Showing 42001 words to 45000 words out of 76752 words

Chapter 15 - ZAFIN RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

ayusher   

26 Aug 2024

8582

jikinta. "Azeema ki tsaida zuciyarki waje d'aya, kinsan har abada banzan cutar da jininki ba, auren wad'annan yaran shine Makullin sirrinmu, ko kina tunanin duk randa shi kansa Junaid ya san sirrinmu zai d'aga mana k'afane? Bayanann ki tuna inada d'a Zubair, ya girmi Junaid, atunaninki shi mahaifiyarsa batason yayi mulki? Had'in auren Junaid da Zeena itace hanya mafi sauk'i wajen dank'a masa mulki da maganin tasowar duk wata k'ura da muka binne a baya".

Ajiyar zuciya Azeema ta sauke, tad'an gamsu da jawabinsa, saidai gaskiya batason had'a zuri'a da hajjo, amma tasan matakin dazata d'auka, sannan tana a kan bakanta Na aura masa d'iyar mashahurin sarki.



******************

Washe gari Azeema da kanta ta buk'aci ganin Junaid. Anutse yai shirinsa cikin kayan alfarma, Azi yai masa rakkiya tamkar kullum.

Bayan an masa iso yasamu shiga har cikin k'uryar d'akinta.

A zaune ya isketa tayi shiru dan ko shigowar shi bataji ba tsabar ta shiga cikin tunani mai zurfi, kallo d'aya zakai mata kuma ka fahimci tana tare da damuwa. Da sauri ya k'arasa gareta, "Umma lafiya kuwa?".

Hannunta ta janye tana sauke ajiyar zuciya, ta kalli Barira dake tsaye a k'ofa. "bana buk'atar motsin kowacce hadima, kowa yaje sai nan da awa d'aya Ku dawo".

Barira ta jinjina kai da fad'in "angama ranki ya dad'e" juyawa tai ta fita zuciyarta na mamakin minene matsalar uwar d'akin nasu, tunda tadawo sashen mai martaba da asubahi batada walwala.

Azeema ta maida kallonta ga junaid dake durk'ushe gabanta, hannunsa ta Kama tana masa nuni daya zauna sosai. Bai musaba ya zauna, murya a raunane Yakuma mai-maita Mata tambayar d'azun.

Tad'an murmusa domin kauda damuwar fuskarta, "Ka kwantar da hankalinka Junaid, babu abinda ke damuna, yanzu natashi a barcine. Nakiraka ne muyi wata magana".

"ina saurarenki Umma" Abinda yace kenan duk da bai gamsu ba.

"Junaid me kake tunani akan Zeena?"

Duk da yasan me take nufi amma sai yai kamar bai sani ba yace "Zeena? Me nake tunani kamar ya?"


Ta daure tace "Junaid zaka iya zaman aure da Zeena?"

Cikeda mamaki ya kalleta, "Umma miyasa kikaimin wannan tambayar?"

"Saboda inason ka aureta".

Y'ar zabura yai cikeda tsoro dan duk da yasan maganar amma bai kawo har an shawo kanta , ta yaya? Kwana daya kacal? Tabbas akwai abin bincikawa a wannan lamari.

Kallanta yai yace "Umma miya birgeki ga yarinyar data fara tozartani farkon shigowara masarautarnan, ama bar wannan rashin sanine amma gaba daya yarinyar nan batada tarbiyyar data dace, meya birgeki dahar kike tunanin had'a jininta da naki?"

Tambayar ta daki zuciyarta, amma saita danne, cikin dai-daita kanta tace, "Ka d'auki hakan matsayin kuskure Na rashin sani, sannan Zeena batada matsala matsalarta daya rashin uwa mai tsawatar mata."

Shiru Junaid yai yana nazarinta, lallai zuciyarsa takuma yarda akwai sirrin dake tsakanin sarki da mahaifiyarsa, to amma nami? Miyasa zai zargi mahaifiyarsa da kansa? Ya salam zuciya wannan k'aryane, ummana bazata aikata komai na son zuciya ba duk da bai gama saninta ba amma yana mata fatan hakan............

