Showing 15001 words to 18000 words out of 66967 words

Chapter 6 - MY BESTIE'S HUSBAND COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Oct 2024

8108

gidan tayi horn security din ya bude Mata ta shiga tabi titi na biyu tayi parking daidai block 29 ta sake kiransa ya bai dagaba sai megadi da taga ya bude Mata ta shiga tayi Parking ta sake kiransa sai taga wani mutum ya fito sanye da rigar kitchen da alamun kuku ne yazo ya qwanqwasa Mata glass din ta zuge ya gaisheta tare da cewa “yallabai yace a shigar dake" Saida gabanta ya fadi tayi kamar tace aa saidai tasawa kanta juriya ta fito ta kulle motar tabi bayansa suka shiga ya mayar da qofar ya kulle taja ta tsaya a parlourn qasan tana qarewa gdan kallo manyan hotunansu ita da Ni'imah da sukayi kafin bikin sun qarawa parlourn kyau kowanne an rubuta world Bestie's tayi murmushi tana me maida hankalinta ga kallon hotunan.
Ji tayi an zagaye weast dinta da hannu anyi kissing dogon wuyanta tare da shaqar qamshinta tayi saurin janyewa lkcn da yake sauke ajiyar zuciya tace “kace inzo zaka bani lkc ka saurareni na roqeka da girman Allah kada ka qara tabani J Wakil ko bance maka komai ba Allah zai sakamin domin Kaine namiji na farko da kataba hada jiki dani"




Lumshe idonsa yayi ya bude yace “gdannan ya dace dake My Bestie dama ace kin shigo kenan" kalmarsa taso bata dariya ta dai dake ta maze tace “meye dalilinka na tozartamin Bestie na bayan ka cire Mata darajarta Kuma kake burin mayar da ita qaramar bazawara?" Takowa ya farayi gabanta tanaja da baya yana sake binta saura qirin takai qofar yayi maza ya shammaceta ya danna Mata key taja numfashi tare da zuba masa ido jikinta na rawa sai hawaye sharr tayi saurin zamewa ta zube aqasa shima ya zauna yakai hannu zai riqo nata ta janye yace.
“Kina tsoronane? Meye kike tsoro game da mijinki mijinki ba fasiqi bane Kuma ko Ina fasiqanci bazanyi dake ba kinada matsayin da sunnah ce ta dace dake ba zina ba Rafi'ah ki amince da buqatata wlh cikin wata daya zaayi komai a gama ke ni idanma wata dayan tayi Miki nisa zan iya ko gobe a daura mana aure saina daukeki mu tafi Indonesia bazamu dawoba Saida bebynmu Kinga lkcn kowa yayi surutunsa ya gama saimu fara sabuwar rayuwa ko?"





Gabadaya kallon mahaukaci takeyiwa Ja'afar Wakil bata bashi amsa ba taja fasali tace “bestie ce tasani zuwa gunka ba zuwan kaina bane tace nabaka hqr Kuma ka fadamin laifinta munyi maka alqawarin gyarawa da qarfin buwayar zatin ubangiji...." Hannunsa ya aza ya dago habarta ya zuba idanunsa cikin nata tayi saurin lumshe nata yayi murmushi yasan duk taurin kan mace indai zata kalli qwayar idonsa saita rusuna yace.
“Naqasunta baya damuna domin nasan dama wacece ita ba wata bace sai yar gidan Hajiya Sahura qawar Hajiya Fatsum Iko mahaifiyata iyayen da basa kwabar yayansu musamman Mata sannan basa basu horon zama da miji sukw dauka cewa izza da iko zasu siyi zuciyar miji nop duk ba wannan ne damuwata ba damuwata shine ki amince dani ki karbi soyayyata idan kin amince wlh na amince zan dawo da qawarki gdannan a daren nan zata zauna albarkacinki Kuma zan wanzar da adalci tsakaninku sannan zanyi hqr da duk wani lapse nata nayita mernege har zuwa lkcn da zan shigo dake matsayin Mata ranar da zanyi asalin angwanci zan huta iyakar hutawa ranar da Prince Ja'afar zai kwana yana wanzar da qauna me yado a zuciya a gurin daya dace"
Harara ta maka Masa tare da miqewa tace “idan Kuma ban amince bafa?" Murmushinsa na Isa yayi ya miqe ya zare doguwar rigarsa idanunta ya sauka a faffadan qirjinsa me yalwataccen gashj tayi saurin dauke idonta shikam bai damu ba ya dauki wandonsa na yadi yasa ya dauki rigar ya sanya yasa hula ya matso gabanta yanata zuba qamshi yace “kofa baki amince ba kin amince Rafi'ah dolene ki aureni domin nasani kowama yasani ni dake mun dace sosai"



