Showing 39001 words to 42000 words out of 76752 words

Chapter 14 - ZAFIN RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

ayusher   

26 Aug 2024

8570

a cikin ukunnan tadace da yarima Junaid?".

Azeema ta dan harareta.

Dariyar farin ciki barira tayi, saboda tunowa da binta tace "ranki ya dad'e mu jirayi tarihin kowaccensu saimu d'ora a mizani, dan yarima yafi dacewa da d'iyar bajimin sarki mai ginannan tarihi".

"Wannan gaskiyane barira, shiyyasa nakeson kasancewa dake a komaina, ko mai martaba bazai San komaiba akai saina gama da shikansa junaid d'in".

"wannan shawara tayi ranki yadad'e".


*****************


"Uwar d'akina ga yariman can yafito daga sashen mai martaba, sai dai kuma ransa kamar a 6ace kamar yanda na kula."

Kamar Zeena tana bama fure amsa saikuma ta fasa "A bace? Ko muje bangarensa? Ai yayanane ba wanda zaice wani abin."

"Amma ranki ya dad'e bak'ya ganin yawan zarya sashensa kamar zai...."saikuma tai shiru ta kasa k'arasawa saboda hararar da zeena ta watsa Mata.

Tace "Gun Yayana zani kinada magana?"

Fure ta zube tace "tuba nake Gimbiya."

A falo suka iske hajjo da Ramlah suna magana sai dai da alama ana jinsu akai shiru, harzata wucesu hajjo ta dakatar da ita "Ina zakije?".

Baki ta turo, "zan d'an fita mik'e kafa mana".

Hajjo taja tsaki tana d'auke kanta. Zeena kuma tafice fure Na take mata baya.


***************

Gaba d'aya ran junaid a 6ace take, yayinda zuciyarsa kemasa wani sak'e-sak'e akan mai martaba. Ya tuna wadda akeson had'ashi aure da ita, yarinyar data tozartashi farkon shigowarsa masarautar, wadda batasan darajar d'an Adam ba, zai aminta da aurenta kawai domin yasamu damar kasancewa da kwatarwa Binta 'yancinta, Ada ba son binta yake amatsayin masoyiyaba, amma ganin matsayinsa da nata ya kawo tazara a tsakaninsu yayi tunanin aurenta, hakanne kawai zai dai-daita matsayinsu tamkar yanda yake gani a tun farko. Yasan kuma babu Wanda zai amince masa da auren Binta kai tsaye, musamman mahaifiyarsa, amma idan ya jingina akan auren Zeena to lallai zai samu yanda yakeso, yanaji a zuciyarsa mai martaba da manufa yake son bashi auren Zeena, inhar kuma yaga bashida mafita dolene ya yarje masa akan auren binta.

Ummana fa!?.

Wani sashen zuciyarsa ya ambata. Kafin samun amsa sallamar Azi ta katse tunaninsa. Azi ya rissina yana sanar masa da neman iso daga Zeena.

Wani kallo ya watsama Azi, kafin yace, "Bana bukatar hayaniya".

Azi ya jinjinamasa kai cike da girmamawa.

Takaici ya kama Zeena jin amsar da Junaid ya bayar abata, wannan wulak'anci har ina, takula yarima Junaid yacika tsauri da rik'o, yakamata ya yafe mata inhar akan laifin data aikatane bisa rashin sani, ita ta rasa meyasa take san ganinsa.

Ranta a 6ace tabar sashen.


***************

Mamaki yakama Binta jin zancen da barira take Mata, wai gimbiya Azeema tace kar asake sakata wani aiki.

Kodai Junaid ne yay magana? To amma jifa yanda ya watsar da ita d'azun, hakan bak'aramin k'ona ranta yayiba, dan har kuka tayi, ita gaba d'aya ya Junaid ya canja Mata, tamkar bashine abokin nan nata dasuka tashi tare suka rayu tareba.

"Ya ALLAH kabani ikon jurewa da wannan sabuwar rayuwa mai cike da rashin ya Junaid a cikinta".

Ta share hawayen da suka ziraro Mata.


*************

Mamaki sosai ya Kama gimbiya Azeema ganin yau kwanan junaid uku bai lek'ota ba, Anya kuwa lafiya?. Kokuma nazarin littatafan tarihi da Mahmud ya bashine suka d'auke hankalinsa?.

"Inaga hakane". Tafad'a a fili tana murmushi da kauda zarginta na farko.

Sai mai martaba da shima a kwanaki ukunnan Sam bai nemeta ba, baki ta ta6e, dan hakan bai dameta sosai ba, ayanzu burin gyara rayuwar d'anta ne a gabanta, dan nan kusa take buk'atar dawowar mulki hannunsa, tunanin yanda zatai da Abdulsalam ne ya darsu a ranta, dolene ta san yanda zatai.




