Showing 3001 words to 6000 words out of 66967 words
zaune daidai lkcn da Ammi suke gaisawa dasu Muhseen idon Ja'afar akan qirjinta ya sauke numfashi tare da cewa “ya jikinki" wata uwar harara ta watsa masa ta dauki hijjab dinta ta zura ta koma can qarshen gadon ta kwanta ba Shiba hatta Abba Saida abin yabashi dariya yace “to Ja'afaru kai me laifine fa ka rabata da aminiyarta"
Murmushi yayi a ransa yace “kema very soon zan daukeki sai naga ya amintar zata kaya tunda kunayiwa dodo daya tsafi" a fili kuwa cewa yayi “kiyi hqr bansan da wannan amintar ba dana bari anyi Rana daya Kinga da duk haka bata faruba".......
_Please share_
_And_
_Comments_
*_Oum Hairan_*
[1/1, 10:17 AM] Mrs AA Fansah: *_My Bestie's Husband_*
*_Ummuh Hairan_*
*_Happy birthday Nazifi Yarimah_*
_Wannan shafin sadaukarwa ne ga Nazifi Yareemah Happy birthday more shekaru da nauyayan money in your bank account da Mata ta gari_
*3-4*
Murmushi Abba yayi yace “yo shirmene irin nasu Koda anyi Rana daya ai bazaa tare gda daya ba Tunda kowacce dai mijinta dole dabanne" shafa Kai Ja'afar yayi yana sake saita injin idonsa akan Rafi'ah data koma qarshen gadon ta qudundune yaja numfashi aransa yanajin dama ace itace zaije ya tarar a gida matsayin matarsa Amma a fili saiya duba agogo yace
"Wanne saqo zaki bani gurin Bestie dinki zamu tafi dare yayi" numfashi taja batare data juyo ba tace “fatan alkhairi" daga haka bata Kuma qara ko harafi daya ba ya sake kafeta da ido Saida Muhseen yajashi suka fita a parlour suka hadu da Abba sukayi masa sallama suka tafi, Basu jima da fitaba suka turo maigadi da ledojin da suka siyo domin kaiwa amarya suka fice daga gidan.
Dubansa Muhseen yayi ganin yanda ya zubawa rufin motar ido yasashi dafashi yace “akwai qura mutumina ka canza tunani don Allah kada ka zamo takobi me yanke qauna kayi qoqarin dannar zuciyarka da hqr da abinda yake halal kodan mutuntaka da Kuma kunya" batare da ya kalli Muhseen ba yace “ka tabbatar da halal dinne dai ko?" Jinjina Kai Muhseen yayi Ja'afar yayi murmushi yace “indai ka yarda halal dinne to kada ka qara cemin na hqr Muhseen bana iya control din zuciyata akan abinda takeso"
Parking Muhseen ya sakeyi ya fita ya sake siyo kayan siyan bakin amarya ya dawo suka tafi suna zuwa yayi musu jagora har parlourn da Ni'imah take zaune tana jiran zuwan angonta suka shiga da sallamarsu duk da cewa Muhseen ne yayi sallamar, Bata amsaba sai qarawa kukanta sauti da tayi suka zauna Shiru na dan lkc shidai Ja'afar zuciyarsa ce ke bugawa inda Muhseen yake tausayin Ni'imah da Rafi'ah kasancewar yafi kowa sanin kafiyar Ja'afar tunda ya furta yanaso to zaiyi duk me yuwuwa yaga ya samu saidai idan abinne yafi qarfinsaGyaran murya Muhseen yayi yana mai farawa da addu'a sannan yayi musu yar tunatarwa ya miqe tare dayi musu sallama Ja'afar ya rakashi ya tafi shikuma ya juya cikin gdan ya zauna a gefen Ni'imah yana kallonta sunfi 30 minutes a haka kafin yasawa kansa jarumta yakai hannu ya bude fuskarta tare da matsawa ya janyota jikinsa ya bude bakinsa a hankali yace.
