Showing 18001 words to 21000 words out of 66967 words

Chapter 7 - MY BESTIE'S HUSBAND COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Oct 2024

8099

Yaya Rashid Aunty Raziqa sai ita auta Rafi'atuh inda suka taso cikin gata saboda mahaifinsu dan bokone Kuma dan siyasa sannan dan kasuwa da arziqi a gdansu bakin gwargwado gashi dason taimakon talakawa.
Don asalin alaqarta ma da Ni'imah cikin taimakon mahaifinta ne shekaru 18 baya lkcn sunada 3 years a duniya mahaifin Ni'ima maqocin shagon Abba ne a kasuwa sai karayar arziqi ta sameshi dake harkar gold sukeyi barayi suka shigo kasuwar sukayi barna Abba ma an taba dukiyarsa sosai amma dake yafisu qarfi Kuma shi kayansa ne na kansa yasa bai tozarta ba inda Alh Sabo mahaifin Ni'ima ya kasance kayansa hadin gwiwa ne don kaso 70% ba nasa bane gashi yana cikin wadanda akafi yiwa barna.
To dake akwai fahimtar juna tsakanin Alh Sabo da Alh Nuhu yasa Alh Sabo yana kuka yake zayyanewa Nuhu halin da yake ciki yana fada masa yasai da gidansa ya rage bashin kudin mutane duk wata kadara tasa ya siyar Amma bai gama biyaba har yanzu da saura 14 million da ake binsa gashi ko abinda zasuci babu a gidansa gidanma sai gdan gado ya koma kuma mahaifiyarsa ta mutu tun yana qarami matar babansa Kuma basa shiri da matarsa don kullum ciki gori takeyi musu.
Sosai Alh Nuhu ya tausaya masa take yayi masa alqawarin bashi gurin zama a gdansa sannan zai biya Masa bashin Kuma zai zuba masa sabon kaya yake juyawa har Allah ya sake dagashi ranar Alh Sabo yayi kukan farin ciki hakance ta faru a ranar Sahura ta dawo gdansu Rafi'ah da zama duk wani alqawari da Abba yayiwa Dad ya cikashi ashe kudin na Sarki Muhammad Wakil ne mahaifin Ja'afar da aka Kai masa sai yace yabarshi kawai ya yafe masa wadanda ya karba na baya ma don banasa bane na abokinsa ne murna ta cika Dad suka taho abin mamaki Abba saiya miqa masa kudin yace yasai gda dasu Amma yaqi karba qarshe suka tsaya a tsakiya kan cewa saidai a sake zubasu a shago ya zamana shima da hannun jarinsa hakance ta faru iyayensu na juya kudinsu gidansu na zaune lfy Sahura irin matannan ne masu homa dajin su wasune sai fankama ta qaru sun samu ci gaba a aro domin ko a lkcn gdan Abba ba qarami bane sosai ta rinqa shigewa Ammi har suka zama qawaye inda aka samu akasi ita Sahura macece me yawo ita Kuma Ammi batada yawo hakance tasa Sahura tafita mutane gata tun a lkcn da bin malaman masifa itakuma Ammi komai akayi sai tace Allah zai iya mata.




Anan gdansu Rafi'ah aka haifi qanwar Ni'imah Yusrah sai sabon balli ya tashi musamman da Sarkin Wakil ya turo matarsa ta tsakiya wato Hajiya Fatsum barka habawa sai firita ita tazama babbar mace har matan sarakai ke zuwa Mata barka to dake hali yazo daya sai Sahura da Fatsum suka dinke duk da Fatsum ta girmi sahura don a lkcn ma yaronta autan ma yana Cairo yana karatu shikuma babban yana Uganda yana karatun Parmarcy matan Kuma biyu tayi musu aure Salma da Dija wanda sune manya.
Haduwarta da Hajiya Fatsum yasata qara kanainaye Dad duk abinda tace shi yakeyi gashi tun a wancan lkcn ba wata biyayya ta cikaba kwanciyar aure idan zaiyi da ita saiya biyata, Ni'imah kuwa da Rafi'ah Allah ya hada jininsu ko bacci baya rabasu dole duk inda sukayi bacci nan suke kwana tsakanin dakunan iyayen nasu sunada shekara biyar aka sasu makaranta tun a lkcn Rafi'ah tafi Ni'imah mayar da hankali a karatu ita wasane akanta sai fada da tsokanar masifa ga surutu ita Kuma Rafi'ah irin silent dinnan ce batada hayaniya duk da tsokanar Ni'imah batada qarfi idan tayo tsokana saita gudo gurin Rafi'ah to itamma ba qarfine da itaba Amma sai ta hana a daki Ni'imah tace a rama akanta.
Haka sukayita tafiya har secondary a jarabawa ne suka raba layi saboda Ni'imah bata samu abinda akesoba sai ta tafi Art ita Kuma Rafi'ah Science Ni'imah taso jan Rafi'ah ta koma art Amma taqi tace na marasa qoqarine a lkcn ne Kuma wata qauna ta qullu tsakanin Rafi'ah da dan wan babanta Yassar Amma fah soyayyar bada Rafi'an akeyi ba duk wani Abu saidai ya fadawa Ni'imah ita Kuma ta fada mata.



