Showing 60001 words to 63000 words out of 66967 words

Chapter 21 - MY BESTIE'S HUSBAND COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Oct 2024

8113

aka zuba aka rinqa bawa yaron Allah Sarki bawan Allah har wata ajiyar zuciya yakeja yanasha yana lumshe ido.



Tausayi ya cika Alh Hashim yanda yaga Rafi'ah ta zubawa jaririn ido duk da kukan da takeyi Saida alamun murmushi suka bayyana a fuskarta tausayinta ita da yaron yasa baisan sanda hawaye ya rinqa zarya a idonsa ba yaron Yana gama sha taja wata ajiyar zuciya ta janye daga riqon da yayi Mata ta matsa ta karbi danta ta rungume a gurin babu wanda Bai zubar Mata da hawaye ba soyayyar da da mahaifi wato ko mahaukaci yasan jininsa kama hannunta Alh Hashim yayi yakaita motarsa ya bude yasata a ciki.
Shiga yayi yaja suka tafi tunda suka taho ta sunkuyar da kanta take ajiyar zuciya shima baice mata komai ba yaci gaba da tuqinsa yana saqa abubuwa da yawa yanzu ahalinta sunanan sunata nemanta ruwa a jallo shikuma gashi Allah ya bashi numfashi ya sauke sukaci gaba da sharara tafiya itai bacci ne ya dauketa batasan sanda suka isoba saida taji ana bugun kujerar da take Kai tayi firgigit ta farka wani abin mamaki sai ta bude baki da ambaton "A'uzubillahi minasshaidanur rajim" mamaki ne ya cika Alh Hashim ya dubeta da sauri yace “ya sunanki?" Zuba masa ido tayi tare da kallon yaron tace “Mahir" sai Kuma ta fashe da kuka jikinsa yayi sanyi ya miqa hannu ya karbi yaron ya bude Mata qofa ta fito saime?
Basai qafa taqi takuwa ba tayi saurin riqe cikinta ta durqushe tace “way.... Wayyohhhh cikina zaz....zai bude ahhhhhhh....." Da sauri Alh Hashim ya iso gareta ya riqota ya sake sakata a mota suka Kuma ficewa daga gdan sai Gombe General Hospital shigar da ita akayi don har ta fice daga hayyacinta suka fara checking dinta da farko sun bata lkc Basu gano matsalarta ba sai suka bige a ciccire Mata qayoyi da kwalaben da ta tattaka a qafarta Saida suka gama wata cikin nurse din ta lura da rigarta data jiqe da wani ruwa me hade da jini jini ta daga rigar da sauri saiga bandege ya jike sharkaf da ruwan miki"


Nan fa suka fita suka sanar da Alh Hisham halin da ake ciki suka shigo tare suke fada masa sai an sake Mata gyaran aikin sabida alamu sun nuna ya balle Allah ne ma yayi da kwananta a gaba da tuni ta daina shaqar iskar duniya, nan take yasa hannu aka shiga da ita dakin Teather a lkcn dare yayi nisa waima don da sanayya ne dake ba boyayyen mutum bane shi a fadin Gombe a mota ya kwana da Mahir idan yaron ya farka sai ya lakata masa Zuma a bakinsa haka suka kwana shidai baiyi bacci ba ya lalace a kallon mahir yanajin dama ace dansane na cikinsa shi ko shegene goye abinsa zaiyi gefe daya Kuma yana tunanin yanda akayi mijin wannan baiwar Allah ya bari ta subuto daga hannunsa da danyen jegonnan tabbas ba banza ba bayan tiya akwai wata caca.
Tunanin abubuwa da yawa ya hanashi gane gari ya waye Saida aka qwanqwasa glass din motar ya dawo hayyacinsa ya dago ya bude Dr Zubair ne yace “ranka ya dade wannan baiwar Allah da alamun ta dan taba gushewar hankali alhmdllh ta dawo hayyacinta saidai fah kamar tayi loosing memory's dinta na baya Abu biyu naji tana furtawa Mahir Ja'afar and tana buqatar kulawa sosai don Allah kada a qara bare ta fita qafafunta akwai ciwo don ba daidai ta koma ba Amma na'urorinmu sunkasa gano Inda ta
samu matsala a brain dinta saidai abin bashida qarfi sosai idan ta samu kulawa ma zai gushe da Kuma addu'a"



