Showing 48001 words to 51000 words out of 66967 words
minasshaidanur'rajim" jikinsa yana rawa duk gashin jikinsa sun miqe riqo hannunsa tayi tace “fatan lfy mijina" wani gwauron numfashi yaja ya zuba Mata idonsa da sukayi ja saboda bacci.
Baice komai ba ya miqe ya fada bathroom yayo wanka ya fito ya zura kayansa ya zauna kusa da ita yace “kinci abinci?" Dagansa Kai tayi ya Jinjina ya miqe yace “zan Dan fita ki kula da kanki kafin na dawo" itadai batace masa qala ba har ya fice ta sake kwanciya kanta ciwo yake ita dsma a laulayin ciwon Kai da amai sune sukafi komi damunta, baccinta tayi sosai sai yamma liqis ta tashi tayi wanka ta shirya cikin wasu fitinánnun qananun kaya tayi kyau sosai duk da ramar da tayi ta dawo parlour ta hada madara da Zuma tanasha tana kallo.
Wayarta tayi ring ta daga suka gaisa Hajiya Innah ce take tambayarta jiki ta amsa Mata suka dan taba hira sukayi sallama, tananan zaune zaman jiran tsammani Bai shigo ba har saida tayi sallar Isha ta sake kwanciya waje 12:30am ya shigo ganin tana bacci yasashi bai tasheta ba tausayi sosai take bashi abinci kawai yaci ya kwanta shima ya janyota ta bude idonta yace “sorry uwar yayana na dade ko?"
Lbr ya fara bata yace “yau na gama komai daya kawoni qasarnan harma naje nayi mana duk abinda ya dace May be Nan da 1 week mu tashi zuwa gida am jiya Mai martaba ya kirani yake fadamin idan mun dawo Kai tsaye na kawoki nan gdan sarauta Zaki zauna a bangaren Hajiya Innah harsai kin haihu so nadai nemi alfarmar yabarki ki zauna a bangarena Amma bazan iya barikin ki zauna a bangaren matan gida ba"
Hakanan tunda ya fara bata lbrn taji gabanta na faduwa taso tayi masa garda sai taga rashin dacewar hakan kawai tayi shiru Amma ranta bai kwanta da komawarta gidan sarautar ba" kwanaki uku ya gamayi musu shirye shirye ta lura da gaske zumudin tafiyar yakeyi itadai batako kulashi tunda babu wani Abu daya fasayi Mata kulawar da yake bata Bai fasa ba sai kawai mayar da hankalinta akan kula da lfyrta.
Ranar da satin kuwa ya zagayo ranar tafiyarsu ta tashi da azababben zazzabi sosai da ciwon Kai ganin yanda yaketa rawar jiki yasa ta boye Masa ciwon nata ta shirya suka fito drivern hotel sinne yakaisu airport suka dago sai Abuja shigar talatainin dare sukayi saboda haka a hotel suka kwana da safe bayan sun karya suka fito shatar mota suka dauka har Bauchi.
Daya a Azare tayi musu shine ya dauki kayansu ya shiga dasu cikin bangarenta da yake ya fadawa Hajiya Innah dawowar tasu tasa an gyara musu bangarensu na gidan sarautar to Nan dinma an dan gyarashi saboda tasan qila shigowar dare zasuyi da addu'a ta sauko a motar saboda tsanantar faduwar gabanta tafi fitowa taji wani jiri ya debeta daidai qofar shiga parlournta ta saki qara ji kake yif ta zube a qasa sumammiya jiyo ihunta yasashi sakin jakar daya shiga da ita a guje yayi waje a kwance ya isheta cikin wani mawuyacin hali jini sai kwarara yakeyi ta qasanta,
Isa yayi da gudu ya dagota yana jijjigata yana Kiran sunanta daidai lkcn Ni'imah ta leqo daga sama ta hangesu gabanta ne ya fadi ta sauko da sauri ta iso ganin yanda ya gigice yasata zagayowa ganin jinin da yake zuba a qasan Rafi'ah yasata sakin ihun kirsa tace “meye hakan Ja'afar ka kaita asibiti Mana jini fah take zubarwa"
Sai lkcn ya iya miqewa ya sureta yasata a mota yana tuqin gabansa na faduwa ganin yanda jinin ke malala har lkcn suna shiga ya dauketa suka shiga ciki likitoci suka rufu akanta suna iyakar qoqarinsu sun jima basuga tashin hankali irin wannan ba jinin yaqi tsayawa da sun tsaidashi sai wani ya tsinke gashi cikin yaqi fita sunyi sunyi su cireshi ma ko zasu samu jinin ya tsaya yaqi abun fah ya zama tashin hankali daga kawotan sunsa Mata jini leda uku, Basu suka samu jinin ya tsaya ba sai wajen shidda na yamma Allah ya taimakesu ya tsaya scaining sukayi Mata abin mamaki cikin yananan qalau dashi Ja'afar ya sauke ajiyar zuciya gabadaya yayi faca² da jini yayiwa Allah gdy da babu abinda ya samu cikinsa yasan wannan kariyar ubangiji ce kawai.
