Showing 30001 words to 33000 words out of 76752 words
to sannan ya juya.
Tana zaune ta samu tai wanka tana shan kunu da kosai bawan ya sanar da ita Junaid na nemanta.
Kallansa tai tace "to."
Yana juyawa ta kalli Hari sannan tace "Hari bari naje."
Ajiye kofin tai sannan ta mike, Hari tace "sai kin dawo."
Binta tai murmushin yake ta fita.
Junaid na tsaye ya juya bayansa a cikin falan yana kallan window, yana kallanta sanda tazo ta wuce, hannunsa daya ba baya, sallama tai, ya amsa ba tare da ya juyo ba.
Shigowa tai a hankali ta tsaya daga nesa dashi sosai tace "Yarima!"
Junaid bai juyo ba yace "Barira tazo nan jiya?"
Kallansa tai kafin tace "a'a."
"Ya akai ke da bakida saurin yadda da mutane kikabi mutum ba tare da kin sanshi ba?"
Shiru tai kafin Tace "cewa akai inje injika."
Yanzu kam juyowa yai gaba dayanshi ya kalleta, tana tsaye tana kallanshi itama, a hankali ya fara takowa zuwa inda take, duk taku daya ji take kamar da bugun zuciyarta yakeyi, yauce rana ta farko a iya tarihinta dashi data taba ganinshi haka ba.
Daf da ita ya matso hartana iya jiyo numfashinsa, gabanta ne ya tsananta faduwa, dagowa tai ta kalleshi.
Yace "waye ya jaki?"
Da kyar ta hadiye yawun bakinta sannan tace "koma wanene ya Junaid baya riga ya wuce ba? Sannan laifi nai shiyasa aka hukuntani, dan Allah kabar maganarnan a inda take."
Ta fada tare da danyin taku daya zuwa baya, shima taku daya ya kara, ta kalleshi jikinta har rawa yadan fara tace "Ya Junaid!"
Yanda tai maganar kamar mai shirin yin kuka, kansa ya juya sannan ya furzar da wata iska ya kalleta yanayin idanunsa ya canza sosai, wanda ya kara tsoratata, tace "Ya Junaid!"
Bai tanka mata ba yanzun ma sai dai ya kara kallanta, bakinta na rawa muryarta na rawa tace "Ya Junaid dan Allah!"
Taku daya yai baya sannan ya kara wani dayan, kallansa tai tace "idan harba da kwakwaran dalili ba dan Allah kar kazo bangaren su Harira domin ni, sannan na koma can da zama, sannan kuma....."
Shiru tai tana kallansa, ta daure saboda kukan dake neman kwace mata tace "dan Allah ka rage nemana, in kuma duk hakan ya gagara zan bar gidan nan."
Tana kaiwa nan ta juya da sauri tai waje, tana fita tai bayan bangarensa da gudu, ta tsuguna ta fashe da wani irin kuka mai taba zuciya, wannan shikadai ne abinda zata masa dan ta zauna kusa dashi, dan in har aka cigaba da yanda ake ta tabbatar wata ran ganinsa ma bazata tabayi ba, wanda a rayuwa bata tunanin zata iya kwana ta tashi bata ko sashi a idanta ba.
Kuka take sosai, ta toshe bakinta, gaba daya fuskarta tai jaa, kuka take har iya karfinta wanda duk wani mai tausayi inyaga halin datake ciki zai tausaya mata.
Junaid kam tana fita ya runtse idanunsa shima bai zataba yaji hawaye sun gangaromai, hannu yasa y taba su, sannan ya kalli hannunsa, inhar mahaifiyarsa zata aikata hakan saboda kawai ya damu da Binta to lalai gaba baisan mezata aikata akan hakan ba.
Kansa ne yaji yana sarawa, ya dauka ganinta zaisa hankalinsa dana Binta ya kwanta me ke shirin faruwa?????
Tabbas dolene ya janye Binta daga jikinsa harsai yakai matsayin da zai kwaceta batare da fargaba ko tunanin za'a mata wani abin ba, yau a wannan lokacin ya dau alkawarin tabbas shi Junaid sai ya ba Binta gatan da babu wace mace data taba samunsa, domin tun yana karami burinsa kenan, akoda yaushe yaganta cikin farinciki, yanzu me zai faru da Basu ganta ba jiya? Haka zatai ta zama harta mutu kenan???????
******
Ayusher
*****
🌞*ZAFIN RANA*🌞
......................
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
*23*
Azeema tana zaune tana jiran Junaid sai dai har dare ba alamarsa, Barira ta kalla bayan tayi sallar isha'i tace "Barira Junaid haryanzu?"
