Showing 39001 words to 42000 words out of 66967 words
“ni Kuma nida tunda ka tafi Ina kwance ko qasa ban sauka ba saida naji kamar ana tabamin qofa nace maka zan kiraka anjima" numfashi yaja kawai sai ta Kama shassheqar kuka abinda ya tashi hankalinsa kenan yace “to meye Kuma daga tambaya sai kuka" jan zuciya tayi tace “ni bansan meye ta tarewa duk wani wanda ya shafeka ba da baya sona nima fah bason aurennan nakeyi ba qarfa qarfa akayimin...."
Katseta yayi da cewa “kinga naji Ni dama tunda ta fada ban yarda ba kawai na kiraki ne don na gasqata ai daga yanayinki ma ansan ke bame fitina bace" jan zuciya tayi tace “to nidai banaso kajawa matarka kunne kada ta qara qoqarin hadani dakai idan wani abu takeji akaina tazo ta sameni zan iya sammata lkc a cikin lkcnka inka yarda" dariya yayi yace “bama na buqatar kowa ya shiga lkcna ya tsaya iyakar nawa ni daya"
Kashe wayar sukayi tayi murmushi tace “salon wasan zai canza dama aunty Bushira ta fadamin saina sawa idona kwallin rashin mutunci zanyi miki illah idan kika matsa Ni'imah badon mijin ba saidon ki gane kowa yanada tasa baiwar" tayi bacci sosai sannan ta tashi ta shiga kitchen ta fara shirya dinner ta bata lkc matuqa wajen shirya musu abincin lkcn data gama biyar saura ta fada bathroom ta dauki wankan susuta megida ta harde a parlourn tana kallo tana chat bai shigo gdanba sai bayan magrib ya jima akanta kafin ta ankara shima Saida ya zare wayarta a hannunta ta dago suka hada ido da Ni'imah dake shigowa bakinnan kamar cokali kawai saita qara fadada murmushinta ta miqe ta rungumeshi tare da lalubo bakinsa ta hada da nata ya tallafo bayanta yana sakin wani nishi me qarfi mutuwar tsaye Ni'imah tayi saboda abin yazo Mata a bazata kallonta Rafi'ah tayi ta daganta gira tare da janyewa daga jikinsa ta shafa sajensa tace “yau na yini da kewarka sai nakejina kamar marainiya ka tafi ka manta damu..."
Rufe Mata baki yayi yace “ah haba kiyi istigfari wlh kina Raina munje anguwa da Mai martaba ne dana dawo Kuma sai na wucce sama mana Visa me kika tanadar min?" Rufe idonta tayi tana yar qaramar dariyar kirsa tace “a..bin...da...ka...fis...." A rarrabe tayi mgnr ya kwashe da dariya yace “wayyoh dadi matata kina shagwabani wai dama haka kike wow! Allah na gde mak...."
Muryar Ni'imah yaji ta rushe da kuka tana cewa “Allah ya isana wlh Allah ya isana kirana kayi don ka wulaqantani a gaban wannan yar iskar matar tak..." Tsawa ya daka Mata yace “keyyyy ki iya bakinki...." Rufe masa baki Rafi'ah tayi tace “Haba ranka ya dade saurin fushi ai ba naka bane ay rarrashi take buqata" sakinsa tayi ta nufeta ta kamota tace “kekuwa rabin jiki kiyi hqr mana ai bamusan dakeba idona rufewa yake idan Ina tare da mijina shine sanyin ruhina salamar rayuwata am sorry please iso muyi dinner yau abinda nasan kinaso fiye da komai shi nayi mana kowa favorite dinki zaici yau a gdannan"Fusge hannunta tayi ta hankade Rafi'ah tace “dake da favorite din na hadaku naci bura ubanku ni zakiyiwa bariki kina kallona kina wani qara rungumarmin miji kina tsotsar bakinsa har kina dagamin gira kice wani baki ganni ba kaikuma kwallon munafiki sullutu sallamamme da aka wanke wani guri aka bashi ya shanye har wani qara shigewa kake jikinta to ka hadiyeta mana qarewar so da kewa munafiki mara adal...."
