Showing 54001 words to 57000 words out of 76752 words
ai."
Dan murmushi tai cikin waskewa tace "hmm...." gani batasan cigaba da zancen yasa yace "ko kinsan Sabisu?"
"Sabisu? Waye hakan?"
"Awwwww nagane shi bawan Mahaifinka, ya akai ka sanshi?"
Dan kallanta yai yana nazari akanta kafin yace " naji su Hajjo na nemanshi ne."
Hajjo? Tai tambayar cikin mamaki, idanu ta zaro da sauri, sannan ta sauke idanta kasa saboda karya gane, yace "eh bandai san dalilinsu ba."
Yake tai tace "Allah sarki."
Har ya mike yace "naji yana wani kauye wai Bukul."
Mikewa yai ya mata sallama ya fita, yana fitowa Falo ya bi bayan kofar da kallo, yace "Umma dan dan Allah ko menene karya zama akwai ki a ciki."
Tunda ya fito ta kasa ko motsi, meke faruwa?
Fitowa yai ya koma bangarensa, bangaren Zeena ya fara shiga sai dai batanan, hakan yasa ya wuce bangaren Binta yana nazari.
Binta na zaune a bakin gado duk abin duniya ya isheta, jin motsin yasa ta fito da sauri.
Tana ganin Junaid ne taji wani dadi ya zo mata wanda har taji idanunta na neman kawo ruwa.
Mamaki ne ya kamashi, a hankali ya tako inda take, yana karasowa ta rungumeshi.
"Ya akai?"
Tace "bakomai."
Dagota yai a hankali ya zubawa fuskarta ido, a hankali ya sumbaceta, sannan yace "kinji haushi ne?"
Cikin sanyin murya tace "naji amma kadan"
Murmushi yai yace "wannan karan nayi laifi dafatan baza'a hukuntani ba."
Dariya ta dan yi tana neman dan matsawa daga jikinsa ya kara kankameta, tana kallansa tace "bari naga wannan karan wani hukuncin za'ama."
Murmushi yai yace "kenan laifin biyu nai tunda jiya nan na taho da safe kenan kowa namai laifi?"
Fuska tadan hade, yace "zan tafi Binta inada abinda zanyi, nazo ne na fada miki."
Jiki a sanyaye ta kalleshi tare da yin murmushin yake tace "Uhm hmm."
A hankalinya zare ta daga jikinsa yace "kici abinci, sannan zan nemi Harira ta kawo miki hadimai, dan ita ta girma ne amma da ita ta dace dake."
Kai Binta ta daga alamar gamsuwa sannan tace "to Ya Junaid."
Sake sumbatar kuncinta yai sannan ya juya ya fita, da kallo ta bishi.
Yana shiga bangarensa yaga Zeena acan.
Tsayawa yai yana kallanta cikin mamaki.
Tana ganinya shigo ta mike da sauri tace "Ya Junaid me kake nufi? Wai me kake san ji gun Sabisu?"
Kallanta yai yace "kije ki sanar da Hajjo inda Sabisu yake, da alama itace take nemansa ba ni ba."
Kallan mamaki ta masa tace "bangane ba."
Shiru yai yana san mata karin bayani sai dai inya tuna yar Hajjo ce sai yaji bazai iya ba, dan ya tabbatar daga tayi subutar baki komai ya wargaje kenan.
Zeena ce ta kamo hannunsa tace "menene?"
Kallanta yai sannan yai murmushi yace "bakomai kawai ina ganin ita take nemanshi bani ba."
Shiru tai tana kallansa ta tabbatar akwai dalilinsa nayin haka.
Shikenan zan fada mata, kallanta yai a hankali yace "nagode."
Dayake bata taba kawo jin hakan daga gareshi ba shiyasa kalmar ta shigeta dakyau, hannunsa ta saki gaba daya jikinta yai sanyi.
Murmushi ya mata yace "zaki iya sanar da ita yanzu?"
Kai ta daga alamar eh, sannan tace "nagode Ya Junaid."
Dame?
Kai ta girgiza alamar ba komai sannan ta fita.
Tana fita ta tsaya a waje, wani sanshi ne yake kara shigarta da darajashi.
Tana kokarin wucewa sashinta taga Harira a bakin kofar Binta da alama abincin safe suka kawo mata.
Binta ce ta bude mata hakan yasa suka hada idanu, su Hari ne suka zube suna gaisheta.
Binta ce ta gaisheta, tana mamakin meyasa batabi ta can baya ba inda zata shiga bangarenta, amma sai data zagayo ta nan?
