Showing 15001 words to 18000 words out of 76752 words
za'a mutu Azeema itama cewa zatai Junaid ne zai gaji mulkin nan.
Suna shiga Binta na tsaye a waje tana shan ruwa saboda gaba daya jikinta ba karfi, tana ganin an shigo da Junaid ta yadda kofin, da sauri ta isa gun tace "Junaid."
Ciki ya shiga dashi ya kwantar dashi dakin Azeema.
Binta hawaye kawai take ganin yanda duk ya canza, ta kara cewa "Junaid."
Azeema ce ta kalleta tace "Yarima Junaid."
Binta ta daga kai alamar to, Bari ta kalla tace "yi maza ki kira wanzami."
Nan bari ta fita da sauri, Azeema ta fito falo dan bada umarnin abincin da za'amai da kayan sawa.
Binta suna fita ta tsuguna gefen gadon tana kuka, dagowa tai tana kallan yanda duk ya canza, hawayen da takeyi ne ya diga a kan fuskar sa, a hankali ya dan bude idansa sama sama.
Kallansa tai tace "Junaid!"
Binta? Ya fada tare da kokarin murmusawa sai dai a hankali idanunsa suka koma suka rufe.....
Tausayinsa ne ya kara kamata hankalinta ya kara tashi, hawaye kawai take.
*Ayusher*
*ZAFIN RANA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*NA Ayusher Muhd*
Shafi na Goma Sha Biyu
Azeema ce ta turo kofa, dauke da kofi a hannunta, kallan Binta tai tace "bamu guri."
Mikewa Binta tai zat fita, a hankali yace "Binta!"
Juyowa tai ta kalleshi, murmushi ta sakar mai hawaye suka gangaro tace "Yarima kagane ni?"
Kai ya daga sannan yace "Yarima?" Dan yaune rana ta farko data kirashi da haka.
Azeema ce ta kalleta wanda ya sa juyawa zata fita, mikewa ya shiga kokarin yi yana cewa "Binta ina za......."
Kallan mahaifiyarsa a gabansa ne yasa ya kalli dakin da yake ciki, sake kallanta yai cikin mamaki, kofin hannunta ta mika mai wanda madara ce a ciki ta shanu, mikamai tai saboda yanda yakejin jikinsa ne ya amsa ya kafa kai bai sauke kansa ba sai da ya shanye ta duka.
Ajiye kofin yai sannan ya kalleta yace "meke faruwa?"
Kallansa tai cikin tausayawa ta zauna a gefen sa tace "Junaid!"
Shiru yai yana kallanta yana san jin abinda ke faruwa, hawaye ne suka zubo mata ta gogesu tace "kasan kullum dakai nake kwana nake tashi? Amma Junaid kana ganina kaki sanar dani kai wanene?"
Abinda ke bakinsa ya hadiya, kallanta yai kamar zaiyi magana ya fasa, mikewa ya shiga kokarin yi yana cewa "ni zan wuce ni da Binta."
Hankali a tashi ta mike tace "Junaid zaka koma ina?"
Kallanta yai yace "yanda kike rayuwarki hankalinki a kwance nima a can hankalina a kwance yake, tunda kin gani na ganki zan koma."
Da sauri tace "kana tunanin zan barka ka koma wani gun? Junaid? Baka tausayin mahaifiyar data rasa danta tun baigama wayau ba? Shekarata nawa rabona dakai? Ka rasa abinda zakacemin sai zaka tafi?"
Juyowa yai ya kalleta, zuciyarsa ce ta karaya, shi kanshi yana kewar mahaifiyarsa amma gani yake kamar mantawa sukai dashi.
Karasowa tai inda yake tace "ka koma ka huta na sa akira wanzami ya dubaka, Junaid bansan meke yawo a ranka ba anma ni mahaifiyarka ce, babu uwar dazata ajiye danta a wani gun tai rayuwar datakeso."
Shiru yai baice komai ba, ganin haka yasa tace " kana san wani abu ne?"
Kai ya girgiza alamar a'a yace "Binta tana ina?"
Kallansa tai tace "Junaid....."
Sai kuma tai shiru tace "ka huta inka tashi sai a kirata."
Kai ya jinjina sannan yace "ina bandaki?"
Nuna mai tai da sauri sannan tace "nasa a kawo ma kaya."
Kaya? Ya tambaya cikin mamaki, tace "eh na tura gun masu dinkin mu na masarauta, nasan baza'a rasa wanda suka ma Zubair ba."