Nace, "turk'ashi, wannanfa shine ga akuya ga kura🤭🚶🏻‍♀".







***************
Ayusher 27
***************


*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍*


{28}


Bude idanunsa yai a hankali ya daurasu akan Azi dake durkushe a gefensa, Littafin dayake nazari na hannunsa ya kulle.

Azi yai murmushi yace "yauma bazaka fita bane?"

Junaid ya kalleshi yace "zuwa yamma."

Azi ya jinjina kai cikin gamsuwa sannan ya mike, haryaje kofa ya juyo ya kalli Junaid, Junaid ne ya kalleshi kallo mai dauke da tambaya.

Azi ya kara rusunawa yace "Binta fa ta zama 'ya, jiya dana ganta, da alama Gimbiya ta zareta daga gun bayi."

Kai Junaid ya jinjina bai ce komai ba, Azi wanda ya fahimci jin dadin Junaid ya fita daga falan.

Shiru Junaid yai a hankali kuma wani lalausan murmushi ya zagaye fuskarsa, baiyi niyyar fita ba saboda yana jiran aike daga bangaren Mai Martaba sai dai jin haka yasa ya mike.

Ciki ya shiga ya fara shirin fita, harya gama shirya wa sai kuma ya koma ya zauna.

************

Kallan Barira tai tace "Anji daga gun Junaid?"

Barira tace "tuba nake ranki ya dade amma haryanzu ba labari."

Shiru Azeema tai, tace "Binta fa?"

Dazu wai zata fita, Azeema ta kalleta tana mata alamar ina?
Kai Barira ta girgiza tace "bansani ba Gimbiya."

Shiru Azeema tai tana dan kada hannunta, badai dan ta bata matsayin 'ya ba take neman zagayewa ta dinga zuwa gun Junadi ba tare da saninta ba?

**********

Mikewa naga ya sake yi sannan ya fito daga cikin dakin nasa, da sauri Azi ya matso yace "Yarima zaka fita ne?"
Kai Junaid ya daga cikin kasaita ba tare da ya amsa ba.
Da sauri suka matso dan yima Junaid rakeyi.

Zeena wacce ta nufi bangaren Junaid ce ta tsaka cak, daga nesa wanda akala yakai taku goma sha biyar tsakaninsu.
Itama ja tai ta tsaya daga inda take.

Zeena ranta yakai matuka gun baci, tun daga sama ta kalleta zuwa kasa, da alama kenan ta fita daga matsayin bayin da take?
Cikin isa ta daga hannu tayima Binta alama da ta zo.

Binta ta kalleta sannan ta karasa inda take.
Wani banzan kallo ta sake mata sannan tace "daga ina?"
Binta ta kalleta tana tunanin wannan tambayar fa?
Zeena ce ta katseta da cewa "ina zaki kuma? A iya sanina kin bar bangaren Ya Junaid."

Binta ta dago ta kalleta sannan tace "zanje gun Harira ne."

"Harira? Wace kenan?"
Shiru Binta tai ganin batasan me zata ce ba, Zeena jin bata tanka mata ba yasa tace "banaji dai mace wacce tasan mutuncinta zata dinga zirga zirga bangaren namijin da batada alaka dashi ba."

Binta ita kanta batasan sanda ta kalleta ba, hatta Fure sai data guntae dariyar data taso mata.

Ganin yanda Binta ta kalleta ne ya harzako Zeena dan dama neman abinda zata mata takeyi, Binta bata nufa ba taji an wanketa da mari.

Kallanta tai cikin tsananin mamakin laifin datai, Zeena tace "me? Zaki rama ne?"

Binta tai shiru, ke yanzu in har kinada hankali ba tattarawa ya kamata kiyi ki dau kafafunki ki koma mahaifarki ba?

Binta yanzu kam ta fara zargin san shi Zeena takeyi.

Junaid wanda ya fito yana tsaye daga bayansu yanajin abinda ke faruwa, ransa yakai matuka gun baci duk da a fuskarsa bazaka gane ba, Binta ce ta dago zatai magana ta ga Junaid, ido ta kuramai ta kasa cewa komai.

A kufule Zeena ta juya dan taga meke faruwa, Junaid suka gani a tsaye yana kallansu.

Gaban Zeena ne ya fara dukan uku uku, wanda idanunta suka firfito waje, a hankali cikin kasaita da takama ya fara taka kafafunsa zuwa inda suke.