Zeena ce ta amsa cikin isa sannan ta wuce, Fure ce ta matso da sauri tace "Gimbiya kina birgeni wato ki nuna mata daga can kike kenan."
Wani kallo tama Fure batace komai ba har suka shiga bangarenta.
Junaid kam zama yai a kan kujera tare da hade hannayensa yana fatan samun nasara akan abinda ya shirya.
Shiru yai yana nazari........
******
Harira na shiga ta kalli Binta, tace "Ranki ya dadw inasan magana dake inba damuwa."
Binta cikin dariya tace "lalai Hari muje ciki."
Da sauri tace "a'a nan ma yayi."
Hadiman sun ajiye abincin sun fita sannan Hari ta kalleta.
Tace "Kiyi hakuri da tambayar da zan miki."
Binta tace "Hari ni ki daina min magana haka kimin magana kanki tsaye yanda muka saba."
Hari ta kalleta tace "ba abinda ya faru daren jiya?"
Kasancewar ta gane abinda take nufi yasa Binta tace "eh."
Harira tace "Gimbiya fa?"
Binta tace "bansani ba amma ta kirani tana sanar dani abu ya faru."
Harira ta kalleta tace "Dama tun kafin aure naso na sanar dake amma bansamu dama ba kasancewar kuna bangaren Gimbiya sai dai yau naga ya kamata ki sani.
Kada ki kuskura ki cigaba da sanyin nan da kike neman daurawa kanki, da can kinada sanyi amma abin bai kai haka ba, yanzu ba ke kadai bace agun Yarima, idan har kika cigaba da abinda kikeyi kina zaune wlh Junaid ganinsa ma sai ya gagareki."
Cikin mamaki ta kalleta tace "bangane nida mijina ya gagaren gani ba."
"Gidan sarauta kike bayan nan ku biyu ne sannan bayanan matarshi yar sarauta ce jinin mulki, kina tunanin shakuwa da san da yake miki zai dawwama ne?"
Binta tace "Harira Ya Junaid ne fa?"
Cikin dan zafi Harira tace "ba namiji bane? Maza duk inda suke irinsu daya, idan har kika cigaba da wannan halin naki kina zaune sai kin rokama zai ganki, me kike mai anan? Banda ki zauna kullum kina kiransa? Kinsan matsalarsa? Kinsan burinsa? Kinsan abinda ke kasan ransa? Kinsan me yake tunani?"
"Taya zansan abinda bai fadamin ba?"
Dole a matsayinki na matarsa wacce kuka taso tare sai kin mike kinji menene matsalarsa, na tabbatar shima yanasan sanar dake bayasan saki a damuwa ne."
Gaba daya jikin Binta ne yai sanyi, Harira tace "anjima zan kawo miki hadiman da zasu kula dake."
Tana kaiwa nan ta mata sallama ta mike.
Shiru Binta tai tana nazarin kallamanta tabbas gaskiya Harira ta sanar da ita.
********
"Me kike anan? Haryaushe akai auren da zaki fara yawo?"
Hajjo ta tambayi Zeena dake zaune.
Zeena ta kalleta tace "kefa Hajjo dadina dake rashin hakuri, sai kiji ai dame nazo miki ko?"
Hajjo ta hade fuska tace "menene?"
"Sabisu!"
Da sauri Hajjo ta kalleta tace "ya ya? Ke a ina ma kika sanshi?"
Ranar ina nan kuke labari da Ramlatu, na samo inda yake."
Da sauri Hajjo ta matso tace "a ina yake?"
"Bukul wani kauye ne."
Kallan mamaki Hajjo ta mata tace "ya akai kika sani?"
Shiru Hajjo tai tana kallanta, Zeena tace "menene?"
"Junaid kikaji yana nemanshi?"
Zeena tai shiru badai Junaid abinda yakeso kenan ba? So yake ai zargin yana nemanshi? Kai ta girgiza sauri ganin abin bai bada ma'ana ba.
Kallan Hajjo tai tace "koma menene ni ki fadamin meyasa kike nemanshi?"
Hajjo ta kalleta ta matso tace "Bincike nake san yi, so nake in samo abinda mahaifinki bai isa ya hana Zubair mulki ba."
Baki ta tabe tace "wai ke haryanzu Hajjo batun ba Zubair mulki yana nan?"
Wata muguwar harara Hajjo ta bata tace "tashi ki tafi gun mijinki da alama nan gaba komai naki ma gun mijinki zai koma."
Zeena ta mike ba musu ta masa sallama ta fita.
Wani irin haushi ne ya kama Hajjo kafin tai maza tasa a kira mata Zubair dan yazo ya sa a nemo mata Sabisu.