_More comments_
_More Typing_



*_Ummuh Hairan_*



[1/31, 2:04 PM] Real Oum Hairan: *_Mbh_*



*_Ummuh Hairan_*



*_Wattpad-realfauzahtasiu_*



*_Telegram Link_*
👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7




*_49-50_*

_____________________________
_____________________________





Numfashi Alh Hisham ya sauke me qarfi ya dauki Mahir ya fito suka nufi masallaci ya sanya towel ya goye yaron ya dauro alwala yatada sallar asuba bayan ya idar ya saukeshi ya rungume a qirjinsa ya nufi dakin da Rafi'ah take hutawa ya bude ya shiga da sallama nurse din dake zaune kusa da ita ta amsa tare da gaisheshi ya amsa tare da miqa Mata yaron tasa hannu ta karba yace “bansan ya zanyi Masa wanka ba ki taimaka kiyi Masa wanka bari na dauko Masa kaya"
Karbarsa tayi ta nufi bathroom ta hada ruwan wankan tayiwa yaron suna fitowa shima yana shigowa da kayan ya miqa Mata tasa Masa kaya ta dago tace “amma Alh ya kamata abawa babie wani Abu yaci akwai alamun yunwa a yanayinsa Kuma kamar ma Bai cika lkcn haihuwarsa ba aka haifesa" Shiru yayi yana tunani can ya dago yace “ok bari asiyo mishi madara" ficewa yakumayi nurse din tanata kallon Mahir kyakkyawa dashi ji takeyi kamar ta saceshi haka dai tayita zaman kula dasu har Alh Hashim ya dawo ta hadawa Mahir madara tabashi yasha taci gaba da kulawa dasu.
Kwanan Rafi'ah biyar a asibitin tana samun sahihiyar kulawa inda Alh Hisham ya rasa ta inda zai bullowa Bari'ah matarsa da batun kawo Rafi'ah gdan da yaga yana neman haifarwa da kansa damuwa saiya share tunanin kawai yaci gaba da kulawa dasu domin ya daukarwa kansa alqawarin bazai taba bari Rafi'ah ta qara shiga wani gararin ba duk abinda Bari'ah zatayi saidai tayi.





Ranar da Rafi'ah ta kwana biyar ana gobe zaa sallameta da yamma ta farfado ta Jima tanajin kanta nayi Mata wani yammmm ta kasa bude idonta sai bakinta da take furta “la'ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalumin" sautinta baya fita sosai hakan yasa Alh Hisham bai lura da wuri ba Saida ta bude idonta taja ajiyar zuciya ta zuba Masa ido tana kallon yanda yaketa yiwa Mahir wasa, dagowa yayi da sauri ya sauke idanunsa akanta saiya miqe da sauri ya iso gareta yace “kin farka alhmdllh yanzu inane yake miki ciwo?" Zuba Masa ido tayi tanason tuno inda tasanshi Amma ta kasa zama yayi a gefenta yace “sannu ya jikinki Ina fatan dai Babu inda keyi Miki ciwo?"
Motsa bakinta tayi da niyyar yin magana Amma ta kasa maqogoranta ya kasa motsawa ya sake bude idonsa akanta tsoro da mamaki ya kamashi ya kwantar da Mahir agadonsa ya taimaka ya dagata ta jingina da bango yayi Mata murmushi yace “dama ba kowacce kalma kike iya furtawa ba kenan sannu Allah ya qara Miki lfy hakanma mun gode Masa" itadai idonta nakan Mahir dinta sai yaga tayi murmushi ta daga hannunta alamun a bata yaron, a hankali yaji tace “Ja'afar" sai ya juya da sauri ganin shi take kallo ya ankarar dashi shine take nufi Kuma ta Kira da Ja'afar numfashi ya sauke ya miqa Mata Mahir ta karbeshi tayi kissing dinsa ta fara kiciniyar fito da nononta tasawa yaron sai ya fice da sauri daga dakin
Bin bayansa tayi da kallo tanason tuna wani Abu Amma Babu hali da gaske ta rabu da ciwon hauka da qarfin addu'ar da iyayenta da mijinta da Hajiya Innah da kuma wacce Alh Hashim yasa akeyi Mata Amma fah ta kasa tuna komai Kuma bakinta ya kasa furta komai sai Mahir da Ja'afar sai addu'a da koyaushe take furta duk wacce takeson furtawa tana bawa babienta nono tana wasa da gashin kansa kyakkyawan yaron nata Kama yakeyi Mata da wani data sani Amma ta rasa tuna wanene Saida ya qoshi ta zare nononta taci gaba da kallonsa daidai lkcn da Nuraiba Nurse ta shigo tace “Masha Allah madam kin farka cikin hayyaci yanzu Alh yace kiyi wanka kafin su dawo bari nakai Masa Babien kafin mu gama"




