Showing 69001 words to 72000 words out of 76752 words

Chapter 24 - ZAFIN RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

ayusher   

26 Aug 2024

8580

Umman."

Nan suka fito.

Ramlatu tana gudu ta nufi bangaren Azeema.

Gimbiya na zaune suna hira da Binta, dan Binta yanzu ta sata ta fito falan ta, Barira sai dadi takeji.

Suna cikin hira ne aka fara bushe bushe, Azeema ta kalli Barira tace "Bari duba ki gani meke faruwa? Wannan busar busace ta Sarki."

Nan Fure ta fita, bata dade ba ta dawo ta sanar da Azeema ai wai sarki me yai murabus yaba Junaid mulki.

Fuskarta dauke da tsananin mamaki tace "AbdulSalam din?"

Barira tace "eh."

Shiru Azeema tai dan tasan tabbas ba abinda zai sa Abdulsalam yabar mulkim nan da yake so, sai dai ta tabbatar Junaid ne yasashi dole saboda abinda ya aikata.
Muryar Binta ce ta katseta datace "Haba Bari sai kace wasa ta ya za'ai murabus ba wanda ya sani."

Barira tace "shine abin mamakin, gun a cike yake dam da alama an shirya dama"

Azeema tai shiru idanunta suka ciciko,babban burinta ada bai wuce Junaid ya samu mulki ba amma batasan meyasa yanzu gaba daya zuciyarta a cike take da tsanar kanta.

Shigowar Ramlatu ce yasa ta hade fuska, Ramlatu ta zauna ta gaisheta.

Azeema ta kalleta bayan ta amsa tace "lafiya?"

"Dama nazo wucewa nace bari nazo na gaisheki, na dade banzo na gaidake ba."

Azeema ta dauke kai ko tanka mata batai ba.

Ramlatu tai dariya tace "Matar Yarima ce?"

Barira tace eh, Binta ce ta gaisheta.

"Ina Gimbiya Zeena? Allah yasa bata wahalar dake kinsam yarinyar nan Hajjo duk ta gama sangartata."

Binta cikin mamaki ta kalleta, dan ita ko saninta batai ba kafin tace "ba abinda take min."

Ramlatu tai dariya tace "ko dayake yanzu farko ne na tabbatar......."

"Ya isa haka nan" abinda Azeema tace mata kenan.

Jiki a sanyaye tai shiru, Azeema tace "inkina gama gaisuwar zaki iya tafiya."

Ramlatu wacce taji haushin haka ta mike tana dariya tace "ba laifi, bari na wuce."

Tana kokarin fita ana sanar da isowar Zeena.

Idanu ta zaro kafin ta dan kauda kai.
Azeema ta kalleta sannan tama Barira alamar ta bata izini.

Nan Zeena ta shigo, tsayawa tai cikin mamaki ta kalli Ramlatu wacce yanzun nan fa taganta da Hajjo, Ramlatu tai saurin kallanta kafin tace "nazo wucewa ne shine na shigo mu gaisa, naga mun dade bamu ko gaisa ba."

Zeena tai wani murmushin takaici tace "ko? Wucewar ce naganki yanzu da Hajjo?"

Ramlatu tai kasa dakai tace "eh zan wuce bangarenane."

Zeena ta jinjina kai tace "haka akeso ki bar layin da zai sadaki da bangarenki kiyi zagaye, kin kyauta da kika zo gaidata."

Ramlatu tai kasa dakai, nan tai sum sum ta fice.

Zama Zeena tai ta gaida Azeema, Binta kuma ta gaisheta.

Kallan Azeema tai tace "Umma Karama dan Allah kinsan meke faruwa? Gaba daya na kasa samun nutsuwa, na tabbatar akwai wani abu dake faruwa, duk da Ya Junaid yace kar nai bincike kar na tambaya amma sam hankalina ya kasa nutsuwa."

Idanun Azeema ne a dan ciciko tace "kibi abinda mijinki yace sannan dake da Binta ku tashi ku koma bangarenku, kar wanda ya sake zuwa nan bangaren har sai Junaid yamin hukunci na."

Kallanta sukai a tare, Binta tace "hukunci?"

Murmushi Azeema tai tace "duk mai laifi dole ne a hukuntashi, kada wanda yasa baki akan abinda ke faruwa, ku tashi ku koma bangarenku."

Jiki a sanyaye suka tashi suka fito.

Binta suna fitowa ta kalli Zeena tace "meke faruwa Gimbiya? Ance murabus yanzu Umma tace hukunci."

