Showing 6001 words to 9000 words out of 76752 words

Chapter 3 - ZAFIN RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

ayusher   

26 Aug 2024

8561

yana tunanin mafarkin dayai mara dadi.


***********

Hannu yasa ya rikota yana neman jawota jikinsa ta dan zare jikinta daga nashi, kallanta yai cikin rashin jin dadi yace "Azeema sai yaushe ne zaki saki jiki dani? Ni fa mijinki ne, shekara nawa kenan?"

Kallansa tai kamar zatai magana sai ta fasa, mikewa zaune yai ya kalleta yace "ko baki amince dani ba a kalla ki dawo yanda muke dake da ke kanki kinsan dake kadai nake iya shawara."

Kallansa tai sannan tace "Abdulsalam, kace har yanzu ba'a samo Junaid ba?"

Kallanta yai yace "eh."

Ido ta kuramai kafin tace "Taya za'ace kamar kai a garin nan neman yaro ya gagareka? Shekara nawa kenan?"

"Shine dalilin da yasa kika kasa sakar jiki dani?"

Kallansa tai, jawota yai jikinsa ya rungumeta yace "kina tunanin zan cutar miki da danki? Ni?"

Tace "a'a amma baka nemanshi."

Dagota yai yace "ki sa a ranki Junaid na cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali, bakya tunanin in kikai wannan fatan zakiga hakan ya tabbata?"

Shiru tai tana kallanshi, yace " ba neman mu'alama ta aure nake dake dole ba amma ki saki jiki dani dan Allah, kinfi kowa sanin bazan taba cutar dake ba."

Murmushi ta masa sannan tace "kayi hakuri."

Kara rungumeta yai a ransa yana cewa kiyi hakuri Azeema.

Su biyu ne a cikin dakin Hajjo ta kalleta tace "kinsa an duba?"

Kallanta tai tace "Hajjo danaje gun malam cewa yai akwai mutum daya da zai hana Zubair hawa mulki indai kin halaka shi to lalai ba abinda zai hanashi hawa."

Tsaki tai tace "dayan fa?"
Yace "ki sa masa a abinci indai yaci to lalai zai ji Azeema ta fita a kansa."

Ta karasa tana mika mata dan abu, Hajjo ta sake yin tsaki tace "Ni wai ke Ramlatu haryanzu hankali bai gama shigarki bane?"

Da sauri Ramlatu ta kalli Hajjo, Hajjo tace "Takawa mijin wanene? Ba mijinki bane?"
Tace "miji nane."

Hajjo ta kalleta tace "sai na fada miki abinda zakiyi ki jawo mijinki gunki? Wannan aikin ki ne ki rabashi da Azeema dan ya soki bawai aiki na bane."

Ramlatu ta daga kai da sauri alamar ta fahimta sannan tace "Nagode Hajjo."

Hajjo tai murmushi tare da rike mata hannu tace "duk yanda za'ai ki kwace mijinki daga gun Azeema, tasa kinyi boranci lokacin Marigayi karki bari yanzu ma ki kare a boranci."

Ramlatu ta ce "nagode Hajjo ke kadai ke sona."

Hajjo tace " Zancen Zubair da wani zancen wani zai hanashi hawa mulki da alama yayi kuskure, dan kannen Zubair maza 'ya'ya nane kuma duk cikinsu kowa yasan Zubair ne mai mulki, kar ki damu ke dai kiyi aikinki."

Ramlatu ta daga kai alamar gamsuwa, sannan tai godiya ta fito.

Hajjo ta bita da kallo, matsalar ta daya Zeenatu, indai ta aurar da ita ta gama, Ramlatu zata kula da Azeema.

*********

Cikin dare yaji mostin bude kofa hakan yasashi bude idanunsa, Azi ya gani a jikin kofarsa, mikewa yai daga kan gado, kayan jikinsa ya canza zuwa kalar tausayawa, sannan ya fito ya maida kofar dakin ya rufe, dakin Binta ya kalla jiki a sanyaye, jiya dama sai sakalci takemai, wai batada lafiya.

Ya dade a jikin kofar kafin a hankali yasa hannu ya murda, kallanta yai tanata bacinta hankalinta a kwance, ya zatai in ta tashi taga baya nan? Duk da gobe zai dawo amma ji yake gaba daya ba dadi, yasan gobe sai kuka in bata ganshi ba.

