Showing 57001 words to 60000 words out of 76752 words
ke kadai yai haka? Kina tunanin kece kikai amfani dashi?"
Kallan Junaid tai tana hawaye, kai ya girgizs mata yace "ko daya, kece akai amfani dake, kece Abdulsalam yai amfani dake."
Me kake nufi Junaid?"
Mikewa yai cikin takaici yace "kiyi tunani dakanki, wannan abinda kika aikata bazan yafe miki ba, kina tunanin kuyi amfani da rayuwar mahaifina sannan kuyi tunanin zanyi rayuwar data dace? Saboda burinki nasan danki ya zama sarki?"
Yanda yai maganar karshe kai kana ji kasan zuciyarsa ta gama raunana da bakinciki.
Hawaye ne suka zubo mai yace "Daga ke har Abdulsalam da duk wani mai hsnnu aciki banaji zan iya yafe muku."
Kafin ta bude baki tai magana yabar dakin.
Yana fitowa yai bangarensa, duhu duhu ya shiga gani saboda kansa dake juyawa.
Hannu yasa ya rike bango da sauri kansa na wani irin sarawa, gaba daya baya gani sosai......
****
Ayusher🏌🏻♀️
****
*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*
{39}
Dakyar ya kai kansa ciki, yana neman faduwa Binta wacce ta fito ganin yanayinsa yasa ta matso da sauri, yana kokarin faduwa ta rikoshi da sauri, kallanta yai bakinsa ne ya shiga rawa, Yaya!
Hannunta ya rike da karfi, ya nuna mata bangarenta.
Rikeshi tai sosai suka shiga ciki.
Tana rufe kofa ya zube ya zauna a kasa.
Mamaki ne ya kamata tace "Ya Junaid!"
Dagowa yai ya kalleta kawai hawaye suka shiga gangaromai, gaba daya ya rasa ta ina ma zai fara.
Ganin yanda yake kuka ne hankalinta ya tashi karara, zama tai kusa dashi a hankali ta sa hannu kan fuskarsa, samun kanta tai da zubar da hawaye.
Hannunsa yasa a kan hannunta cikin rawar baki ya kalleta yace "Binta......."
Kuka ne ya kwacekai wanda ya kara daga mata hankali sosai.
Kansa ya sa akan kafadarta yana kuka, itama hawaye kawai take tana shafar bayansa dan sam ta kasa magana.
Ya dade a haka dan sunyi kusan awa daya a haka kafin ya share kwallarsa, dagowa yai ya kalleta tana hawaye, a hankali ya kakaro murmushi ya mata.
Hannunsa ya daura kan fuskarta yace "kukan me kike?"
Wasu hawayen ne suka gangaro tace "Nima bansani ba Yaya, zuciya ta na kuna ganin kana kuka, ban taba ganinka cikin irin wannan halin ba."
Hannu yasa ya share mata hawayen sannan ya jawo kanta ya daura goshinta akan goshinsa, hakan yasa suna jin numfashin juna yace "Binta!"
Hmm tace dan ta kasa amsawa.
Yace "Bazan iya yafe musu ba dukansu."
Suwa? Ta tambaya cikin sanyin murya, idanunsa ya runtse cikin kunar zuciya yana tuno abinda ke faruwa.
Dago kanta tai ta rungumeshi, kasa magana tai sai kankameshi datai a jikinta.
Idanunsa kawai ya rufe yana kara maimaita bazan yafe musu ba........
Dagota yai kawai ya mike tsaye, kallansa tai tace "Yaya!"
Murmushi yai yace "nagode Binta, samun ki kusa dani ba karamin karfi ya banni ba."
Kallansa take haryanzu batace komai ba, zan wuce.
Kai ta daga alamar to, ya juya ya wuceta zai fita.
"Bazaka fadamin abinda ke damunka ba?"
"Zan fada miki amma bayanzu ba."
Ya bude komar ya fita.
Da kallo ta bishi ta kasa tashi a gun, bata taba ganinsa yana kuka ba tunda take dashi, meya sameshi?
*******
Bangarensa yaje, yai Sallah sannan ya ma Sabi'u sai da safe ya fito.
Bangaren Zeena suka nufa wacce tasha wanka cikin ruwan dayasha hadin turare, sannan ta turara jikinta da turaren jiki.
Ba kwalloya tai na sai dai kamshin da take duk wanda ya ji sai ya yaba, ta taje kanta ta daureshi da ribon.
Abincin daren dake ajeye a gefe ta kalla sannan ta kalli Fure tace "Ya Junaid haryanzu?"
jeFure ta sake fita sannan ta dawo tace "inaji yana hanya."
