Showing 3001 words to 6000 words out of 76752 words

Chapter 2 - ZAFIN RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

ayusher   

26 Aug 2024

8559

za'ace suka taso, tayi aure tana karama sosai, alokacin shi sa'antane.

Ganin yau fuskarsa ba alamun data saba gani na inyai karya yasa tace "Abdulsalam ka taimakeni ka nemomin Junaid? Dan Allah."

Ta fada idanunta suna neman kawo ruwa, tausayinta ne ya kamashi, ya sani sosai ga rashin mijinga rashin da abin ya mata yawa, kallanta yai yace " Azeema."

Kamar ya tabota kawai tasa kuka, durkushewa tai tana kuka tace "Ka taimaken ka nemomin Junaid bazan iya rayuwa babu Junaid ba kaima ka sani."

Idanu ya runtse, tausayinta ya kamashi, sai dai yasan in har ya fada mata zata dawo dashi ne wanda yana karami rayuwarsa zata shiga garari, in ma an barshi da ransa kenan.

Zan nemoshi, sai dai kema ki taimaka ki daure, kallansa tai ta share hawayenta tace "zan sanar ma mutane bashida lafiya an kaishi Daura gun Mamana dan Allah kafin mutane su farga ka nememin shi."

"To Gimbiya."
Kallansa tai kamar zatai magana sai kuma ta fasa, juyawa tai ta fita daga kangon.

Da idanu ya bita tare da dan runtse idanunsa.

Bangarenta ta wuce gaba daya hankalinta ya kasa kwanciya, in jiya ba'a samu matsala ba tasan yau za'a samu, ko a wani halin dan yake?

**********

Mahmud yasha nema harya gaji, ita kam Azeema duk ta rame, duk da ta sanar akan Junaid yana daura ba kowa ne ya yarda da hakan ba.
Bare da akaga yanda ta canza, kowa sai gulma, yan jaje ma da biyu suke zuwa, dayawa suna nata dariya a ransu, na yadda take ji da dan da kuma fatan zamar dashi sarki.

Haka tana ji tana gani aka ba AbdulSalam mulkin garin Biram, ranar da akai nadin nan kam da wani zazzabi ta tashi.

Tayi nema tayi kuka harta gaji, duk tagama fitarda rai akan Junaid gani take halaka mata shi akai.

Gaba daya matan sarki nada a wancan lokacin ana ba Sarki nai ci damar zabar wanda yake so, wanda kuma bayaso za'a nemi fitar dasu ne amaidasu can karshen masarauta.

Bayan sun fita takaba ne Uwar Gidan Abdulsalam wanda a wannan lokacin ta zama sarauniya ana cemata Hajjo, turakarsa ta nufa, yana zaune yana cin abinci ta shiga.

Zama tai gefensa sai data jira ya kammala sannan ta kalleshi, kallanta yai yace "kinada magana ne?"

Tace "Takawa ya zakai da matan Sarki Zubair?"
Kallanta ya sakeyi yace "kamar ya kenan?"

Tace "na yarda kazabi wacce kake so tunda dai matanka mu biyu ne sai dai ban yarda ka auri Azeema ba."

Ido ya zuba mata kafin ya sha ruwan dake gabansa yace "a wani dalilin kenan?"

Kallansa tai sannan tace "kana tunanin bansan tsakaninka da ita ba?"
Shiru yai wannan karan sai kallanta kawai da yake, tacigaba, dukanmu mu biyu matan ka aura maka mu akai babu wacce kakeso, me kake tunani ya hanaka san mu duk wannan tsawan lokaci da mukai tare?"

Kofin ruwan ya ajiye yace "ko ma menene bai dameni ba, sai dai kinfi kowa sanin baki isa ki sani na fasa abinda nai niyya ba."

Kallansa tai kawai sai tasa wata dariya ta takaici tace "na sani ai, nasan wlh dama bazaka bar Azeema ba."
Mikewa yai yace "karki dorawa kanki abinda bazaki samu ba, ke kanki kinsan bazan yadda da maganarki ba to menene na fada?"

Kallansa tai tace "mene?"

Yace "inkin gama ki je ki kwanta da alama bacci kikeji, sannan wlh zan miki sharadi karki kuskura ko da wasa naji maganar nan a gun mutane, kinsan abinda zanyi da wanda bazan aikata ba."

