Showing 30001 words to 33000 words out of 66967 words
haukan bazaisa ki samu abinda kikeso ba"
Hajiya Fatsum taja numfashi tace “ni bantaba ganin jaraba irinta Magaji ba ita kanta Rafi'an ba son auren takeyi ba jiya Muhseen yakemin bayani ni saitama bani tausayi tun ranar da mukaje mukaci mutuncinta da iyayenta tanacan ana bala'i da ita akan ita saiya saketa bazata zauna dashi ba gashi Yama kashe wayoyinsa gabadaya duk neman duniya an kasa samunsa balle asan inda yake" hararar Hajiya Fatsum Ni'imah tayi tace “qarya takeyi munafukace wlh tanasonsa ni nasanta fiye da yanda uwarta tasanta inda batajin sonsa aranta da bai isama ya rabeta ba ranar fa da aka daura aurensu fah da ya dawo yayimin hawan qawara bayan ya gama cemin yayi itace ta tada masa da sha'awa wlh idanda batasonsa ko ystsanta bazai riqeba tujararriyace ta masifa akan abinda takeqi"
Numfashi Hajiya Fatsum ta sauke tace “malam me hawainiya yace dole sai ta shigo gdannan abinda nakeso dake ki sanyawa zuciyarki salama ki barmu dasu wlh daga ita harshi tunda suka taboni saina tashi hankalinsu suda zaman lfy saidai idan anayi a lahira suyi ta shigo din Fatsum cefa" kuka Ni'imah tasa tace “kuma fah itama kwanciya zaiyi da ita kwanciyar aure ko?" Tsaki Hajiya Fatsum tayi tace “to meye don ya kwanta da ita ke kin cika shashanci dukkanku ya isheku indai Magaji ne" numfashi Hajiya Sahura tayi tace “nidai zan koma gurin na gangare ayi yanda bazai kwanta da itaba don nima banason ya hada shimfida da ita irin Haj Amina jarabane idan namiji ya dandanasu baya iya rabuwa dasu kinsansu da tsafin tsiya ke yakamata ki fadamin haka tunda kece kike bani lbrn matar babanku buzuwa" haka suka rinqa saqawa da warwarewa basubar gdan ba sai dare sukace Mata gobe ta fito da wuri zasuje gurin Mal na gangare zasu gabatar da ita sai Rafi'ah ta zama yar kallo Haj Sahura tayi Mata alqawarin gobe zatasa Dad ya canza Mata komai na parlourn ta, sunanan suna saqa da mugun zare Hajiya Innah da Karimah da Hafsatu yayan Hajiya Kaltume da sauran dangin ango sukakai kayan lefen Rafi'ah tare da sanya lkcn biki sati biyu abinda akayi zaayi wata guda Ja'afar ya murza kambu yace shi yagaji da ajiyar Mata a gidan wasu abashi abarsa kawai haka Mai martaba da Dad suka taushi Abba ya yarda a hakan Dad ne yace shi ya daukewa Abba komai da uba yakeyi shi zaiyiwa Rafi'ah nan fah gidan Alh Nuhu ya hargitse aka shiga shirye shirye babu Kama hannun yaro ana bikin auta sha lele dinner kuwa Saida aka shirya hudu tun saura kwana biyar bikin ya dawo wani salo harda Prince Day wasu abubuwa da yawa baiyi a aurensa na farko ba hatta rawar jikin da yakeyi baiyi a bikinsa na farko ba duk abinda akace yana barin jiki zai zaro ya bayar kowa yasan cewa wannan aure na musamman ne a gurinsa Amma fah baisan halin da amaryar take ciki ba tun ranar da yaje tace bata buqatarsa ko waya Bai qara kiranta ba balle yaje itama kuwa ta watsar dashi dama baa gabanta yakeba.
Sai dare yaje gidan ya tarar da hakimar tasa a zaune a parlour sai karkada qafa takeyi bai kulata ba ya haye sama yayi wanka.
