Showing 18001 words to 21000 words out of 76752 words
"kuje da ita gobe a hado mata abubuwan bukata."
Barira tace "to Gimbiya."
Nan Binta ya mike tai bangaren su Barira, tana shiga ta tsugunna tana hawaye, duk da ta fahimci Gimbiya sai dai tana ganin ba'a mata adalci ba ana neman rabata da Junaid wanda bataji ko yini zata iyayi bashi, a yanzu haka ma ji take kamar ta ruga inda yake.
Binta na shiga daki Barira ta kalli Gimbiya cikin jin dadi tace "Gimbiya kinyi maganinta."
Azeema ta girgiza kai alamar a'a tace "matsalar ba ita bace Junaid ne, me kike tunanin zai faru in mutane sukasan ya dawo da mace sannan ba matarsa ba? Macen ma mara asali?"
Barira tace "ya zamuyi gobe?"
Da safe ki kiramin jakadiya.
Jakadiya? Barira ta tambaya, Azeema ta mike ba tare da ta amsa mata ba, taje shiga daki baiwar da Junaid ya aiko ta shigo ta sanar da Barira sakon Junaid.
Barira tace "wayyo tayi bacci, tun dazu dama take cewa bacci takeji kanta na ciwo."
Kuyangar nan da jin haka ta juya, Azeema ta shiga ciki.
Zama tai a bakin gadon ta kalaman Junaid ne ke mata yawo, tabbas akwai wani dalilin dayasa Sarki ya daukeshi, to menene dalili? Baiso danta yai mulki? Kai ta girgiza da sauri dan tasan ba shi bane, tabbas gobe zata bigi cikin Jakadiya taji ko ta san wani abin, dan da dukkan alamu Abdulsalam ma baisan komai ba.
Ta dade tana juye akan gado kafin ta samu bacci ya dauketa.
***********
Jin Binta tayi bacci yasa ran Junaid yadan sosu, sai dai baiyi zargin komai ba, yana nan a zaune yana tunanin cin abinci Azi ya kwankwasa mai.
Bayan ya shigo ne ya sanarwa Junaid akan Sarki AbdulSalam na san ganinsa.
Tare suka fito da Azi dan dama bai sanshi ba bai taba ganinsa ba.
Sun isa fadar mai martaba, yana zaune an jera mai abinci a gabansa, Ji Zagi na sanarda isowar Junaid ne yasa ya kalli bakin kofa, har Junaid ya shigo ya zauna daga can gefe idanunsa na kansa, wani sansanyan murmushi ya saka ya nuna masa kusa dashi yace "dawo nan."
Junaid ya karasa sannan ya gaisheshi, Abdulsalam ya amsa cikin tsananin kulawa sannan yace "Junaid!"
Kallansa yai sai gani yai yayi murmushi wanda yasa Junaid din dan murmusawa kadan shima.
Wai kaine ka zama saurayi haka? Wasa wasa in yaro ba agabam mutum ya taso ba saurin girman sa zaka gani.
Junaid baice komai ba sai dai yanda yake maganar yasa ya dan saki jikinsa.
Abdulsalam yace "bismillah."
Ya fada yana mikamai spoon, Junaid ya amsa sannan suka fara cin abinci tare, sai turomai gabansa yakeyi wanda yasa Junaid din aake murmusawa, Sarki ya kalleshi bayan sun gama yace "Junaid!"
Junaid ya kalleshi tare da maida hankalinsa kansa, ka yafemin nasan duk da umarni ne na mahaifinka ban kyauta ba na barinka danai, da alama san kai nane yamin yawa?
Junaid cikin mamaki tace "san kai?"
Abdulsalam ya jinjina kai alamar eh, yace "kamar yanda kasani mahaifinka ne sarki, ban taba tunanin amsar mulki daga gunsa ba aka sari maban taba kawowa zan mulki kasarnan tamu ba, sai dai daga sanda Yaya ya furta min naji sha'awar hakan, sai dai nasan in har kana nan dole wasu sai sunyi tunanin yin amfani dakai gun karya ni."
Yadanyi shiru kafin ya kalleshi yace "san kai ko?"
Junaid ya daga kai alamaf eh yace "san kai ne."
Sarki ya kalleshi, Junaid ya murmusa yace "amma san kan mai amfani, akalla bakai kayi tunanin fotar dani ba, sannan baka taba tunanin sauke mahaifina ka hau ba, sannan sai daya furta sannan kaji kanaso."