Hajiya Innah ya Kira ya fada mata halin da suke ciki itace tazo asibitin sannan ya samu ya tafi gda yana zuwa ya tarar da Hajiya Fatsum da Ni'imah a parlour sai dariya sukeyi yana shigowa kowacce ta shiga hankalinta Hajiya Fatsum ce tayi saurin cewa “ya me jikin yanzu nazo nake jiran Ni'imah tazo mine mu gano jikin" dadi yaji a ransa yadanyi ajiyar zuciya yace “alhmdllh Allah ya taqaita cikin Bai fita ba Anna tasha wahala Saida akasa Mata jini leda biyar iya yau...."
Miqewa tayi daga zaman da take tace “bai fitaba fah kace ya akayi ya tsaya naji ance faduwa tayi ruf da ciki Kuma ance jinine ya balle Mata" Jinjina kai yayi yace “eh haka Allah yaso" saurin saita nutsuwarta tayi tayi murmushin yaqe tace “to ai gara haka" hayewa yayi sama ya tarar dashi yanda ya tafi ya barshi takaici ya cikashi ya sauko ya fice ya nufi bangaren Rafi'ah anan yayi wanka ya canza kaya ya fito ya sake komawa yanzu ita kadaice ta rafsa uban tagumi ya jima akanta sannan taji shigowarsa tayi firgigit ta dawo hayyacinta tare da miqewa tace “ya me jikin?"
Zama yayi yace “da sauqi inajin yunwa" murna ce ta kamata ta miqe ta shiga kitchen ta hado masa abincin da suka cakuda da magunguna ta kawo masa ya sauko qasa ya bude qamshin abincin baiyi masa ba Amma yunwa yakeji ta gaske haka ya rinqa tsakura yanaci kamar dole daqyar ya iya cokali shidda ya ajiye ya tsiyayi lemon juice yasha badon ya qoshi ba saidon bazai iyacin na arziqi ba qarni yaji abincin yanayi da alamun naman da akasa Bai samu gyara ba.
Dan kishingida yayi yana latsa wayarsa nan danan bacci ya daukeshi hakan yabata damar miqewa ta kunna garwashi tayi turaren da aka bata sannan ta sake zuba wani da akace tayi masa akansa idan ya shaqa nagana ta qare haka kuwa akayi cikin saa ta gama komai ta feshe parlourn d room freshner ta koma ya harde, ya jima yana baccin asara har akayi Isha sannan ya farka da salati yaji kansa ya Sara masa kamar irin sarawar da yayi masa ranar da yaji yanason dawowa 9ja.
Bude idonsa yayi ya zubawa Ni'imah data hade cikin wani less me tsadar gaske ba wata kwalliya tayi ba Amma sai ya rinqa ganin tana wani glowing miqewa yayi yanaci gaba da kallonta yana sauke ajiyar zuciya sama ya haura sabanin dazu yanzun ta gyarashi yayi murmushi yana Shirin shiga bathroom ta bude qofar da sauri saboda tuna cewa bokan shandan yace idan ta kuskura yayi sallah bayan yaci abincin kafin ya kwanta da ita to komai zai lalace ya juye kanta,
Zubanta ido yayi babu kunya ta matsa jikinsa tana matso hawayen kissa tace “ka dawo inason ganinka da jin duminka matarka ta Kama rashin lfy kun Kuma fita yanzun Kuma shine zaka shareni Ja'afar kana azabtar dani don kaga inasonka don Allah kada kasa zuciyata ta kamu da ciwon da zai iya zama ajalin me ita duk saboda so kake wulaqantani bakajin tausayina...."