Saida ya huta sannan ya sauko sanye da kayan bacci ya zauna yana danna wayarsa Rafi'ah ya Kira har tayi Ring ta katse bata dagaba ya sake Kira saboda sosai yake azabtar da kansa da rashin jin nata ta daga tayi sallama ya dube Ni'imah yace “ranki ya dade saraki sai Allah wai bakisan kin sosa raina ba ko?" Banza tayi dashi yayi murmushi yace “shiyasa kullum kike qara mamaye zuciyata kin iyabada hqr sorry My luv wow! Sunan ya hau nikam na gama sa'ar Mata a duniya, am nace ba me kike shiryawa game da shagalin bikin nan ne kinsan fah wannan bikin na musamman ne banason a samu matsala"
Mamaki ya hana Rafi'ah mgn taji yayi dariya yace “kinada basira ok karki damu zanyi qoqarin naga na daidaita komai...." Qit ta kashe wayarta ita tsoroma yabata saikace zararre shi kadai sai zance yake yana bawa kansa amsa, kissing din wayar yayi ya kalli Ni'imah ya tashi ya matsa kusada ita yace “uwargida sarautar Mata ke me kike shiryawa ne?" Dannan zuciyarta takeyi saboda hudubar da Haj Sahura da Haj Fatsum sukayi Mata amma qarshe yakaita zuciyarta tafasa takeyi murmushi yayi yace “mgnr tarihin amarya kece zaki gabatar dashi ranar dinner saboda ke kikasan komai game da ita...." Zabura tayi ta miqe shima ya miqe ya daga Mata hannu yace “baki Isa kice aa ba dolene ramawa kura aniyyarta a gdannan dole kema kiyi Mata abinda tayi Miki bazata rasa wannan gatan ba wlh Kuma banason son zuciya gaskiya nakeso na rantse da Allah kikace aa yau saikin koma gdanku Kuma kikayi son rai wajen gabatarwa sai na tsinke igiyoyin aurena akanki"............
_Hmmm uhmm tab Allah ya qarawa Bestie's hqr wannan tantirin miji naku ya shirya🤔_
_Vote_
_Comments_
_Share_
_Please_
*_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
*_23-24_*
____________________________
____________________________
Hayewa sama yayi yana yan waqoqinsa tabisa da idanunta daya kawo ruwa wai itace zata gabatar da tarihin amarya Kuma har yana iqirarin idan taqi zai qara sakinta zubewa tayi a gurin zuciyarta na hantsilowa tace “allah wannan wannan irin dan iskan mutunne" ta jima tana kuka kafin ta tashi gwiwa a salube ta shiga dakinta Hajiya Sahura ta Kira take fada Mata abinda yake faruwa ta danna Mata ashar tace “ke me kikace masa?" Shiru tayi tana tsiyayar hawaye tace “idan nace zanyi mgn Mom sakina zaiyi nikuma wlh bazan tashi a banza wata tazo taci bulus ba"
Shiru Hajiya tayi daga bisa taja ajiyar zuciya tace “Hakane Kinga bari na Kira uwarshi naji ko zata iya wani Abu" ajiye wayar tayi ta zauna tayi sukuti saida wajen awa daya ta wucce ta kirata tace “ki kwantar da hankalinki kije kiyi idan kin tashi ki zagesu tsaf dagashi har ita wannan shawarar uwarsa ce Kinga ko banza kin bata musu taro...." Katse Mom tayi da cewa “mom bakisan Ja'afar ba itama Barebari batasanshi ba wlh duk abinda ya furta baya masa wahalar aiwatarwa saura fa igiya biyu auren idan na kuskura nayi abinda kukace nasan biyun zai tsinke a bainan nasi"
Tsaki Mom tayi tace “to kiyi abinda ya dace nikam wannan tujararren mijin naki ya fara kaini qarshe wallahi idan na waiwayeshi saiya Raina kansa ace aure ko wata uku baayi ba tashin hankali ya cikashi daga wannan sai wannan kayy wannan Ja'afar din jarfa ne gsky Hajiya Fatsum ta haifo mugun iri irin tsiya irin jaraba" haka suka hadu sukayita zaginsa bata ankara da yana tsaye akanta ba Saida suka gama tana juyowa taganshi harde da hannu a qirji.
Saida taji qirjinta kamar zai tsage tsabar tashin hankali ya shafa gashin bakinsa ya juya ya ficeTsaki taja sosai yaji tsakin amma dake miskili ne bai juyaba ya bude dakinsa ya shiga ya kwanta yanata juyi babu mataimaki takaici ya cikashi ya sake gyara kwanciya kawai yaja pillow ya rungume.
