Showing 63001 words to 66000 words out of 66967 words

Chapter 22 - MY BESTIE'S HUSBAND COMPLETE HAUSA NOVEL

11 Oct 2024

8107






Hawayen tausayinta Alh Hashim ya goge ya fice daga dakin saboda zuciyar Mata ke gareshi abin kuka bayayi Masa wuya Kuma yin kukansa zai qara karya mawa Rafi'ah zuciya, zama yayi yana tunanin abubuwa da yawa da bashu da amsarsu bai ankara ba yaji Bari'ah nayiwa Hajiya Rakiya magiya akan kada ta tafi da Rafi'ah tayi alqawarin kulawa da ita tare da dauke Mata kewa taci alwashin taya mijinta ida wannan kyakkyawan aiki da yayi niyyar aiwatarwa.
Daqyar Hajiya Rakiya ta yarda tabar Rafi'ah a gidan tun daga wannan ranar zaman Bari'ah da Rafi'ah ya koma gwanin sha'awa komai tare sukeyi Bari'ah macece me surutu amma tanada hqr da Kuma sanyin hali wannan abin ya dawwamar da qauna tsakaninsu, yauma kamar ko yaushe suna parlourn sunata hirarsu Bari'ah tanayiwa Rafi'ah koken matsalarsu ta dubeta tace “akwai wani magani da wani Malamin mu ya sanar damu idan akayi amfani dashi indai da rabo zaa dace ki bani bero da takarda zan rubuta Miki mu fita pharmacy mu nemeshi insha Allahu idan kikayi amfani dashi Allah zai dubemu ya bamu babie"




Murna ce ta cika Bari'ah ta tashi ta dauko biro da paper Rafi'ah tayi rubuce rubucenta da rubutunta na likitawa mamaki ya cika Bari'ah ta dubeta tace “dama kinyi karatu ne Rafi'ah?" Murmushi tayi tace “jiya na tuna cewa Ina da medicine certificate a garinmu Amma na kasa tuna a makarantar da nayi karatu Ina takurawa zuciyata akan tuno wani Abu game dani nakasa kawai abinda brain dina take fadamin ni matar aure ce Kuma ni ba matar qaramin mutum bace"
Shiru Bari'ah tayi tana nazarin kalamanta kafin ta miqe tace “idan ance asiri akayi Miki aka haukataki aka baroki da garinku da Mijinki sai kice aa ke ba asiri bane Mijinki ya mutu Kuma a kalamanki kina bayyana ke matar aure ce na rasa wanne zamu dauka a ciki to Allah dai muke fadawa Kuma munsan zai amsa bari na Kira Yallabai idan yana kusa sai yazo yakaimu




Shigewa dakinta tayi ta canza kayanta zuwa doguwar riga tayi rolling mayafin ta fito lkcn da Alh Hisham yake shigowa ya dubeta ta rusuna tace “barka da dawowa" murmushi yayi yace “kun dawo dani ku dole da kukeso to Wai inama kuka samo sunan maganin?" Sunkuyar dakai tayi Bari'ah tace “gulma itane ta rubutamin...." Kallonta yayi da sauri yace “ina kika samoshi?"
Qasa ta sakeyi da kanta tace “akwai wani lecturer dinmu da yake yawan yimana bayani akan abinda ya shafi matsalar haihuwa dayake a bangaren daya shafi matsalolin Mata nayi degree na..." Shiru tayi Alh Hashim yana qare Mata kallo yasan daganan bazata iya sake tuna komai ba shi tausayi na sosai take bashi musamman idan tace Ja'afar dinta ya mutu. Ficewa sukayi kowa jikinsa Babu qwari suka inda suke sakaran zasu samu Basu samu ba sukayi Shiru a mota na tsayin lkc kafin yatada motar yace “na tuna a titin government house naga an bude wani sabon katafaren Pharmacy R&J naji ance na wani babban doctor ne Kuma kamar ance dan Bauchi ne akwai yuwuwar zaa samu acan"
Nufar Pharmacy din sukayi sukabar Rafi'ah a cikin mota Bari'ah na riqe da Mahir a hannunta yaron kyakkyawa dashi Masha Allah fari tass kamar ubansa ta ratsa jininsa ta fito yanda duk Wanda yasan ubansa yana ganinsa zai iya shaida hakan, suna shiga pharmacy din suka miqa takardar da aka rubuta maganin wani matashin saurayi da alamun shine mamallakin gurin ya karba ya dago ya sauke idonsa akan Mahir gabansa ya yanke ya fadi.