Kallan Fure tai tace "lekamin bangaren yarinyarcan ko yana can."
"Ah hb Gimbiya ai yasan kwanankine ya za'ai yaje can?"
Wata harara ta buga mata tace "sau nawa nace ki dai fadamin abinda zanyi? Kinsan Allah kin kosa komawa gun Hajjo na canza ki."
Da sauri Fure tace "bari naje na dubo."
Tana fita falo taji ana sanar da isowar Yarima, Junaid ne ya shigo ya wuce ciki.
Zeena wacce dadi ya kamata ta mike tsaye tana jiranshi.
Yana shigowa ya kalleta, kallansa tai itama cikin jin dadi sannan ta kamo hannunsa tace "Yaya ka iso?"
Kallanta yai sannan yadanyi murmushi tare da kokarin zare hannunsa.
Hannun ta sake rikewa sannan ta jashi zuwa inda aka jera abinci.
Zama yai sannan ya kalleta.
Kusa dashi ta zauna cikin salo da jan hankali ta zuba mai abincin sannan ta tura gabansa.
Shiru yai ya kurawa abincin ido yana nazari, spoon din ta dauka ta diba sannan ta nufi bakinshi dashi.
Kallan spoon din dake gabansa yai yana nazarin yaushe ma rabandayaci abinci yau?
Karasa da spoon din tai daf da bakinsa hakan yasa ya kalleta sannan yasa hannu ya amshi spoon din yaci.
Murmushi tai sannan cikin jin dadi tace "Yaya da alama Hajjo bata sameshi ba, dazu Fure dana aikata tace ran Hajjo a bace yake."
Kallanta yai sannan yace "ko?"
Kai ta daga tace "bansan ya akai ba, kuma Ramlatu ta tabbatar min yana can."
Kallansa ta sakeyi tace "kana tunanin wani ya daukeshi?"
Kila!
Kawai yaci sannan ya ajiye spoon din ya mike yana kokarin zare hiramin daya yafa a kafarsa.
Mikewa tai a hankali tasa hannu a ta zagayo dashi ta cikinsa, ta kwantar da kanta a bayansa tace " Ya Junaid."
Shiru yai baice komai ba, tace " Ya Junaid!"
Juyowa yai ya kalleta ta sake zagayeshi ta bayansa hannu yasa zai zare hannunta ta sake hade hanayenta da kyau.
Idanu ya kura mata yana tuno abinda akai domin sa? Anyi amfani dashi an salwantar da mahaifinsa.
Gaba daya yanayinsa ne ya canza, idanunsa ya runtse da karfi, sannan yace "kiyi hakuri Zeena amma plz ki bani aran kwana uku."
Kwana uku? Ta tambaya cikin mamaki.
Hannunta ya zare sannan ya ajiye hiramin ya kwanta akan kujera yace "kwana biyu naki na binta daya kenan, kiyi hakuri."
Shiru tai tana kallanshi cikin rashin jin dadin abinda ke faruwa.
Daurewa tai ta matso tace "naji amma ka dawo gado mu kwana tare."
Hannunsa dake kan goshinsa ya sauke ya kalleta.
Tace "bansan meya faru tsakaninka da Binta ba smms na tabbatar baka batta ta kwana ita kadai ba."
Ta dauka zaice wani abin sai gani tai ya mike ya kwanta akan gado.
Haka zaka kwanta bakaci abincin bs?
Idanunsa a lumshe yace "banajin ci."
Shiru tai tana kallansa.......
*********
Gaba daya Azeema ta kasa zaune ta kasa tsaye, tama rasa meke damunta, ji take kamar zatai hauka.
Tayi kuka harta gaji, bata taba tunanin akwai wannan ranar da Junaid zai ji wannan kazamin al'amarin data dauka ita kadai tasan sirrinta.
Meyake nufi da Abdulsalam yayi amfani da ita?
Gsba daya kanta ya kasa nutsuwa, Bayan sallar magrib Barira ta shigota sanar da ita zuwan Hajjo.
Gaba daya batajin ganin kowa saboda abinda ke damunta sai dai ta tabbatar in taki ganin Hajjo zatai zargin wani abin.
Haka ta fito gaba daya jiki a sanyeye sai dai tayi kokarin danne wa.
Hajjo na zaune a falo Azeema ta shigo ta zauna.
Hajjo ts zuba mata ido tace "Ina kika boye Sabisu?"
Kallanta Azeema tai tace "mene?"
Hajjo cikin gadara tace "badai sirri kuke boyewa ke da Abdulsalam ba?"
