Showing 21001 words to 24000 words out of 66967 words

Chapter 8 - MY BESTIE'S HUSBAND COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Oct 2024

8097

halayenki qwaqwalwar namiji tanada fadi Amma zuciyarsa jaririya ce an halicceta dason me rarrashinsa da faranta masa yanason tarairaya da tattali uwa uba hqr domin soyayya da rayuwar aure tafi komai buqatar hqr Bestie Ina tayaki murna da samun irin mijin da kikeso Allah ya daidaita yasa kizama tauraruwa a zuciyarsa Kuma ya baki ikon kula dashi"
Numfashi ta sauke tace “amin sarki wa'azi idan sweet yazo zan bashi lbrnki da nasiharki gareni ke har record nayi fah zan kunna masa" murmushi Rafi'ah tayi tace “bakya girma bakya rabo da shirme ki gaisarmin da angonmu bazan dawo ba saina gama exams" sallama sukayi suka aje waya Rafi'ah tanajin farin ciki Bestienta zatayi aure Amma idan ta tuna rabuwa zasuyi sai taji hawaye ya wanke Mata fuska washegari Ni'imah ta kirata ta fada Mata mgn fah ta girma har ansa lkcn biki wata daya Amma angon yabar qasar bazai dawo ba sai ana saura sati daya biki.




Tayi Allah sanya alkhairi tare da cewa saura practicing uku su gama exams suna gamawa zata taho su fara shirye²n biki Ni'imah taci gaba da cusa soyayyar Ja'afar a zuciyarta shikuma bai wani qoqarin koyawa kansa sonta kawai ya karbetane bisa tursasawar mahaifansa musamman Hajiya fatsum da tayi tsalle ta dire tace bazai watsa Mata qasa a idoba da wanne ido zata kalli Hajiya Sahura tace danta bayason yarta.
Wannan yasashi hqr dadin dadawa da roqon da Mai martaba yayi masa na cewa kada ya bashi kunya tunda yarinyar ta amsa shima ya hqr zai sota a hankali tunda batada matsala, dole ya yarda da zabin na iyayensa amma tunda ya tafi Cairo gurin qaninsa bai sake tunawa da itaba Saida yaga saqonta a WhatsApp voice ne a qasa ta rubuta Masa _“Mijina bude kaji abinda aminiyata tacemin game dakai tanada hankali gata da hangen nesa inasonta fiye da yanda nakeson komai"_
Budewa yayi ya fara saurara jin sautin muryar Saida yasa gabansa faduwa hakanan baisan dalili ba yaji ya kwadaitu dason ganin mamallakiyar wannan zazzaqar murya kuma ma'abociyar hankali"




Batare da tunanin komai ba ya rubuta Mata _“to yayi muryarta tayi dadi Allah yasa haka fuskarta take"_ bata kawo komai ba tace _“fuskarta tafi muryarta dadi komanta mekyau ne kyau ya qare tunda aka halicci Bestie dina"_ dariya yayi yace _“anya kuwa sai nakega kamar batafiki ba"_ da wannan ya yaudareta ta turo Masa hoton da sukayi ita da Rafi'ah a kwance yake Amma Saida ya miqe zaune ya zuba Mata ido tanata zuba murmushi yar siririyar wushiryarta sama da qasa ta qarawa kyakkyawar fuskarta kyau gata yar duma duma ma'ana chubby ko inanta a cike kamar babu jijiya da qashi a jikinta dukda batada jiki amma ta wucce kace Mata siririya sumarta har goshinta dauke kansa yayi ya maida hankalinsa ga Ni'imah sai kawai ya rinqa ganin muninta musamman da yake ita siririya ce shikuma Allah yayisa dason chubby star din hoton yayi daidai lkcn da Ni'imah tace _“kayi Shiru Sweet?"_ Ajiyar zuciya ya sauke yace _“ban tantance ba turomin Wanda take ida kadai kema kike ke kadai"_