Baice komai ba dan baisan ma me zaice ba, juyawa tai ta fita, zama yai a bakin gado yai shiru yana tunanin wannan lamari, wai meya faru ne daga sanda aka kulleshi?
Azeema ce ta turo kofa dauke da kaya, mika mai tana cewa "me kake tunani?"
Shiru yai yana kallanta, murmushi ta saki tace "inada abubuwa dayawa danake san tambayarka sai dai ganin yanayin da kake ciki yasa nake jurewa."
Yanzu kam shima murmushin yai, tace "Junaid!"
Kallanta yai tace "Nagode daka jure abinda ya faru,nagode wa Allah daya barmin kai da rai."
Tausayinta ne ya kamashi, juyawa tai da sauri tabar dakin.
Junaid ya dafa kansa, lalai bai kyauta ba da yake jin zafin mahaifiyarsa bayan abar tausayi ce.
Mikewa yai jikinshi duk ba karfi, wanka yai tare da alwala sannan ya fito, kayan ya saka sannan ya tada sallah.
Bari ce ta kwankwasa jin shiru yasa ta koma, kara dawowa tai ta kwankwasa Junaid ya bata izinin shigowa.
Abinci ta shiga jerawa a kan karamin carpet din dake dakin, haka tai ta shigowa dashi tana jerawa, data ajiye na karshen ne ta zube a kasa tace "yarina barka da dawowa."
Kallanta yai yace "ina Binta?"
Tana dakinmu, taci abinci ne?
Cikin mamaki ta kalleshi, tace an kai mata.
Ki duba nasan bata fara ci ba kice mata ta dawo nan.
Cikin tsananin mamaki ta kalleshi, shima kallanta yai yace "da wani abin ne?"
Da sauri tace "a'a"
Mikewa tai ta fito kilisar Gimbiya Azeema wacce ke bada sako akan a sanar wa Safiyah halin da ake ciki.
Gaba daya Azeema ta kasa zama sai ake take gun yan uwanta na kusa dana nesa.
Bari ce ta matso kusa da ita ta sanar da ita abinda Yarima yace " shiru tai cikin rashin jin dadin zancen tace " kice taje"
Da sauri Barira ta kalleta tace "Gimbiya."
Azeema ta juyo ta kalleta tace "ki bar Junaid yai duk abinda yake so, ni zan san abin yi."
Barira ta jinjina kai sannan tai dakinsu.
Kamar kuwa ya sani tana zaune sai jujuya abincin take taki ci, Barira ta sanar da ita sakon Yarima da sauri ta mike ta dau kwanan tai dakin.
Barira ta bita da kallo, cikin takaici.
**********
Hajjo kam sai matse hannayenta takeyi daga zaune, tabbas gaggarumin matsala na neman afkowa a tare da ita.
Zeenatu wacce ke zaune itama tayi shiru tana tunanin abinda ke faruwa.
Zubair ne ya daure yace "wai da gaske yaran nan ne Junaid?"
Hajjo tace "da gaske wlh, yanzu ya zamuyi? Dan wlh akwai gagarumin matsala."
Zeenatu ta kalla wacce tai shiru kafin wani murmushi ya bayyana a fuskarta, Hajjo cikin mamaki tace "ke kuma fa?"
Zeenatu ta kalli Hajjo da sauri tace "ya akai bamu gane ba Hajjo? Yaran nan wlh sam baiyi kama da bawa ba, ko daga yanayin maganarsa zakasan jininmu ne, ya akai idanunmu ya rufe?"
Ran Hajjo ya baci tace "to ke yanzu ana zancen abinda zai biyo nan gaba wato ke abinda ya faru a baya kike maimaitawa?"
Zeenatu ta sake murmusawa tace "abin ne abin birg......."
Uban hararar da Hajjo ta maka mata ne yasa ta kalli Zubair tace "yaya wai meye na damuwa? Milkin nan fa kowa yasan naka ne meye na wani tada hankali?"
Zubair ya kalleta yace "kinba Sulaiman din hakuri?"
Tace "kai yaya ana cikin wannan yanayi wake zancen wani Sulaiman?"
Hajjo tai dan tsaki tace "aiki Fure ta kiramin Ramlatu."