Dagowa tayi tace “ban amince ba Amma zaka dawo da Bestie na Ja'afar inada Wanda nakeso wlh harma munyi alqawarin aure nifa bantaba sonka ba hasalima wlh natsani namiji irinka mara sanin darajar alaqa Ja'afar Wakil please kada kaja alaqar nan har kayi yanda duniya zata fahimta Allah yasani bazan taba iya wannan cin amanar qaunarba bestie ta aminta dani ta dauki amanar kanta da duk wani sirrinta tabani munyiwa kanmu alqawarin rayuwa tare mutuwa tare Amma kana neman kawo mana tasgaro cikin tafiyarmu munyiwa junanmu alqawarin hada yayanmu aure idan Allah yaja rayuwarmu Ja'afar kada ka zama makamin yanke kyakkyawar alaqarnan kaji?"
Ta qarashe mgnr tana durqushewa a gabansa inda idanunsa yake kanta yace “kinason farin cikinta?" Saurin daga masa Kai tayi ya sake cewa “meyesa kika yarda kizo gdana saboda ita?" Sunkuyar dakai tayi yace “talk mana" dagowa tayi idonta cike da qwallah tace “saboda inason ta dawwama cikin farin ciki tare da abinda takeso" murmushi yayi yace “to ita meyesa bazatayi Miki wannan sallamawar ba?" Dagowa tayi suka hada ido ya qanqance qananun idanunsa ya nunata da yatsa yace “duk da cewar zuciyarki taqi gasqata Miki cewar kinasona Amma ni inaji a jikina jikinki da ruhinki sun karbeni Ni'imah itace qaddarar da take wahalar damu babu wani abu naki da yake boyayye a gurina kinason namiji me irin siffata to kin samu nine Rafi'ah nine Ja'afar Wakil ki karbeni kawai a wucce gurin babu wanda ya usa canza qaddarar Allah fah dagani harke babu abinda muka isa mu canza dole mu karbi duk hukuncin da ubangiji yayi akanmu"




Numfashi ya sauke yace “kada ki damu muje a daren nan zanyi Miki abinda kikeso bazaki kwana da ciwon mutuwar auren Bestienki ba Amma kisani a gobe zan sanar da manyana halin da ake ciki dama rashin samun dama daga gareki ya hanani furta musu koma...." Wata tsawa ta daka mishi data sanya gabanss faduwa tace “karka kuskura kada ka fara wlh bazan taba yarda da wannan haukan ba kuma ma Ina katabajin anyi wannan sakarcin to nidai bada yawuna ba idan kuwa ka sanar Kaine da kunya na rantse da Allah saina kashe kaina na huta kowama ya hut...."
Wata fizga yayi Mata ya hadata da jikinsa ya matse yana lalubar bakinta ta fara tureshi ya sake daidaita qirjinta a nasa yanajin yanda dukiyar qirjinta take gugar nasa qirjin, jin yanda electric din jikinsa suke wani touching yasashi saurin sakinta ya zauna a hannun kujera yana cakuda numfashi inda itama tayi baya da sauri tanajin wani shorck a cikinta da bata tabajiba daqyar ta daidaita nutsuwarta yana kallonta yanajin wani sabon baqon yanayi miqewa yayi da sauri yana korar shaidan da a'uziyyah ya dauki key din motarsa yace “muje ko?" Babu musu tabishi tana fita ta fada tata motar baiso hakan ba amma Babu yanda ya iya da ita haka ya shiga taja suka fice jikinta har yanzu wani yammmm yakeyi Mata tanajin wani yanayi da bata tabajiba, gidansu Ni'imah suka nufa Kai tsaye suka shiga tayi parking ta fita ta shiga gdan shikam baima fito a motar ba tana shiga Hajiya Sahura ta washe mata baki tace “da daren nan Rafi'ah lfy" numfashi taja tayi qasa ta gaisar da Mama tace “bestie fah Mama" sama ta nuna Mata tace tanacan tanata aikin kuka kamar kanta ka fara yo bandama abinta mijin da ya sakeki har yana fads Miki Wai sabodakene burinsa bazai cikaba meye na damuwa basai ta qyaleshi ya cika burin ba mugani"