Sakaryar tura masa tayi bai jira me zatace ba ya daukesu to Gmail dinsa ya kashe Wi-Fi dinsa yaje yayi wanka ya dawo ya bude abincinsa yanaci yana kallon hoton kyawun qawar budurwar tasa yana birgeshi yanajin wani yanayi me wuyar ganewa a qasan zuciyarsa tun daga wannan ranar Ni'imah ta samu kansa daya fahimci itanma batada wani abin cewa idan ba lbrn qawar tata ba sai yake biye Mata sosai suyita Hira tana bashi lbrn Rafi'ah don karta gane yanajin dadin lbrn wani lkcn yake gwasaleta amma bata iya dainawa hakanan suka rinqa tafiyar da soyayyar ita a haukanta sone yasa yake biye Mata shikuma sonjin lbrn qawarta yasa yake janta jikinsa,
Ana saura sati biyu bikin Rafi'ah ta dawo suka shiga shirye shiye da invite din qawaye wata rashin saa tunda ta dawo Ni'imah keson hadasu ko a wayane amma taqi karba sai tace “ai batason yasan muryarta yanda zaiyi saurin ganeta so take tabashi mamaki duk ranar da suka hadu, to shima dake dan duniyar qasa da qasa ne bai takura ba duk da yasojin zazzaqar muryar a kunnensa Amma ya hqr yana saita sa'arsa batare daya bari kowa ya fahimta ba Amma bai zurfafa sosai ba saboda shima shima yana tunanin tanda zaayi ana saura sati daya bikin ya dawo saboda ya kasa jurewa yaje takanas ya sami Mai martaba ya fada masa idan da hali a hqr da aurensa da Ni'imah zai kawo wacce yakeso very soon




Kai tsaye mai martaba yace masa Babu hali dole ya dauki yan qafafunsa ya tafi bangarensa inda Muhseen yazo ya sameshi ya dubeshi yace “yadai ango meye ne naga kamar bakafa da walwala" kawai dakai yayi sanin da Muhseen yayi ba mgn zaiyi ba yasashi cewa “wlh wata baby ta rudani Prince Ja'afar na rasa Kuma ta inda zan fara" kallonsa yayi yace “nima halin da nake ciki kenan gashi nace da Mai martaba a hqr da aurennan yace babu hali wlh indai haka so yake to andade ana wahala a duniya ji nakeyi kamar idan ban sameta ba bazan iya rayuwa ba kay nifa nasan akwai qura a gaba don wlh ba aminta ba ko twins ne saina rabasu saina auri kowacce"
Dagowa Muhseen yayi da mamaki yace “suwa?" Batare da tunanin komai ba yace “Rafi'ah da Ni'imah Ni'imah ta kawomin tallan Rafi'ah zuciyata ta karbeta bantabajin son Ni'imah ba Amma son aminiyarta Rafi'ah yana neman zautani gashi a yanzu ban isa motsawa ba ko zan motsa sai na bari ita na sata daga ciki" gumine ya karyowa Muhseen yace “garin yaya hakan ta faru kanaso inaso ya zaayi kena...." Daukeshi yayi da mari yace “ka cire matata ce idan ka matsa wlh kasanni tsaf zan batar dakai" numfashi Muhseen yaja zafin zuciyar Ja'afar da kafiyarsa abar rubutawa ne a world news idan bai tursasawa zuciyarsa mantawa da Rafi'ah ba to tsaf zai iya aikata abinda yayi niyya nacine dashi kamar kuturu.




Miqewa yayi yace “Allah yabada saa Amma Kai kanka kasan abinda bazai yuwu ba ka dauko Ja'afar kasan halin Mata da kishi kuwa da zakaji shawarata sai nace ka cire ka hqr mace tanada sauqin samu alaqa kuwa wuyar qullawa gareta" Bai ko saurareshi ba ya miqe ya shige toilet ya biya buqatarsa ya fito yana goge jikinsa.
Muhseen baiyi fushi ba yace “Dazu Rafi'atuh ta kirani take tambayata meye shirinmu game da events sudai guda biyu zasuyi zasuyi BESTIE'S day sannan zasuyi NIKAH day so mukuma meye namu shirin?" Murmushi yayi yace kace nace duk abinda ta tsara shi zaa wanzar" haka Muhseen ya kirata yanajinsu ya sanar da ita ta amsa da cewa “kace masa muna gdy" daga haka ta kashe wayarta suka kalli juna sukayi ajiyar zuciya a tare.