Barira ta sunkuyo tace "ko na je na kirashi?"
Azeema tai saurin cewa "a'a da alama yana can da yarinyar nan."
Mikewa tai ta wuce dakinta ta kwanta zuciyarta duk ba dadi.
Bata dade da kwanciya ba bacci yai gaba da ita.
Yanda yake nufota ne fuskarshi tana gumi, gudu take hana binta, hannunsa ta kalla taga jariri a rike, gudu take tana keta cikin dajin nan har takai karshe.
Juyowa tai cikin tashin hankali tana hakki, hannayenta ta hade tana neman gafara.
Zubair ka tsaya kaji! Zubair ka........"
A firgice ta farka, da sauri ta jawo bargonta ta gangame jikinta wanda yake rawa, kamar a fili tai gudu nan dan gaba daya jikinta ya jike da gumi, idanunta sun kada sunyi jaa sosai.
Fitilar kwai dake gefenta ta murda da sauri haske ya dan zagaye dakin, shiru tai hankalinta a tashe ta zauna akan gado ta hade kafafunta, tunanin wannan mafarki, ta tabbatar duk duniya ba wanda yasan wannan sirrin to meke faruwa?
Shiru tai tana tunanin kalaman da Jakadiya ta fada mata, da sauri ta girgiza kanta alamar a'a.
Da kyar ta samu bacci ya dauketa a xaunen.
A hankali ta bude idanunta, ganin gari yayi haske ne yasa ta kashe fitilar sannan ta mike ta shiga bandaki.
*********
Fitowa tai bayan ta kimtsa, Barira da ragowar kuyangun ta nata faman gyara bangarensu.
Azeema ta kalli Barira wacce suka zube suna gaisheta suna ganinta.
Azeema tai murmushi tace "Barira kicewa Junaid anjima yazo muje ya gaida Hajiya Inna."
Cikin mamaki Barira ta kalleta, tace "Gimbiya kinsan matar nan ba sanki take ba karta wulakantaki a gaban Yarima."
Wani lalausan murmushi ta saka tace "ki sanar dashi." Ta juya ta shiga ciki.
Barira tai shiru kafin ta aika a sanar da Junaid.
Junaid kam wanda yau ma baisamu baccin kirki ba, yana zaune yana kokarin karatan wasu littafai na tarihi da ya nemi Azi ya amso mai.
Nan Azi ga shigo ya sanar dashi sakon Azeema, yace "to."
Sai daya gama karatawa zuwa inda zai tsaya sannan ya mike ya shiga daki yai wanka ya shirya, a ido inka ganshi bazaka taba kawo akwai abinda ke damunshi ba saboda babu yanayin komai a tattare dashi.
Karin Kumalo yai sannan suka fito shi da Azi, Azi sai binsa yake da kallo, duk da baisan yanda sukai da Binta ba amma ya hasasu ganin yanda taci koka shima tunda ta tafi bai bar kowa ya shigo bangarensa ba sai shi daya kaima littafai.
Junaid ne ya kalleshi yace "Azi sai yaushe za'a daina kallo na haka?"
Azi yai kasa dakai yana dariya yace " wai ka gani?"
Junaid yace "ba dole ba? Kana neman sani na fadi kasa."
A tare suka dan murmusa, can Junaid yace "Waccen gimbiyar tace Hajiya Inna batasan Umma?"
"Gimbiya Zeena?"
Eh
Azi ya danyi shiru kafin yace "bansani ba wallahi Yarima kaga ba'anan na zauna ba nima."
Junaid ya jinjina kai kawai baice komai ba.
Sun isa bangaren Azeema, ya shiga ciki, zama yai yana jira ta fito.
Barira ce ta fito ta zube tana gaisheshi ido ya zuba mata kamar bazai amsa ba, Barira ta kara gaisheshi gabanta na faduwa jitai ya amsa, a hankali ta saki wani ajiyar zuciya.
Junaid ya kalleta yace "Ki sanar da Umma nazo."
Mikewa tai da sauri ta nufi dakin Azeema, da ido Junaid ya bita kafin ya dauke idansa daga kanta.
Azeema wacce ta gama shiryawarta tsaf tasha kwalliya yanda ta saba, dan dama Azeema yar kwalliyace sam baka ganinta ba kwalliya sai dai in bacci take.
Tana zaune tayi shiru tana tunani, dan yatsanta kawai take dan dagawa take saukewa tayi nisa cikin tunaninta har batasan sanda Barira ta shigo ba, sai da Barira ta matso kusa da ita tana cewa "Gimbiya Yarima yaxo yana kilisarki."
