Showing 36001 words to 39000 words out of 76752 words

Chapter 13 - ZAFIN RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

ayusher   

26 Aug 2024

8577

Yau da wuri ya shirya, dan yanason zuwa sashen Umma akan maganarsu ta jiya Na sanin tarihin masarautar, dakuma yagama ji yana buk'atar ganawa da mai martaba akan za6in damar daya bashi.

Shiga yai ta alfarma, daka gansa kaga jinin sarauta na asali, dan akwanakin da yayi a masarautar komai nashi ya canja, ya canja d'abi'unsa sosai tamkar yanda ya lura mahaifiyarsa Na buk'ata. Shi kansa kuma ya gamsu da tsarin nata d'ari bisa d'ari.

Da mamaki yake bin kayan karin kumallo da aka shirya masa a falonsa, yay tsaye ya zuba musu ido kamar yay gamo da abin kallo. Ganin yarasa amsa saiya kwala kiran Azi.

Da hanzari Azi ya k'araso yana risinawa "Barka da safiya yarima".

Kai Junaid ya jinjina masa, sannan yay masa nuni da shiryayyun kwanikan abincin batare da yayi magana ba.

Azi yad'an kuma risinawa yana murmushi "Ranka ya dad'e ai gimbiya ce takawo tare da kuyanginta".

"Gimbiya?" Junaid yafad'a cikin sigar rashin fahimta'.

Fahimtar hakan da Azi yayi saiya fad'ad'a murmushinsa "Ranka ya dade Gimbiya Zeena nake nufi, dazu aka aka kawo."

Bak'aramin ware fararen idanunsa yayi akan Azi ba, yabud'e baki zaiyi magana saikuma yay shiru, ya kauda idonsa ga kwanikan yana fad'in "Muje sashen Ummana".
Da sauri Azi yace "Yarima Abincin fa?"

Kallansa Junaid yai wanda yasa shi yin shiru.

Kai Azi ya jinjina.


*********


Tunda suka fito bayi keta zubewa suna gaisheshi, iyakarsa d'aga musu hannu. Sun kusa shiga sashen Umma yace, "Har gulman ya ishesu?".

Azi dabai fahimtaba yace, "Yarima gulma kuma?".

"Uhm"
Yafad'a a tak'aice.

Murmushi Azi yayi, dan yanzu ya gane miyake nufi, kafin yabashi Amsa sun iso sashen Umma.

Babu dad'ewa da sanar da isowarsa barira ta sanarmasa da izinin shiga inji Azeema.

Yayi taku biyu zai shiga rumfarta idonsa ya sauka ga Binta dake hidimar gyaran falon.

Wani Abu yaji ya gangaro tun daga mak'oshinsa zuwa yatsun kafarsa, yaushe raban da ya ganga?amma saiya danne, yakuma basar tamkar bai gantaba.

Hakan yabama binta mamaki, sannan yayima barira dad'i. Kamar yanda sauran bayin suka zube suna gaisheshi haka itama binta tayi, hannu ya d'aga musu kawai yay gaba, hankalinsa duk yanakan binta daya lura yanayinsa ya tsoratar da ita.

Har cikin d'akin Azeema yashiga bisa jagorancin Barirah, Azeema na kishingid'e bisa dardumar tsakar d'akin, littafine da abin rubutu a hannunta.

Zama yay d'an nesa da ita kad'an yana fad'in "Barka da safiya ummana"

Tai k'asaitaccen Murmushinta danjin yanda ya kira sunanta, hakan namata dad'i ainun, cikin lumshe idanu ta amsa da "barkan ka dai Junaid, ina fata katashi lafiya?".

"Alhmdllh".

Zamanta ta gyara sosai tana kallonsa, saikuma ta d'auke kanta tana kiran barira.

Da sauri Barira ta shigo, batare da Azeema ta kalleta ba tace, "Yauma ahad'amin karin kumallo tare da Junaid".

"Angama ranki ya dad'e, amma a ina za'a shirya?".

Kallon Junaid Azeema tayi alamar jin ta bakinsa. Ya d'an murmusa sanann yamata alama da nan cikin d'aki.

Itama murmushin tayi, sannan ta kalli barira, nuni taimata da nan ta d'auke kanta.