“Kukan ya Isa haka tashi muje muyi sallah mu kwanta" sake narkewa tayi a jikinsa ta bude bakinta a hankali tace “Bestie na Ja'afar bansan halin da take ciki ba na Kira wayarta taqi dagawa" murmushi yayi ya shafa fuskarta ya dora bakinsa saman goshinta yace “cool down please bestienki tana lfy yanzu kafin mu qaraso saida mukaje muka gano halin da take ciki Kuma da safema zan koma kinji"
Daga Masa Kai tayi cikin qauna da sallamawa abokin rayuwa kai ya miqe itama ta miqe yana riqe da hannunta suka isa bathroom din yayi alwala itama tayi suka fito yajasu sukayi raka'a biyu tare da doguwar addu'a a qarshen addu'ar yake fadawa Allah ya shige masa gaba ya bashi nasara akan abinda yasa a gabansa ya dade yana addu'ar sannan ya miqe ya dubeta yace “dauko Mana flat a kitchen yunwa nakeji" miqewa tayi taje ta dauko ta dawo sukaci abincin sukayi brush sukayi Shirin kwanciya.
Koda suka kwanta ya dade yana saqawa da warwarewa kafin ya arawa kansa jarumta ya shige jikin amaryarsa ya fara rage musu nisan lkc ta hanyar yan wasanni Wanda a zahiri yanayi ne don yasan duk amaryar duniya a darenta na farko hakan take buqata Amma badon a kankin kansa yanajin dadin yanayin ba.
Haka dai ya rinqa rarrashin Ni'imah yana bata hqr har yayi nasarar kaiwa ga inda yakeso yakai din ta qanqameshi tana kuka tana kiran Bestie dinta shikuma ya dora bakinsa a nata, dadewa sosai yayi yana raya daren kafin ya samu nutsuwa ya janye jikinsa daga nata ya shiga bathroom ya hada Mata ruwan zafi yazo ya dauketa ya gasa Mata jikinta har yanzun Kuma kuka takeyi tanata jijjiga kai shidai baice qala ba qwarai yadan samu nutsuwar da kowanne ango yake samu a darensa na farko da amaryarsa,
Bayan ya gama taimaka mata suka kwanta tana lafe a jikinsa shikuma zuciyarsa na gurin abar muradinsa aminiyar matarsa Rafi'ah shidai kamar daren jiya bai rintsa ba Saida dare yayi nisa yanata tunanin ta inda zai fara.
Da safe ya rigata tashi ya koma palo ya zauna ya rafka uban tagumi shi kadai yasan yanayin da zuciyarsa take ciki yanajin sarewar gwiwa tare da qoqarin tursasa kansa ya janye daga wannan nannauyan qudurin amma ya kasa samun amintar zuciyarsa, baiji fitowarta ba saijinta yayi a gefensa ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ya riqota jikinsa ya dora lips dinsa a kuncinta yace “kin tashi lfy amaryata" kunyace ta kamata ta sunne kanta yayi murmushi yace.
“I hope babu inda yakeyi Miki ciwo girgiza masa Kai tayi yace “ok tashi mushiga kitchen ta tayaki ki sama mana abinda zamu karya bana jure yunwa kuma duk na juye Miki abinda naci daren jiya" sake sunne kanta tayi yayi murmushi yace “zama ki daina kunyarnan ne" da haka yajata kitchen din yasha mamakin yanda saishi ya rinqa cewa da ita kaza zakiyi kazafa duk bata iya wasu abubuwan na kitchen ba, yaja numfashi yana mamakin yanda akayi hakan ta faru budar bakinta sai cewa tayi.
“Bestie tayi tayi na tsaya na koyi girki ko a gurinta ne naqi saboda ni gsky girki na bani wahala sweet a nemo kuku ko macen data iya girki takeyi ma sosai nake wahala a lamarin daya shafi kitchen" kallonta yayi da qananun idanunsa yace “meyesa qawarki ta iya ke baki iyaba?"
Dariya tayi tace “wannan ai ta daukarwa rayuwa buri 15000k taje tasa Abba ya biya Mata ta shiga cattering school tayi course na 3 months akan girke girke da kula da miji ita ta kasance me buri a rayuwar aurenta tanayiwa mijinta tanadin farin ciki da'iman dawa'un
Wani gwauron numfashi yaja ta dago ta kalleshi yayi murmushi yace “maxa yan gatan Mata Allah yabawa me rabon nan saa" amsawa tayi da Amin sukaci gaba da hirarsu bayan sun gama break din suka koma suka kwanta bai wani takura Mata ba saboda dan banzan raki gareta shikuma bai cikason qorafi ba suka dan taba bacci ya tashi yayi wanka ya fice lkcn goma saura saboda sanin da yayi zatayita baqi.