Kallanta tai sannan tai murmushi, mikewa tai ta kara daidaita zaman alkyabarta sannan tace "muje."
Tare suka fito Barira tana binta a baya, gana ganin Junaid ta saki wani lalausan murmushi na farinciki, Junaid.
Ta fada tana kallansa, Kallanta yai da fuskarsa wacce ita kanta ta kasa meke tattare da ita.
Gaisheta yai, amsawa tai tace "jiya inata jiranka."
Yace "eh dana dawo ne naji banasan fitowa."
Murmushi tai tace "ka gaji da zirgazirga ne shiyasa, tunda ka dawo kake ta fama."
Kasa yai da kansa baice komai ba.
Tace "muje?"
Mikewa yai yace "eh."
Tare suka fito tana nuna mai hanyoyi tare da dan bashi tarihin guraren sama sama, yana biye da ita yana kuma jin tarihin harms tambayarta inda bai fahimta ba yakeyi har suka isa.
Bangaren Hajiya Inna shine daga can karshe karshen ginin, an kewaye mata bangarenta sosai, Azeema suna kokarin shiga ta kalleshi tace "kakatka ce, kayi kokarin sakin jiki da ita."
Kai ya daga alamar to, sannan tace "Zubair mahaifinka shi kadaine yao tsawan rai a 'ya'yanta maza, ta haifi maza guda hudu amma duk sun rasu kafin suyi aure shikadai ne har ya hau mulki sannan ya hayayyafa."
Junaid cikin mamaki da tausayinta yace "ba ita bace mahaifiyar Sarki?"
Tace "AbdulSalam itace ta rikeshi tun yana karami, sai dai ba ita ta haifeshi ba."
Junaid ya jinjina kai, shiga sukai ciki, Jakadiya wacce ta sauka ta koma bangaren Hajiya Inna tana zaune a waje suna hira da wasu, tana ganin Azeema ta mike da sauri, dukansu suka hau gaishesu, Jakadiya ta kalli Azeema cikin mamaki, dan rabanta da bangaren nan ita kanta bazata iya tunawa ba.
Azeema tai gaba Junaid yabi bayanta, Hajiya inna na zaune tana bare goro Jakadiya ta shigo tana sanar da ita zuwan Azeema.
Hajjiya Inna ta dago dayake bata gani sosai, ta kalli Jakadiya cikin muryar tsofafi tace "wace?"
Jakadiya ta kara sunkuyowa tace "Gimbiya Azeema."
"Uban wayace ina nemanta? Karta kuskura ta shigomin nan dan koda wasa bana nemanta, na dauka na fada mata ko mutuwa naj kartazo nan?"
Jakadiya ta kalleta tace "Hajiya kidan saurara tare take da Junaid kar yaji."
Junaid?
Ta fada muryarta na rawa, Jakadiya tace "eh."
Azeema da Junaid da sukai shiru a waje saboda kalaman Hajiya Inna, Junaid ya kalli Azeema wacce itama ta kalleshi tai murmushi tace "karka damu bakomai."
Jakadiya ce tace su shigo, Junaid ya kalli Azeema sannan suka shiga ciki.
Hajiya Inna ta mika hannunta tana cewa "Junaid!"
Matsawa yai gunta ya rike hannunta, kankame hannun sosai tai muryarta na rawa tace "Junaid! Junaid ashe da gaske sukeyi ka dawo."
Ido yake kara kuramai? Ta zare hannunta daya tana shafa fuskarsa cikin farin ciki.
Gaisheta yai t amsa tana cewa "ina ka shiga? Kakarka nata addu'ar ganinka kafin ta mutu?"
Azeema ce ta gaisheta, bata tanka mata ba ta cigaba da cewa "lale lale Junaid."
Azeema cikin sanyin murya takara gaisheta, ran Hajiya Inna a bace tace "tunda na barki kika shigo ai sai kimin shiru ko? Wallahi badan darajar Junaid ba zama a dakin nan bazaki sakeyi ba sai dai bayan raina."
Azeema tai kasa da kanta, Junaid wanda kalam Hajiya Inna suka mai zafi, balle daya kalli Azeema yaga yanda itma kalaman suka tabata da alama.
Hajiya inna ce tace "Junaid barka barkan mu, yau Allah ya amsa addu'a ta."
Junaid ya kalleta yai murmushin yake, Azeema ce ta mike tace "kiyi hakuri Hajiya dama Junaid na kawo miki bari na koma."