**********
Junaid ne ya shigo cikin fadar Zagi na mai kiran Lafiya.
Junaid ya shigo sannan ya gaida mai martaba.
Sarki cikin nuna jin dadinsa yace "Matawalle an shigo?"
Junaid yace "Eh Ranka ya dade."
Nan su Shamaki da su Waziri da sauransu suka fara gaisheshi.
Junaid ya amsa cikin isa da kasaita irin ta 'ya'yan sarki.
Sarki yai dan gyaran murya yace "Dama nasa kazo ne saboda a sanar dakai abubuwan da zaka dingayi a matsayinka ma matawalle."
Junaid yai dan kasa dakai cikin girmamawa yace "to Ranka ya dade."
Galadima ne ya kalli sarki yace "Ranka ya dade naga bai dade da aure ba da nauka za'a barshi ya dan huta zuwa sati biyu."
Junaid kam a ranshi yace ina za'a banni na huta ba'a san nasamu lokacin bincike?
Haka sukai tattauna sannan suka taso.
*********
Azeema tayi shiru tanata zagaye a dakinta tana jiran Barira, can Barira ta shigo da sauri, ta yaye mayafinta tace "Gimbiya na sanar ma Gimbiya Safiya, tace ta sanar ma Mijinta yanzu zai wuce."
Azeema ta jinjina kai cikin gamsuwa.
******
Hajjo ce ta kalli Zubair tace "ka tura kanin nawa?"
Yace "eh Hajjo sai danaga tafiyarsa na shigo.
*******
Junaid na kishingide a bangarensa idanunsa a lumshe a hankali naga ya sake yin wani sansanyan murmushi wanda nace hmmm
🤔🚶🏻♀️
******Ayusher🏌🏻♀️******
*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*
{38}
Yau kwana biyu kenan da tafiyar Azi, gaba daya Mai Martaba yasa Junaid ya shiga hidima ta ko ina.
Yar yanzu ba wacce ya kwana da ita tsakanin Zeena da Binta.
Yau ya kasance ranar Zeena ne, yana zaune a bangarensa bayan ya kammala abubuwan daya kamata yai, shiru yai yana duba wasu takardu tare da fatan dawowar Azi a wannan rana.
Tun safe yake jiran isowarsa amma haryanzu shiru.
Kamar da wasa yaji Azi yace "Yarima nine!"
Zamansa ya gyara yamai iso, Azi ya shigo ya zube a gabansa ya fara gaisheshi.
Junaid ya amsa sannan yace "ya ya?"
Azi ya kalleshi ya danyi shiru.
Junaid yai dan murmushi yace "bakomai, ko baka sameshi ba akwai masu kawoshi."
Kallansa yai cikin mamaki yace "su wa?"
Junaid yace "inata nemanka ne dan ka samin ido ka dubamin bangaren Gimbiya da bangaren Hajjo, amma yanzu kaje ka huta zuwa dare tukun."
Azi yace "na taho dashi ai."
Ka taho dashi? Ya tambaya gabansa nadan faduwa kadan.
Azi yai kasa dakai yace "Sabisu kanin mahaifina ne shiyasa kana fada nasan inda zan sameshi, yanzun ma dan baiyarda ya taho bane saboda yana tsoron abinda zai faru dashi, sai dana zauna na shawo kansa tukunna tuba nake ranka ya dade."
Kallansa Junaid yai yace "Kanin mahaifinka?"
Azi yai kasa dakai cikin daukan laifi.
Junaid yace "yana ina yanzu?"
Yana can waje, a boye, bansan meke faruwa ba amma yace "baisan kowa ya ganshi."
Junaid yace muje na shigo dashi dakaina."
Fitowa sukai suka je inda Sabisu yake, Sabisu babban mutum ne dan a kalla zai kai shekaru 60, Junaid cikin girmamawa ya gaisheshi.
Kallansa yai cikin jin dadin ganin Junaid yace "Yarima! Ashe zan ganka kafin lokaci na yayi?"
Junaid ya kamo hannunshi yace "kayi hakuri duk da bansan meke faruwa ba amma nasan dalilin abinda ya faru ne ka bar masarautar nan."
Shiru yai tare da sauke kansa kasa, Junaid ya kalli Azi yace "mu shiga."
Nan suka shiga Junaid na gaba, su Azi sun ba Sabisu kayan hadimai ya saka, haka suka shigo cikin dari, sunyi sa's suka wuce bangaren Junaid.
