Showing 21001 words to 24000 words out of 76752 words
karama barka barka."
Azeema tai murmushi duk da daurewa kawai tai saboda mutanen dake gun, sannan ta zare hannunta suka gaisa da Hajjo, tare da nuna mata gurin zamanta.
Hajjo ta kalli Zubair tace "muje ka gaisa da kanin naka."
Ta fadi haka ne dan ta batawa Azeema rai.
"Oh hakane fa ashe Yarima Zubair baiga kaninsa ba."
A tare suka jera inda Junaid ke zaune mutane duk wanda yazo sai ya gaisheshi sannan yake komawa ya zauna.
Suna karasowa Azeema ta kalleshi tace "ka gaida Uwar gidan Sarki."
Junaid ya gaishe ta fuskar sa a daure, murmushi ta sake tana cewa lale lale Junaid.
Kallan Zubair tai tace "babban dan sarki."
Junaid ya mika mai hannu, suka gaisa.
Ta bude baki zata gabatar da Zeena tai saurin cewa "ni ai ka sanni."
Junaid sai yanzu ya kula da ita, kallo daya ya mata ya juya.
Wannan abu ya bata mamaki, dan har kasa boyewa tai tace "Ya Junaid!"
Kallanta ya sakeyi tace "baka ganeni bane? Duk da nasan na bata maka amma a karshe ai nice........"
Hajjo ce ta tabata alamar tai shiru, fuskar ta ce ta canza dan da a nishadance tazo gun amma abinda ya mata yasa taji ranta ya baci.
Azeema ce ta nuna ma Azeema gefen Junaid ta zauna, Zubair ya zauna a gefenta, ita kuma ta zauna a dayan bangaren Junaid, Zeenatu na gefenta.
Zeena sai cika take, me mutumin nan yake nufi da kallan da ya mata? Kamar irin yaga shara? Ai ko me tamai bada saninta bane balle ya tuhumeta.
Haushin kayan data saka da bata lokacin datai gun kintsawa ne ya kara kular da ita, meyasa to takesan ta birge Junaid? Tambayar data zo mata kenan.
Da sauri ta kalleshi ya zubawa shirin dawakan da ake ido sai dai inka kula dakyau zakaga idansa ba a gun yake ba.
A hankali ta bi inda yake kallo, hanyar shigowa taga yana kallo, a fili tace "wani yake jira?"
Azeema ta kalleta tace "wa?"
Zeenatu tai murmushi tace "naga kamar kofa yake kallo."
Azeema ta kalli Junaid sannan ta kalleta tace "wasa yake kallo"
Zeena ta kara kallansa tace hala ni naga daban.
Ta fada itama tare da kallan masu wasan.
Gaba daya hankalinsa ya kasa nutsuwa sam abinda ake ma bai sani ba.
Busa da taken isowar mai martaba ce yasa Azeema cikin wani farinciki.
Kallansa tai tacemai "mai martaba ya iso."
Hajjo ta kalli Zubair tace "me yake anan shi kuma?"
Zubair yace "Hajjo karki nuna wani abin."
Kallan Azeema tai wacce ke murmushin jin dadi.
Shigowar mai martaba ya dau hankalin mutane,dan ba wanda yai tunanin zuwansa.
Kusa da Junaid fadawan suka je, Azeema ta mike tana godiya, Sarki ya kalli Junaid yai gyaran murya wanda yasa kowa yin shiru.
Kallan Junaid yai yace sai kuma ya dan murmusa yace "ganin bansan me kake so ba yasa nai tunanin abu daya."
Ya kalleshi yace "nama alkawari a wannan guri na baka izini ka zabi duk wani abu guda daya da kakeso, ko menene shi ni kuma na ma alkawarin yimakashi indai inada hali."
Junaid ya mike yai godiya nan aka hau tafa musu ana taya Junaid murna, Hajjo kam ta cika harta gama batsewa, yanzu kam ran Zubair ma ya baci dan hannunta ya dunkule da karfi.
Kowa ya gama sanin mezai faru domin abu ne mai sauki, Junaid zai nemi abashi mulki kuma dole ne Sarki ya bashi tunda alkawari yai, wannan al'amari ya batawa magoya bayan Hajjo da danta rai, Azeema kam wani dadi ne ya kamata ta sake yima Sarki godiya.
Sarki ya juya ya bar gun, Zeenatu tai shiru itama tana tunanin abinda ya faru a lokacin, me mahaifinta ke nufi.