Gaba daya sakar baki tai tana kallansa, wayaga a dakeka a hanaka kuka, shikam mikewa yai daga gun ya bar mata dakin ya wuce ciki.

Ta fi minti ashirin a zaune agun, tama rasa me zatayi, tazo da zarginta gashi ya tabbata dan tana zargin yana san Azeema ne amma bata tabbatar ba sai a wannan lokacin, lalai akwai tashin hankali, dan bazata taba yarda tai mulki da sannan yanzu tayi ba.

*********

Shikam Abdulsalam suna fita daga takaba ya sanar zai auri Azeema da Salma, wacce itama matar sarki Zubair ce.

Azeema kam damuwar rashin danta ma ta isheta ko bi takan abinda ake batai ba, haka aka daura musu aure aka nemi in tanaso a canza mata fadar ta ko a gyara mata, tace a barta haka.


***********

Junaid kam yasha kuka har ya gaji sai dai a hankali Azi ya dinga daukanshi yana kaishi cikin gari yana kallan yanda mutane ke hada hadar su har shima ya fara sakin jiki, abinka dama da yaro.


A hankali garin ya fara mai dadi, kamar yadda suka saba yau ma sun fita kallan gari su hudu yana ta kallan mutane yana dariya, suna kokarin wucewa aka cillo kaya, da sauri suka kare Junaid, dan sun dauka wani abin cutarwa ne, sai dai kaya ne ya fado, Junaid yadan turesu, ya matso inda kayan suka zubo, wata mata aka hankado waje, saura kadan ta begesu ta fadi kasa, wata yarinya ce ta fito tana kuka ta taho gun matar da alama mahaifiyarta ce, mutumin ya kalleta yace " nace banayi ana aure dolene? Ki tafi gidanku, au ashe fa baki san ma gidan naku bako? Ai dama ance tsintaciyar mage bata mage, munafuka kawai, na sakeki saki uku."

Yana kaiwa nan ya koma ciki tare da rufo kofar da karfi.

Kuka kawai takeyi yarinyar ma tana ta kuka, Junaid tausayinsu ya kamashi, yana neman karasawa gunsh Azi yai saurin rikeshi alamar karyaje.

Junaid ya zare hannunsa yaje kusa dasu kallan yarinyar da bata wuce shekara uku ba tana ta kuka yai.

Kallan matar yai itama yace "Hajiya inaje gidanku?"

Kallansa tai tana kuka tare da girgiza kai alamar bata sani ba.

Kusa da Azi y dawo yace "Azi mu tafi dasu kaga basuda inda zasu zauna."

Da sauri Azi yace "A'a yarima taya zamu dauki mutanen da bamusan su ba? Bamusan halinsu ba? Kana kallo kuma korosu akai."

Junaid yace "kalli fa yarinyar nan kuka take."

Ya fada yana neman yin kuka shima dan yanda take kuka yasa ya tuno da Ummansa.

Da sauri Azi yace "to Yarima amma da sharadin in sukai wani laifin zan korasu."

Yace eh naji.

Da sauri Junaid ya matso ya kalli yarinyar yace "kinasan shan mazarkwaila?"

Kallansa tai sannan ta daga kai, ya kalli maman yace muje gidanmu ku zauna.

Maman ta kalli su Azi, tana tunanin wannan kuma wanene? Su waye?

Ganin ba inda zata zauna yasa ta mike sukabi bayansu, Junaid ya rike hanun yarinyar suna tafiya, har suka isa gidan, suna shiga ya jata ya bata mazarkwaila, tana amsa yace "ya sunanki?"

Tace "Ke."

Kallan mamaki ya mata yace "ke kuma? Sunane?"

Kai ta daga alamar eh, fitowa yai waje inda Azi yake cema Hari ta samar mata makwanci sannan in har zata zauna anan sai ta taimaka da aikin gida, Junaid ya fito ya kalli Mamar yace "ya sunanta? Tace wai ke sunan ta."

Mamar tai kasa dakai cikin kunya, Azi ya kalleshi yace "ai bazata fada ba basa fadan sunan yan fari."

Junaid yace "to ya kenan? Taya za'asan sunanta?"

Azi yace "sai dai a tambayi babanta."

Mamar tai saurin cewa "a'a dan Allah karka tambayeshi zai san inda muke, duk kuma sanda ransa ya baci zai biyomu har nan."