Tunaninsa ne ya katse saboda dafashin da tayi.

Daidaita zamansa yai ya kalleta bayan ya canza yanayin fuskarsa.
"Zan amince da auren Zeena amma da sharad'in in har zaki amince ku hadata da Binta."

Wata muguwar zabura tayi tana kallonsa cikeda tsananin mamaki. "Junaid kanada hankali kuwa?"

Murmushi yai cikin wani yanayi mai wuyar fassara yace "Ummana lafiyar d'anki k'alau."

Bazai taba yiwu ba kai kasan bazan yadda ka auri Binta.

Kallanta yai yace "Na yanke wannan shawaran ne ba dan komai ba sai zargin da nake akwai manufar mai martaba na had'ani aure da Zeena, inhar y'ancinmu kike buk'atar mu k'wata, mulki yadawo gareni kamar yanda kike buri to lallai dolene na had'asu su biyun, inba hakaba zanbi tawata hanyar na bankad'o gaskiya, dan inada abubuwan da ban gansu dasu ba, inason sanin dalilin mahaifina na sakawa a maidani na rayu a ke6antaccen waje bayan yasan mahaifiyata nada ranta......"

Kallansa tai tabbas Junaid jinin Zubair ne wanda ya dace da mulki sai dai in har yayo halin Zubair tabbas ita kanta bazata tsira ba, hankalinta ne ya tashi ta kalleshi tace Junaid Na Neman k'ara Mata zafi akan Wanda sarki ya had'a Mata a daren jiya,

Daurewa tai tace "Amma Junaid hadin auren ba shi bane, yanzu na maida Binta 'ya, zan samo maka wata ka aura."

Ido ya kura mata yace "Me kikace a gaba da daraja abu mai daraja?"

Kallansa tai batace komai ba, yace "indai har bazaku amince da hadin auren da Binta ba to nima bazan auri Zeena ba inyaso kowa yasha zamansa."

Ya fada fuska a hade.

Kallansa tai kanta taji ya fara sarawa, itakam sakayya ce take neman afkuwa da ita.
Mikewa yai yace "in kinyi nazari mayi magana, nabarki lafiya Ummana."

Shiru tai haryabar dakin, meyasa komai baya tafiya yanda takeso? Haryakai kofa tace "shikenan!"

Da sauri ya juyo ya kalleta, murmushin yake ta kakaro tace "shikenan ka auresu, indai inaso in daraja abu mai daraja dole naso abinda abin da kakeso."

Jikinsa ne yai sanyi, ya tako a hankali zuwa inda take ya durkusa yace "nagode Ummana."

Shiru tai batace komai ba...


******
Binta kam gaba daya wani irin zazzabi ne takeji yana neman rufeta, tun abin da ya faru jiya, idanun Junaid take hangowa da yanda ya nuna bai damu da ita ba.


Wasu zafaffan kwala na dana sani ne ke zubo mata, da alama zamanta a gidan nan ya kare.
*****


Zeena kam abincin gabanta kawai take jujuyawa ta kasa ci, kallan Fure tai tace "Fure me kike tunani a kan matsayina gun Ya Junaid?"

Fure tai dariya tace "ai Yarima ya fara fuskartar kedin kece kika dace dashi ko baki ga abinda ya faru jiya ba, kiga yadda ya wulakantata saboda ke."

Kallanta Zeena tai a ranta tace "inafa wulakantata ya jani falo dai ya wulakantani san ransa."
Saura Hajjo abinda ta fada kenan a ranta, mikewa tai tace "muje gun Hajjo."

Da sauri Fure ta taso.....


****


*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍*

{30}


********************

Ran Hajjo a 6ace ta kalli amintacciyar baiwarta. "kina nufin jiya Azeema a turakar mai martaba ta kwana?".