Batace komai ba ta miqa Mata Mahir ta fita bata Jima ba ta dawo ta Dagota suka shiga bathroom ta rinqa nuna Mata yanda zata gasa jikinta tare da tayata sun Bata kusan awa guda sannan suka fito ta miqa Mata Mai ta shafa ta bude wani akwati da Alh Hisham ya hadawa Rafi'ah ta dauko Mata doguwar riga mara nauyi ta bulawus ta Bata tasa yanda bazata rinqa Sosa Mata aikin cikinta ba sannan ta hada Mata shayi ta rinqa Bata suna kallon juna Nusaiba tayi murmushi tace “meye sunanki?" Itama murmushin tayi tace “Rafi'ah” numfashi Nusaiba ta sauke tace “kinyi saar miji yanasonki tunda aka kawoki ya daina zuwa kasuwa balle aikin yananan tare muke jinyarki har kudi ya yankemin na kula dake da babienku nayi Miki murna wlh samun miji irin mijinki sai an tona Allah ya qara muku qaunar juna"Kallonta takeyi da rashin fahimta itama kallonta takeyi a hankali cikin sanyin muryarta tace “Ja'afar?" Girgiza Kai Nusaiba tayi tace “aa Hisham dai" sake itama girgiza nata kan tayi tace “Ja'afar" to ganin bazata fahimta ba yasa Nusaiba binta da eh Ja'afar.




Shikam Alh Hashim gidansa ya nufa cike da fargaba yayi parking ya fito ya nufi cikin gidan rungume da Mahir a qirjinsa hadiman gdan sai kallonsa sukeyi da tsananin mamakin inda ubangidan nasu ya samo danyen jariri kafin ya Isa ciki har saqo ya ishe Hajiya Bari'ah cewar ga mijinta Nan dauke da abin al-ajabi hakan yasata saukowa daga saman ta zauna a qasa ya bude qofar ya shigo ya mayar ya rufe ya juyo sukayi ido hudu ta miqe da sauri qirjinta nabada wani daram.
Ya lura da yanayin data shiga shikuma sai yayi Mata murmushi ya zauna a kusa da ita ya bude fuskar Mahir ya dago ya dubeta yace “uwargida bani ruwa do Allah" jikinta a sanyaye ta nufi freezer ta bude ta sauko ruwa me Sanyi ya taba yace “yayi sanyi mara sanyi nakeso Mahir zanyiwa addu'a" batayi gardama ba ta sake daukowa da qaramin cup na glass ta rusuna ta bashi yaja ajiyar zuciya yayiwa yaron addu'a ya dago kansa ya guntsi ruwan a bakinsa ya hada Dana yaron ya rinqa basa a hankali Bai cire bakinsa ana yaron ba saida yaga ya shanye yayi hamdala yace “kinga wani kyakkyawan babe Bari'ah Yana burgeni sosai" numfashi tayi ta zauna qirjinta na dokawa tace “ina ka sameshi?" Murmushi yayi yace “ina ranar da naje Dambam karbo Miki magani to ranar Allah ya hadani da uwar yaron nan cikin wani mawuyacin hali abin tausayi da alamun sihiri akayi Mata aka kadota daga gdan mijin kinsanni da tausayi saina daukota muka taho nan har Nan gidan mun shigo fah nace ta fito kawai sai ta riqe ciki Ashe aiki akayi Mata aka cire wannan babien a cikinta Kuma aka samu azzaluman da suka haukatata hauka fah tuburan, so shine na dauketa muka tafi Gombe General Hospital anan aka rinqa kula da ita nikuma nasa malamai suka rinqa yimata addu'a har Ubangiji ya kawo sauqi yau yanzu haka ta farfado cikin hayyaci saidai fah ta manta kowa da komai sai danta kadai Babu abinda zata iya fada daya faru a baya"