Miqewa yayi da sauri yana kallon yaron, itama Bari'ah sai tabishi da kallon mamaki kawai sai taga ya miqowa Mahir hannu duk qwuiyar Mahir da baya daukuwa gurin kowa sai taga ya miqa hannu shima yana bangale Masa baki mamaki ya cika Bari'ah da Alh Hisham sukayi murmushi a tare Alh Hashim yace “hukuncin Allah sai sauraro kiga maquiyacin yaron nan yanda ya wani miqa hannu gurin bawan Allan nan"
Murmushi yayi yace “fine boy Nima nayi maka kamar yanda kayimin ko?" Yaron da baifi 17 months ba ya daga Kai sukayi dariya mutumin ya zubawa yaron ido yace “wato Alh danaga yaron nan naku Saida gabana ya fadi tunda nake bantaba ganin kamantayyar halitta irin wannan ba tsananin kamarsa da yayana mamallakin wannan pharmacy din tasa gabana faduwa tare dajin qaunar yaron a raina"
Batare da sunba abin muhimmaci ba sukace “ai dama haka Allah yake ikonsa" Jamal da Dan banzan surutu ya sake dubansu yace zaku bani dama na dauki hotonsa duk da nasan Prince baya cikin nutsuwa Amma zan nuna masa yaron nan nasan zaiji dadin ganin me kama dashi wlh tallahi shi da kuke ganinsa kungansa can a hoto"





Nuna musu hoton yayi yace “ya rabu da matansa du daya ma ana kyautata zaton ta mutu dayar kuwa ranar daya samu lbrn mutuwar dayar ya saketa saki biyu so dama ya taba yanka Mata Kati sau daya yanzu haka baya qasarnan yana Canada sama da shekara daya babu Mata kullum mafarkinsa matacciya zata dawo"
Dariya yayi sosai yace “Allah Sarki Yaya yaci engine brain am mema zaa baku?" Miqa hannu yayi ya dauko maganin tare da rubuta yanda ake amfani dashi yace “amma likitan daya rubuta muku maganin Nan babban likita ne saboda ba kowa yasanshi ba indai Kuna da rabon qara haihuwa zaku samu kwanan nan Allah ya kawo twince"
Su dariya ma yake Basu duk ya susuce sai surutu yakeyi kamar zautacce Alh Hashim yace “nawane maganin?" Murmushi yayi yace “ah haba aini na zama dan gida in wannan ma ya qare ku dawo wlh kyauta zan baku albarkacin wannan zuqeqen yaron me kama da Prince am ni yama sunansa?" Alh Hashim yayi murmushi yace “Muhammad Mahir" wani ihu yayi yace “Allahu Akbar tudu biyu sunan ubana ne dashi Kai dole nayi maka kyauta kaida uwarka"




Bari'ah ce tayi murmushi tace “banice mahaifiyarsa ba qanwata ce tana mota yaro kayi uba a sama dama uwarka ta damemu da kukan Mahir maraya ne" nandanan tausayi ya cika Jamal yace “Allah Sarki buwayi yanzu uban wannan kyakkyawan yaron ya mutu sannu kaji dole uwa taka tayi kuka ni wallahi kayimin yaro ka samu sabon uba kaji?"
Kwantar dakai Mahir yayi a kafadarsa yana dan gwarancinsa saboda maganar Bata fita sosai a haka suka fito zuwa bakin motar Rafi'ah na tsaye tana danne danne da wayarta taji takunsu ta dago idanunta sanye da glass ta sauke idonta kan Jamal hakanan taji wata faduwar gaba ta sake saita idonta akansa shima abinda taji shi yaji tare da amsar wani rikitaccen saqo cikin sakanni numfashi suka sauke a tare itadai kallon sani takeyi Masa Amma takasa tuna inda tasan kamanninsa inda shikuma yake aika Mata da wani saqo.
Kawar dakai tayi tace “mamaki maquiyacin dana a hannun baquwar fuska ya akayi haka?" Murmushi Alh Hisham yayi yace “muma haka mukasha mamakin Nan" mota ta shige tana cewa “wannan ya tabbatar muku Dana Dan gayene baya jituwa da yan gaya shiyasa baya yarda da kowa sai an Gaye" dariya sukayi Jamal yana qara saita idanunsa akanta yace “inason yaronki mamana" da sauri ta kalleshi tace.