Yanda take shigewa jikinsa da qamshin turaren tsafinta yasashi jin wani yanayin sha'awa me qarfi da baitaba jiba game da ita ya sanya hannu ya rungume shafaffun mazaunanta yana shafasu yana sauke ajiyar zuciya a hankali yau dake makirci ta shirya itace harda balle masa bottle din riga abinda akansa Saida afasa kwanciyar da ita a baya idan yace ta cire masa kaya gani takeyi ta fado yau sai gashi tanayi baisata.
Hakan ya tabbatar masa da ta fara nutsuwa ya jata suka zube a gadon sosai ko a wajen playing yasan zaren ba kalar yadin bane Rafi'ah dabance ko a rashin sani ta tabashi sai yaji saqon yakai masa har inda yakeso yaje Amma ita ta wani kwanta tayi masa seqeqe sai breast dinta kawai da take tattaro Masa dake irin manyan boobs dinnan gareta hakan yasa bata haihuba amma sun zube sabanin na Rafi'ah da kullum kamar qara tsaidasu akeyi.
Lkcn daya shigeta ne abubuwa suka rinqa canzawa shi ba dadi take wani samu na musamman ba saboda itan ko maganin Mata bata iya kadawa Tasha ba sai aukin turaren asiri Amma sai yaji yanajin wani shauqi hakadai sukayi suka gama tun kafin su gama ta fara tureshi sabanin Rafi'ah da take qara riqeshi tana dago jikinta sosai yanda zai samu nutsuwa,
Ranar tare sukayi wanka yanata rawar jiki akanta ta cika da mamakin aikin boka Koda yayi sallah cewa yayi ta shirya suje su dubo Rafi'ah batayi musu ba saboda tanason ganin qwal uwar daka fita sukayi anata yauqi da yatsina ita me miji aka shiga mota suka nufi asibitin yana riqe da hannunta suka tura qofar dakin suka shiga,
Lkcn Rafi'ah ta tashi Hajiya Innah ta hada Mata shayi tana Bata suka shigo ta dago kanta idanunta ya fada kansu babu kunyar Hajiya Innah Ni'imah qara shigesa takeyi wai ita me miji shikuma sai wani binta yake murmushi Rafi'ah tayi cikin sanyin muryarta tace “sannunku da zuwa Best Ashe tafiya kayi dazun dana farka nake tambayar Innah kana Ina...." Kafin ta rufe baki ya taso da bala'i “to zama kikeso nayi nayi gadinki saboda ga asararre mara aikinyi hakanma banyi Miki ba dana Nemo Innah ta zauna a gurinki ke wacce irin mara tunani ce daga dawowarmu kin fara cuta saboda kinibibi kada na samu lkcn iyali na ke nifa baayimin iskanci kinsan cin mutuncinki ba wahala zaimin ba ba ciki ba ko bayane dake shashasha kawai....."
_More Comments_
_More Typing_
*_Ummuh Hairan_*
*_39-40_*
_____________________________
_____________________________
Juyawa yayi fuuuu ya fice a fusace sai huci yakeyi inda suka kalli juna da Ni'imah Ni'imah tayi Mata murmushin mugunta tabi bayansa da sauri a jikin mota ta tarar dashi yanata huci ya bude Mata ta shiga shima ya shiga yaja suka fice daga asibitin sukabae Rafi'ah da sanyin jiki da faduwar gaba, sunan Allah ta rinqa ambato a hankali taji Hajiya Innah ta dafata tace.
“Ina mamakin zafin zuciyar Baban Innah shi komai nashi na fada ne ko meye abin bacin rai cikin kalaman ki sai naga kulawa ce da nuna damuwa da abokin rayuwa tasa kika damu da rashin nasa a kusa Koda yake wani abun sai anayiwa rayuwa uzuri kiyi hqr iya wuya kedin dai kece"
Sosai ta rinqa rarrashinta murmushi tayi tace “karki damu Hajiya nasan halinsa yanzu haka wani abun ne ya bata masa rai nasan fushinsa baya jimawa zuwa anjima zai sauko" ajiyar zuciya Hajiya Innah tayi sukaci gaba da tattaunawa saida tasan yanda tayi taga Rafi'ah batabar damuwar abin a ranta ba ranar a asibitin suka kwana saboda jinin da akasa Mata da magrib bai qare ba sai cikin dare.