Zeena tai shiru kafin ta kalli Binta idanunta sun dan ciciko tace "kenan Umma da Abbana sunma Junaid laifi."

Laifi?
Binta Shiru tai tana tunanin kalaman Junaid na rannan.

Zeena ta kalleta tace "wani irin laifi kike tunani?"

Binta ta girgiza kai tace "bansani ba."

Shiru sukai a haka suka koma.



*********

Hajiya inna ta fito daga dakinta dakyar cikin farinciki ta zauna a waje tace "yau ko yanzu na muti Jakadiya hankalina a kwance zan tafi."

Jakadiya cikin jin dadi tace "Barka Hajiya inna, wannan lamari yayi dadi."

Junaid! Hajiya Inna ta fada cikin jin dadi......


******
Ayusher🏌🏻‍♀️


*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍*

{48}

Fure ce ta shigo da sauri, ta kallai Zeena wacce ta zuba mata ido itama.

Fure tace "Gimbiya baki daga cikin gida sunzo tayaki murna."

"Murna? Ai sa bari sai gobe ko?"

Dan tsaki tai sannan ta kalli Fure tace "ke kuma meye?" Dan yanda taga Fure ta zuba mata ido.

Fure ce ta kalleta cikin mamaki tace "Gimbiya yaushe kuka zama kawaye?"

Harara ta maka mata tace "haka kawayen suke? Tashi ki shigo dasu."

Nan ta fita, matan kanen Abdulsalam ne da kuma yan uwa dake zaune anan.

********

Binta tana fitowa ta kali Hadimarta tace "Rali kira min Harira dan Allah."

Raliya tai dariya tace "Ranki ya dade in kina san abu ki baku umarni kawai."

Binta tai murmushi sannan ta shiga ciki itama hankalinta duk a dagule.

Harira ce ta shigo ta gaisheta sannan ta zauna, Binta ta sauko kasa kusa da ita tace "Harira kinji abinda ke faruwa?"

Harira tace "naji sai dai sam na kasa gane meke faruwa."

Shiru Harira tai tana kallan Binta tace "Karki damu, Yarima yasan me yakeyi duk abinda kikaga ya aikata da dalilinsa."

Binta tace "na sani sosai sai dai ina tsoron yana cutar da kansa ne."

Fuskarta dauke da mamaki tace "kamar ya?"

Binta tai shiru dan batasan fadar abinda ke tsakaninta da mijinta duk kankantarsa kuwa.

Harira tai murmushi tace "ki kwantar da hankalinki insha Allah ba komai."

Kai ta daga a hankali sannan Harira ta mata sallama ta fita.

Tanajin yanda ake magana da guda daga bangaren Zeena ita kuma bako mutum daya a bangarenta, mikewa tai ta shiga ciki tana tunanin hukuncin da Junaid ke dauka.

**********


Sai yamma kowa ya watse Junaid ya tunkari bangaren Sarki.

Abdulsalam najin Zagi na sanar da isowar Junaid yaji gabansa ya fadi, sam shi ko sunansa bayasan yaji an fada.

Junaid ne ya shigo ya zauna sannan ya kalleshi.

Abdulsalam wanda a yan kwanakin nan har ya rame ya canza ne ya kalleshi.

Junaid ya kalleshi sannan ya saki wani irin murmushi yace "kayi kokari sai dai saura abu daya."

Kallansa Abdulsalam yai zuciyarsa na tafasa, tari ne ya dan kwace mai yana kallan Junaid.

Junaid yace "a randa akai taron nadi a ranar nakeso ka dau matarka Hajjo ka bar masarautarnan."

Da sauri Abdulsalam yace "muje ina?"

Kafada Junaid ya daga yace "wannan kuma banaji ya dameni."

Gaba daya Abdulsalam ya rasa me zaice, daurewa yai yasan in ya sake bari yanzu ma galaba Junaid zaici a kansa yace "Ragowar matana da kuma Azeema fa?"

Kallansa Junaid yai yace "baka taba jin kunyar zama da matar yayanka wacce kai ajalinsa ba?"

Abdulsalam yace "ni na kasheshi da hanuna?"

Kaikai ajalinsa.

Ita kuma Azeemar fa?

Tanada laifi babba dan haka yanda na ma hukunci itama haka zan mata."

Abdulsalam rai a bace yace "na ajiye mulki yanda kakeso amma duk duniya ba mai rabani da Azeema, in har zan bar nan gidan to lalai sai dai na tafi da ita."