“Muryar dana sani Amma a Ina nasanta?" Kwashewa yayi da dariya yace “up ni a mafarki Mana tsuke fuska tayi tamai da kanta qasa shima baibi takanta ba ya matsa sukayi qusqus dinsu da Alh Hisham sukayi sallama ya leqo yace “hajiya ta zan kawo ziyarar gaisuwa gami da roqon iri inason nima asammin wannan kyakkyawan irin na yafa a gonata"
Wani dogon tsaki taja daya daki zuciyar Jamal hakanan Allah yayisu basa qaunar tsaki, itakam Bata kobi takansa ba Alh Hashim yaja mota suka tafi tunda suka taho take huci tana mita tana cewa “kowanne dan iska sai yace yanasona bayan na fadawa kowa ni matar aurece don mijina ya mutu Yana nufin dole sai nayi wani auren ne to ai banga gawarsa ba balle nayi takaba sudai Basu kulata ba saboda sun saba jin wannan tufka da warwarar tata tace mijinta ya muta ta dawo tace ita matar aure ce.
Suna zuwa gda ta fita a motar fuuuu ita a dole anyi Mata laifi Alh Hashim da Bari'ah suka kalli juna sukayi murmushi Bari'ah tace “wannan karon zanyi iyakar bakin qoqarina guy din ya hadu sosai da alamun zata samu nutsuwa idan ta amince dashi" fita sukayi suka rufanta baya kowa ya fara harkar gabansa bata ware ba sai washegari sukaci gaba da harkokinsu Bari'ah tace Mata zasuyi baqi yau suka kuwa bata lkc wajen shirya dinner itace harda zabar abincin da zaa girka duk Wanda ta zaba sai tace tasan Ja'afar dinta yanasonshi"





Basu gama ba sai yamma liqis ta nufi dakinta tayi wanka sukayi magrib ta dauki qur'ani tana karatu taji an turo qofar ta dago ta kalli Bari'ah daketa murmushi tace “Yallabai yace kizo ki gaisa da baqin kafin su tafi" lifaya ce a nade a jikinta kawai ta miqe ta fito ta nufi parlourn baqin tare da sallamarta gabanta ya qara faduwa ganin mutumin jiya me muryar Wanda ta sani ta kuwa daure fuska Alh Hashim yace “zauna Mana Rafi'ah" tsuke fuska tayi ta zauna tana wasa da yatsunta inda Jamal ya kafeta da ido ganin yau sai taga ya qarayi Mata kwarjini fiye da jiya.
Alh Hashim ne ya kawar da shirun da cewa dama haka Allah yake ikonsa qila dama rabon haduwarki dashine yasa tunaninki ya dawo kika tuna kinyi karatun medicine har kika tuna da maganin da yakamata ki taimaka Mana dashi kika rubuta mukuma muka tafi neman gaibu don Allah ya sani har mukaje pharmacy din farko ban yarda akwaishi ba saboda wani lkcn maganganunki suna sabawa da hankali Amma da mukaje akace akwaishi maganin sune dai nasu ya qare sai na samu karsashin daukarmu nakaimu R&j domin mu siyo kwatsam sai mukayi katarin haduwa da wannan bawan Allah so abinda nakeso dake Rafi'ah ki nutsu ki fahimcesa idan da hali ki buda zuciyarki kigani kozata karbesa kinji" qasa tayi da kanta tana matsar qwallah tace “amma Alh nasha fada maka Ni matar aure ce don Allah ku daina takurani nayi soyayya wlh bazan iyaba zuciyata shi daya takeso Kuma ya tafi yabarni idan bashi ba bazan iya rayuwa da kowa ba"





Mamaki ne ya cika Jamal ya miqe yana riqe da hannun Mahir ya matso gabanta ya tsugunna Alh Hashim ya miqe ya fice, ajiyar zuciya yayi yace “da farko nayi Miki kallon tuhuma dana sani Amma dana tuna wasu abubuwa saina cire tunanin komai araina nasa a zuciyata Kama biyu kikeyi min tabbas hakane Rafi'an Prince ta mutu kwana biyu da haukacewarta an samo gawarta data babienta a dajin Dambuwa Kuma ke ance Mijinki mutuwa yayi so karna jaki da nisa My Raf inasonki Kuma aurenki na daura dambar yi duk da kasancewata saurayi hakan bai dameni ba domin sunnah zan raya ma'aiki shine yayi mana nuni da hakan zan aureki Rafi'ah da gaske wlh tun jiya na afka ki bani hadin Kai bada sauri ba mu fahimci juna ke nifa idan kika amince dani zaki aureni gobe zantada hankalin Azare baki dayanta sai an dauramin aure dake...."
Wani Abu taji ya caki qirjinta da yasata dafewa tace “azare! Azare!! Azare!!! Kamar na tabajin sunan?" Dariya yayi yace “ya Kama babie kina qasar Hausa kice bakisan Azare ba ni dan sarautar Azare ne mahaifina shine sarkin Azare yayana daya namiji yana Canada shekara guda bashida lfy saidai yaji sauqi idan bege da shauqin rashin matarsa da dansa ya motsa Masa Kuma yayi kamar ba zaiyi raiba Ina tausaya masa sosai har kuka nakeyi Masa saboda magauta sun sashi a gaba kawai don ya kasance me jiran gado shi kansa anso haukatashi Allah Bai nufaba sai aka sa Masa tsanar qasar Nan gabadaya wannan dalilin yasashi komawa Canada dazama Amma dukiyarsa duka tana Nigeria duk wata jaha dake arewacin Nigeria idan kika shigeta zakiga R&J pharmacy mallakinsa ne sunansa ne da sunan matarsa marigayiya Rafi'ah....."