Bayan fitar Barira Junaid ya gyara zamansa, kansa a k'asa yace, "Ummana idan abu nada daraja bai kamata a daraja duk abinda ya dangancesa ba?".

Shiru Azeema tayi tana kallonsa da juya maganarsa, saikuma tai murmushi cikeda k'asaita, tad'an sauke numfashi tana kuma kishingid'a "Gaskiyane Junaid, lallai za'a gyara".

Baice komaiba sai d'an d'ago ido dayay ya kalleta, tai masa murmushi.

Tsaf barira da kuyangi biyu suka kammala shirya abinci a gabansu. Bayan fitarsu Azeema ta kalli Junaid taimasa nuni da Bismillah.

Murmushi yayi yafara k'ok'arin zubawa, itadai tana kallonsa. A mamakinta koda yagama saiya matso gareta, fuskarsa d'auke da murmushi yace, "A tsarin masarautar nan Ko inada hurumin cin abinci da matar sarki umman yarima Junaid?".

Wani k'asaitaccen murmushi ta saki, wanda akan dad'e ba'a gansa a fuskarta ba, ta d'ora hannunta dayasha zobunan azurfa da lu'u-lu'u akan nasa, "Wannan shine yanayi da girmamawa mafi soyuwa ga matar sarki kuma Umman sarki insha ALLAH".

Junaid yay murmushi mai sauti, Wanda ya bayyana fararen hak'oransa sosai.

Ahankali suka fara cin abincin cikin nutsuwa da tsintar kai a yanayin nishad'i, gimbiya Azeema najin lallai ta Isa kuma ta cancanta, kaso mafi yawa Na fargabar tazarar dake tsakaninta da d'anta ya ragu, harma tad'anji ta rage jin zafin Binta, balle tunda ya ajiyeta taga ko nemanta baiyi ba gashi yau yazo yana faranta mata rai wanda bata taba tsammanin samunshi a yanzu ba.


Azeema ta kalli Barira tace "Wazirin ya fada miki?"
Tace "eh Gimbiya yace akwai Gimbiya Zainab a masarautar Zazzau, akwai Gimbiya Nafeesa a masarautar Gumel, akwai Gimbiya Kadijah a masarautar Kano."

Azeema tai shiru tana tunani kafin tace "zansa a bincika mun su kafin nawa Mai Martaba maganar."

Barira cikin gulma tace "Mata zaki nemowa Junaid?"

Azeema ta kalleta sai dai bata ce komai ba ta juya tana tunani.

***********


Tunda aka dawo daga kai masa abincin takasa zaune ta kasa tsaye, burinta da addu'arta shine ace yaci dan ta tabbatar idan har yaci to ya fara saukowa kenan.
Ganin lokaci yaja ta kwala kiran fure.

Jiki Na rawa Fure ta iso d'akin, ta risina tana fad'in "gani uwar d'akina".

Wani kallo Zeena tamata, cikeda k'asaita tazauna bakin gadonta, "Fure! Inason kije sashen ya Junaid ki bincikamin yaci abinda muka kai masa?".

Fure ta had'iye yawu tana gyad'a kai, har zatayi magana Zeena ta katseta ta hanyar watsa mata harara....

"to mai kan kifi, halan zakice tayaya zaki sani? Lokaci kad'an yarage na canjaki fure, ko kad'an baki dace da zama hadimata ba sam".

"ALLAH ya huci zuciyarki uwar d'akina, a gafarceni gimbiya".

Banza Zeena Tamata, ta d'auke kanta gefe kawai. Ganin haka sai Fure ta mik'e a sanyaye zuwa sashen Yarima Junaid.


*************

Bayan sun kammala cin abincin su barira suka kwashe komai, Junaid ya kalli Azeema saikuma ya duk'ar dakai. "Ummana yaushene zaizo?".

Cikin nuna jin dad'inta da yanda hankakin Junaid yafara tasiri akan mulki ta amsa masa,

"Nan kusa zaka ganshi, sai dai kafin zuwansa ga tambaya?".

"Ina sauranki". yafad'a batare da ya d'agoba.

"Meka tanada zaka za6a bisa Umarnin mai martaba?".