"Wannan gaskiyane ranki ya dad'e, lamarin ya girgiza kowa, dan ansan dai kwanankine jiyan...."

Zeena dake zaune tana karyawa tai saurin fad'in "To banda munafunci irinna bayi miya ruwanku? Shi Abba bashida damar kusanci da kowacce matarsa a lokacin daya so? Kunsan dalilin kwanan natane dazaku kawoma mutane tsirku"

Duk Harar da hajjo ke zubama Zeena batai shiruba saida takai aya. Sosai hankalin hajjo yakuma tashi, dan dama labarin zuwan Zeena sashen mai martaba sau biyu dukya zomata.

Da sauri tace, "inason a nemamin ison zuwa sashen mai martaba yanzunan".

"Angama ranki ya dad'e".


Babu dad'ewa da tafiyar baiwar tadawo da sak'on mai martaba yanada bak'i Na musamman. Dole hajjo ta hak'ura da zuwan.

Zeena ce ta daure bayan sun fita tace "Hajjo."

Kare hade rai Hajjo tai ta kalleta tace "ke kuma menene?"

Ganin yanayin Hajjo yasa ta kasa cewa komai.

Shikenan, dama cewa zanyi Ya Zubair ya fara karatun?
A kufule tace eh.
Zeena tai shiru tana tunanin ta yanda zatai ta mata bayani.


*********************


Yinin yau gaba d'aya mafi yawan masarautar sunyisane acikin rashin dad'in rai, dan kowa da tabon damuwarsa cikin zuciya.

Gimbiya Azeema, hajjo, Junaid, Zeena, Binta. Sai sarki daketa shirye-shiryen Neman mafita, dan kuwa yayi zama Na musamman da manyan fadawansa akan shirin auren Zeena da Junaid, da tu6e Zubair daga sarautar matawalle a nad'a Junaid.

Dukkan wani hukunci sun yankeshi akan auren Zeena da binta, Wanda za'a d'aurama Junaid arana d'aya, sannan amasa nad'in sarautar matawalle.

Fadawan dabasusan sirrin sarki Abdusslam ba mamaki yakamasu ainun, ganin ansaka bikin auren kusa, sannan zai tu6e d'ansa daga matsayinsa yabama Junaid rawanin bayan Zubair shine babba, shiya kamata afarama aure kafin Junaid. Basuda hurumin bin ba'asi dan haka sukai tsitt.
Lalai Sarki yana da adalci.

******************

Da yammacin ranar Azeema ta nemi izinin ganin sarki Abdussalam.

Kai tsaye yabada izinin shigowarta.

Kokad'an fuskarta babu walwala, sa6anin shi ta sarki dake a washe da farinciki. Koda ta zauna yai k'ok'arin ta6ata saita janye jikinta.

"Ba wannan ne yakawoniba Takawa."

Sarki ya dakata daga k'ok'arin ta6ata, sannan ya gyara zamansa, "ina saurarenki"

"Na isarma Junaid da sak'onka, amma shima yazo da nasa sharad'in".

"Sharad'i kuma? Name kenan?"

"Inhar zai auri Zeena saidai ya hadasu da yarinyar da sukazo tare."

Ta zayyane masa duk yanda sukai da Junaid.

Dukda shi Junaid yafara sanarma hakan saida zuciyarsa ta k'ara sosuwa, cikin danne yanayinsa yace, "To Azeema mizai Hana mu kar6i nasa za6in, watakila akwai nasa hangen shima?"

"Wannan had'in baiminba, amma Zan amince dashi, daga baya Na d'au mataki"

"Mataki?!"

"Wane iri kenan?"

Murmushin da tunjiya batayiba ta Saki, ta mik'e tsaye tana kallon sarki "zakaji koma wanene anan gaba, dan bazan had'a zuri'a da y'ar da batada asaliba"

Shima sarki abdussalam murmushin yayi, dan hakan yamasa dadi dari bisa d'ari. Kafin yabata amsa harta fice.



