Showing 33001 words to 36000 words out of 76752 words

Chapter 12 - ZAFIN RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

ayusher   

26 Aug 2024

8567

hadasu?"
Kai ta girgza alamar rashin sani tace "kawai dai nasan batasanta sannan ta hanata shiga bangarenta, ita da Mai martaba."

Junaid ya kalleta yace "hardashi?"
Eh shima baya zuwa.
Murmushi Junaid yadanyi kadan fuskarsa kunshe da tunani yace "shikenan, in kin gama gani bangaren sai ki wuce, zan shiga nai magrib."

Mamaki ne ya kamata kafin ta tattaro abinda zata fada harya rufe kofa.

Labanta ta cizs saboda takaici sannan ta mike ta bar bangaren nasa cikin takaici.

Idanunta ne taji suna kara cicikowa, kenan ita duk inda tai ba dadi, cikin jin haushi ta shiga bangarenta.

Wata yarinya ta gani a tsaye daga gefe kadan inka shiga.

Kallanta tai a wulakance tace "uban me kike anan?"
Binta ta kalleta tace "ance kina nemana ne."

Ni?
Tai tambayar tana kallanta daga sama har kasa.

Binta tace "haka waccen tace."
Ta nuna fure wacce ta taho da sauri.

Binta wacce kafafunta harsun gaji da tsayuwa ta dan jingina.
Fure ta karaso tace "Gimbiya itace ."

Da saure Zeenatu ta kara kallan Binta cikin mamaki, kece Binta?"
Eh nice.

Batasan sanda tasa wata dariya ba wacce ni kaina na saki baki ina kallanta.

A hankali ta fara zage Binta wacce ta nemi ta daidaita tsayuwarta.

Binta mamaki ya kamata, Zeenatu sai da tagama kallanta tsaf sannan tace "daga bangaren Ya Junaid nake."

Binta ta kalleta da sauri, Zeenatu tai murmushi tace "Ashe abinda ya faru dake kenan? Ayya kiyi hakuri kinsan hausawa sunce babban goro sai magogin karfe."

Binta ta daure ta kalleta tace "me ya sameni?"
Zeenatu ta matso saitin kunnent tace "Ya Junaid ya fadamin komai, tundaga sands ya taimakeki har abinda ya faru kwanan nan."

Idanun Binta ne suka fara sauyawa, tace "mene?"

Zeenatu ta shagwabe fuska tace "na tausaya miki, shima Ya Junaid yana tausayinki sosai."

Bakin Binta ne ya fara rawa, kuka na neman kwace mata, daurewa tai ta kalleta sannan ta sunkunya tace "tuba nake Gimbiya amma nasan ba abinda kikaji daga bakin Ya Junaid, sannan ko kinji ma nasan yayi maganar ne bada wani abin ba."

Zeenatu a zuciya ta kifa mata mari, Binta ta rike gun ta dago tace "menayi kuma?"

Zeenatu tace "tambaya kike? Sai yanzu ma na tuna ashe kece wannan ta rannan.
Sannan yau ya zama rana ta karshe da zaki dinga maida min martani."
Tana kaiwa nan tai ciki.

Binta ta juya ta fita, tana fita tasa kuka, da gaske Ya Junaid ya fada mata komai? Kuka kawai takeyi ta rasa ma me take tunani.


**********
Junaid bayan yayi sallah ne ya zauna akan sallaya yana tunani, ita da Mai martaba? Meyasa? Shiru yai yana tunani, kafin ya mike.

Waje ya fito yadan tsaya a baranda yana dan kallan kofar da zata sada ka da bangaren bayi, Binta ko tana me?
Shiru yai tare da sakin ajiyar zuciya, ganin ba alamarta ne yasa ya juya kamar zai koma.
Jin an bude kofa ne yasa ya juyo da sauri.

Binta ya gani tana tafe tana share hawaye, tsayawa tai daga bakin kofar itama ta zubamai ido, sun fi minti uku suna kallan juna kowa da abinda ke yawo a ransa kafin Junaid yace "Binta!"
Kallansa tai a hankali ta tako, sai dai bata isa inda yake ba tace "Yarima Barka da dare."
Ta juya zata wuce.

Shiru yai ya bita da kallo har ta shiga, meya sameta?
Umma ce?
Abinda ya fado mai kenan.




******
Ayusher
24



*ZAFIN RANA*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ*

*Wannan Littafin Na Saidawa ne ga Duk mai Bukatar siya ya tuntubi 07084161619 mungode*


*25*

Binta!
Tana kokarin rufe kofa taji ya kira sunanta, tsayawa tai cak zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, A hankali ta juyo ta kalleshi.