Zuba Masa ido tayi ta kalleshi ta kalli yaron zuciyarta bata yarda da abinda ya fada Amma batason sanya Masa tuhuma da kanta zata tabbatar da abinda qawarta Rahila ta sanar da ita tagani a asibiti shirun nata ne yabashi damar cewa ki tsayar da zuciyarki Bari'ah bazan cutar dake ba kuma bantaba munafurtarki ba Am Baiwar Allan nan zatazo gidannan ta zauna kafin binciken da nasa akeyimin ya bincikomin inda danginta suke na sadasu da ita so ki nutsu don Allah ki taimaka Mata wajen kula da yaron nan ta dalilin taimakonta sai muma kiga Allah ya bamu namu"
Jinjina Kai tayi tana qara kallon Mahir zuciyarta na Bata cewa Raina Mata hankali Hashim yakeyi fah yaje yayiwa yar mutanen ciki ta haihu iyayenta sun koreta ya dauko zai kawo Mata gidanta ko Kuma auranta yayi a boye yayi Mata ciki shine yanzu yakeson hadasu saboda idanunta daya rufe har Kama taga Mahir da Hisham sunayiMiqewa tayi ta shigewarta dakinta ya bita da sauri yana kiranta don dama ya hasaso faruwan hakan Kiran duniya ta bude taqi budewa bayason Bata Mata saboda itadin amanarsa ce Amma akan wannan jahadin saidai tayi duk abinda zatayi Allah shine zai fitar dashi.




Ya Jima cikin tunanin abinda ya dace kafin ya juya ya sake ficewa ya koma asibitin lkcn Rafi'ah ta samu bacci ya zubanta ido yana kallonta a ransa yanajin ninkin tausayin ta damuwar loosing memories ai ba qaramin abu bane dole tana buqatar kulawa ta musamman sake fita yayi ya samu likitan ya nema Mata sallama suka sallamesu tare da dorata akan magunguna sannan ya koma da Nusaiba aka had a kayan suka tafi yanata zuba mata sannu suka shiga gidan tanata bin gdan da kallo tana son tuna tasan wani Abu kwatankwacinsa Amma ta kasa Kama hannunta yayi har cikin gdan bangaren da yass aka gyara Nan ya kaita ya kwantar da Mahir yace “ki huta sosai sosai zuwa anjima sai nazo nabaki magungunanki" zama tayi ya juya ya fice ita Kuma ta kwanta bacci ya sake dauketa har yanzu akwai baccin gajiya akanta.
Ranar kwana sukayi shida Bari'ah suna rigima kuka takeyi sosai wai yaci amanarta Babu wani taimako matarsa ce Rafi'ah saboda yaga Bata haihu ba shine yayi Mata wannan sakayyar yaso fahimtar da ita Amma taqi ganewa shikam da yaji haushi ya dawo parlour yayi kwanciyarrsa cikin dare yaji Mahir na kuka yaso ya qyaleshi amma yaji bazai iyaba saboda qaunar yaron yakeyi da gaske ya miqe ya bude qofar bangaren a parlour ya tarar da Rafi'ah tasa yaron a gaba itama sai kuka takeyi.




Mamaki ya kamashi yayi dariya shi baitaba ganin wannan rigima ba ki haifi da a cikinki Yana kuka maimakon ki rarrasheshi Wai sai kema kisashi a gaba ki Kama kuka karbarsa yayi ya zauna yana hura Masa kunne har yayi shiru ya koma bacci ita Kuma Bari'ah ta fitto ta nemansa bata gansa ba zuciya tabata yana dayan bangaren ta nufa a fusace ta bude ta shiga sai tayi turus ganinsa kwance a parlourn farko Mahir na qirjinsa suna baccinsu cikin kwanciyar hankali qwafa tayi ta juya ta fice ta kwana zaune tana kuka Wai ya tsallaketa ya tafi gurin shegen dansa.
Da asuba ya farka ya miqe ya kwankwasa dakin Rafi'ah da take zaune tana lazumi ta miqe ta bude ta karbi yaron tare da jinjinawa alamun godiya yayi Mata murmushi ya fice, yana fita masallaci ya nufa lkcn daya dawo ya tarar da Bari'ah ta hade kayanta a akwatu tanata kukan Wai anaci Mata mutunci duk yanda yake tunanin shawo kanta ta dadi ya kasa qarshe yace idan ta fita bai yafeba dole tayi hqr bata fitan ba Amma ko abinci ta rantse bazata rinqa bawa Rafi'ah ba bai wani damu ba hakanan ya amince kullum da kansa yake shigar kitchen yakewa Rafi'ah girki tea ne zai dafa Mata ya soya Mata qwai da duk wani Abu da yasan zata buqata har tayi sati uku a gidan lkcn tayi qwari sosai ta murje Amma Babu baki sai ido yanajin dadin yanda yaga ta saki jikinta dashi abu daya dake neman wargatsa lissafinsa shine yanda take mu'amalantarsa yayi Kama da tanayi masa kallon mijinta sannan taqi karbar sunansa Hisham kullum Ja'afar take kiransa




