya ya dawo parlon ya zauna,
Saida ta gama shirya breakfast dinta ta fito tana jerawa a dinning taji gyaran murya juyawa tayi da sauri suka hada ido ajiyar heart tayi ta fadada murmushinta ta nufishi duk wata gaba ta jikinta tana rawa tana zuwa ta zube a qasan carpet din ta Kama kyawawan yatsun qafarsa tace “barka da safiya mijina" janye qafarsa yayi yace “ki bani abinci yunwa nakeji" miqewa tayi ta nufi dinning din ta hado masa kunun gyadar da tayi ta dauko masa doya data soya sai farfesun kifi tarwada ta kawo masa ta ajiye a gabansa ya sauko qasa cike da zumudi ya faracin abincin, cokalinsa uku a kunun ya ture ya sake Kai doyar bakinsa ya furzar tana kallonsa gabanta na faduwa ya ja farfesun yakai bakinsa kawai sai taga ya ture plate din yaja tsaki ya miqe ya shiga ciki.
A mamakance Kuma a tsorace ta miqe tabi bayansa ta bude dakin ta shiga ya juyo ya kalleta itamma shi take kallo ta matsa a hankali dan nesa dashi saboda har yanzu tanajin Marin da yayi Mata jiya tace “kace kanajin yunwa naga Kuma bakaci abincin ba ka tashi" a hasale ya dago yace “me kikasawa abincin nan yake daci..." Da sauri ta kalleshi ya dakanta tsawar da Saida tasa dan cikinta ya dunqule yace “magana nakeyi Miki kin kafeni da ido" idonta ne ya cicciko da ruwa tace “wlh bansa komai ba...."
Figarta yayi yace “qarya kikeyi kice bakisa komai ba kinsa komai muje kici kiji" a gaban abincin ya dangwarar da ita yace “kici kiji" daukan kunun tayi takai bakinta tasha ita bataji dacinba ta dago tace “ni banji ba" masifa ya rinqayi ta inda ya shiga ba tanan yake fitaba itadai babu abinda takeyi sai kuka ya juya zai fice tabishi da sauri ta riqoshi ta fada jikinsa yasa hannu ya rungumeta sukayi Shiru na dan lkc kafin ya dagota yasa bakinsa yana lasar hawayenta yajata zuwa ciki ya zaunar da ita yace “me kikewa kuka?" Kwantar da kanta tayi a jikinsa tana shafa bayansa ya gane abinda take nufi hakan yasa ya dagata cak ya nufi ciki da ita ya kwantar da ita ya kwanta a gefenta ya zubawa fuskarta ido.
Murmushi yayi yace “meyesa ne Rafi'ah" a hankali ta bude idonta tare da janyo jikinta ta hade bakinta da nasa ya sukaja numfashi tare sun dade a haka tana shafa sumarsa shima yana shafa nata sosai suka tsuma juna kafin su Kai ga cimma burinsu sun jima sosai sannan suka saki juna suna mayar da numfashi ya shafa fuskarta yace “so sweet babe" murmushi tayi masa a rayuwarta batason fada balle mara dalili irin nasa hakanan dai babu wata walwala suka yini Abu qalilan ya rufeta da fada hatta Hajiya Innah data shigo duba lfyrta Saida ta fahimci akwai matsala Amma bata zurfafa ba dake dama tasan fadan halinsa ne, da dare suna zaune duk ta takura saboda Motsin kirki idan tayi rufeta zaiyi da fada wajen Tara na dare wayarsa tayi ring ya wani zabura ya miqe ya Kara wayar a kunnensa bataji me akace ba taji dai yace “to angama ganinan 20 minutes" miqewa yayi ya fice batare da ko ya kalleta ba taja ajiyar zuciya.
Miqewa tayi ta gyara gurin ta shiga daki tayi wanka ta shirya cikin kayan baccinta ta sanya hijjab ta dauki hisnul muslum tana dubawa tana daukan addu'o'i ta Jima zaune sannan tayi addu'a ta kwanta, Shiru goma sha daya har daya bataji Motsin Ja'afar ba wayarta ta dauka ta danna numbersa ta kirasa har tayi ring Bai dagaba sake Kira tayi.
Taji an daga taja ajiyar zuciya tace “Allah yasa dai lfy kake najika Shiru...." Jitayi anyi murmushi sannan akace “dake zama kikayi kina jiran dawowar abinda aka baki aronsa to ai dama kwanciya kikayi kikayi bacci zaifi Miki sauqi Ja'afar kam yayi nisa saidai Kuma gobe idan naga dama na baki aronsa, sorry fah babie"
Qit aka kashe wayar taja numfashi tare da tashi tsaye cike da al'ajabi a ranta take tambayar kanta to dama ana haka kenan? Batada me Bata amsa hakan yasata ta koma ta sake kwanciya kishi na azalzalar zuciyarta hawaye nabin idonta tana karanto addu'ar annabi Yunus “ La'ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalumin" dahakadai daqyar bacci ya saceta itakam tana ganin rayuwa to me tayiwa Ja'afar haka ne daya fara juya Mata baya yana kantafi da mutuncinta.
Washegari har hudu bai shigo gidan ba batayi zuciya ba ta Kira wayarsa akayi rejected takaici ya kamata Amma saita dake saboda kullum Amminta tana fada Mata ibada batada sauqi aljanna ce me sauqi idan ka iya sarrafa zuciyarka tare da naiman daukin Ubangiji a duk lkcn da wani Abu ya kulleka.
Text ta rubuta Masa da zafafan kalamai da tasan zasuja hankalinsa Amma har dare babu reply hakan yasa ita da kanta ta fara zargin ko wani laifi tayi masa ta sake rubuta Masa saqon ban haquri ta tura Masa bai biyota ba har wayewar gari idan barawo ya rintsa itama ta rintsa.
Da sassafe saiga Hajiya Kaltume suka gaisa tace “ina me gidan ko ba anan yake bane?" Qaqaro murmushi tayi tace “Eh ba anan ya kwana ba" murmushi tayi tace “nikam Rafi'ah Anya bazan baki shawara ba a zaman da nayi dake na fahimci kinada tsayawa akan addini sosai alhmdllh Zaki dace a rayuwa Amma fah sai kin tashi tsaye, in baki wani lbr Mana surkarki da tatafi Damagaran bafa kowa take dashi ba neman asiri ta tafi na mallakarwa kishiyarki mijinku ta yanda da quruciyarki da komai zaki zama bora bance kiyi shirka ba Amma ki dan tashi tsaye ki tallafawa kanki rayuwarnan ta yanzu baa zama wlh duk wanda kikaga yana fantamawa to ya miqe"
Kallonta takeyi da rashin fahimta tace “ban gane ba Hajiya" miqewa tayi ta rufe qofa ta dawo ta zauna tace “saboda munafukai masu fakar ido am Rafi'ah da Hausa nayi Miki bayani ki miqe ki dage ki zama tauraruwa a gurin mijinki