Murmushi yayi batare da ya kalleta ba, a ransa yace Umma za6ina bazai saki farin cikiba, dan naji a raina bashine burinki ba. Amma a fili sai ya fad'ad'a murmushinsa "Ummana ina nan Ina nazari dai, kinsan yanzu nake fahimtar komai".


"Gaskiyane". Ta fada cikin jin dadi.


Daga nan shiru ya biyo baya, shi duk hankalinsa nakan me binta takeyi yanzu? Amma ya kamata Umma ta sa Binta aiki kamar Bakwa? Bayan ita ba baiwa bace? Ta ajiye aikin taci abinci? Kokuwa har yanzu tana can tana bautar?


**************

Sarki datun randa sukai taron nan amsar da Junaid ya bada ke damun zuciyarsa, sauke numfashinsa yai tare da dunkule hannunsa.
Meyasa jikinshi ke bashi da matsala? lallai kasantuwar Junaid k'ark'ashin fadarsa babban kuskurene, sannan gangancine, danya lura yaron yana tattare da wata fik'ira dashi kansa baisan yana da ita d'inba, me zai faru idan komai ya fito? Ko kuma idan ya nemi amsar mulkin da yake nasa?

Dolene yay azamar yima tufk'ar hanci, yau zai zauna da shamaki da wambai da waziri bisa shawarar daya yanke akan Junaid d'in, dan dolene yasaka Katanga a tsakaninsu.

Azeema fa?

Wani sashen zuciyarsa ya ambata. Kansa ya dafe, lallai yanda yake haka Azeema take, musamman a yanzu da dukkan motsinta yake akan d'anta da makomarsa, tunda Junaid ya dawo ko gunsa batazuwa sai dai in shi ya aika tazo.

Miye mafita to?.



Nace, "saiku nemo"😂🚶🏻‍♀






****************
AYUSHER 26
****************

*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍*


{27}
Barira ce ta shigo ta durkusa tace "Gimbiya Mijin Gimbiya Safiya ya iso."

Junaid wanda ko mosti baiyi ba bashi kuma da alamar tankawa.

Azeema cikin jin dadi tace "Barira akai Mahmud karamin falina na hutawa."

Da sauri tace to.

Junaid ta kalla, tace "Muje?" Ta fada tana mikewa.

Mikewa yai shima, a hankali ya kalli kofar da zata sadaka da bangaren dasu Binta suke, shiru yai kafin ya kalli Azeema wacce itama kallansa tai, ta fahimci me yake tunani.
Muje Ummana!
Yanda ya sake kiranta ne ya sa taji wani irin dadi ya kamata, kallansa tai cikin jin dadi sannan suka nufi kofa ta baya.

************


Azeema da kanta tayoma Junaid rakkiya k'aramin falonta Na hutawa, Wanda saika isa d'an gata agareta kake shigarsa, shikansa bai ma san da falan ba.

Cike da girmamawa Mahmud ya gaida Azeema, sannan suka gaisa da Junaid cikin girmama juna.

Mahmud cikin jin dadin ganin Junaid yace "Yarima barka da isowa, inata san zuwa dama."

Junaid yace "bakomai."

Azeema ce takuma yima Mahmud bayani akan mai Junaid d'in ke buk'atar sani sannan ta fito daga falan, Barira ta kalla tace "a kai musu kayan marmari."

Da sauri tace to, kallo daya zakama Azeema kasan hankalinta a kwance yake da alama zuwan Junaid yau da yanda ya ke mata yasata jin wani dadi har ta kasa boyewa.

Mahmud da Junaid suka k'ara gaisawa, tareda jajantama juna dakuma murnar dawowarsa.

Daganan Mahmud yafara bashi labarin shud'ad'd'en tarihin masarautar, da sarakunan da suka gabata, da yanda kowa yay mulkinsa da tarihin daya ajiye har zuwa kan mahaifinsa da sarki Abdussalam na yanzu.

Junaid yacika da al'ajabi, tarihin ya k'ayatar dashi sosai.

Fuskar Mahmud d'auke da Murmushi yace, "Yarima wanan shine masarautar a dunk'ule, wad'annan litattafai ne dazaka kuma samun ilimi Na zamantakewa da dabarun mulki, dan sarakunan da suka shid'e sun k'aru da sirrika masu yawa a cikinsu, to lallai nasan kaima zaka k'arun".