Azeema ta daure tace "ke da kika dauke Sabisu shine kikazo dan ki sanar dani ko me? In kin kama sabisun me kike tunanin boyewa?"
Kallanta Hajjo tai sannan tai dariya tace "mene?"
Azeema ta daure itama tai dariya tace "inkin gams tambayoyin da zakimai kya aikon dashi.
Ta wuce ciki, Hajjo cikin kufula ta dau filo tai cilli dashi.
********
Yana sallar asuba ya nufi bangaren Sarki dan kwana yai yana tunanin abinda zaiyi, yanzu kuwa ya gama tattare nazarinsa.
Sarki mamaki ne ya kamashi jin Junaid na neman iso da duku dukun safiyar nan.
Junaid ne ya shigo ya gaisheshi sannan ya zauna.
Sarki ya zauna yace "Junaid ya akai?"
Kallansa Junaid yai batare da ya dauke idanunsa ba.
Sarki cikin mamaki yace "Junaid!"
"Me Marigayi ya sanar dakai lokacin da zai ce ka daukeni ka kaini kauyen nan?"
Kallansa Sarki yai yace "me ya sanar dani? Ba abinda yacemin ka dauka yabar wasiyya ne?"
Junaid yai murmushi tare da sauke kansa kasa, kafin ya hade fuska tamau yace " Ka dauka abinda kuka aikata ba wanda zai sani har duniya ta nade?"
Gaban Sarki ne yai wani mugun faduwa kallansa yai ya kasa cewa komai yana nazarin meya sani?
******
Ayusher🏌🏻♀️
*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*
{40}
Sarki yadan gyara nutsuwarsa yace "Junaid wani shirman ka jiyu? Ina tunanin kai ka girmi aikata irin wadan nan shirmen."
Shirme?
Sarki yace "to nakasa gane me kake san cewa ne gaba daya."
Junaid ya kalleshi sannan yace "ko mu bari anjima mu hadu a fada?"
Abdulsalam cikin faduwar gaba yace "mu hadu a fada ayi me?"
Cikin zazzafan takaici da raunin zuciya ya kalleshi, idanun Junaid gaba daya suncanza sunyi jaa sosai, ya kalleshi bakinsa na rawa na bakin ciki yace "bakaji kunyar kallan Umma dani ba? Baka taba kunyar halakar da mijinta da mahaifina ba sannan ka kallemu kamar ba komai?"
Hankalin Sarki ne ya dugunzuma ya tashi ya daure yace "nifa harayanxu......"
Cikin zafin rai Junaid ya katseshi yace "na hadu da Sabisu, ko haryanzu zaka cigaba da karyatawa?"
Hankalin Sarki yanzu kam kiri kiri ya dugunzuma, yace "Sabisu? Waye hakan?"
Junaid cikin mamakin abinda yace yai dan murmushin takaici yace "ta ina zaka sanshi dama? Kafin in sanar da mutane mugun abinda ka aikata kai gaggawar ajiye mulkin da ka kashe mahaifina duminsa, sannan ka jira hukuncin da ni saban sarki zan maka."
Sarki yanzu ya fahimci inda Junaid yasa gaba, kallansa yai yace "komeya faru na tabbatar baka san mahaifiyarka bace sila? Sannan a dalilin ta cece ka ne akai wannan mumunan abin, shikanshi Zubair din daga baya yasan abinda ya faru."
Cikin tsananin raunin murya Junaid ya kalleshi yace "Abba ya sani?"
Abdulsalam yace "ya san abinda mahaifiyarka ta sa ayi, hakan yasa ya daukeka ya bani na boyeka."
Ha ha ha.....wata irin dariyar bacin rai Junaid yai yace "a naka rashin fahimtar haka ka dauka?"
Abdulsalam ya hade rai yace "me kake san cewa?"
Junaid ya kalleshi cikin zafin rai yace "Ya baka nine yana san ganin iya kacin sanda zakai nadama, sannan ya daukeni daga gunta ne dan ya nuna mata ta nustu ta fahimci halayenka, kana tunanin ya yarda da duk abinda ka fadamai ne?"
Abdulsalam idanunsa ne suka fara canzawa ya turbune fuska yace " ka shiga hankalinka Junaid, duk sanda nakewa Azeema bais yafema danta ba in ya nemi shiga hurimina."
Junaid ya kalleshi yace "ni nawa hurumin daka shiga fa?"
Huruminka?
Junaid cikin zafi yace "mulkin naka ne? Ko kana tunanin badan Hajiya Inna ta rikeka ba har zaka samu damar kai kanka wannan matsayin?"