Amarya Rafi'ah kuwa tananan kullum cikin quncin zuciya take ta kasa karbar auren Ja'afar a qasan ranta kowa dai daya shafeta a salube yake hidimar bikin saboda damuwar da tayiwa amaryar tasu yawa duk wata kwalliya da akewa amare taqi yarda ayi Mata hatta lalle da wankin Kai qememe taqi duk wani daya Isa ya fada Mata taji ya fada tayi kunnen uwar shegu shikuwa Abba dama da aka fada masa cewa yayi a qyaleta kukanma kansa yakeyi babu meyi Mata maganin damuwarta sai Allan daya jarabceta, ranar ranar alhamis akayi kamu juma'ah takanas Hajiya Innah ta turo me kwalliya akan ayiwa amarya nanma tayi tsalle ta dire itafa bazaayi Mata ba dole haka aka qyaleta da yamma likis aka turo wasu arnan motoci domin daukarta wai Prince's day tana kuka tana komai Aunty Murja da Aunty Raziqa suka fito da ita cikin alqabbar da Saida akasha dambe sannan ta yarda ta saka suka sanyata cikin daya daga cikin motocin.
A cikin gidan Sarautar aka ware wani bangare aka kashe masa manyan nairori aka tsara gurin dinner tunda suka shigo sautin sarewi da algaitu ya cika Mata kunne suna busawa da bugun zuciyarta daqyar ta samu ta fara kamo addu'o'i tanayi wasu matane su hudu suka nufo matar da take suka bude suka fito da ita suka kamata anata yi musu ruwan kudade da turare itakam sai ruwan hawaye takeyi da shassheqa.
Wani bangare suka nufa da ita suka shiga Basu tsaya ba Saida sukakai qarshe suka qwanqwasa wani daki aka bude musu suka shiga Saida sukayi Mata guri a gefen gadon sannan suka russuna suka kwashi gaisuwa suka fice matsowa yayi gabanta ya jima yanajin sautin kukanta tanata shassheqa yanajin diran gunjin kukan nata har tsakiyar ruhinsa ya tsugunna a gabanta ya sanya hannu ya dage hular alqyabbar.
Babu kwalliya a fuskarta ga hawaye ya bata fuskar Amma bai hana asalin kyaunta fitowa ba, yaja ajiyar zuciya yana qara sauke injin idonsa akanta idanunta a lumshe suke sosai kukanta yake tabashi ya miqe ya zagaya dakin ya dawo fuskarsa a daure ya sanya hannu ya miqar da ita ya fara qoqarin zare Mata alqabbar ta riqe da sauri ya furzar da iska me zafi ya bude baki yace “ance rabonki da wanka tun shekaran jiya tunda bazaki iyaba ni zanyi Miki yanzu saboda banson qazanta"
Batasan sanda ta bude idanunta akansa ba yaci gaba da qoqarin cire mata rigar ta sake qanqame jikinta tana kuka tace “don....don Allah ja'....." Rufe Mata baki yayi ya dago kanta yace “ki roqeni wani abun Banda wannan tunda Ammi da Abba Basu Isa su saki kiyi ba ni na isa nayi miki"
Baijira cewarta ba ya faketa ya dagata cak tana kuka tana shure² yaqi sauketa Saida ya dangana da ita bathroom din dama ya shirya terming dinsa kawai ya tsomata cikin ruwan alqyabbar kawaiYa cire Mata nanfa suka Dora kokawa kowa naji da taurin kai takaici ne yasa baisan sanda ya keta riqar sabuwar atamfar sharratone din ba ta rintse idonta da qarfi jikinta na rawa ganin ta saki Masa tanata ajiyar zuciya yasashi kunce zanin ya zare Mata komai na jikinta pant da bra kawai yabar Mata ya fara wanketa tayi tayi ya qyaleta tayi yaqi.