Junaid yad'an murmusa, "lallai Na gode da gudunmawarka agareni, zankuma nazarcesu, idan ina buk'atar fad'ad'a ilimi Zan tuntu6eka".

"To Masha ALLAH".

Sun dan sake yin hira kafin suyi sallama.

**************

Azeema ta kalli barira dake durk'ushe gefenta tai d'an murmushi, "Barira daga yau kar a sake saka binta aiki".

Cike da mamaki barira tace, "ranki ya dad'e miyasa?".

Azeema ta gyara zamanta cikeda k'asaita tana wani murmushin da ita kad'ai tasan fassarar kayanta, "karki damu da sanin dalili, kawai inason daraja duk abinda ya shafi Junaid"


Barira ta jinjina kai cikeda mamaki, tasandai ba banzaba, akwai shirinda uwar d'akin nata keyi ta k'ark'ashin k'asa, dan tasan haka kawai Azeema bazata sauko ta nemi daraja Binta ba.

Harzata mik'e Azeema ta dakatar da ita.

"Inason ganin jakadiya".

Barira ta jinjina kai tare da amsawa da to.


****************

Yau sarki Abdussalam ya gagara fita fadanci, sai aiken yana buk'atar hutawa yay musu, sannan yabuk'aci ganin Shamaki da wambai da waziri.

Babu 6ata lokaci suka iso, bayan jakadiya ta nema musu Iso suka Shiga.

Duk suka gaida sarki cikin girmamawa.

Sarki Abdussalam yay gyaran murya idonsa a Kansu, "kunsan miyasa na aika a kiraku?"

Wambai yace, "ALLAH ya k'arama sarki lafiya bamu saniba, sai dai ganin yanda ka kiramu tabbas akwai abinda ke faruwa."

Sarki Abdussalam ne yadan sauke ajiyar zuciya ya cigaba da fad'in "me kuke tunani a game da Junaid?"

Fuskarsu dauke da mamaki suka kalleshi, Junaid?

Abdulsalam yace "duk d'inku kunsan minene ma'anar dawowarsa garemu, sannan kunsan makomar hakan, to yarage ruwanmu Neman mafita, domin yaron yawuce zatonmu, na rasa me yasa nakejin ba daidai ba, me kuke tunani zai faru in ya san abinda ya faru a baya? Wanda idanunsa sun sa na fara tunanin dole mu san abinyi."


Hankalinsu ne ya tashi, dukansu suka shiga nazari.

Shamaki ne ya kalleshi cikin mamaki yace "ALLAH yabaka nasara mizai hana mu tuna baya kawai?".

Da sauri Sarki Abdussalam ya kalleshi yace "Baya?"

Idanunsa ya zare da sauri yace "Bazai yiwu ba, kun manta wacece Azeema a gareni? bazanso aikata hakan ga jininta ba, anema wata mafitar."

Shiru suka karayi.

"Mafita d'ayace" cewar Waziri wanda ya fada yana gyara zama.

"Wacce kenan?" Sarki Abdussalam yafad'a yana maida kallonsa gareshi.

"kayi taron nad'ashi Matawalle ko Galadima, sannan kabashi auren y'arka Zeenatu, hakan zaisa yai tunanin kafi kowa sanshi sannan yarka zata lura da duk al'amarinsa."

Wani zazzafan huci Sarki ya sauke, "shawarar k'arshe dama burinace, dukda ban yanke hukunciba, amma jin kalamanka yasa ka k'aramin k'warin gwiwa, ta farko kuwa kasan dai galadima nada ransa da lafiya, zamu sakashi yin murabus ne ko me? Zubair kuma shike rik'e da sarautar matawalle".

Wambai yay wata Y'ar dariya "Ranka ya dad'e anzo dai-dai wajen kenan ai, dan inhar ka tu6e Yarima Zubair ka d'aura Junaid lallai kowa zaikuma girmama adalcin mulkinka, a lokacin kowa zai fahimci kanasan Junaid fiye da yanda kake san danka, uwa uba Gimbiya Azeema wacce zata kara ganin girma da darajarka."