Ko dai ya hakura da zuwa? Da sauri ya maida kofar ya rufe ya kalli Azi dake kallansa, Junaid yai murmushin yake yace muyi sauri muje mu dawo kafin hankali Binta ya tashi.

Azi ya kalleshi tare da daga kai alamar to.

Sun fito suka fara tafiya dan zuwa kauye na gaba inda ake hawa motar ice dan zuwa cikin garin Biram.


Sun isa suka tadda an cika mota hakan yasasu saurin shiga aka dau hanya.


**********
Ayusher pg 5
***********

*ZAFIN RANA*



HASKE WRITERS ASSOCIATION


*Na Ayusher Muhd*


Shafi na shida



Sun isa garin Biram tunda suka shigo Junaid yake bin ko ina da kallo gaba daya yanayin fuskarsa ya canza.

Azi ne ya kalleshi yace "Yar......"
Kallan da Junaid yamai ne yasashi dan murmusawa yace "Wali."

Tare suka sa dariya dan Junaid yace har su koma da sunan Wali zai dinga kiransa, Junaid bayan sun gama dariyar ya kalleshi yace "Allah ya sa bakin nan karya min tabargaza."

Azi yai dariya yace " ni shigar taka ma tafi ban dariya."

Junaid ya kalli kanshi wasu irin kaya ya saka, wando da riga daban, sannan ya kima wani nadi akansa.

Murmushi yai yace "karka manta da wuri zamu koma dan nasan Binta in taga ban dawo ba kuka zataitayi."

Azi yace "to, dama kudin kayan abinci zan amso ba dadewa zanyi ba."

Junaid ya dan tsaya sannan ya kalleshi yace "wake baka?"

Shiru yai yana kallansa, Junaid ya cigaba da tafiya kawai yana cewa "barshi ma dan banasan ji."

Sun isa masarautar Biram, Azi na isa suka fara gaisawa da dakarun gidan sarki, Junaid na binshi a baya, sun dau hanya zuwa can cikin masarautar, Junaid ya kalleshi yace "mu hadu a tasahar mota kafin rana ta fadi."

Azi yace to, har Junaid ya fara tafiya yace "Wali."

Junaid ya kalleshi, Azi ya matso yace "kayi hakuri da duk abinda zaka gani."
Junaid ya kalleshi ba tare da ya amsa ba kawai yai gaba.

Azi yai shiru yana binsa da kallo, yana tausayinsa sosai, duk da su a tunaninsu gata suka mai amma ta ina zai fahimci hakan? Bayan an rabashi da kowa nashi.


Junaid yana tafe yana kallan cikin masarautar, sam baya tuna abinda ya faru a ciki, duk kuwa yanda yaso ya tuna din.

*********

Yau kamar yanda suka saba akwai rana daya da suke warewa duk matan Sarki na zuwa gun Uwargida sarauniya, a zauna a na cin abinci ana dan hira.

Azeema ce ta kalli Bari suna kan hanyarsu ta zuwa tace "ni wai waye ya kawo wannan bidi'ar??

Bari tai dariya tace "kece ai Gimbiya."

Azeema ta kalleta tace na sani ai, Bari tai murmushi suka karasa, dukansu kowa ya hallara da alama itace karshen zuwa.

Gaba daya ta kula ma gulmar ta akeyi saboda tana shiga kowa yai shiru.
Wucewa tai ta zauna a gun da aka tanada duminta.

Kallan Hajjo tai tace "Hajjo barka da war haka."

Hajjo ta kalleta fuska a sake tace "Azeema barka dai."

Nan kowa ya gaisheta itama, ta amsa fuska a hade dan batasan wargi.

Sun danyi shiru kafin Ramlatu tace "Hajjo ya maganar Gimbiya Azeema ne? An daidaita da Yariman Gobir din?"

Hajjo ta kalleta sannan ta kalli Azeema tace "ai Zubair ya mata magana, kinsan duk inda 'ya'ya mata suke suna shakkar maganar 'ya'ya maza, tunda ya mata magana da alama ta shiga hankalinta."

Azeema ta fahimci magana take neman fada mata, kallanta tai tace "sosai amma yawanci zakiga indai kinsamu yarinya mai jin magana sai kiga kafin ma akai ga haka tafahimta."

Ran Hajjo ya kai matuka gun baci ta kalleta tace "Hakane sai dai akwai lokacin da maza kan taka rawar gani sosai akan rayuwar kannensu, oh bama wannan ba a rayuwar mu ta bahaushi duk yawan jikokinka indai daga gun 'ya'ya mata suke to ba naka bane."

