Showing 12001 words to 15000 words out of 66967 words

Chapter 5 - MY BESTIE'S HUSBAND COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Oct 2024

8110

takalmi sawu ciki yasata dagowa tunaninta Taheer ne abokin karatunta da yake nacin sonta.





Annurin fuskarta ne ya dauke ganin JM ne tsaye sanye yake da alqabba irin tasu ta sarakai hannunsa zure cikin aljihun alqabbar sai baza qanshin wani tsadaddan turare yakeyi me kwantar da hankali fuskarsa dauke da murmushin daya fito da siririyar wushiryarsa, sake tsuke fuska tayi ta fara tattare kayan karatunta zata fice ya ya dora qafarsa ya tare hanyar tare da cewa.
“Bestie kin tashi lfy?" Rafi'ah akwai Dara daran idanu hakan yasa harara bata Mata wuya aikuwa ta jefeshi da wata zazzafa da tasa zuciyarsa harbawa yayi qasa da idonsa tare da zama, zare glass din idonsa yayi yace “zauna muyi mgn don Allah meye kikejin tsoro ne nidai nasan babu macen data Isa tace batasona saboda duk inda namiji yake nakai please ki tsaya mu fahimci juna Rafi'ah muyi auren qauna kada wani qaramin dalili yasa ki bijirewa hukuncin Ubangiji to waima ni meye laifina ne da har kika daga hannu kika mareni kinsan jiya Marin nan ya hanani bacc...." Dafe kuncinsa yayi a karo na biyu data daukeshi da mari ya dade dafe da kuncinsa yanabin Hall din da kallo ya sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya ganin dagashi sai ita a hall din ta sake maida hankalinta a tattare kayanta kawai taji an ruqo weast dinta ta baya.




Ya dora hannunsa a saitin ask dinta duka biyun ya miqe lkcn da tayi mutuwar tsaye ya hada gabansa da bayanta qirjinsa yana gugar bayanta ya matseta tare da Dora kansa saman nata yaja fasali tare da sakin wata qaqqarfar ajiyar zuciya, sai lkcn ta samu damar dawowa nutsuwarta ta sanya hannunta domin bambare nasa Amma saima ya qara matseta ya janyo hannunsa sama daidai tushen qirjinta ya Kama sosai ya riqe yanda yasan duk qarfinta bazata iya motsi ba saboda wata matsiyaciyar kasala daya saka Mata ta bazata ya bude bakinsa muryarsa na shaking yace “ko kasheni zakiyi bazan fasa cewa inasonki ba Rafi'ah I really love you wlh tallahi ko zan mutu saina aureki"




Yanayin da takeji tasa ta kasa ko daga hannunta sai tafasa da zuciyarta takeyi dumin hawayenta da yaji a hannunsa yasashi juyota ganin yanda ta rintse idonta Zara zaran eyes lasher's dinta suka sauka kan beauty face dinta da hawaye yake wankewa yasashi cika da sauqi baisan sanda yakai bakinsa ya fara tande hawayen ba kawai sai shima yaji zuciyarsa ta karye daqyar ya daure ya hadiye nasa hawayen yanajin bugun zuciyarsa na qaruwa tunda yake baitaba ganin masifa irin wannan ba shekara da shekaru anaso ya nuna waccce yakeso ya kasa lkcn da Allah ya nuna masa abinda ya dade yana nema Kuma sai abin yazo musu a baibai tabbas akwai sarqaqiya cikin lamarin shidai duk juyin da duniya zatayi bazai janye qudurinsa ba saboda yasan hakan shine kawai zai dawwamar da zuciyarsa cikin fayyataccen farin ciki,
Janyewa tayi daqyar daga jikinsa ta durqusa a qasa ta kama qafarsa cikin kuka tace “don Allahu huwar Rahamanu Ja'afar Wakil ka daina bibiyata ka janye wannan mugun nufin naka akaina wlh ka dauko hanyar ruguzamin rayuwata ne please Ja'afar nayi maka alqawarin ko wani lapse kega Bestie na wlh da qarfin buwayar Ubangiji zata gyara nidai ka rabu dani Allah matuqar ace babu wani namiji bayankai daya saura a duniya to zan aminta na gama rayuwata babu aure...." Murmushi yayi ya durqusa ya sanya hannu ya Kama hancinta yana murmushi yace “nikuma ko duk duniya matane yanzu ke kadai nake muradi matsayin Mata wlh tallahi matuqar baki amsamin buqatata ba to kuwa zakiyiwa Bestienki asarar igiyar aurenta......."