Kai ya jinjina cikin gamsuwa, da alama. Kowa yayi na'am da hakan, nantake suka fahimci matsalar ta warware, suka cigaba da tsara abinda suke tunani.


****************

Fure dake zube gaban zeena a d'arare tace, "ranki ya dad'e Azi hadimin yarima ya tabbatar min yaci abincin".

Cikeda d'oki Zeena tace, "da gaske?".

"Sosai kuwa ranki ya dad'e"

"Kai fure baki ta6a sani farin ciki irin yauba, lallai kinata tukuycin albishir mai tsoka".

Fure ta washe baki tace "godiya nake ranki ya dad'e, ALLAH ya mallakama yarima Junaid ke".
Zeena ta dan harareta tace "me kika sani?"

Fure tai kasa dakai tana murmushi.

Sosai Zeena ke tsallen murna ita kad'ai a d'aki, jitake kamar anmata albishir da aljanna yau.

Haka ta fito ta gangaro bangaren Hajjo, Hajjo wacce ke kwance duk batajin dadi ta kalli Zeena, kallo daya ta mata ta fahimci Zeena nacikin farin ciki, saidai bata tambayeta ba balle tasani saboda abinda ke damunta ya wuce wannan.



**************"


Tunda ya dawo sashensa yake cikin nazarin zamansu da Mahmud da yanda mahaifinsa ya gudanar da mulkinsa zuwa sarki Abdussalam. Lallai lokacin dazai fito ainahinsa Na jinin sarauta yayi, yakamata kowa ya fahimci sarauta a jini take ba a ayyukaba.

Sabon shiri yasake, kafin ya aika Azi sashen mai martaba Neman ison ganinsa. Anyi sa'a shima mai Martaban yana muradin ganinsa, dan haka babu wani janjani yasamu izini.


A yanda Junaid ya fito dolene kowa ya kallesa, ya rikid'e ya canja gaba d'aya, saika rantse a madarautar ya girma, harira kanta galala tai tana kallonsa, lallai ta yarda mulki a jini yake ba'a ayyuka ba.

Shi kansa Zubair dake k'ok'arin shiga sashensa la6ewa yai yana kallon Junaid, gaba d'aya saiyaji ya raina ajinsa da girmansa, wai harma yaushe Junaid d'in yagama fahimtar shi jinin mulki ne? Jibifa yanda yake wani shak'ar iska da fesar da ita tamkar shine sarkin, lallai aikine babba agabansu, dan wannan yaron idan basu risinar dashiba to zai 6allo musu ruwa.

Oho Yarima Junaid baisan yanaiba.


Itama Hajjo tuni labari yakai Mata, ba k'aramin girgiza tayiba dajin batun, zeena dake gefenta ta mik'e da hanzari tafice, saidai tana fitowa Junaid Na shigewa turakar mai martaba.

Takaici yasata cizon yatsa, takoma da alwashin jiran fitowarsa.

****************

Sarki Abdussalam dake kishingid'e ya zubama Junaid idanu, mamaki yake a ransa yaushe junaid d'in ya koma haka? Koda yake ba abin mamaki baneba, yasan wacece Azeema sarai, komai zata iya aikatawa akan d'anta domin mulkin nan, amma bai tdammaci hakan da wuriba.....

Gaisuwar Junaid ta katse tunanin mai martaba, ya amsa masa da kulawa. Shiru ne ya biyo baya, kowa yana nazarin d'an uwansa, zuwa can mai martaba ya nisa yana gyara zamansa,

"junaid akwai matsalane, Ka buk'aci ganina?".

Murmushi junaid yayi, yad'an girgiza kansa, "A'a Abba, dama za6in daka bani nazo fad'a maka".


Murmushi Abdulsalam yai yace "ina jinka me kakeso?"
Ya boye damuwarsa dake kasan ransa.

"Nayi farin ciki da hakan Junaid, amma kafin sannan gawani albishir".Abdulsalam ya cigaba yana kallansa.

Kallonsa Junaid yad'anyi, saikuma ya murmusa yana maida kansa k'asa.