Azeema ta jinjina kai tace "hakane, sai dai akwai yara dawa Hajjo da baki sani ba wanda daka haifesu gwarama babu."


Fuskar Hajjo ta canza sosai a wannan lokacin dan ranta yakai matuka gun baci, dan har fuskarta sai data nuna.

Dariya ragowar mata suka sa saboda sun fahimci hakan, Ramlatu tace " hakane sai dai kowa nasan ganin nasa."

Azeema ta dan yi dariya kadan tace "sosai, ai gani naka akwai dadi."

Gaba daya hirar ta rage armashi saboda Hajjo tunda ranta ya baci bakomai ma take sa baki.

******

Yana tafe yana waige waige dan ya rasa ta ina zaibi.

Ita kuma wacce ranta ya baci saboda haushin zancen Yariman Gobir din nan da ake mata ta taho cikin bacin rai, tana shawo kwana shi kuma yana juye juye.

Sam bai kula dasu ba yasha gabansu yana waige waige.

Yauce rana ta farko da wani bawa zai tsaya a gabanta.

Cikin tsananin zafin rai ta kalli Bawan dake kula da ita.

Kusa da Junaid ya isa yace "kai dan gidan bafaden, dan gidan asararru, dan gidan wanda basu san kansu ba."

Cikin mamaki Junaid ya kalleshi dan baisan me ya aikata ba haka ake buga mai zagi haka.

Bafaden nan ya hankade Junaid daga kan hanya wanda hakan yasa shi ya fadi kasa, kallansa yai sannan ya kalli mutanen dake bayan mutumin wanda sai yanzu ma ya kula da zamansu.

Mikewa Junaid yai cikin mamaki yace "Bawan Allah me nai daka hankadeni?"

Bafaden ya juya ya kalli Gimbiya wacce ta kara kuluwa, kallan Bafaden tai tace "biyoni dashi."

Tana fadan haka ya cafko Junaid wanda ya kara kallansa yana neman kwace kansa yace "kai malam, meye hakan?"

Jansa yai suka cigaba da tafiya, ganin duk maganar da yakeyi Bafaden bashi da niyyar sakarsa ne yasashi yao shiru.


Zeenatu kam tana tafe tana masifa a ranta dan tabbas taji haushin wannan rainin wayan, wato yanzu ko wani ma kazami rainata zai fara yi.

Bangaren Hajjo tai dan dama can zata.

Tana shiga a harabar tsakar gurun ta kalli baiwarta ta mata alama da ta matso, tana matsowa tace "Fure debo ruwancan ki watsama wancen bawan."

Fure ba tare da musu ba tai hanyar bakin tulun, totulo ruwa tai ta matso kusa da Junaid dake kallan yarinyar ransa a bace, jiyai an shekamai ruwa ba tare da ya ankara ba.

Wani irin sheka yai sannan ya kalli jikinsa, sannan ya kalli matar, baki ta dan tabe sannan tace "Fure karo."

Nan Fure ta kara tutulo ruwa ta kara shekamai.


Junaid yasa hannu ya goge fuskarsa idanunsa haryanzu suna kanta, wanda ita kuma tasa a ranta sai ya daina kallanta zata daina sawa a zuba mai ruwa.

Alama tama Fure nan Fure ta kara debo ruwa ta sheka masa.

An debo ruwa na shidan ne, Zubair yace "meye hakan?"

Juyo tai ta kalleshi wanda ya shigo dan gaishesu, daga bakin kofa ya kalleta, kallansa tai sannan ta kali Junaid, ganin haryanzu ya kafeta da ido ta kalli Fure ta kara mata alama, nan fure ta juye shi a jikinsa.

Ran Zubair ya baci ya wuce ciki, yana shiga ya kalli Hajjo yace "Umma kima Zeena magana."

Kallansa tai tare dayimai alama akan yai shiru, Zubair ya kalleta sannan ya kalli waje wanda hakan yaba Azeema damar fahimta.

Kallan Zubair tai tace "me autar tai?"

Ta fada tana kallan Hajjo.

Nan hajjo tace "kiramin ita."

Yana mikewa Azeema tace "bari naje na mata magana."

Bata jira amsar Hajjo ba tai gaba, nan sauran mata suka mike, Hajjo kam tana tsoron kar Zeena ace abu tai mara kyau yasa ita ma ta mike da sauri.