Kusan komai na bikin tsarinta ne an kashe kudi sosai duk wani saqo ta gurin Muhseen yake zuwa Allah ya sardanta sabani tsakanin Rafi'ah da Ja'afar duk zuwan da zaiyi batanan wannan dalilin yasa basusan juna ba sai ranar dinner ranar ne ganinsu da juna na farko amma shi ya dade yanajinta a ransa da mafarkin cikar burinsa akanta wannan dalilin yasa baisa wasaba a lamarinsa yakebin duk wata hanya da yasan burin nasa zaiyi sauqin samuwa.
Kamar dai yau tunda ya tashi da safe ya shirya ya fice daga gdan Kai tsaye gdansu Rafi'ah ya nufa saboda yaji lbrn dawowarta a gurin Ni'imah da suna waya jiya da dare gaisawa sukayi da megadi yace ya shiga yayi masa sallama da Rafi'ah fitowarta daga wanka kenan tana shafa mai Anti Murja ta shigo tace “ki gama kizo kinada baqo a waje?" Kallonta tayi tace “waye anti?" Iska ta shaqa tace “bsnsani ba Mado ne yazo yacemin kinada baqo kiyi sauri kije don yadan jima"
Jitayi kamar tace bazata ba saidai ta daure ta tashi ta sanya kayanta ta fesa turare da dauki mayafinta kasancewar dama Shirin fita takeyi ta fito gabadaya tun daga nesa taji gabanta na faduwa babu wata alama da take nuna Mata wayene numbers na motocinsa JMW ne so wannan number Bauchi ce BZ124 AZR shiyasa bata kawoshi ba ta matsi motar sosai tana duba fuskarta a wayarta tsayawa tayi a jikin motar ta bude Jakarta ta jefa wayar daidai lkcn ya zuge glasses din motar ya leqo ta dago suka hada ido gabanta yabada wani rass taja baya da sauri tare da cewa “A'uzubillahi"




Zuba Mata ido yayi yana mamakin halinta wato shedan ta mayar dashi neman tsari takeyi dashi wani Abu ya hadiye me daci ya fito a motar ya tsaya a gabanta qanshinsu ya cakudu ya qara matsarta sosai yanda Motsin kirki bazata iyaba yace “Ammatana Rana gurin nsn kinsan farin mutum baya jure Rana a taimakeni ki shiga mota mu tattauna sauri nakeyi Mai martaba yake nemana naji bazan iya zuwa ba sai nazo naganki mun sake tattaunawa" hannunsa yakai zai riqo nata ta janye yayi murmushi yace “mutum da abinsa ake hana masa any way muje ina zuwa da sassafennan?"
Tabe baki tayi ta juya zatabar gurin yayi saurin riqeta ya fincikota ta fada jikinsa yaja numfashi me qarfi yanabin wuyanta da hancinsa yana sunsuna ya dora lips dinsa saman wuyan nata ya sumbata tare da sauke Mata hucin numfashinsa me dumi da dumama yanayi nandanan taji yanayinta na sauyawa a hankali tayi qasa da kanta ya janye tare da bude motar yaja hannunta yasata ya kulle ya zagaya ya shiga yayi Mata key yayi ribbers ya fice daga gdan tunda suka fito kanta yake qasa ta kasa ko daga ido ta kalleshi yayi murmushi yanason mace me kunya wai wannan dan abin take sunkuyarwa da kai to ranar da bis ta dauri sin Kuma baisan ya zasuyi ba.



Rage tafiyar yayi ya juyo ya dubeta yace “ina zamune My brid?" Dagowa tayi ta kalleshi kawai sai yaga ashe kuka takeyi yayi saurin tsayawa yace “kuma me nayi nidin?" Sake qasa tayi da kanta ya kashe motar ya matso jikinta ta janye ya zauna a inda yake yace “menene laifina yanzu Rafi'ah?" Kukanta ta sakarwa sauti tace “kanason hanani farin ciki a rayuwata Ja'afar badon niba ka kyaleni wallahi cikin tekun masifa kakeson jefani banason kana shiga lamarina idanma ganin banyi aure bane yasa kake shigemin ka qyaleni wlh cikin satinnan zan fitar da miji Koda banasonsa indai zaka barni don Allah Ja'afar zuciyata qarama ce shiyasa bana cunkusa Mata damuwa zan iya canyo Mata ciwon da zai zama ajalina...."
Hannunsa ya dora a bakinta yace “yanzun ma wayace kisa damuwa bakifa da wata damuwa ni naji Kuma ni nagani ni zanyi maganin kowacce matsala Rafi'ah kalmar qarshe na rantse da Sarkin da yake nufina da bude bakina ina furuci idan kika qara roqona akan na qyaleki zanyi Miki abinda baki taba tunani ba aurene naji na gani Kuma saina aureki duk Wanda zai mgn ya shekara baiyi ba yanzu haka jirana akeyi naje na bada kudin aurenki a yau zaazo gdanku a kawo ke idan kika takura ma wata gudan saina fasa baki nace a yau zaa dauramin aure dake muga qarshen tsiya haba don Allah ya kikeso nayine da wanne zanji kowa na gdanmu ya daina saurarona ya daina kulani saboda ke badan Mai martaba me fahimta bane Allah ya dorani akan Hajiya Innah ta shigemin gababa da yanzu bansan halin da nake ciki ba Hajiyata kuwa ko gaisuwata bata amsawa ita da yan'uwana saboda ke duk naji na dauka saikece zaki kasa jurewa wanda inada tabbacin bazaki samu matsala da iyayenki ba domin nasan sudin dattijai ne zasu karbi qaddara a yanda tazo musu, please na roqeki ki daina dagamin hankali wlh tallahi kinasona tsorone ya hanaki ganewa qaryane hadisin mutane da suke cewa ana barin halal don kunya babu wata halal da kunya ta Isa danneta saidai idan kaso wahalar da kanka"




