Showing 45001 words to 48000 words out of 76752 words

Chapter 16 - ZAFIN RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

ayusher   

26 Aug 2024

8571

Marin da aka wanka mata ne yasa ta gigice, ta kalli Zeena a ranta tace sau nawa kenan?

Zeena ta kara kifa mata wani, zata kara mata Hajjo ta ce "Ke."

Hannunta ta sauke a zuciye, sannan ta dawo ciki.
Binta a hankali ta bar bangaren kanta na cigaba da sarawa.

Gun Hari ta nufa dan neman magani saboda azabar datakeji.


***********

Mikewa Junaid yai bayan ya gama nazarin da yakeyi a cikin kansa, daki ya shiga yai shiga irin ta alfarma, fitowa yai daga sashensa.
Azi da sauri ya taso yace "Ranka ya dade zaka wani gurin ne?"

Eh ina san ganin Umma ne.

Da sauri yace "To ranka ya dade."

Harira ce ta nufo inda yake da sauri, ta zube ta gaisheshi sannan tace "Yarima!"
Kallanta yai yace "Hari ya akai?"

Shiru tai sannan ta kalleshi tace "Binta a gurina ta kwana jiya."

Oh!
Harira tace "sai dai yau dana tashi na ji jikinta da zafi sosai da alama ta dade bata jin dadi."

Hankalin Junaid ne ya tashi dan duk yanda yaso karya boye damuwarsa sai da abin yaci tura yace "bangane ba?"
Tace " tunda ta shigo take kuka shiyasa nima bansan abinda ya sameta ba, nadai san tace daga gun Hajjo take.

Cikin hanzari ya nufi inda take.

Tana kwance cikin bargo tana rawar sanyi, kusa da ita yaje ya zauna, su kuma suka bar dakin.
Ido ya zuba mata zuciyarsa na tafasa da bacin rai, cikin dakewar zuci yace "saura kadan Binta, saura kadan, na dau alkawarin rama duk wulakancin da aka miki, ki kara daurewa, mun kusa zuwa gurin."

Tana jin kalamansa sai dai ta kasa ko bude idanunta, sai hawaye da suka gangaro ta gefen idanta wanda ya sa ya fahimci cewa idanta biyu.

Mikewa yai ya fito, ya kalli Azi yace "bangaren Hajjo."

Da sauri Azi ya matso yace "da kace......"
Kallan da Junaid yamai ne yasa shi yin shiru.
Hajjo na zaune ita da Zeena da Zubair da Ramlatu, sua mitar abinda ke faruwa.

Zeena dai tana jinsu amma ita tace sai Junaid, Zubair ne ya kalli Hajjo yace "Hajjo nifa nasan Allah akwai abinda Abba yake shiryawa."

Hajjo ta kalleshi tace "koma me yake mulki naka ne sai dai bayan raina a kwace.

Isowar Junaid aka sanar cikin mamaki tace "Junaid?"

Zeena ce ta mike da sauri zatai hanyar kofa, Hajjo tace "gidan ubanwa zaki?"

Juyowa tai tace "Yaya ne yazo ganina."

Yazo ganinki? To ko ganinki yazo sai ki tashi kamar jela? Wai ni yaushe kika koma mara aji ne?

Zeena ta dawo cikin bacin rai ta zauna.

Junaid ne ya shigo.

Sai daya kalli kowa a gun sannan ya zauna ya gaida Hajjo.

Hajjo ta amsa tace "meya kawo sirikina nan?"

Siriki? Ya maimaita hakan a ransa, amma a fili murmushi yai yace "zuwanai nai wata sanarwa."

Sanarwa? Hajjo ta kalleshi fuska a sake, Allah yasa muji alkairi to.

Cikin salo na kasaita da aji ya dago ya kalleta tare da cewa " ni a matsayin danki nake kema, inaso a koda yaushe a dinga daraja abin da yake mallakina."

Cikin rashin fahimta ta kalleshi, yace "shikadai nazo sanarwa, dan ina tsoron abinda zai faru in aka cigaba da wulakanta min abu na."
Ya mike yai sallama ya fita, gaba daya Hajjo ta kasa gane me yake nufi, kallan Zubair tai tace "me yake cewa?"

Zubair ya girgiza kai alamar baisani ba.

Zeena kam ido ta zubamai har ya fita, wani murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace "Hajjo dan Allah ya Junaid bai hadu dayawa ba?"

Kobi takanta batai ba Hajjo ta kalli Ramlatu tace "kinsan me yake cewa?"

Ramlatu ta kalleta tace "Hajjo magana fa ya yaba miki akan abinda kikace kinyiwa Binta."