_Vote_
_Share_
_Comments_
_Please_





*_Ummuh Hairan_*
[1/3, 9:08 AM] Mrs AA Fansah: *_My Bestie's Husband_*




*_Oum Hairan_*



*_Wattpad-realfauzahtasiu_*



*_Dedicated to Mom twins and Ummu Safnah🤩_*



*_9-10_*




Da wani irin sauri ta dago ta kalleshi ya miqe tare da daganta gira yace “wannan shine matakin qarshe da zan dauka indai burina ya kasa cika to zan rusa farin cikin kowa Rafi'ah kinsani kinsan nasani aurena dake ba haramun bane shin bayan Allah da manzonsa wa kikeso ki birge, wa kikeson farantawa da zakiyiwa kanki asarar masoyi?"
Kallonta yayi na dan lkc kafin ya hadiye wani yawu me zafi yace “dole cikin sharrudana idan na kiraki ki daga indan kikaqi na rantse da kadaitar zati saina dawo Miki da qawarki gda domin batada wani amfani a gurina ba ita nake buqataba ke nake buqata haba haba Rafi'ah shin waima kintabajin inda akayiwa namiji dole ne nifa a duniya ke na faraso tayaya zanyi sake damata ta kufcemin?"




Baijira cewarta ba ya juya Saida yaje qofar hall din ya juyo yace “zan kiraki anjima ki kula da kanki" yana ficewa ta zube a gurin cikin toshewar qwaqwalwa da rashin madafa tabbas tana cikin ha'ula'i tama kasa tuna abinyi sai jujjuya biro da takeyi idonta hawaye nata sitirya tanajin yanda zuciyarta ke bugawa da qarfi kwantar da kanta tayi saman kujerar tanajin wani zazzabi yana sauko mata ita dama bata iya sanya damuwa aranta ba yanzu zata fige ta lalace, tananan zaune kamar hoto batasan sanda hall din ya cika da mutane ba saiji tayi an dafata ta dago idanunta da yayi jajir saboda kuka ta saukesu akan Nina.
Nina tace “naga mayenki ya fita dame yazo?" Numfashi ta sauke tace “ya akayi yasan inda nake?" Shafa Kai Nina tayi tace “guy dinne kwarjininsa ya Isa yanda baka Isa ka Raina masa hankali ba wlh tambayarki yayi akazo aka nemeki baa ganki ba shine yace a samo masa wata da takeda kusanci dake so shine akazo aka kirani Ina zuwa na raina kaina Ashe ma Prince Ja'afar ne tabdi aikuwa kina ruwa don wlh soyayya da yayan sarauta bala'i ne baqin naci ke garesu indai su suka furta sunasonka Amma idan aka samu akasi Basu sonka ai ka kade har ganyanka"



Fasali ta sauke ta share hawayenta ta miqe saboda ta haqiqance komai ma yauma bazata gane ba wani garden ta nufa ta samu guri ta zauna ita kadai qwal kowa yana gurin daukar darasi ita kuma zuciyarta tanata kaiwa da komowa wajen tunanin mafitarta akan wannan sarqaqqen lamari daya tunkarota babu shiri tunda ta zauna ta kasa samawa kanta mafita ji tayi gabadaya makarantar ta daukar Mata wani masiffafen zafi idan taci gaba da zama komai zai iya faruwa da ita.
Wannan tunanin yasata tashi ta koma daki ta dauki hand bag dinta da kudade ta fice batare da tabari Nina taganta ba ta samu shatar mota har Azare babu zato kawai Ammi sai ganinta tayi Aunty Murja ta miqe ta tareta tana cewa “subhanallahi uwar manya meye ya sameki a goshinki haka?"
Fadawa tayi jikinta ta rushe da kuka ta kasa furta ka kalma daya hakan yasa tajata suka shiga ciki Ammi ta miqe tabi bayansu kanta ta dora a saman qafar Ammi tace “Ammi..." Amsawa Ammi tayi tana shafa kanta tare da zame Mata dankwalinta tace “kinasona Ammi?" Mamaki tambayar tabasu suka kalli juna anti Murja tace “to uwar manya waye zaice bayasonki wlh munasonki"