Daidai lkcn ne Dad yagama tamfatsa gdansa suka tashi suka koma ranar ansha daru dan Ni'imah qin tafiya tayi inda ita Kuma Hajiya Sahura ta nace saita tafi da yarta har wani cewa takeyi ga sabon gida mi zaayi da tsoho ta manta taohon yayi mata Rana na kusan shekara goma, dukkansu Saida sukayi rashin lfy aikuwa Basu rabuwa sai kwanciyar bacci musamman da Abba shima ya Gina wani gidan kusa da unguwar su Ni'imah duk da dadan nisa Amma yafi dayar unguwar kusa don Nan idan bakasa gandaba da qafama zakaje lkcn ne Abba ya qara aure aunty Murja itama me sanyin hali babu ruwanta, zamansu lfy Lau da Hajiya Amina wato ammi Kuma daidai lkcn ne akayi auren aunty Raziqa shima Yaya Rashid yayi aure gidan ya rage saura Rafi'ah kadai aikuwa itama guduwa tayi sai tayi sati bata gidan tana gdansu Ni'imah wannan aminta tana burge kowa don ko Yassar yasani idan zaisaiwa Rafi'ah Abu to dole saidai yasai biyu ita da Ni'imah inkuwa ba hakaba bama zata karba ba yasha tsokanar Rafi'ah yace “to waini ko ku biyu zan aurane?"




Dariya takanyi tace “nikam da nafi kowa murna gani ga Bestie na gidanmu daya mijinmu daya kaga shikenan aminta tayi Rana" duk lkcn da ta fadi haka sai Ni'imah ta harareta tace “Allah ya kiyaye nayi sharing miji ke nifa wlh Bestie yanda ban taso naga kishiya a gdanmu ba haka zan rayu babu kishiya don wlh yanda nakejin kishin mijina tun kafin nasanshi zan iya kasheshi ns kashe kaina akan batun qara aure" Rafi'ah takanyi murmushi tace “nikam banida matsala akan abinda ubangiji ya halalta Ni'imah kishi kafirci ne shiyasa nake roqon Allah kada ya jarabceni da zazzafan kishin da zai hanani yiwa mijina biyayya kishin da zaisani yin shirka kishin da zai hanani haduwa da Allah salin alin Ina roqon Allah indai yayoni a wannan sahun to ya qaddaramin mutuwa kafin nayi aure don bana fatan na zamewa mijina fitina masifa Kuma bala'in rayuwarsa"
Tsaki Ni'imah takanyi tace “ai saikiyi banza mara sanin ciwon Kai yo akanme zanyi addu'a Allah ya ragemin kishi bayan kishin adone ga ya mace nifa ko akan kishi da Yusrah ma bugawa zamuyi me qarfi ya kwaci kansa Kuma wlh don na kashe kishiya bazan taba nadama don nasan itama ba Sona takeyi ba da zata samu dama zata iya kasheni to da ka bari a kasheka gara Kai ka fara kashewa"