Murmushi ya sakar mata sannan yace " magana nakeso muyi."
A hankali ta fara taka kafafunta zuwa inda yake, idanunta na kansa, tuntube tai saura kiris ta fadi, da sauri ya zabura yace Binta.
Daidaita tsayuwarta tai ta kalleshi har ya sauko daga baranda din da yake.

Kallan juna sukai kawai suka sa dariya, yace "har yanzu dai sai a dinga tafiya ana neman faduwa.
Ta karaso tace "haryanzu dai kafin na fadi an gama razana."

Murmushi suka sakeyi da tuno da yanda sukeyi acan.

Karasowa tai ya zauna a kasa ya zura kafafunsa kasan baranda din, kallansa tai sannan ta zauna daga gefe.
Ya kalleta cikin hasken farin wata yace "daga ina?"
Nadan fitane zagaye."

Zagaye? Ya maimaita tare da yin sansanyan murmushi ganin indai zata fita dashi suke fita.

Kallanshi tai tace "wacce magana?"
"Me kike tunani akan komawa bangaren Umma?"
Kallansa tai da sauri tace "Naam?"
Yace "eh, ko bakyaso?"
Shiru tai tana kallansa, kawar da kansa gefe yai, ganin haka yasa tace "zan koma."

Shiru yai kafin yace "Nagode."
Mikewa tai tace "zan koma gobe in Allah ya kaimu."
Tafiya?
Ya fada ganin ta mike tsaye, juyowa tai ta kalleshi a ranta tace kafi kowa sanin zamana a nan kusa dakai abinda zai haifar.
A fili kam cewa tai na gaji ne.
Ya fahimceta hakan yasa baice komai ba.

Yana nan zaune har ta shiga ciki.

Mikewa yai ya shiga dakinsac zamanta acan shine kwanciyar hankalinsa ya tabbatar intana gunta ba'abinda ta isa ta mata, sannan hakan ne zai bashi damar kwatar mata 'yancinta.


**********

Binta na shiga ta sanar da Harira zata koma gobe bangaren Azeeema, cikin tsananin mamaki Hari tace "Binta hauka kike? Matar da tafi tsanarki kije ki gunta?

Kallan Hari tai ta tuno da kawar da kansa dayai, tace "akwai dalilinsa na yin hakan."

Dalili?
Harira ta tambayeta, Binta ta kwanta tace "eh."
Shiru tai tana tunanin abinda ya faru tsakaninta da Zeena yanzu, me Zeena take nufi? San Junaid take kenan ko me?

Mikewa zaune tai da sauri ta kalli Harira tace "Harira ya ake gane mutum na san wani?"
Harira tace "yanda kike san Junaid."
Ido ta zaro da sauri tace "ni Ya Junaid ai........"
Sai kuma tai shiru, Hari tace "me?"
Kwanciya ta kuma yi da sauri tace "bacci nakeji."

Idanunta ta rufe tana tuno yanda Zeena ke magana, lalai itakam tata ta kare dan ta tabbatar ba abinda Junaid zaiyi da ita yana ganin Zeenah.

A haka har bacci ya dauketa.

Da safe Junaid ya nufi bangaren Azeema, tana zaune a falanta ta lumshe ido tana tunani, ga busar barewa datasa ake mata.

Hannunta daya take dan kadawa wanda duk sands take tunani haka takeyi.

A hankali tace "Barira an kawo rahoton danace?"

Tace "a'a Gimbiya amma nasan Waziri yana hanya."
Sallamar Junaid ne yasa ta bude idanunta dan batai tunanin jinsa ba."

Shigowa yai, tai saurin sallamar kuyangar dakeyin busar, tace "Junaid!"
Gaisheta yai sannan yace "Tuba nake Umma jiya dana dawo bansamu shigowa ba."

Tace "bakomai Junaid nasan kanada dalilinka."

Murmushi yai sannan ya kalleta cikin kulawa yace "Umma wani abu ya hadaku da ita ne? hajiya Inna nake nufi."

Kallansa tai itama sannan ta sallami kowa dake falan ta kalleshi, tace "Karkasa wannan abin a ranka dan nima ban bari ya dameni ba."

Tausayinta ne ya kamashi yace "amma kin mata laifi ne?"
"A'a batasona ne saboda tana jin haushi na auri Abdulsalam wanda ta rika bayan rasuwar Mahaifinka."

Duk da bai gamsu na amma baice komai ba.

Shiru yai kafin ya daidaita zamansa yace "Na umarci Binta ta dawo nan."

Kallansa tai da sauri tace "nan?"