Yanzu kam hucci kawai yakeyi, Junaid ya kalleshi yace "kai gaggawar sauka daga kan mulkin nan, kwana uku na baka, zanga da wani fuska zaka kalli mutane in sukasan tsubu kukai kuka halaka Sarki Zubair, daga kai har mukarabanka su Shamaki da Waziri da kuka hada baki."
Juyawa yai ya fice.
Ya akai ya san komai yaran nan? Ya tabbatar Sabisu baisan ko rabin abinda ya faru ba, ya akai ya sani? Azeema?
Cikin hanzari ya mike ya nufi bangarenta.
Tana kwance akan gado tsabar damuwa har dan zazzabi ne ya rufeta.
Tana kwance ya shigo, idanunta ta sauke kansa cikin zargi ta zuba mai ido.
Shigowa yai ya zauna kusa da ita, yace "kin fadawa Junaid komai hankalinki ya kwanta?"
Kallansa tai idanunta sun ciciko tace "kenan amfani kai dani ka kashe sarki a matsayin ka ceceni saboda san da kake min?"
Abdulsalam ya kauda kai, mikewa zaune tai cikin takaici tace "yaune rana ta farko dana taba dana sani san da na maka a baya ina mugun dana sanin aurenka da nai, wadan nan sune babban kuskuren dana tafka a rayuwata, wanda bazan taba yafewa kaina ba."
Abdulsalam ya kalleta zuciyarsa na kuna yace "saboda wa na aikata duk abin da na aikata? Ko kina tunanin saboda kaina nai? Duk abinda na aikata nayi ne saboda tsananin sanki da nake, ko kina tunanin zan iya cigaba da ganinki tare da Zubair ne? Sannan saboda wa na aikata abinda na aikata."
Ranta a bace ta sa hannu ta tureshi, tace "karka kuskura kace saboda nine, a haukata da haka na dauka amma yanzu nasan babu ni a cikin tunaninka, kayi amfani da halin da nake ciki ne ka biya burin dake ranka."
Sarki ya kalleta yace "koma menene yanzu bashida amfani, abinda ya faru ya faru, ki fadawa Junaid ya manta komai, yazo yana min kashedin na ajiye mulki nan da kwana uku, ke kinsan ba abu mai yiwuwa bane kinsan halina kinsan abinda zanyi da wanss bazan ba."
Ya juya ya fita, ihu ta kwalla tare da sa kanta cikin cinyarta.
******
Hajjo ce ta kalli Zubair tace "da sassafen nan?"
Zubair yace "da kaina na ganshi Hajjo, bansan me suka tattauna ba amma ransa a bace naga ya fito."
Hajjo tace aika a tambayo Zeena muji ko ta sani, kallanta yai yace "wannan yanda take san Junaid zata fadi wani abu ne?"
Hajjo cikin kuluwa tace "aka mugani ko za'a dace "
Junaid yana fitowa ya kalli bangaren Binta, ya kalli na Zeena, sannan ya kalli nashi sanda ya boye Sabisu, Binta yake san gani amma yana tsoron sata cikin wani hali, bangaren Zeena ya wuce. Sai yanzu tai sallah, tana kokarin kwanciya taga anbude kofa anshigo.
Cikin mamaki da jin dadinta kalli Junaid, bata taba kawowa zai dawo ba.
Tunawa yai ashefa yar Abdulsalam ce ko?
Juyawa yai da sauri ta sako tace "Ya Junaid."
Kallanta yai ta matso cikin jin dadi tace "nagode daka dawo."
Ya zataji in taji mugun halin babanta?
Zeena ce ta kalleshi tace "Ya Junaid?"
Kallanta yai yasan tabbas batada matsala duk rashin tarbiyya na gari ne ke damunta sai babbar matsalarta isa data mata yawa da rashin hakuri, kallanta yai sannan ya wuce ya kwanta.
Kaina kedan ciwo nake san kwantawa.
Cikin jin dadi ta matsa kusa dashi ta kwanta sannan ta kankameshi.
Kamar zai tureta sai kuma ya fasa hannu yasa ya riketa, ajyar zuciya tai na jin dadi.
Tausayinta yake, yasan itama sai ta shiga wani hali.
Bacci ne ya daukeshi dan dama baiyi bacci ba jiya.
Yana tashi yaga bata nan, ruwa yaji a toilet da alama wanka take, fitowa yai ya bar mangaren.
Hadimans suka bi bayanshi.
Bangaren Binta ya kalla, kamar ya je kamar kar yaje, daurewa yai kawai ya kalli Hadiminsa yamai alama.
Nan suka sanar da zuwanshi.