Nan Zeenatu ta mike, Hajjo ta kalli Zubair tace "Zubairu karka kuskura adan tsakankanin nan kai laifi, kabi kowa a sannu, kai luf kamar baka nan kafin na samo mafita, dan wallahi barin yaran nan daidai yake da ajiye matsayinka."
Zubair ya kalleta yace "Hajjo kisan yanda za'ai."
Tace "karka damu, in ta gama rama abinda aka ma danta sai musan abinda zamuyi."
Yace "kina nufin sai ta rama?"
Hajjo tai wata dariya tace "bakasan Azeema bane, ita a tarihinta bata barin ta kwana ko a mutu ko ai rai amma sai ta fanshe."
Zubair yai shiru yana tunani.
*****
Suna cin abinci yana tambayeta abubuwan da suka faru tana fadamai, ko mai ya bude sai ya turo gabanta yace "binta ga kaza kin taba ci kuwa?
Dariya tai tace "Ya Junaid nifa bamu shirya bama wlh, ka taho ka barni."
Ahhhh ya rike ciki wai ciwo,
Hankalinta a tashe ta kalleshi tace " Ya Junaid?"
Ganin yanda ta rikice yasa ya saki dariya yana cewa "yanzu mun shirya?"
Hade rai tai tace "Ya Junaid."
Tai maganar cikin shagwaba.
Azeema dake jikin kofa rike da kofar ta kalli Wanzamin dake gefe kansa a kasa tace "ko zaka bari sai anjima?"
Yace to ya juya tare da mata sallama, shiru tai tana tunanin wannan yarinyar, itafa danta bazai zauna yana biyewa yarinyar nan cikin masarautar nan ba, wanda tasan yanzu idan kowa kansa zai koma.
*Ayusher*
Dan Allah ku daina min sharing din littafi, ina iya bakin kokarina na ganin an zauna lafiya da kowa, dan Allah wannan littafin na kudi ne ku daina yadamin shi.
Nagode
*ZAFIN RANA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*NA Ayusher Muhd*
Shafi na Goma sha Uku.
Haka sukai ta hirar su kamar ba wata matsala a gabansu, wanda hakan ba karamin batama Azeema rai ba, zama tai a kilisarta tai shiru tare da zubawa kofar ido.
Barira ta sunkuyo tace "Gimbiya haka zamu barsu?"
Kallanta tai tace "kinsa a gyara bangaren Yarima?"
Tace "eh na tabbatar ma sun gama, badai tare zaki bar........."
Wani banzan kallo data mata ne yasa ta yin gum da bakinta.
Azeema ta mike ta shiga dakin.
Suna dariya suna ganin ta sukai shiru, Junaid ya kalleta, Binta kam saurin mekewa tai tsaye ta ja baya.
Azeema ta kalleta tace "Gashi ganinki yasa Junaid ya ware, angode."
Binta tai kasa dakai tana kallansa.
Murmushi ya sakar mata.
Azeema ta zauna a bakin gado tace "Junaid!"
Yanda ta kira sunan nashi ne ya sa shi kallanta bayan ya amsa, tace "an gyara maka ban garenka, zamuje yanzu ma kaika, dan gobe za'ai taron murnar dawowarka.
Ta danyi ajiyar zuciya sannan ga cigaba "Sai dai inaso kai da Binta ku rage nuna mu'amalar ku cikin jama'a."
Kallan Binta tai sannan ta kalli Junaid, Binta!
Junaid ya kirata, nan bamu guri ya fada yana kallan Azeema.
Binta ta mike tai waje.
Azeema ta kalleshi tace "Junaid kai yarima garin nan ne, idan kowa akanka yake, me kake tunanin za'ace in aka ganka da mace budurwa?"
Junaid yace "menene damuwata akan abinda zasuce? Binta kanwa tace wacce na taso tare da ita a lokacin da banda kowa, ban fahimci dalilin da zaisa na ja baya da ita ba dan yanzu na zama wani abin."
Azeema tai murmushi tace "ba haka nake nufi ba, in kana cikin mutane ne sannan Junaid ko ba dan kai ba ko dan ita ya kamata saboda inba haka ba mutane zasu takura mata."
Shiru yai bai ce komai ba, tace "ka barta anan sai su dinga kwana da su Barira in yaso da safe sai ta dinga zuwa."
Junaid ya kalleta da sauri tace badai tunani kake ku zauna tare ba?
Yace "me zai haka? Bayan haka muka taso?"
Tai shiru kafin tace " Junaid kayi hakuri ka barta anan."