"Idan kina magana kamar mutuniyar arziki wannan mata Allah wadan bakin halin ki da tsinanen san kai da san zuciya, yanzu kila in na tambayeki raban dakiyima Zubair addu'a ma kin manta, ki fita zai taho da kafarsa.
Azeema ta kalli Junaid wanda shima kallanta yakey, Murmushi tai mai ta daga mai kai alamar ba komai sannan ta fita.
Hajiya inna ta kalli Jakadiya tace "zubamin gishiri a kofar data fita."
Wannan kalma ta konama Junaid rai sai dai baice komai ba.
Azeema na fitowa ta kalli Barira wacce idanta ya ciciko tace "meye hakan?"
Barira cikin konar rai tace "ji fa abinda ta miki, in da kara ai bai kamata ta miki hakan a gaban Junaid ba."
Azeema tai murmushi a ranta tace hakan shine ya kamata da batai ba da banji dadi ba
Amma a fili murmushi kawai tai ta fara tafiya
**********
Hajjo sam ta kasa kwantar da hankalinta, ganin yanda Zeena yau ko shigowa batai ba, kenan da gaske san yaran nan take.
Yamma nayi ta mike ta nufi bangaren mai martaba dan ta san lokacin dawowarsa daga fada ne."
Takawa ya cire kaya kenan Zagi ya sanar da isowar Hajjo, jalabiya ya zura ya bada izinin ta shigo.
Hajjo ta shigo ta zauna, gaisheshi tai bai amsa ba yace "Hajjo lafiya? Banyi tunanin ganinki ba."
Kallansa tai tace "me kake nufi da zaka cikama Junaid alkawari akan duk abinda yakeso?"
Kallanta yai yace "akan me zan sanar dake?"
Kallansa tai ranta ya fara baci tace "Naji bakada hujjar sanar dani amma meye matsayin Zubair a masarautar nan?"
Kallanta yai cikin mamaki yace "Mekikesan ji?"
Tace "Ba abinda nake san ji sai dai nazone na tunama, Junaid ba jininka bane, Zubair ne danka wanda ka haifa, duk yanda kake tunanin san mutum baikai san daya kamata kayiwa danka ba."
Ido ya zuba mata yana kallanta tace "sannan abu na biyu ka aurar da Zeena ga Sulaiman din nan dan hankalina ya kasa kwanciya da yanda ta fara maganar Junaid."
Duk da yayi mamakin jin kalamanta amma bai tanka ba, tace "kardai ka manta nice matarka wacce nasoka tun bamuda matsayi, duk da ba sona kake ba ka auran amma a kalla inada hakki akanka."
Tana kaiwa nan ta mike tamai sallama ta fita, shiru yai yana kallanta, harta fita waje yanayin fuskarsa ne ya canza wanda yasani shiga tunanin abinda yake tunani, ban samo amsarba naji yace "waya fada miki?"
Juyawa nai da sauri naga ba kowa agun, da wa yake? Abinda ya fadan kenan, na nuna kaina alamar ni? Lokacin na fahimci wai amsa yaba Hajjo wace ta dade da fita, to me yake nufi da waya fada mata?
Hmmmnmmmm
********
🌞*ZAFIN RANA*🌞
......................
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
Shiru mai martaba yai kafin yai gyaran murya alamar yanada magana, da sauri bafaden dake jikin kofa ya shigo, kallansa yai yace "A kiran Zeena."
Da sauri ya juya ya fita, Zeena dake keance akan gadonta ta rasa ina zata sa kanta, fitowa tai a fussce ta zauna, ta kalli Fure dake zaune agun tace "Fure bangaren Yarima nakesan kije ki kiramin Binta."
Binta? Wacece hakan?
Fure tai tambayar, Zeenatu ta harareta tace "koma wacece meye damuwarki? Kedai ki kiramin ita, sannan ki kirata a boye karki bari Junaid ya ganki."
Fure tace "Gimbiya taya zani bangarensa na kira wacce bansaniba sannan ba tare da ya ganni ba?"
Ni Fure dan Allah kwakwalwarki tana aiki kuwa? Ke ni meyasa gaba daya bakida irin dabaru da fasaha ne? Wlh na kusa canzaki ki cigaba damin halin kifi."
Fure ta juya da sauri tai waje, tsaki Azeema tai tace "bari inga yarinyar da har saboda ita yaje gun Hajjo."
Fure na fita aka shigo neman Zeenatu inji mai martaba.
Mikewa tai jiki a sanyaye dan tasan maganar dai guda daya ce akan aure, shiryawa tai sannan ta fito.
Kallan kuyangarta tai tace "in Fure ta dawo kice su jirani."
Tace to sannan ta wuce.