Kai tsaye Family house dinsu ya nufa ya kwashi gaisuwa gurin mahaifinsa sannan ya shiga cikin gidan matan mahaifinsa uku Hajiya Kaltume itace babba tanada yara biyu Zainab da Ummah sai Hajiya Fatsum wacce itace mahaifiyarsa itace ta biyu tanada su hudu biyu Mata biyu maza sai Hajiya Inna mace me hqr da hangen nesa ya daya Allah yabata Fiddausi Kuma itace qarama a gidan,
A zahirin gidan sarautar Azare wanda yake waje zaike sha'awar mutanen gdan kasancewar daga nesa zakace lfyr Allah suke zaune amma ta qarqashin qasa zaman bashida dadi Hajiya Kaltume da Hajiya Fatsum basa jituwa kullum cikin jifan junansu suke da mugayen asirai hatta Hajiya Inna da take gefe bata shiga lamarinsu idan tsiyarsu ta motsa ba basa barinta Amma dake ta riqe Allah sai ya kasance duk abinda du suka nufota dashi baya tasiri a game da ita.
Akwai wata shaquwa ta musamman taakanin Hajiya Inna da Prince Ja'afar wacce take ciwa Hajiya Fatsum tuwo a qwarya Amma ta kasa maganinta don ko tayi asirin rabasu baya tasiri wannan abin yasa ta qyalesu ta zuba musu ido amma duk lkcn data samu dama takan kushe Hajiya Inna a gurin Prince Ja'afar saidai yayi murmushi kawai tunda yariga yasan halin mahaifiyarsa.
To yauma daya shiga gidan Sarautar bai nufi bangaren mahaifiyarsa ba bangaren Hajiya Innah ya nufa domin ita kadai zai iya tunkara da damuwarsa ta bashi shawara ta gari, Saida ya faki idon mutane ya shiga ya isheta saman kilishi tana lazumi alamu sun nuna sallar walaha ta idar ya nemi guri ya zauna kusa da ita yana wasa da yatsan hannunta,
Sallamewa tayi ta zuba masa ido tun shekaran jiya ta lura da rashin nutsuwarsa da farko tayi tunanin hidima ce da tasha kansa Amma ta fahimci har yanzu yana cikin damuwa, dafa kansa tayi tace “Zuciyar Inna sarkin gobe meye yake tabamin Kaine na fahimci damuwa a tattare dakai tun ranar dinner bikinka" kansa ya dora a kafadarta ya lumshe idonsa sosai mamaki ya Kama Hajiya Inna da taji dumi a kafadarta ta dagoshi tace “subhanallahi Baban Innah me yayi zafi haka don Allah fadamin wlh nayi alqawarin baka mafita a kowacce damuwa ta rayuwarka kaji"
Rungumeta yayi ya fashe da kuka kamar wani yaro ta sake matseshi a jikinta hankalinta yana qara tashi duk da tasanshi da shagwaba kamar mace Amma kuka ba dabi'ar Ja'afar bace, ta jima tana rarrashinsa kafin ya sauke ajiyar zuciya ta sanya gefen hijjab dinta ta share masa hawayen tace “kasa Innah a damuwa baban Innah fadamin mana idan baka fadamin ba waye zaka fadawa?"
Numfashi ya sauke yace “inasonta Innah bazan iya hqr da itaba wlh" sakin baki tayi tana kallonsa tace “to ai ka sameta baban Innah me Kuma kake nema?" Murmushi yayi me hade da Hawaye yace “not ba itaba Innah bantaba qinta ba kuma bantaba sonta ba itakuwa wannan daga kallon farko na fada komarta wlh daga daren ranar asabar zuwa yau zuciyata azabta takeyi akan Rafi'ah"
Dariya Hajiya Inna tayi tace “to Banda abin baban Innah wannan ai me sauqine kaida Allah ya halatta maka hudu kayi daya meye na damuwa dan kaji kanason ta biyu addu'a itace zakayi duk da nasan akwai qura domin mahaifiyarka bazata aminta da wannan sawalwalar ba zatace yaushe ma kayi auren da zaka dauko wani" share goshinsa yayi yace “ba ita kadai ba Innah kowa ma Innah Rafi'ah ta kasance aminiyar matat...." Wata zabura da Inna tayi tasashi yin shiru ta saki salati tace “garin yaya Baban Innah wannan ai abin kunyane Dama Pretty Raf kakewa wannan qwawar aikuwa dole ka hqr wannan amintar bakayi gangancin shiga tsakaninta ba to bandama abinka inakai ina son Bestie din matarka"
Kallonta yakeyi harta gama ya miqe zai fita tayi saurin riqoshi tace “kafa cire wannan tunanin a ranka zamu bata sarai dakai banson sakarcin nan naku na yayan zamani wlh ka kiyayi Hajiya Kaltume taji wannan katobarar takaGirgiza Kai kawai yayi ya fice ta dafe qirji tace “wannan da da rigimar tsiya kake inakai Ina wannan sakarcin" shikam yana fita bangaren Hajiya kaltume ya nufa suka gaisa tanata tambayarsa amarya ya amsa Mata da cewa da sauqi ya tashi ya fice, suka gaisa da baqi ya nufi bangaren Hajiya Fatsum ya tarar da ita tanata cika tana batsewa ya zauna yana gaisheta tana amsawa a daqile bai wani bawa fushinta muhimmanci ba ya miqe ya fice ya dauki motarsa ya fice kawai ya rinqa zagaya gari ya jima yana yawo sannan ya Kira Muhseen yace masa yana gidan ya rakiceshi suka fice yace.