Sarki na juyawa Junaid ya kalli Azeema yace "bari ma duba Azi da alama wani abin ya samu Binta."
Bai ko jira tayi magana ba ya juya da sauri, bayin dake kula dashi sukabi bayansa.
Kallan Junaid mutanen dake gun sukai, ina zaije bayan wannan taran anshiryashi ne saboda shi?
Safiya dake gefe ta mike da sauri dan ta tareshi, sai dai kafin ta karasa yabar gun, ganin kar mutane su ankara da halin da ake ciki yasa ta wayance da zuwa gun Azeema wacce ta cika fal a kasan ranta, Zeenatu ce ta mike da sauri tana kokarin fita daga gun, da alama binshi take san yi taga ina zashi haka, muryar Hajjo taji tace "ina zaki?"
Kallan Hajjo tai sannan tace "kaina ke dan......"
Gun zamanta ta nuna mata da kanta, hakan yasa ta koma ta zauna fuska a hade.
Azeema ce ta mike, cikin nuna jin dadinta da wadanda suka hallari taran sannan ta sanar dasu wasani kala kala da za'a gabatar nan gaba tare da basu hakuri akan Junaid yadanje ganin wanine amma yanzu zai dawo.
Azeema ta kallo Safiya tace "Barira har yanzu bata zo ba ita ma?"
Tace "eh bari na dubota"
Kiyi masa kafin a ganshi da yarinyar."
Yarinya? Safiya ta tambaya, Azeema ta mata alama dataje kawai, juyawa tai ta fita, Zeena da kunnenta ke makale agun taji kalmar yarinya da aka ambata amma bata fahimci me ake nufi ba.
Yarinya? Abinda ke yawo akanta kenan......
Junaid kam yana fita bangaren Azeema yaje, sai dai ba kowa a bangaren, hakan yasa ya nufi nashi bangaren, yana zuwa a bakin kofar shiga ma yaga Hari yace "Hari tana ciki ne?"
Hari hankali a tashe tace "Yarima an rasa inda take."
Idanunsa ne suka fito alamar tsantsan mamaki, hankalinshi a tashe yace "ba'a ganta ba kamar ya?" Yanda yai maganar kadai zaka san hankalinsa ya gama tashi.
Harira tace "ina zaune Azi ya shigo shida Barira tagun Gimbiya wai suna neman Binta, ganin bata nan shine suka rabu zuwa nemanta ni kuma na tsaya anan ko zata zo."
Bai kara tofa komai ba ya juya hankali a tashe, Hari na kiransa amma inaa baibi ta kanta ba, bayinsa ne suka bishi a baya.
Yama rasa ta ina zai fara neman nata ganin yanayi guri ba kadan ba, tunda gashi ko Azi bai gani ba bare Bari.
Haka sukai ta bi suna nemanta, itama Safiya ta fito da tata tawagar suna neman Junaid su kuma.
Gaba daya jikinsa ya gamayin sanyi gani yake ma ta bar masarautar ne, yana tafe yana dana sanim dawowarsa nan, danshi bai ga amfani dawowarsa cikin daula ba ita kuma ta koma ita kadai.
Wata bishiya ya gani, ya tsaya tare da kura mata ido yana tunanin yanda suke zama a bayan gari, yana saman bishiya ita kuma tana kasa suna hira.
Baisan sanda murmushi ya bayyana a fuskarsa ba dan gani yake kamar a wannan lokacin akeyi.
Harya juya yaji alamun ana cilla dutse karami.
Da sauri ya leka bayan bishiyar, tana zaune rike da kananan duwatsu tana cillawa daga inda take.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya saki tare da jingina da jikin bishiyar.
Binta jin yanda yaja ajiyar zuciya ne yasa ta juyo ta kalleshi.
Idanu suka kurama juna yana daga jikin bishiyar ita kuma tana zaune.
Kuka?
Me akamin da zanyi kuka?
To ya naga idanki haka?
Tace "kawai na gaji ne."
Me kike anan?
Tunani?
A tare suka saki murmushi wanda ya bayyanar da begen juna da sukey.
Matsowa yai kusa da ita ya zauna yace "bata kikai?"
Ta dan harareshi tace "eh mana garin neman wani."
Dariya yai yace "Ahhh yazanyi da Bintar nan banaji zata ita yini bata ganni ba"
Dariya tai itama tace "Ahhhh ya zanyi da Ya Junaid banaji inyaga bai ganni ba zai samu nutsuwa."