Itadai miqewa tayi tace “tare muke dashi yana waje yace ta fito su tafi ya wucce" miqewa Mama tayi tace “tabdi Amma yakai riqaqqen dan iska bama zai shigo ba...." Kafin ta rufe bakinta sai gashinan ya shigo sai Kuma tayi shiru harda washe masa baki suka gaisa Dad taje ta Kira a sama yazo suka zauna Rafi'ah ta Kira Ni'imah tana ganinta ta rungumeta tana dariya me hade da kuka tace “da gaske ya mayar dani Bestie wayyoh dadi kema Allah yakaimu ranar da zan saka Miki yana Ina?" Janyo hannunta tayi cike da tausayin qawar tata suka fito ya dubeta ya kawar dakai ita kuwa sai wata kwarkwasa takeyi Masa shi Kuma rabin hankalinsa nakan Rafi'ah Dad ne ya lura da satar kallon Rafi'ah da Ja'afar yakeyi inda yayi gyaran murya zai fara mgn tayi saurin daga wayar qarya tana cewa “ok Ammi ganinan zuwa ki basa hqr" miqewa tayi ta dubi Ni'imah tace “zan wucce Bestie ki kula da kanki don Allah Allah ya kiyaye gaba" zuruf Ja'afar ya miqe yace “bari na rakata ki shirya ki jirani Ina zuwa" kafin ma wani yayi mgn ya fice suka kalli juna ita da Ni'imah Ni'imah tayi Mata murmushi tace “na gde Allah yabar qauna kema ki kulamin da kanki"




Har bakin motar ta rakota ta shiga yaja suka fice suna fita ya dubeta yace “amaryata me kikeso" ko kallon tsiya bai samu ba balle na arziqi mgnr duniya taqi tankasa sai latsa wayarta da takeyi taji yayi parking batare da ya sake mgn ba ya fice taja dogon tsaki tare da cewa “shashasha kawai" Bai wani jima ba ya dawo ya zuba kayan daya siyo a kujerar baya ya sake zama yaja ya nufi hanyar unguwar tasu yana parking ko sallama bata tsaya sunyi ba ta fice ta nufi cikin gda yabi bayanta dake jujjuyawa da kallo ya sauke numfashi ya bude ya dauko kayan yabawa megadi ya shiga dashi shikuma ya fice ya samu sahu ya hau ya nufi gidansa ya bawa driver mota yace yaje ya dauko Ni'imah a gda.
Lkcn da ta shiga ta tarar da Abba suka gaisa yace “ya jikin bestie din" amsawa tayi a gajarce ta haye sama ta cire rigarta da taketa zuba qamshin turaren Mr Ja'afar Wakil ta daura towel ta fada wanka taji an shigo dakin koda ta fito sai taga anti Murja ds kaya ta dubeta tace “anya wannan mutumin ba maye bane Rafi'ah?" Tabe baki tayi tace “dan wahala ba wlh na tsaneshi" murmushi anti Murja tayi tace “ni bawai shi na tsana ba tashin hankalin da zaayi idan ya fadi qudirinsa nake tsoro" batace komai ba ta shafamai a lallausar fatarta ta zura rigar bacci ta kwanta bacci me dadi ya dauketa yauma mafarkinta irin dai wanda tasabane sai ta yanzu take fahimtar inda ya dosa watoar wannan mutumin da take yawan gani ba kowace bane Ja'afar Wakil ne.




Da safe da wurwuri ta tafi makaranta saboda batason damuwa wayarta ma kasheta tayi ta jefata a jaka ranar bata samu zama sai dare ta kunna wayar ta sake sata a silent ta shiga karatu tana ganin kiraye kiraye taqi dagawa sai saqonni sukayita tururuwar shigowa Suma bata budeba tayi kwanciyarta Saida safe ta duba wasu duk shirmen Ja'afar ne taja tsaki ta qara kashe wayar.
Suna garden suna dan tattaunawa wani abokin karatunsu yazo yace “kinada baqi fah Rafi'ah" dafe qirji tayi tace “waye?" Batare da yabata wani attention ba yace “naga motarsa ansa JMW" iska ta furzar tace “kacr bakaganni ba kawai" zaro ido yayi yace “tabdi wlh bazan iyaba wannan guy din yana mgn kamar anyi masa dole" harararsa tayi ta tashi ta koma wani bangaren can nesa ta zauna wata flower ta rufeta taci gaba da karatunta ya akayi ya akayi saiji tayi an qwace littafin ta dago a tsorace.
Numfashi taja tare da miqewa ya zuba Mata ido yace “kina wahalar dani Rafi'ah da wanne zanji ne abubuwa sunyimin yawa fah inason samun sauqi ta bangarenki Amma kinqi tausayamin ya zakiyi da haqqina ne meye laifina don nace inasonki ni bada wani abun banza nasoki ba da aure fah Rafi'atuh meye laifin masoyinki?"