Hannu ya daga zai kwada Mata mari Rafi'ah tayi saurin riqe Hannunsa tace “Don Allah ka rinqa tausasa zuciyarka mijina ai namijin gaske baa sansa da fushi a gidaba idan kana fushi meye sauqinmu ne muda zamu rayu a qarqashinka please yi Mata uzurin nan daka saba da wankama nakeso na tayaka kayi nasan ka gaji Amma naga tumbinka ya sauka ba haka na saba ganinsa ba muje na ciyar dakai yanda zaifimin dadin shafawa" ta qarasa tana shafa tunbinsa murmushi yayi ya dagata cak ya direta a kujerar dinning din takaici ne da baqin cikin abinda bata taba tunani ba yasa Ni'imah juyawa zata fice har takai bakin qofa yace “dokace ba umarni ba kin saba taka dokata Ina qyaleki wannan bazanyi uzuri ga kowa ba"
Sumsum ta dawo taja kujera ta zauna Rafi'ah tai murmushi ta hadawa kowa abincin ta turawa kowa gabansa ta diba a cokali zatakai bakinta ya riqe tasan me yake nufi ta matso da kujerarta ta rinqa bashi tuwon Cous-Cous ne da miyar kubewa da yaji bandar kifi sai fatan doya da yaji hanta babu kunya Ni'imah da ganda tasata yiwa kanta horon yunwa ta zage ciki ta nadi tuwon tasha hadin lemon da Rafi'ah tayi musu na kankana ta miqe ta Kama hanya zata tafi Ja'afar yace “ki jira na gama na rakaki tunda cikinki ya dauka a qa'ida ma fah ba ita zatake girki ba ke zakikeyi mana tunda ita sabon hannu ce da wanne zataji saboda haka daga gobe zaki fara aikinki zuwa sati" ta hadiya iyakar hadiya wai tayi musu girki suci tab aikuwa zaayi zaman yunwa a gdan to ita da wanda zataci ma batason girkawa itace zata girkawa qarata biyu abinci tab zaayi bala'i kuwa" a tsaye ta tsaya taqi zama shima Kuma yaqi tashi saijan Rafi'ah yakeyi da hira itace taga tsaiwar tayi yawa tace “am dare yayi zata gaji da tsaiwa ka tashi ka rakata" juyowa yayi ya dubeta ta kumbura fuska yayi murmushi yace “wlh na manta dake a tsaye sorry muje na rakaki" miqewa yayi itama Rafi'ah ta miqe ta rakasu har bakin qofa tace “asuba ta gari Best...."
Wata uwar harara da yayi Mata tasata juyawa da sauri ta fara harhade kayanta sake gyara parlourn tayi ta kunna turaren wuta a burner ta haura saman shima ta sake Masa sabon gyara tayi alwalar isha tara harta wucce tayi isha tayi shirinta na kwanciya gabanta na faduwa batason nacinsa cikin saa daya shigo din shima bai wani takura Mata ba sukayi baccinsu salamun salamun washegari litinin ta roqeshi alfarmar zataje tayi C.A a school da farko cewa yayi bata isa fara yawo ba Saida yaga ta marairaice masa zatayi kuka sannan yace ta shirya yakaita suna fitowa Ni'imah ma tana fitowa da alamun fita zatayi iyakar son tuno abinda ya wucce dinsa yakasa tuna sanda ta tambayeshi fita Koda yake dama tunda aka fara mgnr aurensa da Rafi'ah bata tambayarsa zuwa unguwa saidai ya dawo ya tarar batanan.