Suna fita waje ana kara shekama Junaid ruwa.

Cikin mamaki da takaici Hajjo ta kalleta tace "Zeenatu!"

Zeena ta kalleta sannan ta kalli matan dake gun, idanunta ta maida kan Hajjo tace "kalli abinda yakemin."

Nan kowa ya kalleshi, ya tsare Zeenatu da kallo haryanzu idanunshi na kanta.

Hajjo ranta ya baci ta kalleshi, Ramlatu ta matsa da sauri ta gauramai mari tace "ka dauke idanka ko sai munsa an dauke mana su yanzun nan?"

Junaid ya dago ya kalli Ramlatu yace "mene?"

Azeema kam idanu kawai ta kuramai, ya yake kama da Junaid dinta?

Wanene wannan?

Zeenatu ta matso tace "mene kace?"

Kallanta yai yace "to fadamin mena miki? Me na miki da zaki aikata min wannan abin?"

Yai maganar cikin fushi.

Baki kowa ya saki, cikin tsananin mamaki, yauce rana ta farko da bawa ya taba magana haka.


*Ayusher.*

*ZAFIN RANA*



*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*


Shafi na Bakwai


Ran Zeena ya kai matuka gun baci, kara wanka mai wani marin tai ta kara daga hannu zata sake marinsa, Azeema tace "Zeena."

Zeenatu ta dakata amma ta kasa sauke hannunta, Kusa da ita ta karaso ta kalleta sannan ta kalleshi tace "me zaisa ki nemi tada hankalinki? Bawa yayi laifi ki bari a hukuntashi amma yin hukunci da kanki ai wahalar da kanki kikeyi. Bafaden nan ta kalla tace "a kulleshi kar a bashi abinci yau."

Da sauri bafaden nan ya fizgi Junaid wanda ya zubawa duka mata ido yana san gane wacece mahaifiyarsa, wacce tasa a kamasa ya kalla wacce kuma yafi zargin itace.

Azeema ta bishi da kallo, har suka fita.

Zeenatu ta kalleta tace "Ai naso na zaneshi kafin a kulleshi wlh, da dabulala zan zuzubamai."

Hajjo ta kifa mata wani kallo sannan ta juya ranta a bace, ganin yanda abu baiyi dadi ba yasa kowa ya mata sallama ya tafi.

Azeema suna fitowa Barira ta kalleta kadan tace "Gimbiya me yasa kika taimakeshi?"

Azeema tai murmushi tace "kina tunanin taimakonsa nai?"

Barira tace "haka dai jikina ya bani Ranki ya dade."

Azeema tai shiru sai can tace "haka kawai nake kallan Junaid a cikinsa, hakan yasa nake tsoron abinda za'amai, sai kuma nai tunanin in na taimakeshi nima za'a taimaki nawa indai yanada rai."

Azeema tai shiru tana tunanin lalai rashin Junaid ne yake damunta wanda gashi har ta fara ganin kamaninsa a kan wanda ta fara gani yau.

********

Hajjo ta zubawa Zeena wata muguwar harara tace "ni wai dan Allah meke damunki? Wato ke bazaki taba barina na samu kwanciyar hankali ba ko?"

Zeenatu tace "yanzu laifina kike gani kenan Hajjo? Kina ganin bawa yana neman maidani kawar wasansa, ta yaya bawa zai mun kallo haka? Wanda ko mutane basu isa su min ba?"

Hajjo cikin takaici tace "ba sai kisa a rufeshi a zaneshi a can ba? Kawo shi nan din na menene? Akoda yaushe in baki kaskantar dani agaban Azeema ba hankalinki baya kwanciya."


Zeena tace "to ni sam haushi daya dameni ba ina nai wani tunanin haka? Gabans fa yaja ya tsaya."

"Tashi ki ban guri kuma ki cire hannunki daga yi mai hukunci zansa Zubair yamai abinda ya cancanta."

Baki ta turo cikin jin haushin abinda Hajjo tace "ai wlh ko an hanata sai ta mai rashin mutunci."

Mikewa kawai tai ta fita ba tare da tace komai ba, Hajjo ta bita da kallo tare da girgiza kai, dole tasamu a aurar da Zeenatu shikedai ne zaisa hankalinta ya kwanta.