Binta kam kallanshi kawai take gaba daya ya canza, ya sake kwarjini, dama haka Junaid yake ko dan ya dawo inda ya dace dashi ne?

sauke idanunta tai daga kansa ganin ya nufo daf da inda suke, Zeena a rude tace "Yaya."

Kallanta yai yace "Zeena? Me kikeyi a nan?"

Ta kalleshi cikin fargaba tace "dama nayi tunani zuwa ne gunka."

Guna?"
Kai ta daga,yace "me kike anan to?"

Kallan Binta tai wacce ganin bai kalleta ba yasa gaba daya taji kafafunta sun fara rawa.

Idan na kasa dake ya miki laifi me zai sa ki kaskantar da kanki a ciki mutane?


Mamaki ne ya kamata ta kalleshi da sauri, Binta kam gaba daya jitai kanta ya fara wani sarawa, juyawa yai zuwa bangarensa, Zeena ta kalleta ta dafa kafadarta tace "dan an sa saban kaya ba'a canza asali."

Tabi bayansa, Azi kam wannan lamari shi kanshi ya daure mai kai, meke faruwa?

Suna shiga cikin falansa kallo kadai yama Azi, suka bar falan dukansu.

Yana tsaye dama bai zauna ba, ita kanta Zeena a tsaye take, cikin salo tace "Ya Junaid."

Bai juye daga inda yake ba yace "ke kika nemi hadin aure tsakani na dake?"

Gabanta ne ya cigaba da faduwa, ta rasa me yasa yau take jin shakkar Junaid haka.

Juyowa yai ya kalleta sai kuma taga ya saki wani murmushi wanda ya kara sata cikin wani yanayi.

A hankali ya tako zuwa inda take yace "me? Bake bace?"

Kallansa tai idanunta duk sunyi jaa, kai kace marinta akai, a hankali tace "nice."

Murmushi ya sake yi yace "kinasona da har kike tunanin zaki jure duk matsalar da zata fito ta bangaren Hajjo da Ummana?"

Yawun bakinta ta hadiya sannan tace "Eh."
Yadan jinjina kai a hankali yace " hakan yayi, sai dai in har kinaso na aure nima sai kinbi sharadi na."

Sharadi?
Ta fada a dan tsorace, yace "eh sai dai in zan aureki tare da kawarki."

Kawata?

Cikin mamaki tai tambayar, yace "wacce kuke hira da ita a waje dazu, na tabbatar yanda kike yar sarki bazaki daga hankalinki akan hakan ba."

Rainin wayau, bayan yasan abinda sukai a waje harya tambayeta yanzu kuma yazo mata da wani rainin hankali? Wai kawarta? Sannan me? Ya hadasu da wannan yar iskar da ba'a ma san tsatsonta ba?

Junaid ne ya kalleta yace "kina so ki aureni wannan ce kadai hanya in kuma baki amince ba kowa yasha zamansa."

Shiru gai tama rasa ta ina zata fara kamo abinda ya kamata.

Junaid yace "ki sanar da Mahaifinki haka dan nasan zai kira ya tambayeki, in kuma baki amince ba kowa yasha zamansa."

Yana kaiwa nan ya fita daga falan ya barta a tsaye kamar gunki.

Binta kam kasa ma shiga gun Hari tai tana tsaye a gun kamar wacce bata numfashi, abun daya faru sai kara dawo mata yakeyi.

Ganin Azi ya fito yasa ta fahimci sune, da gudu tai kwana ta labe, sai dai kafin ta karasa kwanar Junaid ya hangota, tsoransa ma kartaje garin gudu ta fadi taji ciwo.

Haka suka zo ta saitin inda ta boye ya dan kalleta ta gefen ido ya basar, kiyi hakuri Binta idan har banyi hakan ba bayanda za'ai na dawo dake gareni.

Bangaren Azeema ya nufa wacce ganin Junaid baizo ba yasa tasa a kara kiran Jakadiya.

Suna zaune Jakadiya na mata bayani akan binciken da akai, Azeema kowacce aka nuna mata aka mata bayani sai tadan kushe.

Jakadiya tasa dariya tace "Gimbiya taya za'a samu wacce zata dace bayan duk wacce aka baki bata miki ba?"

Azeema tai murmushi tace "bawai basumin bane Junaid dine kamar basu dace dashi ba."

Barira ce tai dariya tace "A idanun Gimbiya, Junaid ne kadai ya cika yanda ya kamata ."

Azeema ta kalli Jakadiya tace "Me Takawa yake a 'yan kwanakin nan?"

Jakadiya tace "nikaina bansan meke faruwa ba, da alama wani nazari yakeyi."