Ya shirya Mata mugunta saboda haka ya nufeta da sauri yana zaro kudi a aljihunsa yace “Au na manta yau zanyi baqi daga Gombe ki bawa Yahaya kudi gasu ya siyo kifi nasan babushi a kitchen dinki wancan kin barsa ya lalace kiyi mana farfesu sannan kiyi mana tuwon alkama miyar kalkashi ki tabbatar kin gama kafin azahar zankai Rafi'ah makaranta May be tare zamu dawo da baqin"
Bai jira cewarta ba ya juya yana murmushi ya shige motarsa yaja har suka fita takasa motsawa tashin hankalinta yanda zatayi wannan wahalallan girkin daya sata ita tunda take a gidansu bata taba ganin anyi tuwon alkama ba Amma wai yau ita zatayisa harma da tagomashin miyar kalkashi ga gyaran kifi da kullum ta gyara sai yace bata iyaba gdanta yana qarni, zubewa tayi a gurin ta dora hannu aka tanaso ta zunduma ihu Amma ta kasa daqyar ta miqe kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta koma ciki ta rinqa zagaye parlourn tana tunanin ta inda zata fara kiran Hajiya Sahura ne ya shigo ta daga da sauri tace “ya munata jiranki boka yace dole sai kinzo aiki zaiyi yadda akeso ke Kuma kina bata Mana lkc" sai yanzu ta samu damar fashewa da kuka tace “Mom wannan dan gadon masifar ne ya hadani da aiki wai baqi zaiyi shine yace nayi masa tuwon alkama miyar kalkashi sannan nayi masa farfesun kifi harda cewa saina hada masa lemo don Allah ki turomin Marawiyyah nasan ta iya tunda girkinsu ne na yan qauye wlh idan banyi ba akwai matsala" Hajiya Fatsum ce ta karba tace
“Ke shashasha ce to ki fito mana idan aka gama abinda zaayi minti nawa ne zaki dawo kiyi masa inma kafi tuwon alkama ne Kuma ma idan ansamu yadda akeso ai bai Isa yace qala ba" dadine ya cikata tace “ok hakane ganinan" daukar Jakarta tayi da mayafinta ta fice tana dariya tana cewa “Ja'afar Wakil ka bonu ka lalace a gurina" mota ta dauka ta nufi qauyen tana zuwa ta tarar da uwar mijin nata da uwarta sunyi gurfane kamar masu neman gafara.
Dariya boka na gangare ya sheqe da ita yace “shegiya haihuwar asara ta sabawa umarnin miji ta fito toke an fada Miki wannan yarinyar a zaune take ai munafurtarki takeyi tana zagayewa tana bin manyan bokaye yo baki ganiba ko a yammatancinku tafiki farin jini ke Saida aka rinqa hadawa da layu da guraye sannan aka samu aka hadaki da wannan kaffafen mutumin da kurwarsa taqi juyuwa to ai baki sani bama tuni burinki yana gaf da rushewa ke wata biyar yana baki kinaqin karba ita kuwa tun ranar farko ta karbe yanzu haka da cikin yariman Azare me jiran gado a jikinta....."
Zaro ido sukayi tare da dafe qirji dukkansu Hajiya Fatsum tace “ciki Kuma daga zuwanta haba boka sake dai dubawa ni dana bashida wannan azarbabin" tsawa boka ya daka Mata yace “ankare nutsu tsinanniya wacce ta fatalar da aljannarta na rantse da bukkata Rafi'ah amaryar danki Ja'afar tanada shigar ciki saidai a dauki mataki Amma cikikam akwaishi abinda yasa naqi yarda na rusa aurennan kenan na hango rabo me zafi yana yawo inma baayi aure ba to zaa lalace ayishi a titi yanzu mafita dayace idan bakwa buqatar cikinnan zanbaku wata laya kusan yanda zakuyi ku haqa saitin inda kukasan koba kullum ba wataran dole sai tabi gurin ku binne to indai kukayi haka duk sanda ta samu ciki ko ya Isa haihuwa indai ta taka gurinnan saiya bare hhhhhhhh tsinannu Kuma karba fa zakuyi ku?"
Tsoro ne ya shigi Ni'imah tace “kayy aa gaski....." Bige bakinta Hajiya Sahura tayi tace “aa ubanki ai dole mu karba ke baki kishin kanki baki fatan ki zama uwar sarkin wataran" kallon Hajiya Fatsum Hajiya Sahura tayi duk hatsabibancin Fatsum tana shayin Sahura take tace “abamu boka nima banason shegiyar yarinyar nan ta hada iri da dana wlh irin Hajiya Amina ai irin masifane buzuwa ce fah tsafi sukeyi su bama asiri ba".............