Binta wacce tai wanka tana zaune tasa abincin safe a gaba tana jujuyawa, jin Junaid yasa ta tashi cikin hanzari ta bude.
Yana shigowa ya kalleta yana dariya yace "ya ganki kinyi wani iri? Kamar mara lafiya?"
Shiru tai kawai tana kallansa, Ahhh tunda ba'a san ganins da alama bari na juya.
Da sauri tace "a'a yaya."
Juyowa yai yana dariya yace "na sani ai."
Rungume ta yai yace "ina wannan zatace batasan ganins?"
Tace "in nace fa?"
Yace "hmm duk randa kika fada kinada kyauta."
Dagowa tai tace "ka tabbatar?"
Yace "sosai."
Murmushi tai sannan tace "Yaya komai dai lafiya ko?"
Kara rungumeta yai yace "komai zai zama lafiya insha Allah."
Murmushi tai sannan tace "Allah yasa."
Kallanta yai yace "inata san na tambayeki, kin tabbatar bakyasan a aikama mahaifinki kinyi aure?"
Kai ta girgiza da sauri tace "in ma ya sani me zai min? Ka manta abinda ya mana?"
Hannunta ya kama ya zaunar da ita gaban abincin sannan yadau cup din tea dinta ya kurba sannan ya mika mata.
Amsa tai ta kurba ba tare da ta musa ba, tsamen dake gabanta ya dauka ya kai bakinta, ba musu ta bude bakin yasa mata sannan yace "zan tura Azi ya nemoshi."
Kallansa tai kamar zatai magana sai kuma ta fasa sai murmushi da tai kawai ba tare da tace komai ba.
Gefen kanta ya shafa yace "yau Bintoto..."
Ture hannun tai ta harareshi tace "Ya Junaid kasan banasan sunan ko?"
Dariya yai yace "Bintalo..."
Ajiye cup din tai tace bazan maci ba.
Na tuba a yafemin.
Dariya tai tace "sai ka fadi abin."
Yace ah to bari na shirya.
Hanayenta ta hade tana jiransa.
Dariya yai yace "Nana Fadima na tuba...."
Dariya yai sosai shikuma ya hade fuska.
Tace "Ya Junaid dan sake."
Naki din.
Ya fada cikin wasa.......
Ayusher🏌🏻♀️
*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*
{41}
Kallan Azi yai yace "ka fita wajen gari ka yadamin jita jita cewar Sarki Abdulsalam ganin dawowar asalin dan Sarki Zubair yasa zaiyi Murabus ya ba asalin magajin sarki mulkinsa."
Azi ba tare da tambaya ba yace "To Yarima."
Nan Ya fita da wasu hadiman Junaid, haka sukai ta yadawa tun daga cikin fada har wajen masarauta.
*******
Sam Abdulsalam ya kasa zaune ya kasa tsaye, afa da marwa kawai yakeyi a cikin kilisarsa.
Isowar su Shamaki ce yasa ya koma ya zauna.
Cikin tashin hankali suka shigo, Mai Martaba meke faruwa?
Abdulsalam ya kallesu yace "yaran nan ya san komai."
Galadima yace "taya za'ai ya sani abinda akai yana tsimma? Hatta wanda yai maganin fa mun ga bayansa."
Abdulsalam yace "to kamar mai aljannu yaran nan hankali a kwance yazo ya sanar dani komai, Sabisun kansa baisan abinda ya faruba rabi da kwata in dai har ba aljanu ne dashi ba to ba yanda za'ai ya sani."
Waziri ne cikin nazari yace "ko dai Gimbiya ta fadamai abinda ta sani ne?"
Taya zata fadi abinda tasan zai ja mata matsala?
Shiru sukai suna tunanin abinyi.
Jakadiya daga waje ta nemi iso cikin tashin hankali.
Kallan juna sukai sannan sukace lafiya?
Jakadiya ce ta shigo ta zube tace "Allah ya taimaki sarki yanzu labari ya karade ko ina akan wai zakai murabus."
Hankali a tashe suka kalli juna sannan a tare sukace "Murabus?"
Jakadiya tace "wai zaka maida sarauta inda take, tunda magajin sarki ya dawo."
Cikin tsakanin tashin hankali sukace "magajin sarki? Junaid?"
Jakadiya tace " ka gafarce amma zance ya gama karade gari anata jinjinawa adalcinka."
Sallama tai ta fito.
Ba karamin tashin hankali bane ya bayyana a fuskokinsu, musammsn Abdulsalam wanda yakeji duk duniya ba mai rabashi da kujerar mulkinsa.
Shamaki ne