Sarki Abdussalam bai fahimci murmushin Saba, ya danne ya Fara magana,

"Duba da wasu abubuwa danai na fahimci yakamata kayi aure, kai idan masarauta ne, hankalin kowa a kanka yake kana ganin matsalar data afkou wancen lokacin, hakan yasa yai tunani hadaka aure da kanwarka Zeenatu."

"Zeenatu?"

Junaid yafad'a yana kallon mai martaba fuskarsa dauke da matuk'ar mamaki. Shi kansa mai martaba ya fahimci haka, dan haka ya gimtse fuska yana fad'in,

"Umarnine Junaid dan dan Sarku matarsa ta farko dolene yabi umarnin wacce aka zaba masa."

Jinjina kai junaid yashiga yi yana wani irin murmushi "Sosai ka cancanci nabi Umarninka domin matsayin mahaifi kake a gurina, naji na kar6a da hannu biyu".

Sarki Abdussalam ya murmusa, dan aganinsa yasamu nasara a matakin farko. "ALLAH yay maka albarka Junaid, ina sauraren za6inka."

"Abba za6in nawa nima bamai wahala baneba, domin duk bisa bigire d'aya muke".

Bigire daya?


Gaban sarki Abdussalam ya fad'i, kardai mulkin?. Kafin ya nemo amsa maganar Junaid ya katseshi......

"Inason izinin Auren yarinyar da muke tare acan, binta!..."

"Binta?"

Sarki Abdussalam yafad'a a harzuk'e wanda yau ne karo ma farko da Junaid yaga yayi magana haka "Junaid maidamin murtani akan rashin kar6ar za6ina yasaka tunanin had'amin yarinya da Y'ar talakawa marar usul ko me? Ni nai tunanin taho maka da ita saboda ganin kana bukatar kwanciyra hankali anan, yanzu kuma ka kawo zancen so?"

Shiru junaid yai yak'i tankawa, yay kuma kicin-kicin da fuska babu alamar fara'a, danmmi za'a kira binta mara usili? To lallai inhar zai auri zeena sai dai da binta, inba hakaba kuma zai 6allo ruwa gaba d'aya kawai, saiya auri wadda basaso d'in da k'arfin mul......

"Dakai nake magana". Sarki Abdussalam ya katse tunanin junaid.

"Dago ido junaid yay ya kallesa, fuskarsa babu alamar fara'a, hakan ba k'aramin razana sarki Abdussalam yayiba, dan ainahin marigayi sarki Zubair yagani a fuskar Junaid d'in, kasa cewa uffan yayi, saiya samu kansa da sassauta fushinsa, yace,

"Nabaka lokaci kayi tunani, bani kad'aiba ko mahaifiyarka bazata yarda da za6inka ba, har gwara ni zan iya hakura amma kai kasan Azeema bazata taba yadda ba."

Junaid ya murmusa, "Tuba nake Ranka ya dade ba binta kawai ba, ko Zeena bazata aminta ba, daga zuwana na shaida hakan."

Yana gama fad'an hakan yamik'e ya fito cikeda kasaita da izza, wadda tasaka sarki Abdussalam kasa d'auke ido daga kallonsa. Har yaushe Junaid d'in yay irin wannan canjawar?.


Junaid na fita ya tsaya a waje a hankalu ya juyo ya kalli bangaren Abdulsalam, bai taba tunanin shima xai zo mai da magana haka ba, juyawa yai cikin isa ya nufi bangarensa.

******************

Jakadiya ta kwashi gaisuwa wajen Azeema kafin tace, "Ranki ya dad'e gani".

"Na ganki ai". Azeema tafad'a tare da zuba mata ido. Takuma gyara zamanta tana kallon jakafiya dake gurfane.

"Jakadiya inason bincike akan y'ay'an sarakunan k'asar zazzau, Gumel, kano".

"Angama ranki ya dad'e".


Jakadiya na fita Azeema ta kalli barira, "Naji ance jiya mai martaba yayi zama Na mussaman da waziri da wambai da shamaki".

"Eh lallai ranki ya dad'e anyi hakan, amma naji k'ishin-kishin akan auren gimbiya Zeena ne".

Baki Azeema ta ta6e, saikuma tayi murmushi

Barira cikin san gulma tace "Gimbiya yanzu wace d'iyar sarkice

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login