********************


Binta abin duniya duk ya isheta, gaba d'aya ganin Junaid yamata wahala, anbata y'ancin kanta amma an nisantata da yayanta, Wanda tasani tun a k'uruciya.

Shi kansa yamanta da ita gaba d'aya, hangensa ma da takeyi daga nesa yanzu ya gagareta, batada aiki saina kuka da zaman d'aki, ko wajen harira ma yanzu tabar zuwa tun randa Zeena ta mareta ya Junaid kuma yai halin ko in kuma da ita, ga zazzabi dake cin jikinta, abin haushi ba wanda ya damu da yanayin da take ciki.

Takanje wajen bishiyr kwanaki ta zauna taita tunani, kewar mahaifiyarta da Junaid na damunta, wanda ayanzu haka datasan ina zata samo mahaifinta da babu abinda zai hanata guduwa garesa, wanda ya koresu ba tare da ya sake waiwayar su ba?

Da ire-iren wad'annan tunanin take rayuwa yanzu, sune abokan hirarta a koyaushe, dan tasan abokin hirrar nata dai yamata nisa gaba d'aya.



Zeena da suka fito daga bangaren Hajiya Inna ta hango Binta a zaune ajikin bishiya kamar yadda ta saba zama wato jikin bishiya.

Tsayawa tai tana kallanta cikin takaici, da tuno abinda Junaid ya aikata mata akanta, sannan wai da ita za'a hadasu zaman kishi? Lalai zata fuskanci wulakancin da har gwara ta hakura.

A hankali ta tako zuwa inda Binta take wacce batama ganta ba tana zaune tana rubutu a kasa.

Fure ce tace "uban me kikeyi anan kin tarewa Gimbiya hany?"
Cikin mamaki Binta ta mike sannan ta matsa, duk hanyar can bata isheta ba sai tazo nan?


Zeena ce ta mata wani kallan banza sannan tasa kafa a inda Binta zata wuce ai kam Binta ta afka kasa, da sauri ta dauke kafarta sannan ta girgiza kai cikin takaici tace "kina mace amma bakya kallan hanya inkina tafiya."
Taja dan karamin tsaki ta wuce.

Binta dake yashe a kasa ta dago ta bita da kallo.

Fure ce ta kwashe da dariya tace "Gimbiya!"

Zeena ta hade rai tace "menene?"
Da sauri tace bakomai.
***********************

Washe gari labarin auren yarima Junaid yafara zagaye cikin masarautar, sai dai babu wanda yasan wacece amaryar, sai kus-kus ake da hasashen y'ay'an manyan sarakuna dake da alak'a da masarautar.

Hakan yakuma tada hankalin hajjo, dan aganinta Zubair ya cancanci wannan auren gatan ba Junaid ba, gashi jiya tabuk'aci ganin mai martaba amma yak'i aminta su gana.

Tarasa mi ake 6oye matane itakam.
Gashi sarki yak'i cewa komai gameda auren Zeena da Sulaiman

Mamakine ya kamata ganin Zeena ko kad'a bata damu da zancen auren na Junaid ba.

Shiru tai tana tunani kafin tace ina Zeena?

Tana ciki Hajjo.
Hajjo tace "a kirata."

Zeena ce ta fito daga daki tana kwance tana hutawa, duk da dai haushi ke damunta ana zancen bikinta amma kwakwata Junaid ko nemanta bayayi, ita kuma tana san ganinsa amma kunya takeyi.

Hajjo ta zuba mata ido cikin zargi tace "kinji Junaid wai zaiyi aure ko? Dazu Ramlah ke fadamun."

Zeena ta kalleta cikin waskewa tace "Hmmm."

Ido Hajjo ta kara kura mata tace "sai yaushe zaki fadamin me kukai keda Mahaifinki?"

Zeena ta kalleta tace "Hajjo!"

Hajjo tankankance ido tana kallanta.