Yanzun ma a tare sukai dariya kafin tace "Allah yaya wannan gidan naku yai girma."
Yace "bakya sanshi mu koma?"
Kallansa tai a ranta tace ta ina zan sake rabaka da iyayenka?
A fili tace "in nace mu koma zaka yarda?"
"Kina musu? Kin dai sanni ko?"
Da sauri tace "wasa nake Yarima, ban isa ba."
"Kin tsorata kenan?"
Tana dariya tace "tuni ma."
Mikewa yai yace "muje."
Mikewa tai suka fara takawa a tare, suna tafe suna hirarsu yana bata labarin abinda akai batanan duk da shima bakomai ya fahimta ba.
Suna shawo kwana Safiya ta hangoshi, da sauri ta karasa, tace "Junaid kazo ka koma, mutane na nemanka, karsuyi zargin wani abin."
Kallanta yai yace "Ba'a gama ba?"
Tace "eh karkasa mutanen da sukazo dominka suji ba dadi."
Ta karasa tare da kallan Binta.
Yarinyar dazu?
Junaid ne ya kalli Binta yace "muje?"
Kayan jikinta ta kalla, sai a lokacin ta kula da irin shigar dayai da kuma irin shigar da Safiya tai, jitai tasha jinin jikinta, ta kalleshi tai murmushi tace "a'a kaje ni zan jiraka a inda ka ganni yanzu."
Kai ya girgiza alamar a'a sannan yace "sai dai in mu tafi tare ko ki zauna gun Hari."
Safiya ta kalli yarinyar itama cikin rashin jin dadin wannan abu, wacece? Ina ya samota? Da alama soyayya ce mai tsananin karfi tsakaninsu wanda ita kanta ganinsu na farko tare yasa ta fahimci haka, tab lalai da matsala......
Muryar Binta ce ta katseta tace "zan jira gun Harira."
Nan suka karasa bangarenshi sai dayaga ita da Harira sun rike hannu sun shiga sannan ya juya.
Harira na rufe kofa ta jawo Binta ta rungume, wanda jin haka yasa Binta sakin kuka, tabbas yanzu kam jikinta ya fara bata Junaid ya mata nisa, yafi karfinta.........
*Ayusher.....*
*ZAFIN RANA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*NA Ayusher Muhd*
*Shafi Na Goma Sha Bakwai*
Azeema ce ta zauna a bakin ta wuce ciki bayan ta gama sallamar da jama'ar ta, tana shiga ta zauna a gefen gado cikin bacin rai.
Safiya ce ta turo kofar a hankali ta shigo, kallanta Azeema tai tace "ya wuce?"
Safiya tace "nayi nayi ya taho nan yace ya gaji ne amma ni nasan saboda yarinyar nan yake san komawa."
Safiya ta karaso tace "wacece wai?"
Azeema tace "ina ma na santa? A can inda suka taso ya hadu da ita."
"Yanzu haka zamu bar yarinya mara asali tana juya Junaid? Taya zamu dawo da abinda muka rasa hannunmu yana haka?"
Azeema ta kalleta a hankali ta saki wani lalausan murmushi wanda Safiya tace "Umma me kike tunani?"
Kallanta tai tace "ke a naki tunanin Junaid nada wayau a wannan lokacin?"
Tace "bangane ba."
Azeema ta murmusa sannan ta mike tsaye tace "baisan komai ba, banda ita a wannan lokacin, me kike tunanin zai faru in aka kamata da gagarumin laifi?"
Safiya tace "bangane ba, hankalinsa ne zai tashi?"
Azeema ta kalleta sannan tai ajiyar zuciya tace "basu kwana biyu zan dau mataki a na ukun, kwana biyun zan barshi ne yai bankwana da ita."
Safiya ta kalleta dan sau da dama in Azeema na magana ba komai take ganewa ba.
Jin kamar ta sauke nauyin dake kanta ne yasa ta mike ta shiga toilet.
Safiya ta bita da kallo.
********
Binta ce zaune Hari na taje mata kai, Hari tace "hanzu kin ware da kikai wanka?"
Kai ta daga tana murmushi tace "Bansan ya akai naji kuka yaki daina zuwa min ba dazu."
Hari tai murmushi tace "Binta!"