Miqewa tayi tana tattare takardunta tace “meye laifina Nima don nace banasonka bakuma zan taba sonka ba nikam bantaba ganin mayen mutum irinka ba ka rabu dani ka fita a rayuwata kaqi bafa ayinso dole to me kake nema danine maci amanar qauna?" Sosai yaji dacin kalamanta Amma bashida meyi shine ya kawo kansa dole ya jure iyakar wuya watarana sai labari.
Murmushi yayi yace “albishir nazo nayi Miki yau naje na samu Dad mahaifin Ni'imah na sanar dashi inasonki da aure yaje ya sami Mai Martaba ya sanar dashi Kuma inason komai ayishi a game cikin one month kamar yanda akayi na aminiyarki saboda haka daga yanzu ma zaki iya fara shirye shiryenki Nima zan fara daga yau bansan ra'ayinki ba zaki zauna a gidan sarauta ko Kuma Zaki zauna da bestie dinki"........




_Vote_
_Comments_
_Share_
_Please_





*_Ummuh Hairan_*
[1/4, 10:07 AM] Mrs AA Fansah: *_My Bestie's Husband_*





*_Ummuh Hairan_*




*_Wattpad-realfauzahtasiu_*



*_13-14_*



_Ina mamakin mutane da basawa rayuwa uzuri, shin Ina tunaninmu yake tafiya da muke manta komai yana gudana ne bisa iko da sahalewar Ubangiji bawai ra'ayinmu da_ _iyawarmu ba? Am sorry to say sisters and brothers mgnr addini babu ra'ayi a cikinta, idan har kunya zata saki kibar halal to shakka babu aure shine Abu na farko daya kamata ki bari saboda babu abinda yafishi rashin_ _kunya a duniya Amma Kuma shi Ubangiji da kansa yake cewa_ _(WALLAHU LA YASTAHAYI MINAL HAQ) tabbas Allah bayajin kunyar gaskiya saboda haka mu cire son rai mu tunkari gaskiya komi dacinta da ciwonta, Oum hairan ba son rai take rubutawa ba gaskiya take rubutawa wannan karon🤗_



___________________________
___________________________



Miqewa tayi tsaye ta zuba masa manyan idanunta masu saukar masa da kasala a mamakance take kallonsa yayi murmushi ya juya yana tafiya yana cewa wani abune zaikaini Indonesia Amma dole zan bari sai angama komai na bikinmu saboda bazan ballo ruwa nabarki da tarewa ke kadai ba, tabbas bakida laifi a cikin wannan lamarin amma duniya bazatayi Miki adalci ba hakanne yasa na shirya sanya qafar wando daduk Wanda ya nemi uzzurawa rayuwarki"
Baijira cewarta ba ya fice daga garden din Nina dake zaune tanajinsu ta taso tace “tabdi nidai bantaba ganin nataccen mutum irin JMW ba shi ko tsoro bayaji baya ko tunanin me zaije yazo?"
Jinjina Kai tayi tace “so yake ya yankemin duk wata walwalar rayuwata Nina yacika son kansa da yawa duk wani Abu da zan nusar dashi ya kasa ganewa wai har takai ga yaje ya fadawa Dad mahaifin Ni'ima wannan haukan nasa...." Zaro ido Nina tayi tace “wht? Da gaske tabdi kina ruwa Dan kuwa duk juyin da duniya zatayi indai manya suka shiga mgnr nan to kuwa saikin aureshi Kinga aminta zata qara qarfi gaku aminai gaku kishiyoyin juna...."