Ido Sarki ya kuramai cikin tsananin jin dadin kalamansa, kafin yace "nayi mamaki."
Junaid yace "kayi hakuri in na bata maka, sau da dama nakanyi magana ne akan abinda raina ya bani."
Sarki yace "hakan akeso ai, ya zama ko za'aji haushi ka aji amma a kalla ka fadi abinda ka sani."
Junaid ya kalleshi suka murmusa a tare, Sarki yace "gobe za'ai taron dawowar ka zakaga mutane da dama da baka sani ba, yan uwanka da duk baka san dasu ba."
Yace "haka Um......"
Sai yai shiru, sunan nama wahalar fada?
Ya kalleshi tare da dan shafar wuyansa, Abdulsalam yace "gashi nima so nake ka dinga kirana da Abba ba yanda kakecemin Kawu ba sanda kana karami."
Junaid ya kalleshi da sauri, dariya sosai AbdulSalam yai wanda har fadawa sukai mamakin wannan lamari, yace "wasa nake ma, wato har ka fara hangowa ko?"
Junaid yace "ya nuna?"
Sarki yace "sosai, sai kayi kokarin gun nuna abinda ke ranka, dan nan masarautace za'ai amfani da abinda kake so a cutar dakai."
Junaid ya jinjina kai alamar gamsuwa, me yasa yaji ya sake da mutumin nan daga haduwa daya? Lalai y cancanci a kirashi sarki yasan yanda zaiyi yaja mutum jikinsa.
Sunyi sallama Junaid ya fito fuskarsa a sake, Azi yace "da alama Yarima kaji dadin zuwan nan."
Junaid ya kalleshi yace "ya nuna?"
Azi yace "gashinan a fuskarka."
Da sauri Junaid ya hade fuska yace "Azi, a duk lokacin dakaga ina kokarin bayyana abu a fuskata kamin alama yanda zan gane, kafin na saba."
Azi yi dariya yace "koyarwar da akai yau kenan?"
Junaid ya ce "eh."
Haka suka wuce bangarensa ya zubawa abincin nan ido kafin yasa a kwashe sannan ya shiga ya kwanta, kan binta sosai yake mata ciwo? Yaso biyawa daga gun Sarki saidai yana tsoron karya tashesu daga bacci.
***********
Hajjo ranta yayi mugun baci mikewa zaune tai a kan gadonta cikin tsananin takaici, yanzu bangaren da take so ya barma Zubair har fadamai tayi shine ya ba wa wani Junaid? Fuskar tabta hade ranta yayi mugun baci, dan dama dazu da Ramlatu tazo haushi ya kamata da taga itama Ramlatun yanzu tsoron Azeemar take, yanzu kuma sai taji wannan zance?
Tayi tsaki yafi cikin kwano kafin bacci ya dauketa.
Da safe tana tashi aka kawo mata labarin cin abinci da hirar da Junaid sukai da Sarki jiya wanda har ana jin dariyarsa har waje.
Cikin takaici ta cilar da kofin dake hannunta, wanda ya kusa bige Zeena datake kokarin shigowa yanzu, tana ganin haka ta fara kokarin juyawa.
Cikin tsawa tace "ina zaki?"
Zeena ta juyo ta dawo ta zauna, Hajjo ta kalleta tace "kinba Sulaiman din hakuri? Kindai san gobe zai koma ko? Da yau dai tafi ma Takawa yace ya bari ayi taro dashi."
Kallan Hajjo tai tace "ni wlh ba hakurin dazan bashi, koma naje kara batamai rai zanyi dan wlh ba sanshi na......"
Hajjo ta buga mata kallo tace "kema nema kike ki batamin rai? Dama tun shigowar yaran nan masarautar nan raina yake baci kema so kike ki karamin da wani?"
Zeena tace "Hajjo kinga Junaid din ne? Baki ganshi ba da ya sa kaya har........"
"Kin rufemin baki ko sai na sa an kulleki a daki?"
Zeena ta kalleta a tsorace, Hajjo tace "me kike tunani zamuyi a cikin wannan yanayi, dan in muka bari abu yai gaba daga ni har ku ba wanda zai tsira..."
Zeena tai shiru dan tasan gaskiya Hajjo ta fada, dole su san mafita kafin abu yai tsamari.......
*************
*ZAFIN RANA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*NA Ayusher Muhd*
Shafi na Goma sha Biyar.