Junaid ya kalleshi, Abdulsalam yace "in komai ya fito ai ba ni kadai zata kwabe wa ba."

Junaid yai shiru yana nazari akansa kafin ya mai sallama ya fita.

********

Bangarensa ya nufa? Yana tafe ana mai buda yana kan doki, mutane na biye dashi, har ya isa bangarensa.

A bakin kofar shiga daga ciki mata ne a cike suna jiransa, Yana shigowa suka fara tayashi murna, yana amsawa.

Jakadiya tada wanda har da ita a ciki tace "Yarima au Sarki zance barka da sauka Takawa!"

Junaid ya daga kai sannan yai ciki.

Zeena wacce ta gama daukan kwalliyarta, tana jiran su fita taje gun Junaid.

Azi Junaid ya kalla yace "Sabisu na nan ne?"

Azi yace "dazu da kana fada ya fita wai dan kokari zai ga gari."

Murmushi Junaid yai suka nufi ciki.

*****

Zubair wanda yake tafe Arim na rike dashi, da kyar suka karasa bangaren Hajjo saboda yanda gaba daya bakin ciki da takaici suka gama galabaitashi.

A kasa daram yaga Hajjo ta baje ta zauna a kasa hankalinta a tsananin tashe.

Kallanta yai bayan ya shigo ya zauna a gabanta, wasu zafaffan hawaye ne suka zubo mai yace "anya Hajjo ni dan Abba ne? Ace yana mahaifina amma gaba daya bai damu dani ba baya sona?"

Hajjo wacce tashin hankalinta ya ninka na Zubair ta kalleshi hankalinta a tashe tace "Zubair gaba daya yau ina tunanin kafin dare zan karasa lahira, banaji zan iya rayuwa a haka, ta yaya ma hakan zai faru?"

Ta fada kanta na wani irin sarawa, tana rike shi.

Zubair yace "Goggo ki tashi kije gun Abba dan Allah, wlh ni kam bazan taba yadda ba."

Ranta a bace ta mike ta shiga dakinta ta kwanta.

Zubair cikin takaici ya mike ya nufi bangarensa.

********

Kallan Harira yai wacce yasa tazo yace "ki sa a hada mana abinci duka a nan, ki sanar dasu suzo nan."

Harira tace "To Ranka ya dade."


Bayan sallar isha'i kuwa Zeena da Binta suka nufi bangaren Junaid, yauma Binta ta yi kwalliya sosai, dukansu sai kamshi sukeyi.

Junaid ya sallami kowa a bangarensa dan yanzu saboda komai ya kusa kammala Sabisu ya koma bangarensu Azi.

Binta ce ta fara isowa, Junaid na ganinta ya saki wani murmushin jin dadi, tun dazu yake san ganin fuskar nan."

Binta ta kalleshi, hannayensa ya bude alamar tazo, murmushi tai a hankali sannan ta zo ta zauna kusa dashi bata rungumenshin ba, kallanta yai ya dan turo baki kadan tare da kauda kansa gefe.

Jiyai ta sumbaceshi a kuncinsa, juyowa yai ya kalleta yace "wannan cin hanci ne?"

Murmushi tai ta dan matso saitin kunnensa tace "in na rungumeka uwar gida ta shigo ince me?"

Hannu yasa kamar mai nazari sannan yace "itama in tazo sai ta rungumeni."

Wata harara ta galla mai tace "da cewa nai bazata rungume kan ba?"

Yace "ba haka kila ce ba?"

Haushi ya kamata tace "Allah zan rama."

Ta fada tare da hade rai.

Sanar da isowar Zeena ne yasa ya kalli kofa, shigowa tai cikin shiga ta isa da matsayi.

Tayi kyau sosai, gefen damanshi ta zauna sannan ta gaisheshi.

Amsawa yai fuskarsa a sake.

Shiru suka danyi kafin ya kalli Zeena wacce gaba daya hankalinta da tunaninta rabi makan tasan abinda ke faruwa.

Hannunta ya kamo ya rike, da sauri ta kalleshi cikin sanyin murya yace "Zeena!"

Jikinta ne gaba daya yai sanyi sai idanu data zuba mai, Junaid yace "Ga Binta nan, inaso ki kula da ita, kece uwar gida sannan matsayinki a masarautarnan mai karfi ne, yanzu komai na rayuwa zai canza, bakoda yaushe zan samu damar kula daku ba dan haka ina rokonki da ki ajiye duk wani halaye naki da kikasan basu da kyau, ke yanzu uwa ce ga mutane dayawa dolene ki zama abin koyi ga mutane, bazan yadda da sakarci da cin zarafi ba kamar yadda kika saba a baya."