Naam
Hari tadanyi shiru kafin tace "sai kinyi hakuri dan rayuwar masarauta ba daya take da rayuwar da kika sani ba, sannan dole sai kinyi hakurin janye jikinki daga gun Junaid inba haka ba daga ke har shi kuma bazaku tsira ba."
Kallanta Binta ta juyo tai tace "bangane ba Hari."
Hari ta daure mata kanta tace "bazaki gane ba duk bayanin da zan miki sai dai inaso ki kula da mutanen masarautar nan, karki yarda da kowa inba Junaid."
Binta ta daga kai alamar fahimta sannan tace "Mahaifiyarsa fa?"
Hari ta kalleta tace "itace mace ta farko da zaki kula da ita, dan kowa ansan cikinsa amma ita ba wanda yake sanin nata, sannan ba sarauniyar dazatai murna da danta ya kwaso mata mace wacce ba yar mulki ba irinki"
Binta cikin rashin fahimta tace "ni ai tare muka taso."
Hari ta mike tace "da alama an gama taran naji masu busa sun daina."
Binta na kokarin fitowa Junaid na shigowa bangaren.
Daga nesa ya kalleta cikin jin dadi, gashi tai wanka ta sa kaya duk da kayan ta ne nacan amma tayi kyau.
Fuskarsa dauke da murmushi yake kallanta harta karaso inda yake.
Tace "wai harkun gama?"
Fuskarsa ya canza yace "ko na koma?" Yai maganar yana neman juyawa, da sauri tace "wasa nakeyi."
Kallanta yai yace "Muje?"
Kai ta daga suka nufi cikin kilisarsa yana nuna mata.
Sannan yace "dazu na tafin miki da abu amma Azi ya manta inda ya ajiye saboda nemanki da akai tayi."
Tace "ina binka bashi."
Dariya sukai a tare.....
**********
Ran Hajjo yakai matuka gun baci dan abinda akai a tarancan ba karamin bata mata rai yai ba.
Kallan Zubair tai tace "kaga abinda nake ce maka ko? Idan har bamuyi da gaske ba yan kallo za'a barmu a gidan nan."
Zubair ya kalleta shikanshi abinda ya faru ya bata masa rai, yace "Amma Hajjo abinda mai martaba yai dazu ya kyauta?"
Ramlatu wace ta biyesu ce ta kalli Hajjo tace "sai fa mun dage inba haka ba komai zai lalace ne ba tare da mun shirya ba."
Hajjo ta kalleta sannan tace "Zubair jeka zan nemeka."
Nan Zubair ya mike ya fita, Hajjo ce ta maida dubanta kan Ramlatu tace "kin samo yanda za'ai?"
Ramlatu ta kalleta tace "karki damu ina tunanin ido zamu zuba komai zai wakana ne in muka sa hannu kadan."
Hajjo tace "me kike nufi?"
Murmushi ti sannan ta kara matsowa tace "kinsan ya taho da yarinya daga can inda ya taso?"
Cikin mamaki Hajjo tace "yarinya kuma?"
"Eh dazu bakiga ya fita ba ana taro, haka kawai jikina yaban akwai wani abu shine na tura abi bayansa."
Hajjo cikin kaguwa tace "sai akai ya?"
Ashe yarinya yake nema
Hajjo mamaki karara ya bayyana a fuskarta tace "meye tsakaninsu?"
Ramlatu tai dariya tace "meye tsakanin mace da namiji ai ko daga yanda ya mike yabar gun alamace ta tanada babban matsayi a gunshi."
Wata irin dariya Hajjo ta saka wanda ki kaina ban taba jin tayi dariya haka ba, har kwallace ta taru a idanta sannan tace "zanso ganin halin da Azeema ke ciki."
Ramlatu tai dariya itama tace "shiyasa zamu taimaka kadan muja baya muyi kallo."
Hajjo tace "kisa a sanar da cewar Junaid ya taho da mata daga can tana zaune a bangarensa."
Ramlatu tace "angama Hajjo."
Dariya suka sakeyi, Hajjo tace "ashe fadan ba namu bane, tsakanin uwa sa d'a za'ai."
Ramlatu tace "sosai mu namu ido, har na kosa naga abinda zai faru."
Hajjo tai murmushin jin dadi tace "nima."
Zeenatu dake tsaye a kofa zata shigo ne taji suna zancen ta juya ranta a bace tana cijen lebe, yarinya? Itace kenan wacce Azeema ke magana dazu?