_Comments_
_Share_
_Vote_





*_Ummuh Hairan_*
[2/2, 6:28 PM] Real Oum Hairan: I think you'd like this story: "MY BESTIE'S HUSBAND" by realfauzahtasiu on Wattpad https://www.wattpad.com/story/252522858?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create_preview&wp_uname=realfauzahtasiu&wp_originator=YZa%2Bnq8Gv74dk%2Br3fmroHt2fOS%2BrJAgPESvojabuR6mlrCBKlGcg1k%2FY8%2FEhPI0MmEXId7KOWuX%2F9qb4sodRsV9pyRkdk1Kk%2Bbe1YCuenDmpizIAObNjZFqoveTxmA0%2B




*_Mbh_*



*_Ummuh Hairan_*



*_Wattpad-realfauzahtasiu_*



*_Telegram Link_*
👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7




*_53-54_*

_____________________________
_____________________________





Shiru tayi batare da tace masa komai ba ya zuba Mata ido yana jiran tace Amma taqi cewa sai ya miqe yace “kiyi tunani akan manufata ta alkhairi ce gareki dani baki daya idan kin yanke hukunci zan kiraki sai naji ya ake ciki saboda nasan mataki na gaba" tabe baki tayi ta miqe itama yabita da kallon mamaki tunda yake baitaba ganin birkitacciyar mace irinta ba tama saurareshi din babu dama.
Qwafa yayi daidai lkcn da Alh Hisham ya shigo suka qara gaisawa yace “yadai ta amince kuwa?" Murmushi yayi yace “aa batama cemin komai ba inaga barinta zanyi ta nutsu tukunna saita yanke hukunci" numfashi Alh Hashim ya furzar yace “haka takewa kowa bazatace maka komai ba saidai kawai zan baka dama ka turo magabatanka ayi mgn inaganin hakan zaisa ta samu nutsuwa"




Kallonsa yayi da sauri yace “da gaske?" Murmushi yayi yace “eh da gaske mana" hamdala yayi yace “Amma naji dadi sosai gobe kuwa zan tafi Azare zan sanar da Mai martaba abinda ke faruwa idan ya amince jibi ma zamuzo"
Jinjina Kai Alh Hashim yayi suka fita ya rakashi har gurin motarsa cike da kulawa inda yabar shirgin sha Tara ta arziqin daya hadowa mahir sun jima suna tattaunawa sannan sukayi sallama ya tafi Alh Hashim yana komawa gida ya Kira rafi'ah balbaleta da fada yayi abinda Bai tabayi Mata ba yana tuhumarta dalilin wulaqanta Jamal.



Hawaye ta rinqa sharewa tsayin lkc yana fadan nasa kafin ya sauko ya zauna yanayi Mata nasiha taci gaba da matsar hawayenta kamar tana daukar abinda yake cewa, Saida ya dakata sannan ta dago tace “bazanyi jayayya da abinda ka zartar ba Amma inason ki fahimceni wlh bansan komai game dani ba inaji a jikina Ni matar aurece Amma bana iya tuna komai so kuyi hqr ki qyaleni na rayu a haka har zuwa lkcn da Allah zai kawomin qarshen matsala ta tabbas akwai wani Abu da kullum zuciyata ke qoqarin tunawa ta kasa"
Shiru yayi na dogon lkc Itakam Allah yayi Mata baiwar saita kalami idan ya biyeta bazasu tsinanawa rayuwarta abin arziqi ba dubanta yayi yace “amma da sharadin zaki daina fita ko Ina don na gaji da mazan dakemin sinturi a gidana" saurin daga Kai tayi tace “na amince da hakan" dariya ma taso ta bashi saidai ya dake ya tashi ya shige ciki miqewa tayi ta shige ciki ta Kama danta suka kwanta ranar kwana tayi bata rintsaba ta takurawa kwanyarta son tuno abinda ya goge a cikinta hakan yake haifar Mata da matsanancin ciwon kai.