Hawaye ne suka zubo mata ta daga kai alamar to.

Junaid ya saketa sannan ya kalli Binta wacce gaba daya jikinta yai sanyi, yace "Binta!" Kallansa tai ya rike hannunta yace "kece karama, banasan wani abu daya danganci rashin kunya ko wani batanci daga gareki, duk da nasan halayenki sai dai inaso ki kiyayi kanki daga biyewa mutanen da zasu kawo miki gulma da kuma hadaku da mutane."

A hankali Binta ta daga kai alamar fahimta.

Murmushi Junaid yai sannan yace "muci abinci?"

Zeena ce ta kalleshi tace "Abba yama laifi ko?"

Yanda tai tambayar ne yasa ya kalleta, saboda tambaya ce da aka yishi cikin shakkar amsar da zataji."

Yanda take kallansa yasa yasan a tsorace take yace "karkisa irin wadan nan abin a ranki, Abdulsalam mahaifinki ne ki daukeshi a fuskar da kika sanshi, nima zan daukeshi a fuskar dana sanshi."

Kallanta yai sannan ya kalli Binta yace "Bismillah!"

***
Ayusher🏌🏻‍♀️

*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍*

{49}

Kasancewar ranan kwanan Zeena ne bayan sun gama cin abinci Binta ta musu sallama ta nufi sashenta.

Zeena tasa su Fure suka kwashe kwanuka, kallan Junaid tai wanda yasashi kallanta yace "me kike san cewa?"

Tambaya nake sanyi kuma bansan ta yanda zanyi ba? Kasan haka na taso magana ina fadarta ne daga raina, sai dai yanzu nasan dole ne na dinga sanin abinda zan fada kafin ya fito daga bakina."

Cikin jin dadin kalamanta yace "menene?"

Idanunsa ta kalla wanda ke mata kwarjini ga so da take masa har cikin jikinta tace " Hajjo......" ta kasa kuma karasawa sai kasa da idanunta datai, jitai kwalla tana neman zubo mata, haka kawai jikinta ke bata laifin Abba mai karfi ne tunda har ya iya ajiye mulkinsa saboda shi.

Idanunta a runtse tana kokarin maida kwallarta ne taji hannunsa akan fuskarta gaba daya jikinta ne ya amsa, a hankali ya dagota ta kalleshi, da kyar ta kakaro murmushi ta mai wanda suka kara bayyana kwallarta dake neman zubowa, yanda ya zuba mata ido ne yasa kwallar suka gangaro a kan hannunsa.

Idanunsa ya lumshe sannan ya sake kallanta, murmushi ta sake yi na dauriya tace "Yaya na sani ni mai laifi ce, ma taso ba ruwana da halin da wani zai shiga a dalilina, wannan banzan halin nawa ya ja mutane dayawa sun shiga wani hali ciki hadda kai, banda bakin da zan nemi ka saukaka ma mahaifiyata da mahaifina......."

Wasu kwalla ne suka sake gangarowa akan hannunsa, wannan lokacin shine karo na farko dayaji Zeena har ransa, ya aureta ne saboda burinsa ma auran Binta, san Binta a jininsa yake tun baisan kanta ba take da babban matsayi mai karfi a ransa, sai dai a wannan lokacin ya fahimci Zeena ta samu guri a ransa, dan tabbas tausayinta yakeji sosai, ya sani yanzu shi kadai ne da ita, dole ko dan haka ya boye abinda mahaifinta ya aikata in ba haka ba mutane ma kinta itama zasuyi.

Hannu ta dago tana neman share hawayenta, hannunta ya rike da daya hannunsa, jitai zuciyarta na kara raunana, kallansa tai tana san sake magana kuka ya kwace mata.

Jawota jikinsa yai ya rungumeta, sai datai kuka sosai sannan ta daina, ba tare da yace mata komai ba, sai data gama sannan yace mata "Karki damu komai zaizo da sauki insha Allah, sannan in har kika canza halayenki komai naki zai canza, kada ki manta na fadamiki kece ido na nacikin gida, dole ne ki dinga sanin abinda zaki dinga yi daga wannan lokacin."

Kai ta daga tana kwance a jikinsa tace "insha Allah bazan taba baka kunya ba."