Mai Martaba na zaune gabansa katan Littafi na fiqihu ne yana dubawa, Zeenatu tana zuwa bakin kofar ta canza yanayin fuskarta a nutse ta shiga bayan ya bata izinin shiga.
Zama tai daga gefe zama irin na ladabi.
Abdulsalam ne ya kalleta yace "Mahaifiyarki tazo akan na aura miki Sulaiman."
Da sauri ta kalli Sarki tace "Ranka ya dade tuba nake amma Allah bana san shi."
Wani murmushi yai yace "ni kike kalla kice bakyasan zabina?"
Kallansa tai ta maida kanta kasa tace "Allah da kaima kanaso bazaka tambayi ra'ayi na ba, zartar da auren kawai zakayi tunda Hajjo tama magana, amma kiran dakamin da tambayar daka min ya nunamin bakaso."
Shiru yai yana kallanta kafin yai wani kalausan murmushi yace "to naji tunda bakyaso sannan banaso fadamin wa kikeso? Inbaki dashi kuwa na aura miki wanda yamin."
Kallansa tai da sauri sannan ta maida kanta kasa, yace "baki dashi."
Tace "akwai amma matsalar ba wanda zai yadda dani."
Wanene?
Shiru tai gabanta na wani irin faduwa, a hankali tace "Yarima."
Me kikace?"
A hankali tace "Yarima!"
Ido ya kura mata sannan yace "Kina tunanin Azima da Hajjo zasu yadda?"
Ta kalleshi idanta ya ciciko tace "na sani, shiyasa nake tsoro."
"Tashi kije."
Da sauri ta kara kallansa, yace "kin fadi ra'ayinki sannan kinsan bazai yiwu ba, ko kina da wani abin cewa?"
Cikin sanyin jiki ta girgiza kai alamar a'a.
Mikewa tai ta fito daga fadar.
Tana fita Abdulsalam ya mike ya shiga ciki, shiru yai yana tunani, abubuwa guda biyu suna mai yawo akai, me zai faru idan daga baya asiri ya bayyana?
Sai dai me? Yna tunanin ba abinda Zai faru tunda a lokacin Junaid yana auren Zeenatu in yai sa'a ma harda d'a.
To amma in kuma asiri ya tuno kafin faruwar hakan fa? Ko kuma Junaid ya rufe idansa akan komai fa? In kuma abin ya shafi har Zeenatun fa?
Wadannan dalilai sun sa gaba daya kansa kullewa.
*******
Zeenatu na fitowa ta nufi bangaren Junaid, wanda ita kanta batasan nan ta nufa ba sai data ganta a kofar shiga.
Da sauri tace "Fure me muke anan?"
Da sauri wata kuyanga tace "Fure bata nan ai."
Zeenatu ta kalli bangaren sannan tai ajiyar zuciya, samun kanta tai da juyawa.
Gimbiya?
Abinda taji an fada kenan, juyawa tai cikin jin kunya, Azi ne Junaid na gefensa.
Kallan Junaid tai a hankali tai dan yake tace "wucewa nazo yi nai."
Junaid ya kalleta sannan yace "tanan?"
Eh, naje bangaren Mai Martaba ne."
Oh!
Yace sannan ya nufi hanyar shiga.
Ya Junaid?
Juyowa yai ya kalleta, tai murmushi tace "bamuje gun Hajiya Innan ba."
Kallanta yai yadanyi wani tunani akasan ransa kadan kafin yace "zaki shigo?"
Shiru tai tana kallansa, yace "inbakyaso ki barshi."
Tace "tunda kai ka gayyacen ina zan ki zuwa."
Shiga yai tabi bayansa, zama tai tana kallan bangaren yanda aka gyara shi, murmushi tai tana cewa "dole Hajjo taso aba Ya Zubair nan."
A hankali tai maganar sai dai Junaid ya jita, kallanta yai bayan ya zauna yace "daga bangaren Hajiya Inna nake."
Cikin mamaki tace "haba? Kai dawa?"
Yace "Umma ce takaini."
Ido ta zaro tace "Umma karama? Garin ya?"
Garin ya kuwa? Yai tambayar cikin bugar ciki.
Zeena tai shiru kafin ta kalleshi tace "Hajiya Inna ta haramtawa Umma karama zuwa bangarenta."
Junaid yace "meyasa? Bayan sirikarta ce?"
Kallansa tai kamar zatai magana sai ta fasa.
Can tace "Ya Junaid saboda haka kace nazo?"
Yace "me? In saboda haka ne bazaki shigo ba?"
Tace "bance ba amma a kalla nadanji haushi."
"Meya