Junaid ne yasa aka kawo mai abinci, sai dayaci sannan ya kalleshi yace "Baba kayi hakuri amma na rasa meyasa nake da tambayoyi dayawa akaina game da masarautar nan."
Sabisu ya kalleshi yace "Yarima ya akai ka dawo?"
Junaid ya bashi labari a takaici.
Sabisu cikin jinjina kai yace "Alhamdulila da baka dawo ba sai daka mallaki hankalin kanka."
Junaid ya kalleshi duk da gabansa na faduwa saboda tsoron abinda zai tono amma yace "Sabisu kasan meyasa mahaifina ya kaini can wani gari? Ba da sanin mahaifiyata ba?"
Sabisu yai shiru kafin ya kalleshi yace "Yarima!"
Junaid ya maida jankalinsa kansa yace "ka sanar dani, koma menene zan dauka."
Ajiyar zuciya yai yace bakomai na sani ba sai dai zan sanar dakai abinda na sani.
Junaid ya tattare hankalinsa kansa cikin danne damuwar dake ransa.
Gimbiya ta dade tana neman haihuwar da namiji sai dai a duk sanda ta haihu cikin rashin sa'a sai ta haifi mace.
Sannan abin ya dameta haka ma mai martaba saboda yasan irin san da Gimbiya kema Abdulsalam amma saboda burin zama matar sarki uwar sarki yasa ta ajiye komai ta aureshi.
Sarki Zubair na tsananin san Gimbiya, haka sukai ta fama amma duk sanda ta haihu sai dai ta haifi mace, daga bayama haihuwar ta tsaya, dan sai datai shekara hudu sannan ta sake samun ciki.
Wannan cikin data samu yazo mata da matsala sabods tasha wahala akansa burin su kawai wannan karan a dace a samu d'a namiji.
Cikin yardar Allah Gimbiya ta haihu ta haifi d'anamiji, sai dai abin mamaki da tsoro yaran yazo ba lafiya, tunda aka haifeka bakai kuka ba sannan bakai bayan gida ba, bayan haka yanayin yanda kake numfashinka ba daidai yake fita ba.
Sai dai wannan rashin lafiya taka Azima ta sa an boyeta, dan inba ni da Mai martaba ba bawanda ya sani a iya sanina kenan.
Sarki yasa an nemo masu magani cikin sirri amma abu yaki yiwuwa.
Duk an fara cire rai dakai, dan har ta fara hakura akan a sanar da mutane dan da alama bazakai rai ba.
Kwatsam wata rana Abdulsalam ya ziyarci Mai Martaba, tun daga sanda ya fito daga bangarensa ......"
Shiru yadanyi tare da dan share kwallarsa, Junaid wanda gaba daya yake jin kalaman Sabisu a kwanyar kansa yace "inajinka."
Sabisu ya cigaba "Tundaga wannan lokaci Sarki ya fara rashin lafiya, sai dai abin mamaki randa ya kwanta rashin lafiya ranar kai kashi, haka dai ya cigaba da daurewa sai dai mu munsan yanda yake jinya, yana jinya kai kuma kana samun sauki, ranar yana tashi daga bacci ya umarci a fara gini a filinsa dake cam wani kauye, tun daga nan kuma lamari sarki ya canza, kullum zaka sameshi shiru yana tunani.
Ciwon sa baya tashi sai dare, yasha wahala matuka sai dai da safe inka ganshi bazaka gane ba sai dai ramewa dayai.
Sarki ya hana matansa kwana a bangarensa sai dai adanyi hira sannan su koma.
Ka samu lafiya sosai, hankalin kowa ya kwanta banda Sarki dake ta fama.
Akwai wata rana da ya zauna shi da Shamaki nada bana yanzu ba, tun daga wannan rana Sarki ya canza kwarai da gaske, ya fara janye jikinsa daga kan komai, sai ya zauna yai shiru yana tunani.
A lokacin kana shekara 7 ciwonsa ya tsananta, har Allah ya dau ransa."
Shiru Junaid yai gaba daya ya kara sashi a duhu duk da dai ta wani bangaren ya dan warware masa wasu abun, kenan shi dan Zubair ne da Gimbiya na gaskiya.
Kallansa yai yace "bakasan me suka tattauna ba?"
Sabisu yace "bansani ba Yarima, sannan sai da mai martaba zai rasu ma Abdulsalam ya kira."
Azi, Junaid ya kirashi, da sauri ya shigo yace "ka kai Baba ya huta a bangarenku, kar ka bari wani yasan wanene shi, sannan inda dama ka zauna dashi."
Azi yace "angama ranka ya dade."