Matsowa tai cikin gulma tana san sanar da ita har Junaid ya kira bayan sun zauna dasu Shammaki aka sanar da isowar Junaid.

Da sauri ta suka tattare Barira ta nunawa Jakadiya hanyar baya ta fita da sauri.

Azi ne ya kalli wacce tai ison ya sake mata alama dan ta sake sanarwa.

Barirace ta karaso da sauri ta bude kofar, sannan ta basu hanya.

Junaid ya shiga ciki, kallan Azeema yai wacce ta gyara zama kai kace ita kadaice dama a gun.

Zama yai ya gaisheta cikin kulawa.

Kallansa tai cikin wani jin dadi tace "Barka da isowa Yarima, har ina tunanin aikawa kazo, ganin kwana biyu banganka ba."

Junaid ne ya kalleta yace "Tuba nake Umma na."

Wani dadi ne ya kamata, tace "Ya zanyi, ai ganinka ya wanke komai."

Murmushi yai cikin jin dadi.

Barirace ta sunkuyo tace "Yarima, Gimbiya ta maida Binta matsayin 'ya."

Kallan Azeema yai sannan ya sunkuyo yace "tana godiya Ummana."

Shikenan? Abinda yazo mata ranta kenan, ganin ba wani farin ciki a fuskarsa yanda ta zata.
Sai dai hakan ya mata dadi ta wani bangaren.

***************

AbdulSalam ne yai shiru, yau ya gama tattare duk wani hukunci da zai dauka.
Shammaki ne ya kalleshi su biyu a cikin falan, yace "Ranka ya dade ka gama tunanin?"

Abdulsalam yace "eh. Dole ne mubi abinda yakeso inhar munasan abinda mukeso ya samu, sannan inhar munaso mu binne abinda yake tattare da rayuwarmu."

Kayi shawara mai kyau Ranka ya dade, kayi hakuri mu bashi abinda yakeso, ni inaga wahala ma kadai ya isheta a gadan nan da batada kowa.


Kai Abdulsalam ya jinjina yace "inka fita kasa a kira Zeena."

Nan Shamaki yai sallama, a waje ya bada sakon Takawa sannan ya tafi.

Zeena wacce tunda ta shigo bangaren Hajjo ko kala batace ba, duk kuwa da maganar da Hajjo ta mata bata iya tankawa ba.

Zubair ne ya kalli Hajjo yace "Hajjo kin bincika mai Junaid suka tattauna da Mai Martaba?"

Hajjo ta kalleshi tace "Zubair sau nawa zaka tambayeni ne? Menene matsalar ka ne nikam? Bantaba ganin ka cikin wannan yanayin ba."

Ya kalleta fuska a kumbure yace "Hajjo bakiga yaran nan bane shi yasa."

Tsaki taja tace "kaidai kayi kokarin bin karatun ds akema karka kuskura ka bari yaran nan ya sake wulakantani dan wlh bazan taba yadda ba."

Baki yadan kara kumburowa sai dai baice komai ba.

Harara ta bugawa Zeena tace "Ke bansan iskamci kinshigo ko kala bakice ba."

Fure ce ta shigo da sallama ta zube tace "Gimbiya Mai Martaba yana nemanki."

Wani murmushin jin dadi Hajjo tai da alama Sarki ya yanke hukunci akan maganar Sulaiman datamai.

Mikewa Zeena tai kamar mara rai ta nufi kofa.

Hajjo ta sake wani murmushi jin dadi.

Nace Zai zama kuka😂🚶🏻‍♀

*******
Zeena ce dukufe a gaban Mai Martaba ya kalleta yace "Zeena!"

Kallansa tai tace "Naam Abba."

Shiru Abdulsalam yai kafin yace "maganar Junaid namai magana."

Kallansa ta sakeyi sai dai batace komai ba dan ta riga tasan me zai karasa ce mata.
Sai ji tai kuwa yana cewa "Yace inhar zai aureki sai dai ya hada da yarimyar daya taho da ita."

Shiru tai wanda hakan yasa Sarki yace "Zeena! In kinsan bazaki iya ba ki hakura ki auri Sulaiman."Yai maganar cikin kakkausar murya dan ya fahimci inya mata lago lago zata lalata komai.

Kallansa tai tace "a'a na amince."

"Kin tabbatar zakisa Hajjo ta yadda da abin nan?"

Kanta tsaye tace "eh."

Yace "jarki fadawa kowa maganar Binta, sannan Hajjon ma karki mata zancen ki da Junaid harsai munyi magana dashi."

Tace to, mikewa tak ta fito gaba daya jikinta ba karfi kai kace wacce ta tashi daga jinya ce.........