Kamar zai sake magana sai kuma yaga kamar bai dace haduwarsa ta farko da mahaifiyarsa ba ya dinga bijire mata haka ba.
Shikenan.
Azeema tace "Nagode Junaid Nagode."
"Ga amanar Binta nan."
Tace "ni na taho maka da ita karka damu zan kula da ita, sannan Azi da Hari da ragowar bayin da mukace su taho sun iso su suka gyara ma bangarenka."
Cikin jin dadi ya kalleta, tace "Junaid!"
Naam
"Kai jinin mai Martaba ne karka yadda wani ya kawo ma raini, sannan duk wanda ya nemi yima zancen banza........."
Sai kuma tai shiru ganin kamar bayasan maganar duba da yanayin da fuskarsa tai.
Murmushi tai tace "Junaid yaushe zaka ban labarin rayuwar dakai."
"Ba wani labari, mun daiyi rayuwar mu tundaga yarinta har kawo yanzu."
Kai ta jinjina tace "Alhamdulila."
Shiru suka danyi saboda rashin sabon dake tsakaninsu, kafin yace "meye dalilin sarki na kaini can?"
Kallansa tai da sauri saboda batai tunanin tambayar ba, tace " bansani ba wlh, sai dai nasan yayi hakane dan hankalin ka ya kwanta."
"Bawai ina inajin haushi bane, sai dai haryanzu ina ganin akwai dalili bayan waccan."
Shiru Azeema tai jin kalamansa yasa itama ta fara tunanin tabbas dan kawai Junaid yai rayuwa hankali a kwance bazai zama dalilin da zaisa ya dauke danta bada saninta ba ya boyeshi, tabbas akwai wani abin kenan? To menene?
Junaid ne ya kalleta yace "karki damu nayi maganarne ba tare da nazari ba."
Murmushi tai cikin jin dadi a kalla yana da dogon nazarin da akesan mai mulki ya kasance dashi.
Mikewa yai yace "Su Harin suna ina?"
Tace "bari nazo muje."
Dakin huta, ta mikr tana cewa muje na fara nunama hanya.
Nan suka fito, Binta bata gun hakan yasa yace "Binta fa? Barira tace "ta shiga bandaki."
Yace "bari na jira ta fito."
Azeema ta kalleshi tace "muje Junaid in ta fito sai Barira ta kawota."
Ya kalli Barira wacce tai saurin cewa zan fada mata inta fito.
Nan suka nufi waje, a hanya sai kallan Junaid ake ana gaisheshi, Suna kokarin yin kwanar dazata sadasu da bangaren Junaid ne sukaji ance "Barka da Yamma."
Juyowa Azeema tai, ta hade fuska tsam tare da binta da kallo, Zeena ta karaso fuska a sake, Junaid kam ganin ba dashi ake ba bai ko juyo ba.
Zeena tace "Nazo bada hakuri naga zaku fita."
Azeema tace "hakuri? Laifin me kikai?"
Tace "Tuba nake na yi abinda na bata miki rai."
Azeema ta juya batace komai ba, dan bataji zata hakura tabbas sai ta fanshe.
Zeena ta bi bayanta tana kallan Junaid tace "Yarima kayi hakuri bansan kai wanene ba lokacin."
Juyowa yai ya kalleta, tsayawa tai tare da kura mai ido, maida kansa yai hanya baice mata komai ba.
Shiru tai bata kara daga kafarta ba wanda hakan yasa du Azeema sukai gaba.
Fure ce tace "Gimbiya menene?"
Zeena ta kalleta da sauri sannan ta kalli gun da su Junaid suke, haushi ya kamata tace "uban me kike da har suka wuce mu?"
Fure tace "tuba nake Gimbiya."
Takaici ya kamata tace "meye ma amfanin fitowar? Ko so kike na bisu kamar jela?"
Fure tace "tuba nake Gimbiya."
Cikin takaici ta juya ta koma bangaren Hajjo.
Azeema kam wani irin dadi ne ya kamara dataga kallan da Junaid ya mata wanda ta san hakan ne ya tsorata ta tabbas jinin sarautar na nan na yawo a jikinsa.
Yana shiga ya hango Azi na gyra harabar waje.
Azi na ganshi ya matso cikin tsananin jin dadi, kasa yai da kansa yace "Yarima."
Junaid ya kalleshi cikin jin dadi yace "Azi kunzo lafiya?"