Yanayin Rafi'ah bata musu balle jayayya hakan yakansa da taja taga Ni'imah ta kafe akan ra'ayinta saita qyaleta abinda ta dauka wani abin halitta ce baka Isa canxa mutum ba haka watanni sukayita turawa tafi na tafiya har shekaru saura wata bakwai candynsu akasa auren Rafi'ah da Yassar murna gurinsu baa cewa komai Yassar kusan yanayinsu daya da Rafi'ah shima sanyine dashi yana nuna Mata madarar qauna me mantar da zuciya damuwa kullum suna tare babu abinda yake rabasu su uku sai bacci wani lkcn suna zaune sai kawai Ni'imah ta Kama kuka idan suka tambayeta sai tace tana tunanin ranar da Bestienta zata tafi ta barta ta kwana ta yini bata ganta ba, itama Rafi'ah saita Kama kuka abinka da quruciya tasha samun Yassar ita dashi ta roqeshi ya auresu su biyu yakanyi dariya yace.
“Bakida hankali yarinya ni ba mijin mace biyu bane Kuma ko zan qara aure Ni'imah batayimin ba banason farar mace sannan ta cika son jiki da rakin masifa ke nifah har tausayin mijinta nakeyi" akan haka Wai yana kushe Bestienta akwai lkcn da Saida sukayi sati uku basa mgn har saida manya suka shiga abin saboda ita Rafi'ah tata matsalar kafiyar masifa indai aka sake ta furta abu to komai wuyarsa sai tayi shiyasa iyayenta suke takatsantsan da furucinta dama Hausawa sunce muskilin mutum wuyar sha'ani gareshi shiyasa yawa yawan mutane suke cewa ta fiye jin izza kamar wata yar sarki wasu suce don tana dakyaune take wulaqanta mutane.





Wanda a zahirin rayuwa ma ta gaske tafi Ni'imah sanyi da sauqi hali kowa takaka da me kudi natane saidai in taku batazo daya ba Amma dake bata da magana sai aka fassarata baibai, lkcn da suka gama exams sukayi candy ansha shagali iyayensu suka shirya musu party sannan Yassar ya shirya musu wani lkcn bikinsu saura wata biyar.
Ita Rafi'ah ba ma'abociyar son zama babu bawa brain aiki bace hakanne yasata zaqula wata makarantar amare ana koyar da girke² da kwalliya da tarairayar miji, da murnarta tazo ta fadawa aminiyar tata aikuwa Ni'imah ta sheqe da dariya tace “cabb kina da aiki kice innayi auren ma wahala zanyi da har zantafi wani koyan kula da miji da girki wlh bazan iyaba kema ki zauna ki huta abinki girki ko kuku yayi ai tarairaya kuwa yanda ya koyan haka zanyi masa" Rafi'ah tosa jan hankalinta Amma taqi jikinta a sanyaye taje gida take fadawa Aunty Murja ta rinqa rarrashinta tace “ance sai hali yazo daya ake abota amma ku taku halin ya bambamta nisan yayi yawa kamar misalin sama da qasa Kuma kun kasa rabuwa bazaku rabuba abin daga Allah ne kawai ki bari zan fadawa Abbanki ya biya muku idan ya biya ai dole zataje"
Haka kuwa akayi Abba ya biya musu Amma fir Ni'imah taqi zuwa saima ta kwanta tace batada lfy itakuwa Rafi'ah ta rinqa zuwa makarantarta tana dauko darasinta, sosai take kwashewa abin gwanin ban sha'awa idan tazo gida tayita practice Ni'imah tana Mata dariya tana cewa “wallahi anma Raina muku hankali yo wannan abin zaa koya mini tab kina ruwa itadai bata kulata Saida tayi wata uku tana training din sannan aka yayesu aka basu certificate ita harda gift saboda tana cikin dalubai masu hazaqa na shekarar.
Shirye shiryen biki ya kankama sunata tsare²nsu ya rage saura sati shidda tafiya ta Kama Yassar zasuje daurin auren abokinsu Jos da zai tafi yazo sukayi sallama daqyar suka rabu hakanan duk jikinsu a sanyaye, dake yammace lkcn da suka tafi wajen bakwai na dare mahaifin Yassar ya Kira Abba a waya take Abba ya miqe yana salati inda kowa dake parlourn ya miqe suna tambayarsa “menene?"