Hmmm🚶🏻‍♀

*******
Ayusher🏌🏻‍♀


*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍*


{29}


Zeena tana fita Abdulsalam yai shiru yana nazari, Junaid ya kamata yasa a kiramai ko Azeema?
Dan tabbas yana san al'amarin nan ya faru cikin gaggawa tunkafin Junaid ya gama fahimtar masarautar.

Idanun Junaid ne suka fadi masa a lokacin daya mai zancen indai zai auri Zeena to lalai sai dai ya hada da Binta.
Bari ya shawo kan Azeema ya tabbatar ita bazata taba yadda da wata Binta ba, dole yai amfani da ita.


A daren ranar sarki Abdussalam ya buk'aci ganin Azeema a matsayin wadda zata kwana a sashensa.

Tunda yammaci jakadiya ta Isar mata da sak'on mai martaba.

Bata wani ja lokaci ba ta amsa kiransa itama, dan tanason jin wane zamane yayi dasu wambai kwana hud'u da suka wuce, sannan tana san tamai magana akan auran Junaid da takeso ayi.

Sai wajen tara Na dare ta kimtsa cikin shiri Na alfarma da baza k'amshi, ta d'ora had'ad'iyar alk'yabbarta, barira ce kawai tamata rakiya sashen mai martaba.

Bayan sanar da zuwanta jakadiya tamata iso.

Tana shigowa cikin turakar tasa ya mike a hankali ya tako zuwa inda take.

Azeema ta kalleshi cikin kulawa tace "Takawa!"

Abdulsalam ya mika mata hannunta, hannu tasa ta rikoshi, ya jawota har jikin gadansa sannan ya zaunar da ita akan gado, dagowa tai ta kalleshi sannan tai murmushi.

Zama yai kusa da ita shima sannan ya jawota jikinsa ya rungume.
Murmushi ta sake yi sannan tace "AbdulSalam!"
Bai saketa ba har sai daya biya bukatarsa.
Jawota yai jikinsa ya sake rungumeta, tadan tureshi kadan tace "Menene?"

Hannu yasa akan fuskarta yace "Me kike tunani in muka hada jinin mu aure?"

Jinin mu?
Ta maimaita tana kallansa, kai ya daga mata yace "Zeena da Junaid nake nufi."

Yanda take kallan kwayar idanunsa ne ya sashi sake cewa "menene?"

Mikewa tai zaune da sauri tace "bangane Zeena da Junaid ba."

Shima zama yai sannan ya kamo hannayenta yace "badai na tunanin Azeema zataki hada jininta da nawa, dan na tabbatar sirri na nata ne."

Kallansa tai idanunta cike da tsoro tace "Abdulsalam?"

Yace "me? Ba hakan bane? Na tabbatar duk abinda nai a baya kin sani sannan baki taba furtawa wani mai numfashi ba a doron kasa ba, kinga hakan yasa nasan ni dake sirrinmu na juna ne kamar yadda nima duk abinda ya shafi ki sirri nane."

Hannunta ta zare da sauri wanda gaba daya taji jikinta yana rawa.

Bakinta na rawa tace "zan wuce bangarena."
A daren nan? Ya fada yana kara rike hannunta, me kike tsoro? Bayan komai a tafin hannunki yake? Ki kwanta kiyi bacci hankalinki a kwance.

Yanda take kallansa yanzo kallo ne mai cika da shakka.......

Ya d'auke Kai yana wani murmushin k'asaita, yasan wacece Azeema sarai wajen rik'o da ra'ayin kai, amma ya tabbata a wannan ga6ar yamata kamun da bata Isa su6ucewa ba.

Itama komawa tai ta zauna zuciyarta na sake maimaita maganganunsa, dolene tayi hak'uri sai asuba ta koma sashenta tamkar yanda sukeyi, dan inhar takoma yanzu hakan zai d'auki hankalin wasu, duk yanda taso bacci ya dauketa kasawa tai.

Idan ita ta amince Junaid fa? Ko kad'an bataga ta inda junaid ya dace da Zeena ba, sannan tama Yaya jininta zai kasance waje d'aya dana hajjo? Dukma ba wannanba, hajia iya zama ta amincene? Kai, wai miyasa Abdussalam yay wannan tunaninma?....

Wannan tambaya da zuciyarta tai matane ya sakata juyawa ta kalli Sarki Abdussalam dake kwance shima yana kallonta. Murmushi yamata. Batareda ta maida masa murtani ba tace. "Kozan iya sanin dalilinka Na wannan had'in?"

Murmushi yakumayi, sannan yatashi zaune yana matsowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login