Junaid yace "shikenan sai in bata aran nawa sunan, itama adinga ce mata Junaid."

Dariya suka kwashe dashi duka, Junaid yace "to an rasa sunanta, Azi ya ce to zan dinga kira miki sunayi in anzo kanshi kindaga kai."

Haka suka dinga Junaid nata dariya har sukazo kan Binta, nan ta daga kai.

Junaid ya juyo da sauri yace "Binta."

Nan suka shiga ciki yana gaba tana binshi a baya, Su Hari suka bisu da kallo kafin suyi murmushin jin dadi, ganin ya sake sosai.


*Ayusher Muhd*



*ZAFIN RANA*

Haske Writers Ameen

Pge 4

Bayan shekara goma sha biyu.

Wata irin shakuwa ce mai tsananin karfi tsakanin Junaid da Fatima wato Binta, tare suke komai nasu, mahaifiyar Binta ta rasu shekara hudu da suka wuce a lokacin tana shekara goma sha daya, Binta tayi kuka har ta gaji, a lokacin ta kara sanin mahimmancin Junaid, shikam dama Binta ita ta maye gurbin Umma, kanwarsa, Abbansa da kuma aboki, sun taso komai nasu daya, dan hatta abinci ga nata kwanon ga nashi sukeci, daki kuwa dama a gefen dakinsa take kwana, shima sai sun ci hirarsu sun gaji, lokaci suna yara ma sai dai tai bacci anan Hari ta dauketa, a da Junaid yana kuka sosai na rashin su Umma amma zuwan Binta yasa duk ya daina.

Tun bayan daya kawosu ya umarci kowa na gida karya kara ce masa Yarima a kirashi da sunansa.

Duk da basa so haka nan sukai dole saboda umarni ne wanda kuma sun san dole su bi.

Kamar yanda suka saba yauma sunje can bayan gari suna zaune suna hirarsu.
Yau yana saman bishiya ita kuma tana zaune a kasa tana bare gyada.

Kallanta yai yace "Binta ni sai yaushe zaki ban gyadar ne?"

Kallansa tai tace "ka manta yau baka da ita?"

Da sauri ya mike ya zauna yace "ban gane ba?"

Tace "to wayace ka hau sama ka barni a kasa?"

Yace "wayace mutum har yanzu ya kasa koyon hawa bishiya?"

Baki ta dan turo tace "ba wani yaushe ma ka koyamin? Kullum sai dai kai ka hau ka kyaleni a kasa."

Dariya yai yace "to ke kina mace wai me ke hadaki da hawa bishiya?"

Fuska ta hade tace "kusan duk matan garin nan nasan sun iya hawa sai ni."

Matsa matsa zan sauko.

Bata matsa ba ta kawar da kanta gefe irin fishin nan, saukowa yai ya zauna gefenta ya debi gyadar ya fara ci bai ce mata komai ba, haushi ya kamata ta mike ta dau kwanan gyadar zata bar gun, hartai taku shida bataji yaje komai ba a zuciye ta juyo ta kalleshi, idanunsa na kanta yana cin gyadarsa, tana juyowa ya sakar mata murmushi.

Ta harareshi tace " bazaka ce na dawo ba?"

Kallanta yai sannan yace "to dawo"

Tace "bayan baka ce ba sai dana fada?"

Mirmushi yai sannan ya nuna mata gefe yace "zoki zauna in baki labari."

Baki tadan zumburo ta karaso gun ta zauna, kallanta yai yace "Kinsan me?"

Kallansa tai tare da girgiza kai alamar a'a.

Mikewa yai yana dariya ya wafce kwanon gyadar ya fara gudu.

Mikewa tai ta bishi tana cewa "Allah Ya Junaid ka bani."

Dariya yai tayi yana gudu har sai dayaga ta gaji sannan ya zube a kasa ya kwanta yana kallan sararin samaniya, kwanciya tai kusa dashi tana dariya, cikin haki.

Sun danyi shiru kafin can yace mata "Binta!"

Kallan sa tai cikin nutsuwa saboda yanda ya kira sunanta, yace "Mama? Kina tunaninta?"

Kallansa tai sannan tace "wani sa'in, sannan kasan a makaranta ance mu dingama iyaye addu'a."

Murmushi yai sannan yace " ni bana tuno fuskar Ummana yanzu."