Aikuwa ta Raina kanta ta dirzu miqewa yayi ya bare sabon towel ya miqa Mata fuskarsa kamar Bai taba dariya ba yace “ki tashi jiranmu akeyi ki fito banson sakarcin nan naki" yana fadin haka ya fice daga bathroom din yama fice daga bangaren gabadaya qarasa wankan tayi jikinta har yanzu rawa yakeyi tana jera masa Allah ya Isa dama Wanda ya fada mass batayi wanka ba, towel din ta dauro ta fito ta ishe wannan matar da taje yimata kwalliya taqi da wata me kamala a zaune a dakin tsoro ya cikata amma sai taga wannan kamilar ta matso ta kamo hannunta tace “na zaci can zaa kaiminke Ashe Baban Innah ya murda kambu to hakanma yayi Salamatu kiyi ki shiryata goma na dare zaa fara walimar naga yanzu har takwas kinsan Magaji ba hqr ya cika ba" zaunar da ita tayi Salamatu ta miqa Mata Mai ta fara shafawa har yanzu ta kasa tsayar da ruwan idonta bayan ta gama salamatu ta fara aikinta ana kwalliyar hawaye na gogewa daqyar Hajiya Innah ta rarrasheta tayi shiru akayi kwalliyar tabata wani arnen leshi tace tasa ta sanyashi yayi masifar yimata kyau kasancewarsa maroon daurin dankwalinta ma an dauki kusan 30 minutes sannan aka gama Hajiya Innah ta bata sabuwar alqabba milk da akayiwa ado da Marron tasa Mata takalmin alqabbar shima milk ne sai awarwaro na gold masu tsadar gaske dayan hannun Kuma agogo sai zobba da dankunne da sarqa habawa wannan rana ta musamman ce duk da bata cikin nutsuwar zuciya data kalli kanta a madubi Saida tayi hamdala tare da ajiyar zuciya.
Bude qofar sukaji anyi jakadiya ce tazo ta fadi gaban Fulani Innah tace “Allah ya qara Miki lfy Mai martaba Magaji ne yace ayi muku mgn taro fah yayi taro ku kadai ake jira" dago Rafi'ah tayi tace “mun gama yanzu zamu fito" turaruka ta fesa Mata ta Kama hannunta suka fito kicibis sukayi dashi a qofar shigowa bangaren ya kalli Rafi'ah ya kawar dakai yace da fulani Innah “sannu mun wahalar daku" murmushi tayi tace “nadai fada maka idan kun tashi yanda zakuyi" kallon Rafi'ah yayi yayi murmushi yace “natsani wannan kukan wlh ki daina babu abinda zai hana saima tunzurani da kikeyi"
Tsakaninsu da gurin zamansu babu nisa ya janyota jikinsa ya shaqi qamshin turarenta ya sauke ajiyar zuciya suka fara takawa a haka tanata qoqarin janyewa yaqi bata dama takan wani farin carpet sukabi wasu dogarai na takensu gaba da baya sunata kirari da ihu tuni sautin dake tashi a gurin ya canza akasa na gidan sarautar saida suka zauna sannan mutane suka rinqa tasowa suna zuwa suna kwasar gaisuwa suna zuba mawa amarya da ango kari Ni'imah na gda batasan wainar da ake toyawa ba.
Saida lkc yaja sosai ta samu labari aikuwa kishi da baqin ciki ya tunzurata ta dauko mota ta fito tana rayawa a ranta wato ita bata isaba shiyasa baiyi Prince's day a aurenta ba sai wannan auren cin amanar ya tarawa mutane, anacan anata shagali biki yayi biki taro yayi taro ango sai washe baki yake yana satar kallom Rafi'ah da tayi kicin² da fuska taketa jan zuciya shi hakanma nishadi yake bashi, batare da sunyi tsammani ba kawai saiji sukayi an wankesu da ruwan Sanyi qarara abinda yaja suka miqe gaba daya MC baisan me akeba yanata zuba babatu saiji yayi ance “ku dakata yaku taron tsinannanu Wanda kuka taru saboda auren tsinanne da tsinanniya to ku sani dukkanku kunyi kadan kuci mutunci na harni zaaci Amana a cuceni........