Yayi iyakar yinsa yaga ta gane ta kasa ganewa inda Bari'ah take qara samun hujja da yanda Rafi'ah take mu'amalantar mijin nata da Kuma irin son da yake nunawa Mahir kullum sai yayiwa Mahir shopping idan ya fita takanas Bari'ah da taga bashida niyyar saukowa ya sake Mata bayani tayi tattaki har gidan surukarta tana kuka ta fada Mata cewa Hisham ya kawo Mata mace gda ya ajiye Kuma harda ɗa a wata majiyar ma ance dansa ne yayi Mata ciki ta Haifa Masa shine iyayenta suka koreta shikuma ya aureta,
Sosai hankalin tsohuwar ya tashi duk da ta yarda da ingancin danta Amma mgnr Bari'ah abar dubawa ce dubanta tayi tace “kije zanzo anjima idan ya dawo" haka kuwa akayi da magariba ya dawo daga aiki yayi wanka ya zura doguwar rigarsa ya nufi bangaren da Rafi'ah take domin dauko dansa Mahir da ya qara kuɓulɓul dashi a parlour ya isheta tana sallah shikuma Mahir na kwance a kusa da ita yanata kallon sama yasa hannu ya daukesa ya zauna a kujera yana cillashi sama yaji an bude qofar an shigo ya dago da sauri sai yaga Hajiya Rakiya mahaifiyarsa ya shafa kansa tare da cewa “Ahhh Hajiya kece da daren nan?" Zubawa Rafi'ah ido tayi tana tunanin inda taso sanin fuskar yarinyar tana cewa “ashe haka ka zama Hashim dan shege a zuri'ar mu...." A gigice Rafi'ah ta dago ta dubi Hajiya Rakiya sai hawaye sharr a idanunta shima Hashim saurin kallon mahaifiyarsa yayi yace.
“Hajiya nasan cewa baki yanke hukunci da ka a mafi yawan lokuta ma baki amsar hujja saman yaqini wlh tallahi banida wata alaqa ta kusa da wannan baiwar Allan bayan taimako, Nan ya kwashe komai ya fada Mata tayi shiru tana nazarin kalamansa ita kanta Bari'ah sai jikinta yayi sanyi ya share qwallar idonsa yace “ke daga ganin nutsuwa da kamalar wannan baiwar Allan bata cancanci wofintarwa ba duk inda ahlinta suke sunanan suna haqilon nemanta jiya nabada hotonta a kafafen yada labarai da jaridu domin a cikitomin ahlinta ko Ubangiji zaisa a dace"





_Comment_
_Share_
_Vote_





*_Ummuh Hairan_*
[2/1, 7:44 PM] Real Oum Hairan: *_Mbh_*



*_Ummuh Hairan_*



*_Wattpad-realfauzahtasiu_*



*_Telegram Link_*
👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7




*_51-52_*

_____________________________
_____________________________




Jinjina Kai Hajiya Rakiya tayi ta dubi Rafi'ah ta miqe ta Isa gabanta lkcn ta idar da sallah ta zauna kusa da ita ta Kama hannunta kuka takeyi sosai, cikin yanayi na tausayi Hajiya Rakiya tace “kiyi hqr kinji yata Allah yasan komai Kuma shine yakeda maganin komai" kwantar da kanta tayi a kafadarta ta sake rushewa da kuka cikin yanayin da batasan ya akayi ya wanzu ba ta bude bakinta da cikin watanni hudun baya iya furta komai tace.
“Wlh banida wata alaqa da Hisham a baya ne ma yakemin Kama da uban Dana Ja'afar amma yanzun ya daina...." Miqewa Hisham da bari'ah sukayi tare suka Isa gabanta yakai hannu zai tabata sai ya tuna da mgnrta uban danta Ja'afar tuni ya dawo nutsuwarsa yaja fasali yace “dama bakinki Yana mgn kikaqi yimin mgn tsayin wata hudu?" Cikin kuka tace “aa yaune naji Ina iya furta wasu kalmomin sannan inajin kamar inason tuno wani abu game Dani Amma na kasa don Allah wacece ni ya akayi nazo nan Kuma inane nan?"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login