Numfashi yaja ya sake dubanta da idanunsa da suka canza kala yace “Rafi'ah ni ba yaro bane nasan kaina bazan taba yarda na cutar da zuciyata saboda wata ba watanma wacce zuciyata ta kasa karbarta sannan ta kasa bani kulawar da nake buqata, kema inaso ki bude tunaninki ki yarda da zabin Ubangiji gareki Wai Ina raba dare kikeyi kina roqon Allah yayi miki zabi na alkhairi to meyesa alkhairin yazo kike qoqarin sanya hanu kiyi fatali dashi haba meye haka don Allah wacce irin yarinta ke damunki ne?"
Ya qarashe mgnr da qaraji abinda yasanya jikinta daukar rawa ta toshe kunnenta idanunta naci gaba da tsiyaya tta bude dan qaramin bakinta tace “kai ba alkhairi bane a gareni wlh bazaka taba zama alkhairi ba banasonka Ja'afar banasonka bazan taba sonka...." Fincikota yayi da qarfi ya sanya hannunsa yayi baya da kujerar ya turata ta kifa rigingine tana kokawar tashi yabita ya danne idanunsa a rintse itama ta rintse nata jikinta yana rawa ta sake sakin Kuka me sauti yayi saurin hade bakinsu guri daya suka rinqa kokawa tanason qwatar kanta ta kasa sake kwanciya yayi a jikinta ya riqe hannunta yaci gaba da shan bakinta wasu hawaye masu zafi suka sulalo daga idonsa suka zuba akan nata ya bude idonsa a hankali yana kallon yanda hawaye ke ambaliya a idanunta.





Cigaba yayi dashan bakinta da wani salo Mai fitar da hayyaci daqyar ta tattara qarfinta ta tureshi shima saboda mutuwar da jikinsa yayine yasa ta samu wannan damar ta tashi da sauri yana sauke numfashi yana qoqarin saita kansa yace “kada ki qara cemin bakya sona Rafi'ah Ina ganin mutuncinki kada ki zubar dashi da kalamanki ni qaunarki nakeyi Kuma aurenki zanyi ba iskanci zanyi dakeba ki koyi tauna kalamanki akaina idan kika horar da zuciyata da rashin adalci da tausayi zakifi kowa wahala domin kece a cikinta saboda haka duk haukan data debo sai kinfi kowa hadiya so ki rinqa tauna lafazinki akaina"
Bai bari tayi mgn ba yaja motar da sauri har yanzu jikinsa a mace yake ya sake juyowa yace “bana tambaya sau biyu Kuma bana bada umarni sau biyu ki fadamin inda zaki idan ba hakaba zan tafi dake gidanmu duk sanda kika shirya mgn kyayi" a gajarce cikin gunji kuka ta fada masa inda zata yayi murmushi ya juya akalar motar ya tsaya a wani Mall yayi Mata shopping ya dawo yaja suka tafi daqyar take bashi directions na inda zata har sukaje qofar gidan yayi horn aka bude suka shiga yace “inane nan din?" Qin bashi amsa tayi ya daka Mata tsawa yace “mgn nake Miki inane nan?" Cikin kidimewa tace “gig...gidan Aunty Raziqa" ajiyar zuciya yayi ya bude Mata yace jeki Kuma ki jirani zan dawo komai dare na daukeki wlh kikayi gangancin tafiya zakisha mamakina"........