Batason shirmen Nina don sosai zuciyarta take tuquqi har wani daci takeji a saman harshenta itakam ta gamu da alaqàqai ya zatayi ne Ja'afar ya gane Kuma ya yarda batasonsa zama tayi dabar bisa gado tana jin kanta na wani juyawa yau duk arhar hawayenta ya qafe qaf yaqi zubowa namiji hankaka tabbas namiji buhun qayane namiji ciwon yatsa, tama rasa da wacce kalma zata fassarashi tayi daidai dashi Ja'afar ko iya haka yabarta ya gama da ita ya rusa alaqarta da Bestie dinta, wayarta ce ta dauki ruri tayi firgigit ta duba saitaga number Bestie gabanta yabada wani rass tunaninta lbr yaje Mata aikuwa ta kasa daga wayar sai lkcn kuka ya qwace Mata ta rinqa kuka me shiga rai itakam tana ganin masifa a rayuwarta yanzu badan mutuwa data dauke Mata Yassar ba da tuni ba wannan zancen akeyi ba.
Ji tayi an dafata ta dago ganin Nina yasata sake rushewa da kuka tace “bansan me zance da Ni'imah ta yarda dani ba a lkcn da wannan qazamin lbrn yaje Mata Nina kaina ya kulle wlh narasa gane mafitar rayuwata sai nakejin kamar na kashe kaina na hut...." Rufe Mata baki tayi tace “subhanallahi wannan ba kalmace ta Muslumci ba Rafi'ah ki daina idan fah Allah ya qadarta aurenki dashi bakida tsimi bakida dabara idan Kuma bai qaddara ba ko kinaso bazai yuwuba to ki fawwala masa komai duk wani motsinki yana yuwuwane da amincewar lillahi"



Shiru tayi kafin daga baya ta dago tace “amma mijin aminiyata Nina haba abin ya wucce tunani yakasa saurarona ya fahimci nufina wlh Koda baya auren Ni'imah ni baimin ba bawai don baikai ba aa halinsa ne baiminba banasonsa Nina ya zanyi ya gane banasonsa" murmushi Nina tayi tace “aa fah qaryane wannan wlh duk inda namiji ke kaiwa asoshi JMW yakai kawai dai kice saboda Ni'imah ne bakiji kinasonsa ba kuma ma badan dai mu Mata bamuda lissafi wlh mijinta tunda yaji a ransa batakai masa ba har ya darsa aure aransa to kuwa sai yayi ni sainaga da a auro maka bare da bakasan halinta ba ai gara wacce kasani tasanka in zata iya cutar dakai kasani idanma bazata iyaba kasani namiji fah idan yasa kansa Abu idonsa rufewa yake kunnensa toshewa yakeyi,
Sannan nifa sai nake ganin kamar itama bazata tashi hankalinta ba tunda tasan ba haramun bane" dago idonta tayi tana share hawayenta tace “bakisan Ni'imah ba bantaba baki lbrnta ba Nina Ni'imah qawatace aminiyata tun bamusan kanmu ba tun muna qanana nasani tanada zafin kishi ni da ita Tasha fadamin tsaf zata iya kashe mijinta ta kashe kanta indai yace zai qara Mata kishiya saboda bazata iya sharing din miji ba da wata to balle ni da ni kaina nasan indai na yarda na auri mijinta to naci amanar qauna kuma qauna bazata yafemin ba Ina tayata kishin mijinta saboda nasan tanasonsa fiye da yanda kike zato, nifa dana auri mijinta gara na mutu babu aure yafimin sauqi wlh ko bansan Ni'imah ba lbrn kishinta aka bani zan guji mijinta domin dawwamar lfyta da kwanciyar hankali na balle ni nice me bada lbrn"





Numfashi Nina ta sauke tace “to ilahi ya kyauta Amma ki daina kukannan kiyi addu'a ki tashi muje muyi C.A dinnan mu fito sai ki tafi gida nima gda zan tafi tunda anbamu hutun qwaqwalwa hakan zaibaki damar samo bakin zaren domin wannan mutumin da gaske yake wlh" miqewa tayi suka fita sai yamma suka gama C.A din ko hostel bata koma ba ta nufi gida hakanan tunda ta sauka a mota ta tari adaidaita taji gabanta yana faduwa jikinta a mace ta shiga gidan tana jin faduwar gabanta na tsananta,
Ajiyar zuciya tayi ganin parlour babu kowa tayi hayewarta sama tayi wanka ta canza kaya sannan ta fito,



********

*_Waiwaye adon tafiya_*


Mahaifin Rafi'ah Alh Nuhu mutum me jan iyali a jiki da kyautata musu kwata² su ukune Allah yabashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login