Tare suka fita Junaid yai shiru yana nazarin gaba daya a binda yake kwakwalwarsa, indanunsa ya rufe yanna tattara tunaninsa, yafi tsawon awa biyu a haka kafin a hankali naga ya bude idanunsa.
Idansa ne naga yai jaaa sannan ya mike daga inda yake.
Fitowa yai Hadimansa suka taso da sauri.
Azi wanda ya zo gunsa ne ya matso yace "Yarima!"
Junaid ya kalleshi yace "Dawo da shi dakina."
Dakinka?"
Azi ya tambaya, Junaid yace "eh yanzu."
Nan Azi ya juya da sauri, fuskar Junaid kadai xaka kalla kasan ba wasa a tattare dashi.
Ba a jima ba sai ga Azi ya dawo da Sabisu, nan suka shiga ciki, Junaid yace "ka zauna anan."
Nan yace ina na isa zama a bangarenka?
Junaid yace "ina tsoron abinda zai faru kana can ne."
Sabisu ya jinjina kai, Junaid ne ya kalleshi cikin nazari yace "Akwai maganin da ka sani wanda yake amfani da jinin wani?"
Gaban Sabisu ne ya fadi ya kalli Junaid yace "me kake nufi Yarima?"
Junaid ya kalleshi yace "idan baka sani ba shikenan."
Ya juya, Sabisu ne yace "sai dai masu sidabaru."
Junaid ya kalleshi baice komai ba ya fito, bangaren Azeema ya wuce kai tsaye.
Tana zaune cikin bacin rai tana tuno abinda sukai da Mahmud yanzu.
tace "kana nufin Hajjo ta daukeshi kenan?"
Mahmud yace bansani sai dai ina zuwa kauyen ance wani yazo wai Hajjo ce ta aikoshi."
Azeema ta sauke ajiyar zuciyarta, me Hajjo take sanji?
Barira ce ta sanar da isowar Junaid hakan yasa ta gyara zamanta tare da daidaita tunaninta.
Junaid ne ya shigo cikin dakinta.
Cikin nuna farin ciki tace "Junaid."
Zama yai sannan ya gaisheta, amsawa tai tace "kwana biyu banjika ba."
Kallanta yai ya kura mata ido, wanda har tadan sha jinin jikinta tace "Junaid!"
Sanda ina karami banda lafiya ya akai na fara samun sauki lokaci guda? Bayan alokacin an hakura da yin magani?"
Gaba daya jikin Azeema ne ya fara rawa, hannunta ta hade ta matsesu tana kokarin danne fargabar kalamansa wanda bata taba tunanin ji ba.
"Zan fado kamar haka, Wata taga dan data jima tana nema yazo ba lafiya ga wanzamai da duk wasu masu magani sun kasa warkar dashi, hakan yasa ta nemi zuwa gun malaman tsubu, ta nemi wanda ta yarda dashi sukaje gun su biyu, bokan tsubu yace mata in tanaso danya ya warke to lalai sai ta sadaukar da jinin daya daga cikin iyayensa.
Saboda tsoro da fargabar jin abinnan yasa ta dawo tare da hakura da abinda take nema.
Sai dai tasan wanda ta dauka bazai iya jurar ganinta cikin wani hali ba, hakan yasa ya koma ya nemi ai amfani da jinin mahaifin yaran, aiki ya fara ci daga sanda aka fara amfani da mahaifinsa.
Haka rayuwar mahaifinsa ta karkare shikuma dan ya samu sauki."
Idanunsa ya dago wanda sukai jaaaa sosai kai kace garwashi ne, yace " Watan nan Umma ce, wanda ta yarda dashi Abdulsalam ne, sannan mahaifin Zubair ne."
Kafafunwanta ne suka shiga rawa hankalinta yayi kololuwar tashi, gaba daya ta kasa magana saboda gaba daya ta kasa daidaita tunaninta, bata taba tunanin wannan rana zatazo mata a duniyar nan ba.
Junaid ya runtse ido wasu zafaffan kwalla ne suka zubo mai yace "kina tunanin abinda kikai kin cici danki ne saboda kina sansa? Ko kina tunanin abinda kikai Abdulsalam ya aikata ne saboda yana san danki? Ko kina tunanin Zubair be san me kuka aikata ba?"
Hankali a tashe ta sauko kasa, ta fara girgiza kai tace "Junaid Allah bansan komai ba, bani nace Abdulsalam ya koma ba, Allah bansan wannan abun ba."
Hannunsa ta kamo ya kwace hannunsa yace "baki sani ba? Bayan kinsan Abdulsalam yana sanki? Sannan ke a naki tunanin Abdulsalam sabods