Shiru Hajjo tai ta tattaro kalamansa sannan ta fahimta.

Hucci ta fara yi kai kace kumurci, Ramlatu ta girgiza kai tace "Hajjo sai dai kiyi hakuri amma Junaid yafi karfin Yarima Zubair." Tuba nake da fadan haka.

Mikewa tai tana huci tai dakinta, da karfi ta bugo kofar wanda sai daya razana su.

Bangaren Azeema ya nufa, tana zaune tana sanarda Safiya abubuwan da za'a bukata na biki, Junaid ya shigo.

Cikin nuna jin dadi ta kalleshi tace "anjima nake tunanin a kiraka mu tattauna."

Kallanta yai yai dan murmushin yake sannan yace "Umma na gode da kula da 'yar can da kikai, da amincewa da ita a matsayin surukarki da kikai."

Azeema jikinta yai sanyi, ji tai bata kyautawa Binta, jin kalamansa yasa tasan tini yake mata a fakaici.

Insha Allahu za'a gyara Junaid.

Godiya nake Ummana.

Kallansa tai gaba daya sai jikinta yai sanyi, Safiyya tace "Junaid tunda ta amince zaka aureta ai tayi kokari, ni kaina nayi mamakin hakan."
Junaid yai murmushi yace "Ai Umma mai san abinda nake so ce ni na san hakan."

Azeema tai shiru dana sani da jin haushin kanta ya kamata......


*********

Lokaci ya karato

A 6angarrn su Zeena kam itadai tana cikin murnarta, duk kuwa da tanajin zafin hadin zama da binta, ganin bintar ma ya gagareta gaba d'aya, dan hajjo gaba d'aya ta hanata zuwa sashen Azeema, amma hanata fita gaba d'aya, kullum tana sashensu Ana mata gyaran jiki irin Na y'an gatan Amare, shi kansa mai gayya mai aikin ya Junaida ganinsa yamata wahala.

****************

Binta kam ta dawo bangaren Azeema, sai dai a yanzu taga canji sosai, dan Azeema da kanta ta sanar da ita auren da za'a hadata da Junaid sannan ta nemi ta kular mata da danta bayan auransu.

Duk da a kasan ran Azeema bawai san Binta take ba sai dai a yanzu tasan ita kadaice mafitarta, dan tasan Zeena ta Hajjo ce dole ne ta kama Binta kafin danta ya zama dan kallo a gareta.


*******

Da wannan aka shiga hidimar biki, ranar laraba akayi kamun daya k'ayatar ainun, Zeena kuma kawai akaimawa banda binta, hadalima bata lek'o wajenba.

Hakan yabama Junaid haushi, yarasa mikuma ake 6oyewa game da bintar, tunda sun aminta ya aureta shi baiga wani abun 6oye-6oye ba kuma.

Dukda mutanen dake cike da sashen Azeema haka yanemi ganinta.

"Barira ki sanar masa zanzo sashensa cna damesa, dan babu ta inda zai iya shigowa nan".

"To ranki ya dad'e.

Barira tazo ta sanarma Azi amsar Azeema. Shima yaje ya sanarma Junaid dake zaune a falonsa yana nazarin wani littafi

Ba tare da ya kalli Azi ba yace, "babu damuwa".

Tashi Azi yai yafita.



**************

Bayan sallar isha'i Azeema ta iso sashen Junaid, a falo ta iskeshi kwance ido a lumshe, sai dai da alama ba barci yakeba, dan yana d'an kad'a k'afarsa.

Sallamarta ta sakashi bud'e idanunsa, sannan ya mik'e zaune sosai. Zama tayi kan babban tum-tum da aka k'awata kwalliyar falon dasu.

"Junaid lafiya kuwa ka buk'aci ganina?".

"Lafiya lau Ummana, barka da dare?".

"Barka dai, ya hidima?".

"Umma kuza'a tambaya ai, ni wace hidima nake?" Yak'are naganar da murmushi. Itama murmushin tamasa.

A nutse yafara magana "Ummana wai Yaya tsarin bikin nan yake?".

"Ban fahimci tambayar takaba?".

'Dan jimm yay yana tunani, saikuma ya sauke numfashi yana gyara zama, "Ummana ina nufin yau kamu Zeena kawai Na gani, kina ganin bayan an d'aura auren mutane suka fahimci ba Zeena ce kawaiba bazasu kalli adalcin wannan masarautar a matsayin mai rauni ba? Hakan kuma tamkar rage darajane, duk mai mulki bazai yisaba saida talaka, Yaya muke tunani idan talakawan suka fahimci mun fifita kanmu sama da su? Anya bazasuji kamar bamu dace muzama masu mulkarsuba?".....