Ajiyar zuciya tayi tace “meyesa yakeson kasheni da kalamansa?" Abin ya daurensu Kai suka hada baki sukace “waye?" Kuka ta sake sawa tace “my Bestie husband" a razane suka dago dukkansu sukace me yayi miki?" Cikin matsanancin kuka tayi musu bayanin komai Ammi ta rinqa sallalami tana tafa hannu inda anti Murja tayi shiru itama tana mamakin wannan tashin hankali.
Dagowa anti Murja tayi tace “no wonder biri yayi Kama da mutum wlh tun ranar da yazo ya kaiki makaranta na fahimci wani Abu gashi kullum sai yazo yagaida abbanku" Ammi ce tace “tabdi Amma wannan yaro yakai mara kunya to yasaketa Mana ba kansa zaiwa asara ba shashasha ya dauka ke sakarya ce da zaki biye masa kuci amanar aminiyarki har wani da aure aa da uban aure yakesonki" fada Ammi takeyi ta inda tashiga ba tanan take fitaba kamar ta ari baki tare da yiwa yar tata kashedi me qarfi da nasiha Saida taga hankalinta ya dan kwanta sannan tace “kiramin shi na tsawatar masa" daukar wayar tayi da murnarta zata kirashi Aunty Murja tayi saurin riqe hannunta tace.




“Amma Hajiya kinsan cewa hakan ba haramun bane ko?" Numfashi Hajiya ta sauke tace “nasani qanwa to Amma Kuma ai kunya tanasa kabar halal yanzu idan mukayi sake mgnr nan ta fita da wanne ido zan kalli Hajiya Sahura ita Kuma Rafi'ah da wanne ido zata kalli Ni'imah haba tofin ala tsinen ma duniya kadai ai ya ishemu balle Kuma ga wannan aminci daya zama zumunci nikam gara a take abin tun anan namiji ba kunyace dashi ba" duk yanda Anti Murja taso hana Hajiya Ammi Kiran Ja'afar taqi ta dauki wayar Rafi'ah ta dauki number say ta kirashi jin muryar babba ce yasashi saita nutsuwarsa yana kallon Muhseen tace.
“Sunana Hajiya Amina nice mahaifiyar Rafi'atuh yanzu da dawomin a hargitse tana kuka harma da alamun zazzabi a jikinta take fadamin abinda ke faruwa so don Allah a daina wannan wasan Ja'afar bashida amfani zai taba musu zumunci kasan Mata da kishi" numfashi ya sauke tare da sake saita muryarsa yace “ba wasa bane Ammi iyakar gaskiyata kenan wlh bazan iya hqr da Rafi'ah ba saboda ita nakeso qaddara ce kawai ta bani qawar....."




Katseshi Ammi tayi da tsawa tace “karna kumaji banason shirme kaima Ashe sakaraine haba Ja'afar ya zakabari shaidan yayi tasiri haka a kanka Ina zakakai haqqin raba zuciyoyi biyu Rafi'ah da Ni'imah abotarsu tun suna qananu girma da bambamcin ra'ayi da sabawar halaye baisa sun rabu ba saikaine zaka nemi rabasu to indai dama burinka kenan rabawar kafin ka raba ni na raba Rafi'ah tabar matarka har abada...."
Saurin kallonta Rafi'ah tayi tace “Ammi...." Hannu ta dora Mata a baki taci gaba da cewa saboda haka ka kiyayarmin yata bakai babu ita har gaban abada soyayya ta haramta gareku ko babu ran Ni'imah balle tana raye...." Yanason yin mgn Amma fir Ammi taqi bashi dama ta kashe wayarta tana tsaki ta dubi Rafi'ah tace “kekuma ki sawa zuciyarki salama ki janyewa Ni'imah har zuwa lkcn da komai zai daidaita dama bawai son naki yakeba so yake ya rabaku shine ya bullo tanan saboda haka kiyi cooling mind dinki kinji"




Jinjina Kai tayi ta miqe tayi wanka ta dawo ta kwanta wayarta tayi ring tana dubawa taga sabuwar number da yayita kiranta jiya ce ta kashe wayar gabadaya tayi kwanciyarta bacci ya dauketa ko babu komai zuciyarta ta samu nutsuwa bacci tayi sosai har yamma dake bata sallah ta tashi ta sake wanka ta zari key ta fice ta tafi gidan yayarta Raziqa acan ta qarasa yininta sai dare ta koma gida taci abinci ta kwanta zuciyarta ta samu nutsuwa tunaninta yana bata mgnr da Ammi tayi masa zaisa ya janye.
Bude wayarta tayi saqon farko da taga yana yawo akan sensor din ta bude shine ya rubuta Mata _“wahala zagi duka dauri a gdan yari bazaisa zuciyata ta hqr dakeba Rafi'ah inanan akan bakana inasonki Kuma aurenki zanyi ki haifamin kyakkyawar Baby kamarki"_ bata gama karantawa ba Kiran Bestienta ya shigo gabanta yabada wani rass tadai daure ta daga ta Kara a kunnenta tace “bestie da darennan haka...." Kuka taji ta fashe dashi tace “na shiga uku Rafi'ah Ja'afar ya sakeni wlh bansan me nayi masa ba..."