_Vote_
_Comments_
_Share_
_Please_
*_Ummuh Hairan_*
*_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad-realfauzahtasiu_*
*_25-26_*
_____________________________
_____________________________
Tasowa dogarai sukayi da sauri sukayi Mata cahhh suna fadin “Saita kalami yar talakawa...." Saurin daga musu hannu yayi ya miqe ya taka cikin cikar Izzarsa ya Isa gabanta tanata huci tana cije lebe, dafa hannu yayi tsammaninta marinta zaiyi sai taji ya sauke hannunta a kafadarsa ya janyota jikinsa ta fara qoqarin fincikewa yasa dukkan qarfinsa ya mannata da qirjinsa ya karbi abin mgnr yayi gyaran murya cikin sauti me nuna asalin izzar sarauta yace “da farko inayiwa baqinmu barka da zuwa tare da baku hqr a bisa abinda wannan zautacciyar tayi muku akasi aka samu baasan ta fito ba tadan hadu da matsalar brain ne idan abin ya motsa tana fuzga so do Allah kowa yayi calm down komai zai wucce am Sarkin gda da Sarkin qofa ku mayar da ita bangarenta a qara Mata tsaro don gaba kadan duka zata fara"
Yana fadin haka ya dago sakar Mata murmushi ya daga Mata yatsa ya barta tsaye sororo kafin ta ankara taji an cafeta sama an fice da ita daga gurin aka cillata a wani killataccen bangare a gdan shikuma ya koma gurin amaryarsa yana zama ta miqe ta fice daga gurin a guje ya sa aka bita itama aka riqe masa ita ya taso ya iso gareta yasa hannu ya kamota ya fice da ita daga cikin taron bangaren da aka fara kaita nan ya nufa da ita ya cillata saman kujera ya fara bala'i yana cewa “kema mahaukaciyar ce irinta da zaki biyeta ku watsarmin da mutunci a bainan nasi?
Miqewa tayi tana huci tace “akanme zakace mata mahaukaciya bayan kafita hauka da kana tunanin zaka samu wannan damar ka gama shimfida son zuciyarka a banza ne kana tunanin ko ita ta qyaleka duniya zata qyaleka ne? Ja'afar Ka cutar damu Allah ya isa wlh bazamu yafe maka ba Kaine Ummul aba'isin kowacee masifa ta rayuwarmu da dadi da wuya mun jurewa juna har kawo lkcn daka riskemu Ashe Kaine qaddararmu Kaine bala'in da zai fado rayuwarmu ya rusa mu kacina son kanka da son zuciya Wanda na tabbata duk Wanda yabi son zuciya qarshensa nada......"
Wata fusga da yayi Mata ta hanata qarasa kalaminta ya cillata gadon yabita ta zulle a guje ta nufi bathroom yabita ya sake wartota ya hadata da bango yace “qarya kikeyi Rafi'ah bazan taba nadama ba a rayuwata giya nasha ko caca nayi kokuwa zina na nemeki da ita da zakice zanyi nadama? Oh God" ya fada tare da bude qofar a fusace ya fice daga dakin ta koma ta zauna tana wani irin kuka me ciwo tana tambayar kanta me hakan yake nufi kenan ya kawota bangare babu kowa ya ajiyeta babu kowa nata.
Tana wannan tunanin taji an bude qofar an shigo ta dago da sauri ganin qanwar Ammi Bushira da Aunty Murja da Aunty raziqa yasata miqewa da sauri qarasawa sukayi gabanta Aunty Bushira ta Kama hannunta ta zaunar da ita tace “bazaki daina kukannan ba ko gashinan kinjawa kanki Ja'afar ya rantse bazakibar gdannan ba kinzo kenan...." Dagowa tayi da razane tace “ban gane ba?" Aunty Raziqa ce ta harareta tace “wannan haukan da kukeyi Kuna gwara kan mijinku babu abinda zaija muku sai raini da wulaqanta ita idan kishi yasata ta haukace ke mene hujjarki na haukacewa to wlh Abba yace ki kiyayi fushinsa sarai zaku raba hanya indai akan aure ne kowa ma yasan mijinku bai kyautaba to Amma shima ya zaiyi da zanen qaddararsa tun kafin a haifeshi sukayi alqawari da Ubangiji na duk wani Abu dazai faru dashi tun daga ranar da ya fara shaqar iskar duniya har zuwa Rana ta qarshe a rayuwarsa haka kema haka Ni'imah to akanme zaku haukatashi ku mayar dashi ball a tsakaninku ita ta bugashi nan ke ki bugashi can ko kin dauka saboda ya aureki don yana mijin aminiyarki babu alqalami tsakaninku to wlh ki dawo hayyacinki nasan iyayenmu basu barmu da jahilci ba saidai kana sane ka take sani sakarya kawai da takeson wasa da damarta"
Durqushewa tayi a gurin sosai kalaman Aunty Raziqa suka ratsata Aunty Murja ta dora da nata itama me ratsa bargo kafin Aunty Bushira ta cafe da cewa “gashi Allah ya baki mijin da yake sonki duniya ta shaida hakan Amma kinason yin sakacin sane masa kibi a sannu duk abinda hqr Bai bada ba to tashin hankali ma baya badashi dole yace yau a gdansa zaki kwana