Azi yai saurin zubewa a kasa yace "tuba nake yarima na barka cikin wani hali."
Junaid yai murmushi yace "nina umarceka ka barni ai, ina su Hari?"
Suna ciki hala dan da suna nan.
Kai ya jinjina sannan suka shiga ciki, yanda aka gyara gun me gashi kato sosai ya birgeshi.
Azeema tace "Junaid nan asali da bangaren Mai Martaba ne, anan mahaifinka ya zauna, sai dai shekaru biyar da suka wuce aka kara fadada masarautar wanda aka sakema Takawa wani ginin shine ya tashi, dazu ya turo akan abude maka."
Junaid ya kalleta yace "amma hakan ba matsala?
Tace "ba wani matsala tunda umarnin Sarki ne."
Junaid ya jinjina kai alamar gamsuwa yana kara kallan gun, Azeema ta shiga nununamai yanda gun yake.
***
Zeena hartaje zata shiga bangaren Hajjo ta kalli Fure tace "Fure ni me zasuje yi bangaren Takawa na da?"
Fure tai shiru, Zeena tace "kin fadamin ko kuwa?
Fure tai kasa dakai tace "Sarki ya bar ma Junaid."
Ido ta zaro tace "mene?"
Kallan Fure ta karayi tace "Hajjo ta sani?"
Fure ta girgiza kai alamar a'a.
Zeenatu tace mu koma bangarena baza'a huce a kaina ba.
*******
Da sauri Binta ta shigo, sannan ta kalli Kuyangar data jata wai akan an aiketa, Barira ta kalleta tace "kun dawo?"
Binta tace eh tana kallan bangaren Junaid.
Barira tace "kije ki huta shima ya tafi bangarensa saboda ya gaji wai yana san hutawa."
Binta tai shiru cikin rashin jin dadin ya tafi ya barta ta shiga ciki.
*******
Azeema ta dade acan kafin ta fito ita da kuyanginta.
Junaid ya kalli Hari yace "Hari haryanzu Binta bata karaso ba?"
Tace "Yarima!"
Itakam Hari girma duk ya fara zuwa mata ta kuma san zamansa da Binta bazai yiwu yanda yake tunani na, sai dai batasan me xatace mai ba.
Junaid ya kalleta yace "Hari ki tura a dubo, dan tazo taga nan."
Hari tace to Yarima ta fito.
Shiru tai tare da kallan Azi wanda shima kallanta yake, su sun san yanzu Junaid zai san me ake nufi da sarauta, ilolinta, matsaloli da kums kalubalen dazai fuskanta.....
*********
*ZAFIN RANA*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*NA Ayusher Muhd*
Shafi na Goma sha Hudu
Har bayan sallar isha'i Junaid baiga Binta tazo ba, ga abincin dare an jera mai amma baibi takansu ba, hankalinsa ne ya tashi, fitowa yai ya kalli Kuyangun dake tsaye bakin kofa ya kalli ta farkon yace "Ina Hari?"
Tace tana daki, yace "kinsan bangaren Umma?"
Tace "Gimbiya Azeema?"
Yace "eh, kije kice ma Binta tazo."
Tace "to Yarima sannan ta juya."
********
Binta zaune a gaban Azeema, Azeema cikin sakin fuska tace "Binta nasan kin damu da Junaid sannan kin shaku dashi ta yanda bama zato a lokacin da bashida kowa sai ke, sai dai ina neman alfarma daya daga gurin ki.
Binta ta kalleta kadan sannan ta maida kanta kasa, Azeema tace "dan Allah ki dan janye daga Junaid."
Gaban Binta ne ya fadi, hankali a tashe ta kalleta, Azeema ganin yanda abin ya shigeta yasa ta murmusa tace "ba cewa nai ki janye daga gareshi gaba daya ba alfarma nake nema ki dan bari wannan uwar data rabu da danta shekara da shekaru ta dan samu damar shakuwa dashi na wasu yan lokuta."
Idanun Binta ne suka ciciko. Azeema tace "nasan zaki fahimceni, kimin wannan alfarma kinji Binta?"
Binta ta daga kai alamar to hawaye suka gangaro mata, Azeema ta rike hannunta tace "nagode kwarai da yanda kika taimaki dan nan nawa, ma tabbatar samunki kusa dashi ne yasa ya iye jure rashin mu."
Wasu hawayen ne suka cigaba da zubo mata, Azeema ta kalli Barira tace