Jin yayi shiru sai Azeema ta sauke ajiyar zuciya, lallai gaskiya Junaid ya fad'a, kuma tagane tayi kuskuren barin jama'a su fahimci sirrinta a wanan Karon....

"Anyi kuskure Junaid, amma namaka ank'awarin ganin gyara a safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu".

Murmushi yamata yana kamo hannunta "nagode Ummana mai share kukana da fahimtar abinda ya cancanta cikin sauk'i".

Murmushi jin dad'in yabon nasa ta Saki, takai hannu taja hanccinsa batareda tace komaiba.

Sun d'an kuma tattauna abinda ya dace dasu kafin tamasa sallama ta koma.


**********

Bangarenshi aka gyara sosai saboda girmansa, daga ciki aka tashi su Harira nan ma aka kara budashi.

Babban shashin mai kunshe da manyan bangare da girma da tsari shine na Zeena.

Binta kuma aka bude bangaren su Hari aka kara girmanshi aka mata nata bangaren, su koma su hari aka maidasu can baya.


Guri yayi kyau da tsari duk kuwa da cewa bangaren Zeena yafi kyau, amma Junaid ko damunsa hakan baiyi ba.......
*********

Abdulsalam kam nata bashi shirin naba Junaid matsayin Galadima, bayan anyi aure.......




*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍*


{32}

A daren ran da akai kamun Zeena, Azeema ta kira Binta tasa Barira tai mata gyaran jikin dan taji kunya sosai da Junaid ya mata magana da kanshi.
Haka Barira da Safiya suka gyara Binta wacce gaba daya ta tabbatar rashin gata ne ya mata yawa, yanzu ace za'ai bikinta har yau Junaid baice mata komai ba? Tun randa yazo gunta tana kwance agun Harira har yau ganinsa ma sai dai daga nesa.

Haka dai take daurewa dan tasan duk duniya batada kowa banda Junaid, sannan kuma tasan ba mantawa yai da ita ba tunda har zai aureta.

********

Zeena na kwance ana murza mata hadin gyaran fata Hajjo ta shigo, kallanta tai tace "ni Zeena kun taba zance da Junaid?"

Gaban Zeena ne ya fadi ta kalleta tace "sau nawa kuma?"

Hajjo tace "ni fa gaba daya gani nake kece kikesan abin nan ba shi ba."

Zeena ta juyo tace "Hajjo ni dai ni nace naji na gani, ke makwan kiyi murna ma 'yarki zatai aure a inda kike amma sai kawo maganganu kikeyi."

Hajjo ta juya ta fita batace komai ba.

Shiru tai a falo ta kalli Ramlatu tace "me kike gani?"

Ramlatu tace "me zai hana kiyi taro na biki randa aka daura auren? Ki gayyaceshi mutane zasu ga yana santa, hakan zaisa adaina yada cewar itace takeso, sannan inba damuwa ki gayyaci waccen kucakar, ki kaskantar da ita."

Hajjo ta jinjina kai cikin gamsuwa tace "Hakan yayi, yanzu ki fara shirye shirye, zan sa a kira Shamaki na sanar dashi."

Da sauri tace to.

**********

A hankali jiki na rawa ta bude mayafin dake lulube agun, zube wa tai kasa da sauri jikinta na kakkarwa, a zabure ta bude idanunta dama tasan mafarki ne, a hankali ta kwantar da kanta jikin gado tare da sakin ajiyar zuciya.

Jin ana kwankwasawa ne yasa tace "waye?" Ta miki jiki a sanyeye.
Daga waje Barira tace "Gimbiya kin farka?"
Azeema tace "eh."
A hankali Barira ta bude kofar, sannan ta zube ta gaisheta tare da cewa "Gimbiya dama Hajjo ce tace "yau bayan an daura aure da yamma akwai taron data shirya."
Azeema tace "taro?"
Eh.
Shiru tai tana nazari dan ta tabbatar akwai abinda yake a kasa.
"Da wani abin ne?" Azeema ta tambaya ganin Barira bata mike ba.
Tace wai harda Binta.

Azeema tace "Hajjo me kike shiryawa?"

*******

Yau karfe 1 na rana aka dauka auren Junaid da Zeena, sannan aka daura auren Junaid da Binta.
Akuma gun ne Sarki yai ma Junaid albishir na bashi sarautar Galadanci.

Gaba daya ido aka zubo masa.