Bangren Azeema tun safe ake ta baki, sai hidima aketayi, Safiya kam itace shugabar taro, sai karban baki takeyi, suk ala ala take itama ta samu ganin kanin nata.
Jakadiya ce ta shigo ta baya, inda ta shiga dakinsu Barira, Binta na gyara dakin ta shigo, kallan Binta tai tace wacce ke gaisheta tace "daga ina? Dan ban sanki anan ba?"
Binta tai kasa dakai dan batasan me zatace ba, Jakadiya tai dariya tace kin dade anan ne?
Binta tace "a'a jiya nazo."
Jiya? A ranta ta maimaita sannan cikin dabara tace "oh ko kece kikazo tare da Yarima Junaid?"
Binta ta daga kai alamar eh, Jakadiya tace da mace ya dawo kenan? Boyeta ake anan?
Jakadiya tace "amma kamar ke ba baiwa bace bako?"
Binta tace eh, Jakadiya tai wani murmushin gamsuwa da abinda take tunani, fuskarta a sake tace "ina Barira kice na shigo."
Binta ta leko, ganin yanda mutane sukai yawa yasa ta koma ciki, Jakadiya ta leka sannan tace "daure ki fita."
Binta ta kalleta tace "ban hango Bariran ba."
Jakadiya ta leko da kanta, daga can gefe ta hango Safiya na hidima tace "jeki gun waccen kice tazo Jakadiya na nan."
Binta ta fito tana bin gefe gefe, ba wanda yabi ta kanta saboda sunata hirarsu, kusa da Safiya taje, ta kasa mata magana saboda tanata magana da wasu, Jakadiya dake leke tana kallanta ta girgiza kai tace "tab harna tausayawa rayuwarki."
Safiya ganin taki tafiya yasa ta kalleta tace "lafiya?"
Binta tace "Jakadiya ce wai tana dakin can."
Safiya ta mike da sauri tai ciki gun Azeema.
Azeema na zaune, Barira tana gyara mata kai, ga kujerar da take kai daga kasa turaren sura ne aka sakashi yake turarata, kayan da zata sa na gefe.
Safiya ta shigo ta sanar da ita zuwan Jakadiyar, Azeema wacce idanta ke lumshe ta bude su ta kalli Safiya tace "ki shigo da ita nan a boye."
Nan Safiya ta juya ta nufi dakinsu Barira, Binta na tsugunr a gefe ta shigo nan tace "muje."
Babban mayafi ta rufa mata suka wuce cikin dakin da sauri.
Suna shiga Azeema ta kalli Barira da Safiya tace "ku bamu guri."
Nan suka juya suka fita.
Jakadiya na zube a kasa, Azeema ta kalleta sannan tace "Jakadiya! Ya zaman gun Hajiya inna?"
Jakadiya ta dago tace "lafiya kalau sai abinda ba'a rasa ba, ya sabuwar Jakadiyar?"
Azeema ta kafeta da ido wanda yasa Jakadiya sauke idanunta kasa tare da shan jinin jikinta.
Wani kasaitacen murmushi ta saki sannan tace "Me kike boyemin?"
Kallanta Jakadiya tak tace "ni?"
Idanta na kanta batace komai ba, Jakadiya tace "me zan boye miki ni kuwa Gimbiya? Girma ya kamani me zai sa nai abinda zai sani cikin tashin hankali?"
Azeema ta murmusa sannan tace "ya akai ni kuma nakeji a jikina kina boyen wani abin?"
Jakadiya ta kalleta tace "Wallahi Gimbiya ba abinda nake boye miki"
Azeema tace "na yarda wasa nake miki."
Jakadiya tai ajiyar zuciya, Azeema ta sake kallanta tace "lokacin Marigayi akwai wani abu daya faru wanda har ya canza yanayinsa?"
Jakadiya tai murmushi tace "Gimbiya dama ai dole akwai ranar da zakaji baka jin dadi ko a batama rai, balleshi Sarki?"
"Ba irin wannam nake nufi ba, yanayin da harku kuka san akwai matsala?"
Jakadiya tai shiru tana nazari kafin ta kalleta tace "na kasa tuno komai Gimbiya, a gafarceni."
Azeema tace "shikenan, sai dai duk sanda kika tuno ki sanar dani."
Jakadiya ta mike, harzata fita ta juyo da sauri tace "Gimbiya!"