Washegari har Tara baizoba aka sallamesu Hajiya Innah ta dauki waya ta kirasa ya daga suka gaisa ya tambayeta me jiki tace “da sauqi dama sàllamarmu akayi shine mukace ko zakazo ka daukemu" Shiru yayi na dan lkc sannan ya dago yace “aa Hajiya kawai bari na turo driver yazo ya daukeku ku wucce can fada kawai ni na danje unguwa ne idan na dawo zanzo" bataja mgnr ba ta kashe wayar ta miqe ta fara hada kayan lkcn da drivern yazo ta gama hadawa suka fita suka tafi suna Isa yana shigowa gidan ya tsaya jikin motarsa suka fito duk munafukai suna jira suka abinda zai faru qarasowa yayi ya rusuna suka gaisa da Hajiya Innah ya dago ya zuba idonsa akanta tayi wani haske ta qara ramewa yaja numfashi ya dubeta yace “ya jikin naki?"
Sunkuyar da Kai tayi tace “da sauqi" fasali ya sake ja yace ”nasa an qara gyara can bangaren muje na rakaki" kallon Hajiya Innah tayi idonta ya ciko da ruwa tayi saurin girgiza Mata Kai dole tasa ta hadiye kukan, taimako daya da Allah yayi mata tsakaninsu da Hajiya Innah babu nisa hakan tasa suka taka da qafa ya bude qofar shiga part din ya shiga itama ta shiga da Bismillah tana qarewa bangaren kallo tun daga waje zakasan ya kashe mazan kudi wajen gyarashi.
Yana tafe tana biye dashi a baya har suka shiga ya bude qofar parlourn ya shiga itama ta shiga ya mayar da qofar ya rufe ya juyo ya zubanta ido itanma shi take kallo fuskarsa a daure take sosai hakan ya tabbatar mata da babu wargi, rabashi tayi zata wucce ya riqo hannunta ta tsaya cik matsowa yayi ya riqo qugunta yana jan numfashi ya matsota sosai yace “meye yake damunki ne?" Dagowa tayi da mamaki so take tayi mgn Saidai yanda ya kafeta da ido yasa ta kasa furta komai sakinta yayi ya sanya hannu a aljihunsa ya zaro kudi masu kauri ya miqa mata yace “ki riqe saboda tsaro ki kula da kanki"
Juyawa yayi ya fice tabisa da kallo yaja Mata qofar ya rufe itakuma ta taka taje ta murda Mata key ta nufi step din shiga dakin ba bene bane Amma an daga dakunan sun danyi sama sabanin babban parlourn da take a qasa nan din ma akwai parlour Amma baida girma sosai kujera daya ce doguwa sai wani qaton kilishi 24 pillow sai TV da dispenser sai manyan flowers da aka qara qawata parlourn dashi gefe Kuma akwai qaramin dinning table me kujera biyu.
Tsarin wannan parlour yayiwa Rafi'ah tayi ajiyar zuciya ta bude daki daki daya ta shiga shima an gyarashi sosai gadone na alfarma aka saka komai yaji taja fasali ta zube kudin daya Bata ta fara rage kayanta ta fada wanka ta jima tana wankan tanajin dadin ruwan kafin ta fito ta shafa mai ta bude wardrobe din kayanta ne jere reras ta dauko wasu masu sauqin nauyi tasa ta kwanta tana hutawa ta Jima a kwance tana tunanin abubuwa da yawa sannan taji ana taba qofar ta miqe a gajiye ta fito parlourn tana tambayar waye.