Gaba daya jikinta ne yai sanyi, idanunta suka ciciko, tana neman yin kuka.

Jikinshi ya bashi duk da ba kallanta yake ba, yace "karki soma kukan nan."

Ta ce "Nasan kanasan yin kukan kaima."

Juyowa yai ya kalleta yace "yaushe na ce miki?"

"Nasan saboda kar na damune yasa kake nuna baka damuwa."

Murmushi yai ya mike zaune yace "ko kadan, na girma ne shiyasa kema ya kamata ki daina kuka da wuri kinga kin girma kema."

Itama mikewa tai ta zauna gyada ya mika mata tace "ka baremin."

Murmushi yai sannan ya fara barewa, kallansa tai tace "wai ina Azi yake zuwa a duk bayan kwana 40?"

Kallanta yai kamar bazai yi magana ba sai kuma taji yace " maybe gidan mu."

Cikin mamaki ta kalleshi tace "gidan ku?"

Yace "eh kin manta nace miki Umma nada rai?"

Mamaki ne ya kamata dan da inya fada tana dauka wasa yake mata dan ta kwantar da hankalinta.

Ganin yanda ta bude baki tana kallansa yasashi dariya, yace "menene?"

Cikin mamaki tace "to wai me kake anan? Ka koma gida mana."

Kallanta yai yace "bansan ina bane gidan namu, sannan abinda na sani kawai shine nasan Umma nada rai, shikadai kawai na sani."

Ajiyar zuciya tai cikin rashin jin dadi kafin tace "ko mubi Azi in zai koma?"

Kallanta yai yace "oh ko mu bishi? Amma sai dai a boye dan bazai yadda ya kaimu ba, yau saura kwana....."

Sukai irge a tare sukace bakwai ya je.

Junaid yace "karfa muje da nisa kisha wahala, sannan shi kinga da doki yake zuwa."

Shiru tai cikin rashin jin dadi, yace "to ko na bishi in naga gidan sai nazo mu koma tare?"

Da sauri tace "a'a salan kaki dawowa."

Ta fada tana rike rigarsa.

Dariya yai sannan yace "inki dawowa kamar ya? Ta ina zan barki inyi rayuwa ta daban?"

Itadai bata yadda da wannan shawarar ba hakan yasa ya hakura ma da zancen.


*********

Masarautar Biram

Zaune take akan kilisarta kuyangunta na gefenta, ita kuma tana zaune tana jin kidan da ake mata, murmushi ne ke bayyana a fuskarta najin dadi.

Bude kofar da akai ne yasata ta bude idanunta dake lumshe, kallanta tai har ta zauna.

Masu kida ne zasu ci gaba ta kallesu sannan ta musu alama da su fita.

Hajjo ta bude idanunta ta kalleta, sai da suka fita tace "Menene?"

Budurwar data shigo ta kalleta tace "Umma nikam bazan auri dan Sarki Gobir ba."

Hajjo ta kalleta sannan tace "to wa zaki aura? Wai mi meke damunki? Kowa sai kice bakyaso? Ko ce miki akai zabinki muke nema?"

Kallanta tai tace "ni haushi yake bani, bazan aureshi ba."

Hajjo ranta ya baci, tace "kina kallo babban burin mahaifinki yaga ya aurar dake, amma ke sam bansan menene matsalarki ba."

Shigowar Wani Saurayi ne ya sata kallansa.

Yarima Zubair ne ya shigo, babban dan Abdulsalam wanda ya haifa tun Sarki nada rai, ya samai sunan Zubair wato sunan Yaynsa.

Kallanta yai yace "ke kike biye mata? ku daura mata aure kawai ku kaita, sai muga me zatai."
Ya karasa tare da zama, Zeenat ta kalleshi tace "kash ya akai haka? Gashi kai ba kaine babana ba."

Kallanta yai a zuciye yace "mene?"
Kafada ta daga mai sannan tace "na manta."

Kallan Umma yai yace "Umma yarinyar nan wlh ta gama rainani, kuma ni ba sa'anta bane."

Haushi ya kama Hajjo tace "Ku rufemin baki ko? Ko kunyama bakwaji, gida cike da makiyanku amma ku dinga fada."

Shiru sukai basu sake cewa komai ba.

Hajjo ta kalli kuyangar ta tace "Takawa yana ina?"

Kuyangar tai waje da sauri, bata dade sosai na ta dawo, kallanta Hajjo tai tace yana ina?