Junaid wanda yasha ado iya ado yana sanye da wata dakakiyar shadda fara, yasha babban riga da rawani, kana ganinsa kaga ango.

Kallan Sarki yai yace "Nagode amma Mai Martaba wannan sarautar bata Zubair bace?"

Sarki yai murmushi yace "Tashi ce amma na fahimci yana bukatar hutu, kaine ya kamata ka wakilceshi shi ya samu ya nutsu yai karatu."

Junaid yai kasa dakai yana nazarin wannan abin dake faruwa.

Zubair dake gefe ya cika ya batse sosai, kallo daya zaka mai kasan lalai an bakantamai rai.

Junaid ne ya daure ya dago ya kalli Sarki, fuskarsa bazaka taba ganene me yake cikin ransa ba.
Murmushi ya saki sannan ya kalli Zubair yace "Tuba nake Yarima, nayi laifi."

Zubair ya kalleshi, dan sam ba wanda yai tsammanin jin haka, kallan mutanen gun yai ya kasa danne bakin cikinsa, yace "bakomai."
Yanda yai maganar ne yasa kowa ya fahimci ransa ya baci matuka.

Junaid ya kalli Sarki yace "Ban isa bijirewa umarnin sarki ba sai dai inaso sarki ya duba rashin jin dadin hakan da Yarima Zubair yaji."

Wato dan ya nunawa mutane Zubair na bakin
ciki shi yasa ya fara mai magana kenan?
Nan Sarki ya kara tabbatar lalai Junaid inbaiyo wasa ba sai ya wargazasu.
Daurewa yai ya kalli Zubair yana murmushi yace "Zubair!"

Zubair yai kasa dakai da sauri yace "tuba nake ranka ya dade bawai ban amince bane."

To yanzu fa?

Da sauri yace "Na amince Allah ya tayashi riko."

Junaid ya kalli Sarki kadan.

Fitowa sukai aka fara tayashi murna, sannan aka kunce rawaninsa aka mai wani na bashi Galadima da akai.
Nan aka shiga busa.

Hajjo na ta bada umarnin taron da za'ai aka shigo mata da wannan bakin labarin.

Ranta yakai kololuwa gun bacci, har ta sabi alkyabba zata fita Zubair ya shigo.
Cikin kumburim fuska tace "dan hauka kana zaune aka kwace mulkin ka aka ba waccen yaran?"

Zubair kamar zaiyi kuka yace "ya zanyi Hajjo cikin mutane fa Abba ya sanar da hakan."

Hajjo ta fara hucci na takaici tace "haka zamu zauna har babban mulkin ma ya kwace kenan?"

Zubair yace "bazai taba yiwuwa ba wannan, yanzu ki barshi in ma munyi fadan mu za'awa dariya."

Hajjo ranta ya kara bacci ta zauna tana nazari.........

*********
Kasancewar Azeema tasan abinda Abdulsalam yake shirin yi shiyasa ko mamaki batai ba, haka suka cigaba da hidima da mutane.

Binta na can bangaren Junaid na da sanda yana yaro saboda gaba daya bangaren Azeema a ciki yake.

Da yamma kowa ya fara shirin zuwa taron da Hajjo ta shirya.
Binta ce ta kalli Safiya wacce ta mika mata kaya tace "muje ki shirya."
Cikin mamaki Binta ta kalli kayan, Safiya tai murmushi tace "ke matar Junaid ce yanzu dan haka martabarshi itace taki."

Haka suka shiga daki da kanta Safiya ta shiryata, mutane sai gulma suke akan Junaid ya auri yarinyar dayazo da ita, wasu suce wacce take kwana a bangarensa da.

Ba karamin kyau Binta tai ba, dan ita kanta batasan tana da kyau haka ba sai yau.
Tayi kyau sosai, atamfashi ta saka mai kyau, sannan aka daura mata alkyabba ruwan kasa tayi kyau sosai da sosai, gashi tasha turaren wuta na tsugunno.

Safoya ta shigo ta sanarda Azeema akan angama shirya Binta, tace "to sai kum dawo."

Cikin mamaki Safiya tace "bazaki ba?"

"Eh, banajin dadi." Safiya tace to.

Barira ta kalla tace "jeki duba ki ga ko Junaid ya shirya."

Nan Barira ta fita.
Junaid na zaune a kasan falansa yana nazarin bashi sarautar nan da akai, wajen bangarensa kuwa maroka ne keta kiraki, Azi ta samu tace "Yarima ya tafi?"

Ina kenan?

Tace "taran da Hajjo zatai mana."

"Oh, bansani ba bari na duba."
Tace "to dan ita Binta har ta shirya."