Batasan sanda ta hantsilo daga gadon ba tace “wht! Garin yaya?" Kukane ya hana Ni'imah mgn Saida tayi me isarta tace “wlh bansani ba nidai qalau muka rabu dashi kawai naga ya dawo yana huci ya shiga dakina ya Kama hadamin Kaya na biyosa Ina tambayarsa kawai sai cemin yayi gda zanje na huta idan ya dawo daga Abuja zai nemeni, inata murnata muka fito Saida ya kawoni gda ya zaro kudi yabani kinsanni da kudi kamar mejin yunwa da abinci na karba nayi godiya saiya zaro takarda ya miqomin yana murmushi nace tameye budar bakinsa sai cemin yayi nice katangar da nake neman kare mass cikar burinsa qila idan ya nesanta dani ya samu muradinsa.
Yana fadan haka yaja motarsa ya fice daga gidanmu yabarni tsayi Ina dubawa naga saki daya ya rubutamin wlh yanzu haka Ina asibiti Rafi'ah wai Ashe yanke jiki nayi na fadi, ya zanyi Rafi'ah inason mijina meye yasa ya yankemin wannan hukuncin?" Sosai Rafi'ah take kuka tana furta Hasbunallahu wani'imal wakil a ranta tana Jinjina girman rashin mutuncin Ja'afar Ashe da gaske yakeyi zai iya sakin Bestienta to meye laifinta da zai hucce fushinsa akanta ya sawa aurenta rauni?
Ta tafi wannan tunanin taji Ni'imah tace “Rafi'ah kiyi wani abu don girman Allah yaqi daga wayar kowa na gdanmu qila ke ya daga taki please Rafi'ah ki taimakeni kada Ja'afar yayimin nisa wlh bazan iya rayuwa da wani namiji bashi ba" numfashi Rafi'ah ta fusgo tace “ok ki kwantar da hankalinki insha Allahu zanyi qoqarin ganin komai ya daidaita please ki daina kuka haka kada wani ciwon ya shigeki bari naji ko zan sameshi"




Kashe wayar tayi cikin dimuwa da gushewar hankali ta taqarqare ta runtuma ihu abinda yaja Ammi da anti Murja suka shigo dakin a guje har suna hardewa suka tarar da ita riqe da Kai tana ganinsu ta tashi tana jifa da abubuwa tana cewa “na shiga uku no Rafi'ah Allah meyesa kayimin haka ya saketa Ja'afar ya saketa akaina meyesa ya aikata haka...." Riqeta Ammi tayi tace “ya saketa fah kikace?" Dagakai tayi tace “wlh yanzu ta kirani tana kuka take fadamin Ammi ya zanyi ne ni Bestie tanason mijinta shikuma yana sona wlh ko mijina takeso zan iya sallama matashi balle natane ni Ina zansa kaina ta Ina zan fara ne?"
Zaunar da ita Ammi tayi tace “kai ni bantaba jin masifa irin wannan ba wannan wanne irin international dan iskane duk wata hanya ta maslaha kulleta yakeyi Kuma yana sane yake kulleta" numfashi anti Murja tayi tace “dama Saida nace kada ki kirashi Hajiya yanzu gashi an bata goma daya Bata gyaru ba kuma babu me gyara wannan barakar sai Rafi'ah daganan ne zuciyar mutane zata fara rawa a fara tunanin wanne irin matsayine da ita a gurinsa da iyaye zasu kasa sashi Abu ita tasashi Kinga sai a shiga komar bincike da an binciko gaskiya shikenan Abu ya lalace"