Tasowa Zeena tai ta zo gabanta ta tsuguna ta riko hannunta, Hajjo kallanta kawai takeyi tace "Hajjo ki barni na auri Ya Junaid dan Allah, ni banga namijin dayamin ba irinshi."

Hannunta Hajjo ta zare da sauri tace "me kike nufi?"

Zeena tai shiru kafin tace "nice!"

Kece? Kece wa?
Da karfi ta fadi hakan wanda yasa hankalin Zeena ya tashi, Hajjo ta tureta ta fito daga falanta.

Bangaren Azeema ta nufa cikin hanzari.

Inba da dalili ba Hajjo bata taba zuwa bangaren kowa sai dai ta aika azo.
Kafin Barira ta mata iso harta fada ciki.

Azeema dake zaune tana nazarin abubuwan dake faruwa kawai taga Hajjo a tsakiyar falan ta, cikin mamaki ta kalleta tace "Hajjo?"
Hajjo cikin bacin rai tace "wani munafurcin kuke shirin yi ke da Takawa?"

Kallan gadara Azeema ta mata sannan tace "koma me muke hadawa mijinki ne ai, bakya tunanin shi ya kamata ya sanar miki koma wani irin munafurci ne"

Hajjo ta kara kufula tace "kina tunanin hada Zeena da Junaid aure saboda ku amshi mulki kin dauka ban san me kike shirin yi ba?"

Wani lalausan murmushi Azeema ta saki sannan tace "sai Junaid ya auri Zeena ne zai amshi halak dinsa?"

Halak?
Cikin kufula Hajjo ta tambaya, Azeema tace "ba Halak dinsa bane?"

Mene?

Hajjo ta fara huci, Azeema tai murmushi tace "Ni yanzu banasan jan magana tsakanina dake a matsayin mu na sirikai."

Gaba daya ran Hajjo ya gama baci, takai bango makura, a zuciye ta juya tai waje.

Azeema tai tsaki tace "ko wayake san yar taki?

*********

Bangaren Abdulsalam ta nufa a zuciye.

Yana zaune suna tattauna abinda suka tsara shi da Hakimi, Hajjo ta iso, Jakadiya da sauri ta matso tace "Hajjo."

Daurewa tai tadan saita nutsuwarta, tace "yimin iso."
Da sauri Zagi ya fara sanar da isowarta.

Abdulsalam ya kalli Hakimi yace "kaje zan nemi ka."
Nan ya mike yai musu sallama.

Hajjo ce ta shigo rai bace.

Zama tai sannan ta kalleshi.

Gani tai fuskarsa a murtuke daurewa tai tace "Yanzu abinda akamin an kyautamij?"
Name kenan?

Tace " yanzu taya zaka hada auren Junaid da Zeena? Sannan bada sanina ba?"

"To yanzu kin sani ai? Sannan yarki bata sanar dake ba?"
Kallansa tai rai a bace, yacigaba "itace take sanshi kinsan yanda akai na shawo kansa ne? Ko kuwa tijara zakimin?"

Shiru tai tana kallanshi cikin takaici.

Yace "idan har baki amince da auren nan ba to tabbas ko me yaje ya dawo bazan taba shiga zancen 'ya'yanki ba."

Ya mike yai ciki ba tare da ta tofa kofa komai ba.

Hajjo kamar tasa ihu yanzu haka zata bari komai ya faru ba tare da tayi wani abin.

Haka ta fito jiki a sanyaye.


*******

Zan iya cewa babu wani farin ciki gaduk 6angarorin ma'auratan, idan kacire sarki kawai. Sai dai kowa yana dannewa wajen 6oye k'in auren


A 6angaren Junaid kam yana farin cikin kusantowar binta gareshi, yayinda wani sashe na zuciyarsa yake takaicin auren Zeena, amma kokad'an baya nuna hakan, saima farin cikinsa dayake, ko baccinya kwanta wani irin dadi yakeji akan zai dawo da Binta kusa dashi. Ko yayarsa Safiyya datazo tana nuna takaicinta da duk aurarrakin nasa nuna mata yayi duk za6insane.