Tana shiga bangarenta ta wuce daki ta rufe kofa cikin takaici da jin haushi, shiyasa Junaid ko kallan mutumci bai mata ba dazu kenan?
Tabbas sai ta dawo da hankalinsa kanta, shiru tai kafin tace meye nawa nasan kaida hankalinsa kaina?
Shiru tai tana tunanin sa tun daga sanda yazo a matsayin bawa har zuwa wannan lokacin data ganshi.
Idanu ta lumshe kafin ta kifa kanta kan gado, tabbas sam Junaid take kuma ta riga tayi alkawari duk sanda ta samu namijin da takeso ko za'a mutu sai ta sameshi.
****************
Yau wani irin nishadi ya tashi dashi, fitowa falansa yai dan yaji motsin Binta, kallanta yai cikin jin dadi yace "kin tashi?"
Ta kalleshi tace " ya akai kasan nice?"
Murmushi yai sannan ya zauna yace "me kikeyi?"
Gyara
Alama ya mata datazo ta zauna, nan ta matso ta zauna tare da kallansa tace "menene?"
Yace "fadamin zakiyi ya akai ranan? Ya akai su Sarki da Umma sukaje can?"
Ajiyar zuciya tai sannan ta fara bashi labari.
Kallan bakinta kawai yake tanata magana, murmushi kawai yakeyi.
Safiya wacce tazo dan suyi sallama ta tsaya a jikin kofa, jin yanda abin ke mai dadi ne yasa tasan tabbas da matsala, kwankwasa wa tai sannan ta shiga.
Binta na ganinta ta mike da sauri, Safiya ta kalleta Binta ta mike zata fita, Junaid yace "ina zaki?"
"Harira ke nemana."
Tana kaiwa nan ta fita.
Safiya ta zauna tana cewa "ko kunya ta take?"
Yace "kila dan tanada kunya gata batada saurin sabawa da wanda bata sani ba."
Safiya tace "hakane, zan wuce ne nace bari nazo dan nasan ba zuwa zakai ba."
Yace "a'a bansan zaki wuce ba da zanshigo."
Ta kalleshi cikin kulawa tace "Junaid!"
Kallanta yai bai amsa ba, tace "dan Allah ka dinga zuwa gun Umma, sannan kayi kokarin sakin jiki da ita, bakasan tashin hankalin data shiga na rashinka ba."
Kai ya jinjina alamar gamsuwa sannan tacigaba "Umma duk duniya bata hada sanka da kowa, kowa yasan haka, kai kanka sanda kana karami sanda kake mata daban ne, ya kake tunanin takeji yanzu gaka a kusa da ita amma Kamar kana nesa da ita?"
Junaid yai shiru sai dai yanzu ya fahimci lalai bai kyauta ba, tace "kayi kokarin canzawa dan Allah."
Insha Allah!
Abinda yace kenan, ta mike tace "zan wuce."
Nan ya fito har waje ya mata sallama, akan sai ta taho da yaranta dan ya gansu.
Gana fita taji ana gulma akan Junaid ya taho da mata daga can wasu har da kari wai tana da juna biyu.
Hankalinta ne ya tashi ta nufi bangaren Azeema.
A zaune ta tadda ita akan kukerarta.
Safiya ta kalleta tace "Umma kinji abinda ke faruwa?"
Azeema ta kalleta tace "naji, ynzu Barira ta jiyo a waje."
Safiya ta zauna cikin tashin hankalu tace "amma ya naganki haka?"
Azeema ta kalleta sannan ta dau madarar dake gefenta ta sha sannan tace "kin manta na basu kwana biyu?"
"Wani kwana biyu Umma ana cikin wannan yanayin?l
Azeema ta lumshe idanunta kadan sannan ta ajiye cup din tace "ki gaida Mahmud."
Safiya ta zuba mata ido, kamar zata sake magana sai ta fasa, mikewa tai tare da yin sallama ta fita.
Azeema ce ta kalli Barira tace "matsan kafata wajen yatsuna."
Barira ta kalli kuyangar dake gefenta tai saurin matsawa ta fara matsa mata.
**********************************
*ZAFIN RANA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*NA Ayusher Muhd*
*Shafi Na Goma Sha Takwas*
Kankace zance ya gama karade masarautar nan, ta ko ina zancen da ake kenan, wasu sunce ma ciki gareta, a cewar wasu ma wai ta haihu sun boye dan ne, zance dai kala kala.
Azi ne ya shigo da saurinsa