*******

Junaid kam na zaune a inda aka garkameshi, guri ne wanda duk kasa ne a gun, sai itace da aka samu akayi daki daki karami wanda kana iya ganin na ciki, dakunan da ake rufe bayi insunyi laifi.

Daga can gefe ma wani ne a garkame, kallan Junaid yai yasa dariya yace "me ka aikata kai kuma?"

Junaid ya kalleshi ba tare da yce komai ba, saboda mugun sanyin dake shiga cikin jikinsa, ga gari da sanyi ga kuma ruwan sanyi na tulu.

Amma wannan wace irin muguntace, me ya mata? Ransa yakai matuka gun baci, muryar na gefensa yaji yace "da alama laifi kai sosai harda ruwa?"

Junaid ko kallansa yanzu baiyi ba, ya runtse idanunsa yanajin wani mugun sanyi na ratsashi.

Yaushe zasu bude mu?

Abinda ya tambayi bawan kenan, mutumin yasa dariya yace "yaushe? Lalai yaran nan ka rainamin hankali, kanaso kacemin bakasan in aka kulle bawa sai yayi kwana hudu ba?"

Da sauri junaid ya bude idanunsa ya kalleshi, kwana hudu? Bama awa hudu ba?

Binta? Azi? Hari? Abinda ya fado mai kenan, yanzu in Azi yai ta nemansa fa?

In Binga taga bai dawo ba ya zatai? Hankalinsa ne yakai kololuwa gun tashi.

Ya zaiyi?

Yana nan a zaune gaba daya hankalinsa ya gama tashi, balle dayaga rana ta fadi.

*******
Wannan littafin na kudi ne, ga duk mai san siya bai san yanda zaiyi ba ya tuntubi number daya daga cikin marubuta na Haske, mungode.
*******


Azi sai kara duba hanya yakeyi, sai dai ba alamar Junaid, ganin dare ya fara yi sosai yasa ya koma cikin masarautar cikin tashin hankali, da kuma fatan Allah yasa ba wani abin ne ya sameshi ba.

Abinka da gida katu, Azi duk ya rasa ina zai zagaya.

Junaid kam gaba daya hankalin sa ya gama tashi, gashi ba wanda yake a gurin sai dakaru.

Ya ja baya yasa kansa akan itacen nan yana tunani.

Kai!

Abinda yaji ance kenan, da sauri ya bude ido, yarinyar nan ce ta dazu.

Kallansa tai tamai alama daya matso.
Da kamar kary matso sai dai san ta yafemai ta bari ya fita yasashi matsowa.

Kallansa tai tare da yin wani murmushin mugunta tace "Kana tunanin zamanka anan shine samun saukinka?"

Junaid ya kalleta sannan yace "dan Allah kisa a budeni akwai abubuwa masu amfani daya kamata nayi yanzun nan."

Baki ta sake tana kallanshi kafin ta saki muguwar dariyar tace "masu amfani?"

Kamar me da me kenan?

Junaid yai shiru tace "ayyya ya za'ayi dan wallahi sai kayi kwana goma a cikin nan, aso samuna na ma sai kayi wata, zaka san ni Gimbiya Zeenatu ni ka zubama ido."

Ta juya tana neman tafiya, da sauri ya sa kansa a jikin itacem yace "kiyi hakuri ki barni na fita."

Kallansa ta juyo tai sannan tace "sai naga kana zubarda hawaye sannan kukan ma sai kayi na jini tukun na."

Ta juya ta tafi.

Junaid ya bita da kallo cikin mugun takaici, bawan nan ya kalleshi yace "wai Gimbiya kama laifi?"

Junaid bai kalleshi ba ya koma ya zauna.

Bawan yace "yaro kana ruwa, Allah ne kadai zai ceceka wlh."

Junaid ya kalleshi yace "da gaske saita bari sai nai kwana goma?"

Bawan yasa dariya yace "kai daga wani kauyen kake ne? Yo nasan ko a kauye kake kasan abinda zai yiwu."

Junaid yai shiru, Bawan yace "ka nutsu in kayi sa'a ta sakeka nan da kwana goma."

Junaid ya runtse idanunsa cikin tashin hankali.

Ta ko ina Azi ya nemi Junaid har alfijir ya fito bai huta ba.

Ganin abu yaki yiwuwa kawai ya koma bangaren Mai martaba, dole ya fadamai, to amma yace me?

Yana neman komawa yaji wasu da suka fito zasu nufi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login