“Rakani zakayi da dubo Rafi'ah" harararsa yayi yace “bakasan gidan nasu bane sains rakaka Kai nifa bazan yarda ka dauramin jarfa ba kaidai da baka tsoron abin kunya sai kaje kayitayi ka shiryane"
Bude Masa mota yayi yace “jeka kawai don Allah basai ka zageni ba" ficewa yayi daga motar yace “eh naji bazani ba idan nayi niyyar zuwa ai basai naje tare dakai ba" Bai kulashi ba yaja motarsa ya nufi unguwar tasu Rafi'ah me gadi ya bude Masa ya shiga ya turashi yace ayi masa sallama da Rafi'ah tana zaune a parlour Mado megadi ya shigo yace “Hajiya kinads baqo a waje" wani tsaki tayi tace “kaje kace bananan" kallonta yayi da sauri yace “baayi hakaba Hajiya baqin jiyane fah daya cikinsu ne ya dawo" murmushi tayi tunaninta abokinta ne Muhseen ta miqe tana gyara mayafinta ta fito tana dariya dake baya ya juya bata ganeshi ba ta qarasa takai hannunta ta lakaci wuyansa tace.
“Ya Bestie na ta kwana Muhseen jiya ban iya bacci ba inata tunanin yanda zasu kasance Bestie na akwai raki da mit...." Mgnr ce ta maqale lkcn daya juyo ya zuba Mata ido taja baya da sauri harda dan tsallenta tace “wayyohh sorry don Allah...." Yanda tayidin ne ya bashi wani nishadi yayi murmushi yace “Notting is true haka bestienki take ta cika raki" ajiyar zuciya tayi tace “tayi maka ko? Ai dama nasan zatayi saidai hqr" lips dinsa ya lasa qirjinsa na bugawa yace “ya jikinki Ina fatan kinji sauqi" murmushi tayi tace “naji sauqi wlh yanzu ma Shirin fita nakeyi yau Monday inda lecture 2:00pm" agogo ya duba yadan zaro ido yace “kuma har 1:40 kina gda ai kin makara murmushi tayi tace “driver ne ya batamin lkc ya fita cefane bai dawoba dama ai ta wucceni shiga Bauchi a wannan lkcn kawai dai zan tafine na zauna a hostel bazanke dawowa ba sai weekend"
Agogo ya yaske dubawa yace “to ki fito muje na saukeki dama nima Bauchi zan shiga" kallonsa tayi taga ita yake kallo taso musawa ya daga Mata hannu yace “don Allah kada mu fara haka dake wlh banson musu kashemin gwiwa yakeyi" Shiru tayi tana jujjuya abin a ranta a ganinta dai sai take ganin kamar Bai daceba ta bisa su tafi, katse Mata tunani yayi da cewa “ki dauka Nima Bestie dinki ne mijin Bestie ai shima ai Bestie ne ke dagayau ma nima sunana Bestie"
Dariya tayi data bayyana kyawawan haqoranta yar kyakkyawar wushiryarta siririya sama da qasa ta dauki hankalinsa ya kwantar da kansa a saman mota ya zubanta ido katse dariyar tayi yayi ajiyar zuciya yace “jeki fito Ina jiranki" juyawa tayi ya sake lefewa jikin motar yana me qare Mata kallo yana sauke numfashi sosai take daukar hankalinsa.