Amsa Mata akayi da cewa “nice Rafi'ah Ashe kun dawo to sannu kinji" jin an ambaci sunanta yasata budewa batasanta a zahiri ba domin bata taba ganinta ba ko lkcn da aka kaita bangaren fuskarta a rufe take, Hajiya Kaltume ce ta kawar da shirun da shiga parlourn tace “tubarkallah Masha Allah guri yayi kyau to ai haka yafi Amma da duk ya debeku ya tareku guri guda don shirme musamman ma ke da kike buqatar kulawa yanzu sannu kinji"
Sunkuyar dakai tayi ta durqushe da niyyar gaisheta tayi saurin Dagota da cewa “subhanallah kula kada kiyi barna haba yarnan keda ba lfy ta isheki ba ai bakya tsugunna ba zauna abinki ni uwarki ce banason ki takurawa kanki da jikana" tana mgnr tana zaunar da ita a kujera tace “to ya jikin jiya munji mugun labari Koda yake Allah ya taqaita wahala
A kunyace ta amsa Hajiya Kursum ta rinqa janta da Hira harda guzurin agwalumarta ta kawo Mata ta miqa Mata tace “kinsan abinki da me wannan Abu da son tsami tsami shiyasa na bayar aka siyo miki" kamar tayiwa Rafi'ah kyautar aljanna haka taji sukayita yar hirarsu tanata nuna kulawarta tare da bata shawarwari kamar gaske, shigowar Hajiya Innah ne yasata miqewa suka kalli juna Hajiya Kaltume ta harari Hajiya Innah tace “to Rafi'ah ki kula da kanki kinsan gdan namu gidan yawa bakasan cikin wani biyune ba saiya lashe maka kurwa" itadai bata tanka ba Hajiya Innah ta zauna tace “Allah ya kyauta" Shiru ce ta dan ratsa kafin Hajiya Innah ta bude kular da tazo da ita tace “dambu nayi Miki da fatan yakuwa ko Zaki iyaci naga duk kin fige wannan jika yana wahalarmin dake"
Kunyace ta kamata tayi murmushi tace “bantaba ganin yar da take kunyar uwata ba saike tashi kici abinci" xuba Mata tayi ta zage taci dambun sosai don ta dade tanason sa tunda ta samu ciki dashi da tuwo bata taba daina kwadayinsu ba sosai taci sauran ta ajiye tace taci da dare a kalamai baa bayyane ba Hajiya Innah take nunawa Rafi'ah tayi hankali da mutanen gdan fada gidan makirci ne kowa da abinda yake zuciyarsa, sosai ta shiga taitayinta ta qara Mata da cewa idan kadaici ya dameta tana gama abinda take ta taho bangarenta, Jinjina Kai tayi ta qara da cewa mutane da yawa sunayi maka dariya Amma basa qaunarka munafikinka yafi maqiyinka illa domin maqiyi baya zama kusa dakai balle ya samu damar cutar dakai Koda kuwa zai cuta maka saidai yabi ta gurin munafikinka da hausawa kance gadon bacciñka so kibi a sannu dariya ba so bace wata dariyar tafi sukar wuqa ciwo"
Maganganun sun shigeta ta nutsu kuwa tana nazarinsu lkcn da sukayi sallama tace “ki kulle bangarenki kiyi kwanciyarki ki huta surukarki batanan tace Damagaran balle kice zakije gaisheta" tana fita ta kulle part din ta shiga kitchen ta ajiye kayan abincin ta dawo ta dan gyara gurin data zauna
Sake Shirin kwanciya tayi tabi lfyr gado ta kwanta tana dan chat dinta bacci taji ya fara sumamarta yasata miqewa ta dauro alwala ta dawo ta sake kwanciya tare da qarawa a.c qarfi bacci ya dauketa cike da kewar mijinta ko a waya bai nemeta ba ita Kuma yanayinsa yasa ta dan tsorata ta kasa kiransa da wannan tunanin tayi bacci wajen biyun dare ta farka ta sauka a gadon ta nufi bathroom ta dauro alwala wannan sabonta ne tun batasan kanta ba Amminta ta sabar Mata da tashin tsakiyar dare ko bata sallah saita tashi tayi alwala tayi tulawar qur'ani tare da istigfari hadi da addu'o'in da suka sauwaqa harma jikinta ya saba da zaran lkcn yayi saita tashi.
Ta Jima tana jero nafilfilinta sannan ta shiga jerawa Allah kirari tare da neman albarkar aurenta da zuri'a ta gari tare da roqa musu dawwamar zaman lfy da fahimtar juna ta dade sosai tanawa mijin nasu addu'ar samun budi da kariyar Ubangiji a duk inda yake.
Bata koma ta kwanta ba Saida aka Kira asuba nanma tayi ta Jima tana azkar hakanan sai ta rinqajin gabanta yana faduwa ta roqi Allah ya sassauta Mata duk wani Abu da yake tunkarota yabata wuyan dauka tare da addu'ar kada Allah ya