Azeema ta kalleta, Jakadiya ta sake zubewa tace "akwai wani lokaci guda daya, wanda ko abinci dakyar yakecin kadan, fita inba fadaba baya zuwa ko ina? In baki manta ba ko ku matansa inkum nemi ganinsa cewa yake ku koma."
Azeema ta kalleta da sauri tace "na tuna, amma lokacin ya yanayinsa yake?"
Tace "ba wanda ya sani, saboda shi kadai yake zama."
Azeema tai shiru kafin tace "nagode, zan aiko da sako."
Jakadiya tai godiya sannan ta rufa babban mayafin nan, tana fita Barira dama na kofa tai dakinsu da ita.
Jakadiya ta bude kanta sannan ta kalli Binta wacce haryanzu ita kadaice a dakin."
Tace "ina Yariman?"
Binta tace "yana bangarensa."
Jakadiya ta kalleta tace "inhar kinasan kasancewa dashi sai kin cire tsoron dake ranki, nan masarautace in kika cigaba da haka rayuwarki ma bazaki tsira da ita ba."
Tana kaiwa nan ta fita, Binta tai shiru tana maimaita kalaman nata, itakam Junaid take san gani duk abin duniya ya dameta.
Tunani tai ko ta fita ta kofar itama ta nemeshi? Ko kallansa tai ta dawo?
Wannan shawarar tasata ta fita.
*************
Yana zaune yayi shiru, wata hadadiyar alkyabba dakakiya mai matukar tsada da kyau Azeema ta aiko mai da ita, kallo daya kayima Alkyabar nan sai ka sake kallanta saboda tsananin daukan idon da take dashi, ga wani hadaden takalmi na sarauta a gefe.
Fuskarsa kawai inka kalla zaka san duk wannan abin baya gabansa. Azi ne ya shigo ya kalleshi yace "Yarima ya baka shirya ba?"
Junaid ya kalleshi yace "an dubo Bintan?"
Azi yace "anje itama wanka takeyi."
Junaid ya kalli kayan yace "jiranta nake tazo ga gani kafin nasa."
Azi ya kalleshi yace "inka saka zaku hadu acan gun taron, kaga sai taci gani dakyau."
Junaid ya kalleshi sannan yace "rikemin wannan nata ne."
Azi ya kalli ledar ya bude ciki, dariya yasa yace "yanzu Yarima duk abinda kaci sai ka tafi mata dashi?"
Yace "kaima kasan Binta, ba lalai ta iya cin abinci acan ba, shiyasa zanyi magana mu dawo nan da ita."
Hari dake shirin shigowa ta tsaya jikinta a sanyaye, sai dai tasan bazai taba yiwuwa ba.
Azi ma kallansa kawai yake, dan yasan rayuwar dayai acan shida Binta basu isa ko rabi suyi anan ba."
Junaid ya dau kayan ya shiga daki ya shirya, murmushi yai yace "harna hango idanki."
Aikowa akai akan ya fito, hakan yasa ya karasa shiryawa ya sa turare sannan ya fito.
Hari na hangoshi ta hau guda tana cewa "Yarima Allah ya kara lafiya ya kawo zuri'a ta gari."
************
Cikin fada Hajjo ta kalli Fure tace "bata gama ba?"
Fure ta kara lekawa dakin sannan tace "yanzu take karasawa, Hajjo ta kalli Zubair ta mai alama daya mata magana sannan ta hade fuska tana cewa "ko uban me takewa kwalliya?"
Fitowa tai tare da hade fuska tana cewa "dan Allah Hajjo ki bari na kara gyara fuska ba."
Kallan mamaki Hajjo ta mata tundaga sama har kasa, bugagiyar hamshakiyar alkyabbar da akai rabin shekara ana yinta saboda taron sallah shi ta sa?
Zeenatu ta kalleta tace "nayi kyau?"
A hankali Hajjo ta kalli fuskarta, sannan ta maida idanunta kan kafarta, takalmin da Mai Martaba ya kawo mata wanda ko sashi batai ba shi ta sa?
Zeenatu tace "Hajjo!"
Bakin ciki tsabar ya cikawa Hajjo rai kasa magana tai, gaba kawai tai Zubair yabi bayanta, sannan itama ta bisu.
Duk inda suka wuce kallan Zeenatu ake saboda tsabar haduwar datai, wanda koni sai dana sake waigawa.
*******
Katan filin da aka gyara shi dan yin wannan taran suka nufa, masu hawan doki suna gefe suna jiran a fara dan suyi wasa.