Kuka Rafi'ah takeyi kamar ranta zai fita itakam Ammi abin ya girmi tunaninta dole ta fice daga dakin anti Murja ce tayita rarrashinta bata gamayin Shiru ba wayarta ta fara ring ta dauko da sauri number Muhseen ta gani cikin zaquwa ta daga “ya haka suka tambayi juna a tare" taja numfashi tace “meyesa abokinka zaiyimin haka meyesa zai yiwa soyayyar Bestie na irin wannan mugun butulcin meyesa zai sanya rayuwata a kwale²n masifa wannan wacce irin lukutar jarabace Muhseen ya Ja'afar yakeso nayine wlh kaina ya kulle na rasa Ina zansa kaina ko babu Ni'imah Ja'afar baiyimin ba a matsayin miji balle tana tsakani tayaya yakeso na tunkari wannan gudumar masifar da ya jefani a ciki?"
Fasali Muhseen yaja yace “wlh akwai matsala Rafi'ah duk wata qofar alfarma Prince Ja'afar ya kulleta takice kawai a bude har gidansa naje yace bashida lkcna Kira kuwa nayi masa yafi dari yaqi dagawa don Allah ki kirashi qila ke a dace ya saurareki" shiru tayi ayyana ta inda zata fara kiransa katseta Muhseen yayi da cewa hakan zaki daure ki kirashi Rafi'ah Shirin barin qasar yakeyi idan muka sake yabar qasarnan baa daidaita komai ba tofa auren Bestienki ya hau gorar wahala tsakiyar teku domin ni nasan waye Ja'afar fiye da tunaninki wlh akan biyan buqatarsa baya duba alaqa kota kwabo Kuma bashida kirki indai akan ra'ayinnsa ne zai iya batawa kowa rai"




Jinjina Kai tayi cikin qoqarin aro juriya tace “sh...shikenan zan kirashi" kashe wayar tayi ta lalubo numbersa gabanta na duka ta latsa har tayi Ring ta katse bai dagaba ta sake Kira shima bai dagaba saida ta kirashi sau goma bai dagaba ta rubuta Masa gajeran saqo tace _“please Mr Ja'afar Wakil ka daga don girman Allah"_ cikin seconds saqonsa ya shigo kamar haka.
_"Gobe 7:30 zan wucce Indonesia banida lkcn daga wayarki idan kinason mgn dani dake kece zan iya baki 30 minutes cikin lkcna kizo gidana ki sameni yanzu ba dazuba ba anjima ba"_ zaro ido tayi waje tanajin wani tafasasshen gumi na karyo Mata bata gamajin zagayar kalamansa ba Ni'imah ta kirata ta daga ta fashe da kuka tace “Bestie yaqi daga wayata wai saidai naje gida na sameshi nikuma bazan iya zuwaba" wani kuka Ni'imah ta rushe dashi tace “kada kiyimin haka Rafi'ah ki taimaki igiyar aurena wlh Ja'afar ba dan iska bane bazaiyi Miki komai ba kije kijimin meye laifina ki bashi hqr da yawuna idan yabar qasarnan zan dade banganshi ba kije Rafi'ah please kije"...........





_Vote_
_Comments_
_Share_
_Please_





*_Oum Hairan_*
[1/3, 9:17 PM] Mrs AA Fansah: *_My Bestie's Husband_*





*_Ummuh Hairan_*




*_Wattpad-realfauzahtasiu_*




*_11-12_*




_____________________________
_____________________________



Girgiza Kai Rafi'ah tayi tace “Aa Ni'imah mijinki azzalumine bashida adalci baison me sonsa ba meyesa laifin wani zai shafi wani...." Katseta tayi tace “naji Rafi'ah nidai ki taimakeni kije don darajar qauna da aminta kinji" ajiyar zuciya tayi jikinta ya qara sanyi tace “shikenan zanyi qoqari bari zance da Ammi zanzo gurinki asibiti duk yanda mukayi zakiji" ajiye wayar tayi ta fara kaiwa da komowa a dakin zuciyarta cunkushe da tsoro yanzu ita ya zaayi ta taka taje gidan Ja'afar Wakil da wanne irin yanayi zai karbeta?
Tambayar da takeyiwa kanta ta kasa samun amsa kenan daqyar ta iya sawa kanta juriya ta dauki doguwar rigarta ta zura tayi rolling mayafin ta dauki takalmi da wayarta da key din motar Ammi ta fice daga dakin ta nufi dakin ammi tana bisa sallaya ta zauna bayan ta idar da sallar ta dubi yar tata tace “ina zaki?" Sunkuyar dakai tayi qarya ba dabi'arta bace shiyasa takejin nauyin yinta to yanzun dai dole ta kamata tace “zanje wajen Bestie ta kirani tanason ganina urgent don Allah kada kice aa Ammi" murmushi ammi tayi tace “toni na Isa na hanaki kidai kula da kanki don Allah Kuma ki Kama bakinki tsakanin Mata da miji sai Allah akansa sai taji haushinki"




Jinjina Kai tayi cikin jin dadin sa'ar da Allah ya bata ta fito ta dauki motar ta fice Kai tsaye unguwar da martaba estate take ta nufa Saida taje daidai get din tayi parking ta dauki wayarta ta kirashi bai dagaba saboda yaga tsayawar matar koma yaji a jikinsa itane hakan yasashi turo mata da number

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login