_Hmmm! tab Rafi'ah kina ruwa🤣_




_Vote_
_Comments_
_Share_
_Please_




*_Ummuh Hairan_*
[1/5, 9:08 AM] Mrs AA Fansah: I think you'd like this story: "MY BESTIE'S HUSBAND" by realfauzahtasiu on Wattpad https://my.w.tt/aw40FbchNcb





*_My Bestie's Husband_*




*_Ummuh Hairan_*




*_Wattpad-realfauzahtasiu_*




*_17-18_*



___________________________
___________________________



Ficewa tayi da sauri har tana neman kifawa yabita da ido yana fitar da wata iska me zafi shima ya fito megadin ya Kira ya tambayeshi ko me gidan yananan ya amsa masa da “Eh yau yana hutu" ajiyar zuciya yayi yace “kayimin sallama dashi" da sauri megadin ya nufi cikin gidsn domin yasan waye Ja'afar Wakil a parlourn ya tarar dasu aunty Raziqa tanata rarrashinta tana tambayarta abinda ya faru.
Dubansa sukayi yace “Abuh Aulad ake Kira a waje" fitowarsa kenan suka fita tare da mamaki suka rungume juna Dr Naseer yace “Prince JM yau a gidana Amma dai ba zuwana bane wannan don nasan bakamasan gidana ba rabona dakai tun a Victoria I-land 3 years kenan" hularsa ya cire yace “wlh amaryata na kawo gdanka shine nace a kiraka nasan gdanka mana bandaisan matarka ba Ashe yayarmu ce?" Mamakine ya cika Dr Naseer yace “wa kenan?" Harararsa yayi yace “wace baquwarku yau?" Saita nutsuwarsa yayi yace “pretty nagani a parlour tana kuka dama tare kuke?" Murmushi yayi yace “itace amaryata wlh yarinyar tana wahalar dani sosai narasa ta Ina zan bullo Mata ta fahimceni" sake dubansa yayi yace “amaryarka ko budurwarka?" Dagowa yayi yace “duk daya itan budurwa tace Kuma amaryata saura kwanaki 29 idan ka cire yau saura 28 idan banda gobe saura 27 so ba laifi bane donna kirata matata fatane da Allah zai cikashi"



Wani numfashi Dr Naseer yaja yace “amma yaushe kayi aure inace baafi 3 mouths ba?" Daga Masa Kai yayi yace “eh ai kasan hudu Allah yace muyi ni ba zuwa nayi kayi jaridarka akaina ba ka kula kuma kayiwa matarka kashedi kada ta kuskura tabar Rafi'ah ta tafi ko nakai goman dare banzo ba zanzo ta jirani nazo na mayar da ita gida" yana fadin haka ya miqa Masa hannu yace “ka Bata kulawa sosai itadin rayuwata ce" mota ya shiga yabar Naseer tsaye shanye da baki Saida ya fita daga gdan megadi ya kulle qofar sannan ya juya ya shiga har yanzu kuka takeyi ya zauna ya zuba Mata ido ya dade yana nazarinta kafin ya furzar da iska yace.
“Ina kika samo wannan dan Izzar Rafi'ah Ja'afar Wakil fah?" Miqewa aunty Raziqa tayi tace “wai dama shine ai mijin aminiyarta ne meye hadinta dashi?" Kallon Raziqa yake yace “soyayya Mana harma da ranar aure yacemin saura 29 days a daura aurensu ni abokinane tun muna secondary bashi da sauqin mu'amala Izzar masifa ke gareshi indai ya nuna abu yace yanaso to ko zasusha wahala dagashi har abin saiya sameshi baya kula mace duk kyaunta nayi mamaki da akace zaiyi aure yasha fadamin shifa mace bata gabansa zai iya rayuwarsa shi kadai saboda baison damuwa to sai gashi baifi 3 mouths da aureba ya dauko wani aure ya akayi Rafi'ah?"
Matsawa tayi gsbansa ta Kama hannunsa tana kuka na fitar rai tace “wlh bansani ba bansan tsautsayin da yasa yasanni ba Uncle kayi wani abu akai mijin Bestie dinane ya yakeso nayi idan taji wannan baqin qudurin nasa?"



Miqewa Naseer yayi yace “hmmm ai kawai hqr zakiyi don wlh tunda kika kuskure kika fada komarsa to sai ya samu ko ta tsiya kota tsiya-tsiya" sake zubewa tayi a gurin ta riqe qafar Aunty Raziqa tace “nashiga ukuna meyesa kowa abinda yake fadamin kenan wlh banasonsa" kamota Raziqa tayi tajata dakinta tunda taga qanwar tata tasan tana cikin tashin hankali amma batayi tunanin yakai hakaba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login