Masu wasan takobi ma na gefe, masu kidan kalangu ma suna ciki, busar sarewa kawai ke tashi.
Yarima wanda ya taho akan doki ne ya nufi bangaren Azeema dan su tafi tare kamar yanda ta aika a sanar mai.
Yana shiga yaga bangarenta makil da mutane, mamaki ne ya kamashi ganin jiya fa aka aika, ya akai mutane dayawa suka samu halarta haka?
Nan ya fara gaisawa da mutane, kowa sai fara'a yake ana mai lale lale da dawowa, duk yanda yaso ya hango Binta abin yaci tura saboda yawan mutanen dake ta matsowa gunsa.
Safiya ce tazo ta nemi da kowa ya tafi gun taro suma gasunan tahowa, nan kowa ya sa takalminsa ya fita.
Safiya tsayawa tai tana kallan Junaid hawaye suna gangaro mata.
Jiki a sanyaye ya kalli Azi, da sauri Azi ya matso ya radamai cewa yayarsa ce.
Junaid ya matsa kusa da ita, murmushin farin ciki ta hau yi tana goge hawayenta.
Nuna mata yai da yatsarsa akan ta goge nan.
Nan ta goge tana dariya, tace Junaid Barka Barka
Murmushi yai, fitowar Azeema ce ta sa suka maida hankali kanta.
Fadar uban gayun da Azeema tai ma bata lokaci ne, dan ta kashe lokaci ganin ta fito a yanda takeso.
Junaid ya matsa ya gaisheta.
Fuskarta dauke da fara'a tace "Yarima muje mutane na jira, dan wasu komawa zasuyi a yau."
Kallan cikin gidan yai sannan yace "Binta fa?"
Tace "muje yanzu zasu taho da bata karasa shiryawa bane, kasan mu mata akwai wuyar shiri."
Nan suka tafi yana sake waigawa, barira tai daki da sauri dan su fito suma.
Sai dai me? Ba Binta ba alamun ta, idanu ta zaro a tsorace tai kofar baya dan nemanta.
A waje kuwa Binta tana tafe tana neman gidan Junaid, tun abin na mata dadi hartazo ta gaji, sai neman gun take gashi duk wanda ta nema dan ta tambayeshi daga yaga yanayinta zaiyi gaba.
Tana tafe tana share hawayenta dan itakam batama san inda take ba.
Daidai nan ne lokacin dasu Zeenatu da Hajjo suka taho ta kan layin, Binta na share hawayenta sam bata gansu ba, sai jitai an bigeta ta baya.
Da sauri ta nemi juyawa wanda hakan ya bugi hannunta.
Da sauri ta ja baya sannan ta kallesu.
Zeenatu ranta yakai kololuwar matuka gun baci, tana huci ta daga hannu ta sharara mata mari, wanda ya gigita Binta.
Tace dago.
Binta ta sake dagowa ta kara kifa mata wani marin wanda sai dayasa ta tafadi.
Ta daga wani zata kara mata, Zubair ya riketa yace "ya isa muje."
Hajjo ta makama Binta harara sukai gaba.
Wani irin kuka tasa tana kiran Junaid, dan tabbas raban da a mareta haka harta manta.
Kuka take sosai, ta kasa ko mikewa.
A can gun tro kuwa duk wannan abin da ake hankalin Junaid baya gun, ganin Binta taki zuwa yasa ya mike ya kalli Azi yace "muje naga taki zuwa."
Azeema dake zaune kusa dashi ta kalleshi tace "ina zaka?"
Yace "naga haryanzu Binta batazo ba?"
Haushi ya kamata amma ta murmusa tace "yanzu zata zo ko kuma Azi yaje ya dubo ko basu gama ba, hakan yayi?"
Junaid ya kalli Azi yamai alama dayaje, nan Azi ya juya.
************
Ayusher
***********
*ZAFIN RANA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*NA Ayusher Muhd*
Shafi na Goma sha Shida
Azi na fita su Hajjo na shigowa gun, duk inda Zeenatu ta gifta zakiji ana gimbiya kinyi kyau, kanta ne ya kara fasuwa ta tabbatar abinda ke kwance a kasan ranta zai karbu.
Azeema tana ganinsu ta mike dan tarbar Hajjo wacce kowa keta gaishewa.
Azeema na karasowa Zeena ta matso ta wani riko hannunta, duk da suna shiri da Zeenatu amma yau ce rana ta farko data taba riketa haka.
Zeenatu cikin farincikin tace "Umma