Cikin kidimewa Abba yace “Yassar ne sukayi hatsari ya karye a wuya yanzu ma haka suna asibitin garin nan" ai Bai rufe bakiba Ni'imah da Rafi'ah suka saki wata qara itadai Rafi'ah zubewa tayi a gurin matsayin gawa aka kinkimeta suka fita asibitin da Yassar din yake sukaje aka kaita wani daki suka fice suka nufi Emergency cikin motar su hudune shi kadai Allah ya karbi rayuwarsa wayyoh zokuga kuka gurin Ni'imah na tausayin aminiyar tata da ta dauki so da qaunar duniya ta dorawa saurayin nata tana kuka tana cewa.
“Mutuwa! Wayyoh mutuwa meyesa kikayi mana haka meyesa kika daukewa Bestie na mijinta innanillahi wa innah ilaihirraji'un Allahummah ajirnih fih musibati wa'akalifni khairin minha" kuka take me tsayawa arai daidai lkcn Rafi'ah ta fito a guje ta nufo gurin ganin yanda kowa yake kuka yasata runtumawa dakin a guje ta nufi inda su Abba suke lkcn an janyo zani zaa rufe masa fuska ta fuzge zanin ta saki wata qara tare da fadawa jikinsa hawayenta yana malala tana jijjigashi tana cewa “Yassar ka tashi banason wasannan dama ka saba idan muna Hira ka kwanta kacemin ka mutu na fada maka banaso ni banaso wayyoh Yassar dina kada ka tafi kabarni wlh yau zan fada maka kalmar da ka dade kanacewa na fada maka naqi fadanta inasonka don Allah ka tashi....."
Likitan ne ya share hawaye yace “baby saidai hqr Allan daya baki ya karbi abins....." Daga gadon ta sulale bata sake sanin inda takeba sai bayan kwanaki uku ta farka taga Ni'imah a kusa da ita sai kuka takeyi ta tashi a firgice tace “mafarki nayi ko Ni'imah Yassar dina yananan ko?"




Kukan Ni'imah ne ya qara tsananta tace “ya zamuyi da wannan qaddarar haka Allah yaso Rafi'ah kinada tawakkali da dangana don Allah kada ki bani kunya ki dauki wannan qaddarar da hannu biyu Allah yafimu sanin abinda yake nufi daya dauke Yassar na tabbata zaiyi Miki zabi mafi kyawun kyau mafi alkhairin alkhairai" rungume juna sukayi sukaci kukansu me isarsu baki Rafi'ah ta kasa budewa saboda zuciyarta azalzalarta takeyi abubuwa da yawa suke tunkudowa daga zuciyarta sunnason bakinta ya furta idan ta furta Kuma zata iya ficewa ma daga muslumci a hankali ta fara furta astagfurullah! Astagfurullah!! Astagfurullah!!!"
Kawai sai tayi dif sai shassheqar kukanta da yake tashi Abba ne ya shigo ya matso da sauri yace “subhanallahi kukan kukeyi uwar manya to ya zaayi sai hqr Allah yana tare dake shikam Yassar ai yadace yasamu shaida Kuma yayi mutuwar shahada tasa tayi kyau saura mu Allah yasa muyi kyakkyawan qarshe irin nasa" janyota yayi yana share Mata hawayen yana bubbuga bayanta daqyar da taimakon Ni'imah suka samu tayi shiru Ni'imah ta hada Mata shayi tasha kadan tabata magungunan tasha Dad da Abba sukazo suka tafi dasu sunata yimata nasiha hakance ta dan sanya zuciyarta sanyi amma tuquqin mutuwar yana qasan ruhinta wannan dalilin yasa taci alwashin bazata qara son wani namiji ba a rayuwarta balle ya tafi ya barta.......




_Vote_
_Comments_
_Share_
_Please_





*_Ummuh Hairan_*
[1/4, 6:51 PM] Mrs AA Fansah: I think you'd like this story: "MY BESTIE'S HUSBAND" by realfauzahtasiu on Wattpad https://my.w.tt/Mbal0x4hMcb




*_My Bestie's Husband_*





*_Ummuh Hairan_*



*_Wattpad-realfauzahtasiu_*




*_15-16_*



_Ina qara jaddada muku kada wata ta bini pc tacemin please to beginning wlh bazan tura maki ba ki tambaya a duk groups din da kikaganshi My Bestie's Husband is Free book_



_____________________________
_____________________________



An dade sosai kafin Rafi'ah ta saki jikinta taci gaba da rayuwa kamar kowa kyawunta da nutsuwarta yasa take samun masoya ta ko Ina ita Kuma tayi kicin² ta sanya shuni da tabo ta liqe idonta taqi kallon kowa taqi sauraron kowa dake autace babu wanda ya matsa Mata duk da abin yana damun Abba sosai ga aminiyarta da samarinta tana sauraro Amma ita ko samarin Ni'imah bata kulawa duk wanda yazo saidai tace ta gaisheshi qarshe ta dage aka sama Mata admission a ATBU ta fara karatun medicine itakuwa Ni'imah daqyar saboda Rafi'ah ta yarda ta fara diploma a mass communication shima don ta rasa tsayayyen saurayine ne yawancinsu yan Shan minti ne sai suzo su lallabeta su matseta su tafi Saida sukayi kaca² da Rafi'ah akan hakan sannan ta hqr ta daina kulasu suka duqufa karatunsu.
Dayake taga bacin ran Bestie dinta abinda bata taba ganiba tsahon rayuwarsu yasa ta shiga taitayinta ta mayar da hankali a karatunta ashe dama tanada qwaqwalwar iskanci ke hanata karatun da gatan taga idan bata iyaba Rafi'ah zata koya mata yanzu Rafi'ah bata zama Kullum saitaje cikin garin Bauchi daga Azare ta dawo sai kadaici ya fara damunta ta zauna tayi zugum tana tunanin wataran fah rabuwa zasuyi kowacce ta tafi gidan mijjnta, haka sukaci shekara daya sukaci biyu Ni'imah ta gama diploma dinta tayi saa kuwa ta samu point me kyau.