_More Comments_
_More Typing_
_Ummuh Hairan_*
*_Wattpad- realfauzahtasiu_*
*_Gmail-fauzahtasiu41@gmail.com_*
*_YouTube- Open eyes multimedia_*
*_Telegram_*
👇
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7
*_33-34_*
_____________________________
_____________________________
Dariya boka ya sake sheqewa da ita ya dauko wata laya ya miqawa Hajiya Fatsum yace “to debabbiya wacce ta saki danta ta Kama gaibu wannan asan yanda zaayi a binne ta da an binne mgn ta qare ciki zai lalace duk lkcn data tsallaka gurin da aka binne amma ayi takatsantsan kada ido ya gani" murmushi Barebari tayi tace “haba boka yau muke tare mukayi aikin da yafi wannan wahala ma bare wannan gashi shekaru sunata tafiya 38 years taqi fasuwa kawai kabar komai a yanda yake ni zanji da komai"
Ashar ya qunduma Mata yace “hhhhh shegiya yar fashi da dabara ashefa ke har fashin rayayye kikeyi ki sanya matacce a wannan aikin bazaiyi Miki wahala ba dama na irinku ne marasa imani kije kiyi yawwa sai wannan ruwan rubutun duk yanda zaayi yau yakai cikin Rafi'ah kota abinda zataci ne indai batayi Bismillah ba to aikin gama ya gama sauran bayanin zakugani da idanunku Amma fah kubi a sannu idan kika kuskure kwabarki zatayi ruwa asirin da kika Dade da binnewa zai fasu" tsawa ya daka musu suka firgita yace “ku tashi tsinannu uku wadanda basuda rabon lahira" tashi sukayi da baya da baya suka fita daga bukkar bokan suka nufi mota kowanne da abinda yake aunawa itadai Hajiya Fatsum tunanin abinda kaje yazo takeyi tunda take da Ja'afar iyakar sonta data mallakeshi ta kasa ta kashe millions of Naira don kawai ta cire masa jin Hajiya Innah aransa Amma ta kasa saima ya zamana kamar qara musu shaquwa takeyi yanzun ma game da abinda ya shafi Rafi'ah tafi tsoron Hajiya Innah fiye da ita kanta Rafi'an domin ita tasan an gama da ita indai maganin nan yaje cikinta to mgn ta qare sallar farillah ma sai anyi da gaske zatakeyi bare nafila.
Cikin saa har suka koma qarfe daya da rabi Ja'afar bai dawo ba da sauri suka nufi qofar bangaren Rafi'ah dake Intalok ne basusha wata wahala ba suka qwaqule daya daqyar sukayi haqa suka jefa layar gashi kuwa sun iya saiti dake tsofaffin mushirikai ne bayan sun gama suka mayar da abinda suka bambare suka debo farin yashi a waje suka zuba suka sake zuba ruwa suka saki ajiyar zuciya tare,
Bangaren Ni'imah suka shiga suna mayar da numfashi Hajiya Fatsum ta dubi Ni'imah tace “ah ke abin naki harda qazanta Magaji ya tsani qazamin mutum gsky ki zage wajen tsafta idan ba hakaba kina ganinsa zaiyi Miki fintinkau" yatsina fuska tayi tace “to Hajiya ga yan aiki harsai wani nayi aiki girman ma ai yanada halin da zai nema mana kuku tunda dama babu inda akace na rinqayi masa girki" tabe baki Hajiya Fatsum tayi tace “ai gakinan gashi ni Ina ruwana" kitchen din suka shiga su uku sukayi Mata tuwon alkamar da miyar kalkashi sai farfesun kifi cikin lemukan ne tace a hada na kwakwa a zuba rubutun a ciki saboda duk lemukan duniya Rafi'ah tafi sonshi, aikuwa suka zage suka hada ta dauka tasa a freegde suka tayata ta gyara bangaren su kansu ba wani iya gyaran sukayi na tsanaki ba andai burbura sukayi suka tafi saboda basason yauma ya dawo ya tarar dasu a gidan ita Kuma Ni'imah ta fada wanka ta kashe kala ashe iskanci ke hanata kwalliya ta iya,
Dawowa tayi parlour ta harde abinta Ja'afar ya shigo gdan bai shigoba sai bayan la'asar sosai suka shigo shiga Rafi'ah ya daukota daga makaranta tunda suka shigo taji gabanta na faduwa ta fara karanto addu'o'in neman tsari ya bude Mata motar Ni'imah na kallonsu ta window ya riqe Mata jakar ta fito ta sunkuya ta karba ya lakace Mata hanci sukayi dariya ya Kama hannunta suka shiga ciki,