Azi ya shiga, ganin Junaid a zaune yasa yace "Yarima baka shirya ba?"
Junaid ya kalleshi yace "banajin zani."
Azi yace "to shikenan dan dama Barirace ke tambaya wai Binta ta shirya."

Binta? Ya tambaya cikin mamaki.
Azi yace eh.
Junaid yace "bari na shirya muje."

Murmushi Azi yai sannan yace to.

Daki ya shiga ya cire shaddar nan yasa wata shaddar, haka kawai ya jawo shadda mai ruwan kasa ya saka.

Yayi kyau sosai dan dama Junaid akwai zagi da haiba.

Cikin isa da takama ya fito daga bangarensa, maroka nata kirari.

Dokin da Azi ya fito dashi yahau suka nufi gun taran.

**********

Katan gun taro na masarautar suka nufa, am gyarashi sosai, mutane sun cika agun, da alama har an fara gabatar da shagalin.

Isowar Junaid ne yasa aka bashi hanya kowa ya shiga kallansa.

Junaid ya sauko daga kan doki sannan ya nufi ciki, Azi da sauran hadimansa na take mai baya.

Zeena na zaune cikin shiga ta alfarmar gaske, wanda kudin da aka kashe gun shirya ta ma ba kadan bane.

Tana zaune akan wata had'ad'iyar kujerar mulki, tayi kyau iya haduwa.
Dauke kansa yai daga kanta sannan ya duba inda zsi hango Binta.

Bai ganta ba hakan yasa ya fara sa kafa cikin gun yana dan amsa gaisuwar da ake mai.

Me zai gani? Daga kasan Zeena ya hango binta zaune kan tabarma, Safiya na tsaye itama ranta da alama ya sosu.
Hajjo wacce ta shirya wannan wulakancin ce takalleshi tace "barka da zuwa Ango."

Kallanta yai sannan yai murmushi yace "barka dai Hajjo."

Kusa da Zeena ta nuna mai ya zauna, ya kalleta sannan ya kalli Zeena yace "Ayya Hajjo bayana ciwo yake banajin zama akan kujera, kasa nakeso."

Kasa? Cikin mamaki ta tambayeshi a hankali.
Yace "eh."
Kallan manyan mutanem data gayyata tai sannan tace "Junaid ka daure ka zauna akan kujera saboda mutane."
Mutane? Ya za'ayi? Yanzu kuma naji ma zaman kasan bazan iya ba, komawa nake san yi."

Ido Hajjo t zaro tace "komawa?"
Yace"eh Hajjo ni na kawo kaina kuma inada ikon komawa."

Zeena wacce ta zuba musu ido tana san sanin me suke tattauna wa haka.

Hajjo tace "ni matsayin mahaifiyarka nake kuma na umarceka daka wuce ka zauna."
Yace "to Hajjo zan zauna."

Yana fadin haka ya fara takawa, murmushi Zeena ta saki cikin jin dadi, kallansa tai cikin so tana jin wani dadh na ratsata.

Har yakai jikin kujerar ta kawai ya karasa kan tabarmar da Binta ke kai ya zauna.

Ido aka zubamai, kowa ya saki baki, balle da akaga kayansu iri daya.

Zeena gaba daya jitai kanta ya kulle, Hajjo kam kasa ko motsi tai.

A hankali Binta tace "yaya me kake anan?"

Kusa da kunnenta ya matso cikin rada yace "na jure ganin ana wulakantaki ne dan ba yanda zanyi, yanzu kuwa ke matata ce bazan iya jure ganin ana taba min ke ba, ko wanene kuwa."

Murmushi ta saki wanda gaba daya idan mutane na kansu, Safiya kam tama rasa me zatai, lalai wato Azeema tasan akwai abinda zai faru shiyasa batazo ba.


Tab🙊🚶🏻‍♀️



*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍*

{33}

Gaba daya Hajjo kallan mutanen gun ta shiga yi wanda suke gulma da zunden abinda ke faruwa, Zeena kam hawaye ne taji ya zubo mata ta zubawa Junaid ido wanda ko kallanta baiyi ba.

Hajjo ta kalli Zeena wacce kana ganinta kasan tana cikin tsananin kunci.
Safiya ta daure ta kalli Junaid tace "ya isa haka nan, bari zan maida Binta ka zauna ku rabu lfy, ka gama wulakantasu wannan ma ya isa."

Binta ta kalleshi tace "ni zan koma yaya, kayi hakuri."
Mikewa tai Junaid yabita da kallo suka bar gun, Ramlatu ce tasa dariya tace "masha Allah, dama mun shirya haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login