A lkcn ne karatun Rafi'ah ya fara zafi hakance tasata yanke shawarar komawa cikin makaranta da zama saboda tana cinye lkcnta a go and come sannan ga surutun Ni'imah ya fara isarta Kullum mgnrta aure aure shiyasa tasa Abba ya Kama Mata hayar hostel ya zuba Mata komai da komai ta koma can da zama amma duk weekend tana dawowa gida idan har ba lkcn exams bane babban abinda yake damunta shine yawan mugun mafarkin da takeyi da Bestienta da wani mutum da bata ganin fuskarsa kullum mafarkin baya zuwa Mata da siffar alkhairi da farko takan dauka shirmene na mafarki amma da abin ya ta'azzara saitake fadawa Abba.
Shine yake cewa da ita mafarkin shirme baa riqeshi gabadaya dole ya kasance an manta wani bangare nasa ko an mantashi gabadaya yakance Mata ta dage da addu'a Allah ya rangwanta qaddararsu tabbas mafarkin da abinda yake nuna Mata zuwanshi dama akan samu haka indai mutum ya kasance me taqawa da miqa lamura ga Ubangiji to allah a yanayiwa wasu ludufi na nuna musu abubuwan da zasu faru gaba a mafarki domin su roqeshi sauqi da rangwame"
Wannan dalilin yasa ta qara matsa qaimi wajen roqon Allah sauqi rahma da taimako cikin kowacce qaddara me kyau ko akasinta, suna tsaka da kakar exams ne lkcn tana level 300 Ni'imah ta kirata da murna suka gaisa tace.




“Albishirinki Bestie" amsawa tayi da zaquwa tayi dariya sosai tace “nakusa zama amarya shekaran jiya Sarki Muhammad Wakil ya kawowa Dad ziyara shine yaganni bayan ya tafi ya Kira Dad yake cemasa, idan baiyimin mijiba yanaso ya bawa danshi Prince Ja'afar Wakil aurena wai shekarunsa sunyi nauyi 36 amma bayada niyyar fitar da Mata duk angama nuna nasa yammatan dangi yace basuyi masa ba ance ya kawo sama da shekara yaqi cewa komai har yayan abokai sarakai duk ya kaishi ya gani duk yace basuyi daidai da text dinsa ba"
Numfashi Rafi'ah ta sauke cikin murna tace “Alhmdllh ranar da muka dade muna jira tazo amma kedin kinyi masa?" Murmushi tayi tace “to ganinan dai yazo jiya dake yana gari yazo weekend Amma ko 5 minutes baiyi ba ya tafi Kuma bayan gaisuwa ko kalma daya Bata shiga tsakaninmu ba Saida zai tafi yabani hundred k wai nasa Kati ke kinganshi kuwa hadadden guy dan gayu ga DATA a hannunsa motar da yazo da itama jiya naga ansa tallanta a JAA LIFESTYLES 60 millions Kinga kuwa ai zan fantama ko?"




Rafi'ah bata fiye dariya ba saidai murmushi amma kalaman qawar tata Saida suka bata dariya tace “kullum burinki a kudi ya qare kamar wacce kika tashi da haushin talauci meyesa ne Ni'imah ki bari don Allah kudi basuda wani muhimmanci a aure soyayya tafi komai indai da rufin asirin ci dasha da sutura da gurin zama majority's na Mata tunanin kudi sune jin dadi shine ke wahalar damu bance kudi ba abinso bane aa nima inasonsu Amma banaso su zama abin duba a mizanin auratayya ki auri mutum domin Allah da Kuma cancanta Bestie Kuma kada ki auri namijin da baya sonki ki auri wanda yakesonki idan kinji kinason dole saikin aureshi to kiyi qoqarin koya masa sonki tanyar kwadaita masa kyawawan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login