Suna shiga suka fada wanka yau wankanma tare akeyinsa itadai duk a kunyace take Amma batada mafita hàka sukayi suka fito ta shiga kitchen da sauri dama tanada miya data soya jiya ta dafa musu farar shinkafa ta hada salat ta zubo musu suka baje a parlourn sunaci suna Hira tuni ta manta da komai ta zage tana bashi lbrn irin wahalar da tasha jiya da irin ciwon da kanta keyi bayan sunci abincin ya dauko Mata paracetamol a clinic dinsa na cikin gdan yabata tasha ta miqe da gaske yau taci biro da yawa kanta sarawa yakeyi ta shige daki ta kwanta
Sannu ya rinqayi mata yana tofa Mata addu'a a goshinta hardai ya samu bacci ya dauketa wannan dalilin ne ya hanata zuwa dinner lkcn dinner tanata baccinta yana jiran ta tashi har Tara na dare gashi Ni'imah ta dameshi da kira kawai saiya tashi ya tafi shi kadai tana ganinsa shi kadai tace “ina take?" Yanda tayi tambayar yashi qara saita injin idonsa akanta yace “wa kenan?" Qasa tayi da kanta tace “Rafi'ah Mana naga kun shigo tare Kuma naga yanzu kazo Kai kadai ita bazakayi Mata dole tazo taci abincin anan ba?" Murmushi yayi yace “bayin kanta bane yanzu hakama tana bacci kantane ke ciwo sosai karki damu ita batada matsala"
Shiru tayi zuciyarta cinkushe da takaici da baqin cikin yanzu idan batazo ba duk shirinsu ya rushe" kallonsa tayi tace “Amma daka tasota ai qila ta yini bataci komai bane batason cin abinci idan abinta ya motsa saita kwana uku bataci wani Abu me nauyi ba" baice Mata komai ba yayi Bismillah ya faracin tuwon yana korawa da lemon abarbar duk da bayajin yunwa Amma yaci da kirki ya dago ya kalleta sai juya cokali takeyi ta kasacin abincin yace “bake kikayi abincin nan ba dandanon girkin ba naki bane na Barebari ne"
Da sauri ta dubeshi yace “banason musu akan abinda nariga nayi yaqini akansa kodai kinje ko Kuma tazo wanne ne ya faru a ciki?" Hade rai tayi ta fara qunquni yayi murmushi yace “bazaki nutsu ba da kinkwantar da hankalinki sai yar uwarki ta koya Miki da muka tafi nake fada Mata cewa tayi zakisha wahala na kiraki na fada Miki ki jira ta dawo sai kuyi" harara ta watsa masa tace “sai Kuma nace Ina neman taimakonta"
Ganin ta juyawa zancensa ma'ana yasashi jan bakinsa ya tsuke ya tashi yayi gyatsa yayi hamdala yace “babu wani Abu ko zan tafi?" Miqewa tayi da sauri tace “bari na baka wannan lemon kwakwar nasan tanaso Kuma zataji dadinsa kasa Mata a freedge idan ta tashi saitasha" yaji dadin nuna kulawarta ga abar qaunar tasa ya karba yayi kissing nata yace "kin fara hankali Saida safe" ficewa yayi yabarta tsaye cikin jin dadi tasan indai Rafi'ah taga lemon to bazataqi shaba da zaran Kuma Tasha to aikin gama ya gama zasu kassarata cikin sauqi
Koda ya koma din tana kwance har lkcn bata tashiba shine yaga baccin yayi yawa ya tabata yaji ta sauke numfashi tare da bude idonta tar akansa ya sauke Mata murmushi yace “ya kannaki?" Lumshe idonta tayi ta bude tare da miqewa zaune tace “yayi sauqi shine baka tasheni ba akayi magrib har akayi Isha" Hannunsa ya dora bisa goshinsa yace “sorry my heart nabarki ki hutane yanzu tashi kiyi" miqewa tayi yabi bayanta da kallo yanajin wani yanayi a jikinsa tausayinta yake hanashi takura Mata ya lura itan tanada wani hali ko zatasha wahala indai tasan Abu haqqinka ne to bazata hanaka ba wannan dalilin ya darsa masa tausayinta,
Baiji fitowarta ba saiji yayi ta ja hancinsa ya sauke numfashi tare da zamewa ya kwanta yana kallonta har ta idar da sallar ta zauna tana lazumi ta dade sannan ta tashi ta shiga wanka ta fito tayi Shirin kwanciya yace “au na manta qawarki tabani coconut Just tace na kawo miki" murmushi tayi tace “na gde Amma yanzu banajin sha'awar komai wani baccin nakeji zansha da safe Ina fatan kasamin a