Kwanaki suka rinqa tafiya cike da abubuwa masu rikitarwa duk yanda Jamal yaso ta bashi hadin Kai taqi yaje ya samu Mai martaba da maganar auren shine yace masa ya fara samun soyayyar yarinyar tukunna gashi abinda yake tunanin bamai wahala bane yayi masa wahalar samu, duk da bata bashi damar soyayya ba Amma tana sakin jiki dashi suyi hira.
Abinka da abinnan da hausawa suke cewa me da Wawa soyayyar da yake nunawa Mahir tasa takejinsa a jikinta idan yaga haka yakan dauka fara sonsa tayi Amma da yayi mgn sai tace itafa uban danta kawai takeso bayanshi bata ra'ayin kowanne namiji a duniyaWannan kalma na Sosa zuciyar Jamal saidai bashida wata madafa shi s hakanma dadi yakeji duk da ya zurma da yawa yakan taushi zuciyarsa akam ta sassauta Masa kar yaje yayi saukon bukukuwa ya Gina zuciyarsa da qaunarta Rana daya ta juyansa baya Da wannan tunanin yake ragewa kansa shauqi game da ita




Al'amarin Ja'afar kuwa tunda Rafi'ah ta Bata ya shiga kwale²n masifa tun suna sakaran ji ko ganinta har suka fara fidda rai tsayin wata guda shikam yaqi lfy kullum cikin faduwar gaba da ciwon qirji yake, dadin dadawa Ni'imah da taketa qoqarin dole wai ita saita gogensa tunanin matarsa da dansa yakanyi Mata kashedi me qarfi game da hakan saidai taqiji wannan yasa suka rinqa samun sabani idan taje ta isheshi da mita wani lkcn idan takaici ya isheshi ya ware qwanji yayi Mata mugun duka ranar saidai ta kwana a bangaren Hajiya Fatsum.
Ana haka watarana ya zaneta cikin dare tazo ta isheshi aikuwa ba arziqi ta gudu bangaren Hajiya Fatsum tana kuka anan hajiyan take fada Mata tayi hqr bayin kansa bane aljani sukasa ya cire masa tunanin Rafi'ah sannan ya batar dashi shine suketa fada da zuciyarsa da aljanin idan ya ciks takurawa ma haukacewa zaiyi shima, suna tsaka da wannan tattaunawa kawai sukaga wani jan haske ya keto bango ya nufosu gadan gadan take suka watse suka rinqa tsere Amma Saida ya cimma Hajiya Fatsum kawai saiji sukayi ta fasa qara ta fadi qasa Tim tundaga wannan Rana ta zama kamar mutum mutumin babu motsi babu magana babu komai a wannan ranar ne Kuma bakin Rafi'ah ya bude,




Sosai hankalin kowa ya tashi Amma banda Ja'afar da ya fara susucewa kullum cikin hada kaya yake ana riqeshi zaibar gari wata Rana da bazata goge ba cikin tarihin rayuwarsa yana kwance da dare kawai saiji yayi an qwala mass Kira ya miqe a firgice saijin murya yayi ana cewa dashi "Canada ka tafi Canada matarka da danka sunacan zaka ishesu acan"
Aikuwa batare da tunanin komai ba ya miqe cike da farin ciki ya dauki passport dinsa da master card dinsa da wasu takardunsa masu muhimmanci ya sace jikids qafa ya fice ta bsyan gdan saboda masifa ma ta katanga ya haura Hajiya Kaltume tana kallonsa tayi dariya tace “shege da kace bakaji ya tafi inda ajalinsa yake" tunda ya fita bai tsaya a ko inaba sai a inda zaiyi Visa ta tafiya kudi ya saki sosai akan cewa shifa tafiyar gobe gobe yakeso sunyi iyakar bakin qoqarinsu suka sama masa ta jibi daqyar ya hqr ya karba ya fice ya nemi masauki ya qarasa kwana washegari kuwa kashe wayarsa yayi Bai budeta ba Saida ya sauka a Canada ya nemi mazauni ya huta sannan ya bazama gari neman farin cikinsa duk Wanda yagani indai baqar fatane saiya tambayeshi inda zaiga Rafi'ah a qarshe ma mutane sukamai dashi mahaukaci kwana da kwanaki yana bilayi daganan zuwa nan a kwana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login