Bata jimaba ta fito dauke da Jakarta da dan qaramin trolley dinta ya karba yasa a but ya bude Mata ta shiga suka tafi, tafiya sukayi ta kurame babu me cewa da wani qala Saida suka biya wani guri yayi Mata siyayya sosai sannan suka qarasa tayi masa godiya ta shiga ciki ya jima sannan yaja motar ya juya domin bashida wani uzuri a cikin Bauchin ya dauki hanyar komawa gida, cike yake da nishadi duk da bata wani basa fuska ba Amma yaji a jikinsa zai samu dama sosai ya shigeta zaiyi amfani da qawarta ya kafa kansa a zuciyarta.
Bai koma gidansa ba sai dare yana shiga ya tarar da ita a kwance a parlour ya qarasa ya zauna kusa da ita tace “ina ka shigane tun safe inata kiranka busy?" Shafa kansa yayi yace “wlh naje duba Bestie dinki na tarar tana Shirin komawa school Kuma driver ya tafi cefane bai dawoba so kawai saina dauketa nakaita shine sai yanzu na dawo" hawaye ta share tace “kuma shine baka kawota naganta ba ka wucce kakaita school?" Murmushi yayi yace “sorry naga bata buqaci zuwanba tukunna kinsan yanzu ni takejin haushi har mukaje hararata takeyi ta gefen ido"
Dariya tayi tace “Allah Sarki tawan bari na kirata" daukar waya tayi ta kirata Saida tayi ring sau uku sannan ta daga tace “zuciyata ya kk" dariya tayi tace “lfy ya gwauranta?" Dariya tayi tace “alhmdllh masu miji kiyimin godiya yau na wahalar Miki da mijinki" haka sukayita Hira yana kallon Ni'imah daga qarshe ma ta tashi ta shige ciki tabarshi shanye da baki tunani ya addabi zuciyarsa ya miqe ya shige daki yayi wanka yayi Shirin kwanciya ya fito ya dan tsakuri abinci ya sake komawa ya kwanta saman kujera, fitowa tayi a shirye tsaf cikin Shirin baccinta itama zama tayiYa riqota jikinsa tace “wai ita Bestie yaushe zatayi aurene?" Murmushi tayi tace “ai batada niyya saurayinta ne Kuma dan uwanta Yassar ya rasu 2 years back so tun lkcn taqi bawa kowa dama wlh sweet munji mutuwar Yassar a lkcn bikinsu saura wata biyu"
Jinjina Kai yayi ya miqe ya shige daki ya kwanta tare da daukar wayarsa ya fara danne dannensa ya jima sannan ta shigo ta zauna a gefensa ya janyota jikinsa suka kwanta daqyar suka raya daren tanata kukanta da Safe ya sake ficewa a cikin kwanakin satin an barji amarci daidai gwargwado duk da amaryar raguwace bata iya dauke mijin yanda ya kamata hakadai aketa tafiya gefe kuma kullum wutar qaunar aminiyar matarsa qara ruruwa yakeyi a ransa duk wata hanya da zaibi yaga ya samu kusanci da ita Amma ya kasa samun dama dabara ce ta fado masa ya dauki lambarta a wayar Ni'imah sai yayi kamar zai kirata sai tsoro ya kamashi ya hqr ya qyaleta amma hqrnsa kullum qara qaruwa takeyi.
Yau tun dare yakejin qarshen qarewar hqrnsa daqyar a daddafe yakai safe tun safen ya tashi ya shirya tana kallonsa har ya gama ya dubeta yace “zan shiga cikin gari me zan taho Miki dashi ki gama hada kayanki jibi zamu tafi" bai jira amsarta ba ya fice da sauri ya fice daga gdan ya dauki hanya,
Kai tsaye ATBU ya nufa ransa fess ya lodar Mata uban kayan shop ya qarasa makaranta yayi parking ya dauki wayarsa ya kirata bugu daya ta daga suka gaisa taso gane murya tace “bangane me mgn ba" murmushi yayi yace “kizo bakin get dinku rumfa ta biyu zakiga wayene" yana fadin haka ya kashe wayar ta zubawa wayar ido tana mamakin irin wannan Kira miqewa tayi ta dauke mayafin rigarta tayi rolling ta fito riqe da wayarta tana tunanin to wayene wannan?
Tsayawa tayi a harabar gurin tana kallon motocin can nesa taga an bude wata zazzafar mota ya zuro qafafunsa ya jima yana kallon yanda