Yana bangaren Gimbiya Azeema batada lafiya.

Hajjo tai tabe baki tace "aikin kenan."


*******
*Ayusher Muhd*




*ZAFIN RANA*

*Haske Writers Association* 💡

Pge 5

Bubuga kofa yake iya karfinsa amma ba alamar budewa da take shirin yi, iya karfinsa yake jijigata yana kiran Binta, daga ciki itama kuka take sosai tana kiransa, gaba daya duhu ne agun babu haske ko kadan.

Daga kasan dakin ya hango hayaki yana fitowa, da sauri ya zabura ya mike daga baccin da yakeyi.

Gabansa ne ke dukan uku uku, gashi gaba daya ya jike sharkaf da zufa, kansa ya dafa sannan ya fito daga cikin dakin nasa.

Tsakar gida ya nufa yana tafe yana tunanin abinda ya faru ynzu, ji yai ance "Yari......"
Juyowa yai ya kalleshi saboda garin tar yake da hasken farin wata.

Azi ya matso ya rusuna yace "Junaid lafiya? me kake a daren nan?"

Junaid wanda idanunsa sukai ja jawur ya kalleshi sannan ya cigaba da tafiya, da sauri Azi ya bi bayansa har suka fita daga gidan.
Kara kallansa yai yace "Ina zaka?"

Junaid bai tsaya ba hakan yasa Azi kara binsa, sai da har suka fara shiga cikin gari, duk gidajen mutane a rirufe kowa ya kwanta, ga gari yai sanyi saboda lokacin sanyi ne.

Zama yai akan wani dandali dake gefen wani gida.

Azi ya karasa kusa dashi ya tsaya.
Junaid ya kalleshi yace "zauna."
Azi ya zauna ba tare da yai magana ba, Junaid bai kalleshi ba yace "Saura kwana nawa kaje?"

Da sauri Azi ya kalleshi, Junaid yai murmushi yace "akoda yaushe ina san tambayarka abu sai dai zuciyata na tsoron amsar dazan samu daga gareka."

Azi ya kalleshi cikin tausayawa.
Junaid yai dan shiru kafin yace "ada ina tunanin laifin me na aikata haka da za'a kawoni nan tun ina karami, ba wanda ya taba zuwa yaga a wani hali nake ciki? A yanzu kuwa komai ya fita a kaina gani nake rashin so ne yasa ba wanda ya damu dani."

Azi da sauri yace "ba haka bane Yarima."

Junaid yace "Yarima?" Ya saki wata dariya na takaici.

Azi ya kalleshi yace "Gimbiya batasan an kawo ka nan ba."

Kallansa yai, da sauri Azi ya rufe bakinsa, Junaid cikin mamaki yace "wanene yasa a kawo ni nan kenan? In har Umma bata sani ba?"

Azi ya kalleshi a tsorace, Junaid yai murmushin takaici yace " kasan ba dadan kai ko Hari wani sa'in kuna cewa Yarima ba da tuni na manta ko ni wanene? Fadan sunan da kuke wani sa'in shi kesa nake rike wanene ni, sai dai hakan baisa na dau matsayin da daraja ba, nasan a yanzu ba wanda ma yake tunawa da anyi wani yaro mai suna Junaid."

Shiru yai tare da kallan Wata, yace "in zakaje wannan karan zan bika."

Zanje naga mutanen da suka kulleni wace rayuwa sukeyi."
Gaban Azi ya fadi ya kalleshi yace "Junaid......."

Junaid ya kalleshi yaga duk ya tsorata, dariya yadanyi yace " binka zanyi ba a matsayin Junaid Yarima ba a matsayin yaran daka taho dashi daga can."

Azi haryanzu kallanshi yake yana tsoro, Junaid ya dafa kafadar sa yace "ba abinda zai faru, dan ni dakai kawai zamu ko Binta bazan dauka ba, na tabbatar in kaga na bata anan ai kasan ba abinda zan aikata."

Azi ya jinjina kai yace "to, amma....."
Junaid yace "mu fita da daddare."

Azi yai murmushi dan yana mamakin Junaid yanda wani sa'in kan canki abinda yake neman fada.

Junaid yai gaba, Azi ya mike yabi bayanshi, suna zuwa gida mai makon ya shiga ciki ya samu gu ya zauna,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login