Murmushi yai, dagowa tai a hankali ta kalleshi sannan itama tai murmushi tace "nagode da ka bani dama."

Mikewa yai sannan ya mika mata hannunsa, wani irin dadi ne ya kamata ta mika masa nata hannun cikin wani irin jin dadi da ita kadai tasan yanda takeji.

Hannunta ya kama suka shiga daki, a bakin gadan ta zauna cikin kunya, tana cewa "yau na fara shigowa dakinka."

A hankalinya taka zuwa inda take ya zauna a gefenta, hannunsa dataji ta ratsin cikinta ne yasa ta dan rike numfashinta tare da saukeshi a hankali.

Kansa ya sako ta kafadarta yace "garin ya ya?"

Gaba daya ta kasa magana saboda wani irin yanayi data tsinci kanta a ciki, dan juyowa tai ta kalleshi, hannu yasa yai baya da ita a hankali ta kwanta akan gadon, idanunta na lumshe sai gabanta dake wani irin faduwa.

Bakinsa ya sa a cikin nata................

**********


Washegari!

Cikin tsananin kunya ta tashi, bakowa a dakin hakan yasa ta dinga tuno abinda ya faru jiya tana dariya tare da rufe fuskarta, da alama da sukai sallar asuba tare ta koma bacci lokacin ne ya fita.

Mikewa tai zuciya daya, jin zafin datai ya ratsa ta ne yasa cikin kunya ta koma ta kwanta.

Junaid kam bayan ya gama karatunsa yana ganin gari yayi haske ya mike ya nufi bangaren Azeema.

Gaba daya ba kowa a hanyar dan duku dukun safiya ne, ita kanta Azeemar tayi sallah kenan tadan kishingida a inda ta kwanta din, barira ce ta leko ta sanar da ita isowar Junaid.

Mamaki ne ya kamata matuka, jitai baccin idanta ya ware ta kalleta tace "ya shigo."

Da sauri ta gyara zamanta, gabanta na faduwa.

Junaid ya shigo ya zauna sannan ya gaisheta, kallansa tai cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa tace "Junaid!"

Kallanta yai bai amsa ba, murmushi tai tace "banyi tsammanin ganinka ba."

Fuskarsa a hade take babu alamar fara'a a tattare dashi, kallanta yai yace "nazo ne na sanar dake abubuwa guda biyu."

Jikinta a sanyaye ta kalleshi tace "inaji!"

Nasan kinsan abinda ya faru kin kuma san jiya Sarki ya ajiye mulkinsa, daga yau har zuwa sanda xa'ai nadi bazan sake cewa komai ba, sai dai ina so kisan daga wannan lokacin zan yanke hukunci akan abinda kika aikata a dalilin san zuciyarki.

Azeema ta daga kai cikin dana sani tace "nagode Junaid."

Bai amsa ba yace "mijinki nace ya bar masarautar nan shida matarsa yace sai dake zai tafi."

Fuskarta ta hade tace "ni?"

Junaid ya mata kallan eh, haushi ne ya kara rufeta tace "zan dau matakin wannan, ma tabbatar wannan me kadai abinda zan iya na taimakeka, ko da kuwa hakan ya kasance na bi shi ne to lalai zan tafi dashi dan samun sauki da kwanciyar hankali a masarautar nan."


Kallanta yai yace "Ta yaya kika bari san zuciya ya rufe miki ido? Kinsan yanda nake ji a duk sanda na sa abinci a bakina? Ina tuna ina ci ne a maimakon mahaifina, ko me nakeyi abinda nake tunani kenan, taya a cikin mutanen duk duniya ace ke? Ta ya......"

Idanunsa ya runtse cikin takaici.

Azeema ta share ta kasa cewa komai, idanunsa ya bude yace "ina sauraran yanda zaki sa ya bar masarautar nan."

Kallansa tai cikin wani yanayi, mikewa yai ya mata sallama ya fita.

Da kallo ta bishi har ya fita, tace "Abban Zubair da ace kana da rai na tabbatar da sai kafi kowa alfahari da yanda danka yake, wannan shine halin cikaken Sarki, karya kuskura ya karaya kar kuma ya ragawa duk wani mai laifi koda kuwa mahaifiyarsa ce."

Murmushi tai tana mai jin haushin kanta.

******


Dare........
Junaid wanda ya dawo daga fada sunyi karamin zama akan wata shari'a wacce yau ya fara aikinsa.
Daga nan sukai sallah ya taho, kallan bangaren Binta yai sannan yai murmushi yace "Azi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login