Hajiya Inna ma tayi fada sosai, sai dai data kira Junaid shi yace mata shi ya zabi hakan.

Hakan yasa bata iya kara cewa komai ba.......

Zancen auren Junaid da Zeena yazo har kunan Binta, ranar tayi koka sannan ta san zamanta anan ya kare, dole zata tafi koda kuwa batasan inda zata nufa ba.


***

*ZAFIN RANA*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ*

{31}

Hajjo sai safa da marwa take a cikin dakinta, Zeena na zaune a kasa tana bin kafafunta da kallo.
Hajjo can ta juyo ta kalleta tace "da wacece?"

Zeena ta kalleta tace "watace da suka taho tare, amma ya akai kika sani?"
Cikin kufula Hajjo tace "Banza shashasha, wannan wannan wlh kinfi Zubair dodadiyar kwakwalwa, banda hauka da jakanta har yaushe kika fara san Junaid da zaki yadda ya miki kishiya tun kafin ya aureki? Nasan dai a matsayinsa na yarima dole ne bazai zauna da mace daya ba amma a kalla ke ki shiga ki haihu tukunna mana."

Zeena tai shiru a ranta tace "nima ce miki akai ina san hakan?"

Hajjo kamar ta zuba mata duka takeji tace "sa a kiran yarinyar na ganta."

"Ki ganta kiyi me?"
Kin wuce ko sai na kifa miki mari?

Zeena ta mike rai a bace tana 'yan kunkuninta.

Fure ta aika tace "jeki kira Binta, karki bari Umma karama ta ganki."

Fure tace "Gimbiya ina na isa shiga bangaren......."
Kafarta ta saka ta taka tata kafar, yar kara Fure tai sannan tace "Angama Gimbiya."
Da sauri ta juya ta fita.

Fure tayi sa'a taga kawarta wacce take aiki a bangarn Azeema nan ta turata ta kira Binta.

Binta dake sa kaya ta fito da wanka da kyar saboda zazzabin dake cikin ta ne ta kalleta sannan tace "gatanan zuwa."

Rigarta ta saka sannan suka fito tare.

Hajjo tayi shiru tana tunanin munafurcin da aka kulla tsakanin Azeema da Sarki dan tasan wlh tabbas akwai dalilin dayasa Azeema ta yarda da hadin nan.

Shigowar Zeena ne yasa ta kalleta, Zeena tace "gata a waje."

Hajjo ta fito cikin falanta tasa Binta ta shigo.

A hankali Binta ta shigo ta zube kasa tana gaisheta, Hajjo bata amsa ba sai dai ta zuba mata ido tana kallanta kallan kurula, Binta kam gabanta sai faduwa yakeyi hakan yasa ta kasa dagowa.

Ke!
Hajjo ta kirata da haka, Binta ta dago a hankali, fadamin wanene mahaifinki?
Binta a hankali cikin faduwar gaba tace " tun ina karama ya koremu bansan inda yake ba."

Mene?
Binta ta kalleta ta kasa amsawa saboda hawaye dake neman zubo mata.

Uwarki fa?

Zeena ta kalli Hajjo da sauri, Binta ce ta goge hawayenta tace "ta rasu."

Ha ha ha....ta rasu?

Binta bakinta na rawa tace lalai ya nuna mana halin rashin tarbiyya daya samu ta iyaye, ya rasa wanda zai hadaki kishi da ita sai wannan abar?"

Binta wacce kanta ke sarawa ta kasa gane me suke nufi.

Zeena cikin jin haushi ta zuba mata ido tana harara.

Fita daga nan.
Hajjo ta fada, Binta ta mike da kyar ta fito.

Da sauri Zeena tasha gabanta, ta kalleta tana huci tace "kiyi gaggawar sanar da Ya Junaid bazaki aureshi ba, ko ki hada shirgin tsumokaranki ki bar gidan nan."

Zan bar gidan nan in har Ya Junaid yace na........

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login