Ta kalleshi cikin tsananin mamaki, dan bata taba tunanin ko ita tace ba zai yadda da hakan.

"Eh, sannan inasan sanin yanda yanayin masarautar take tun lokacin da suka gabata."

Azeema ta kalleshi cikin jin dadi tace "ba matsala, zan sa Mahmud mijin Safiya wanda yake Hakimi ne shi ya sanar dakai komai."

Muje? Ta tambayeshi.
Yace "Eh amma akwai dalilin kiran ne?"

Tace "lokaci lokaci yakan kira mata da yaransa a tattauna."
Junaid ya jinjina kai kawai.

Mikewa tai suka fito, a bakin kofar fita suka ga Binta wacce ke kokarin shigowa rike da ledar kayanta.
Da sauri ta rusuna ta gaisheta, Azeema ta kalleta tace "Binta kin taho?"
Eh.
Shiru tai tana wani tunanin, kafin ta kalli Junaid tace "Junaid me kake tunani in ta bimu?"

Ina?
Murmushi tai tace "Su Barira ma suna zuwa dan taje itama bana ganin akwai matsala."

Junaid yai shiru duk da ya tabbatar akwai wani abin a ranta sai dai rashin sanin menene ya hanashi musawa.
Barira ta kalla sannan tace "Bari a ajiye kayan ku biyomu."
Nan suka shiga ciki.
Kayan kawai suka ajiye suka fito, Binta na tambayar Barira akan ina zasuje.
Barira ga shareta kamar ba da mutum take magana ba, hakan yasata yin shiru.

Bangaren Mai Martaba Sarki Abdulsalam suka nufa.

Fadar sa aka bude musu kofa, Zagi ya sanar da isowarsu.

Jakadiya na tsaye a bakin kofar tana musu barka da zuwa.

Hajjo, Zeena, Zubair da su Ramlatu da ragowar matan sarki da yaransu sun hallara da alama sune sukazo karshe.

Hajjo ta hade fuska, Azeema ta zauna a inda aka ware dominta sannan Jakadiya ta nunawa Junaid inda zai zauna, zama yai su kuma su Binta da ragowa bayi suka koma gefe suka tsafsaya, Binta tana tunanin me take anan?

Azeema kam kallanta tai kadan tace gwara ki fahimci Junaid ya miki nisa hakan ne yasa na kawoki.

Zeena ce ta zubawa Junaid ido cikin jin dadi da mamaki halim da take neman tsintar kanta a ciki.
Gani tai ya dago ya kalli wani gun, idanuntanr suka kai kan Binta, wani irin kululun bakin ciki ne ya kamata.

Sanar wa isowar Mai Martaba da Zagi yai ne yasa kowa ya daidaita.

Abdulsalam ya shigo ya zauna tare da kallan su.

Kowa an ajiye kayan marmari da abinsha a gabanshi.

Bayan an gaida Mai Martaba ne ya kalli Junaid yace "Dafatan Junaid ka fara warewa da zaman nan?"
Junaid yace "Alhamdulila."

Andansyi shiru kafin Sarki yace sannan yace "Bari mu fara gwada tambaya kamar yanda aka saba, dan a tattauna a kara rike sanin juna."

"Idan akace za'a sai Sarki nawa kuke tunanin ya kamata a siye shi?"

Hajjo ce ta kalleshi tace "Rankanya dade wannan tambaya ta ina za'a nemo amsarta?"

Sarki bai kalleta ba yace "wannan tambaya inaso Zubair ya bani amsarta"

Zubair ya kalleshi yaga yanda Sarki ya hada rai yace "ta ina za'a sai sarki? Ai wannan sai dai bayi, idan kuma har akaje ga siyan sarki to lalai sai dai a kwashe duk tattalin arzikin garin a sai shi."

Wani kallo Sarki yamai yace "idan aka kwashe arzikin kasar sai kuma ai rayuwa dame?"
Zubair yai shiru, Ran AbdulSalam ya baci saboda haushin amsar daya bashi, kallan Zeena yai wacce itama taji haushin ansar."

Zeena me kike tunani?

Kallansa tai tace "indai za'a sai sarki to kenan ya zama ba sarki ba"

Yace haka ne indai har aka siye shi ai ya tashi daga matsayinsa, Junaid kai fa me kake tunani?

A siyeshi a silai

Silai?

Azeema ta kalleshi da sauri tace "Junaid!"

Nan kowa ya fara yan kananan maganganu, Zeena ce ta kalleshi itama hankalinta a tashe.

Binta kam idanunta kawai ta runtse dan tasai halin Junaid duk abinda ke ransa fada zai, yanzu me ya kawo zancen silai? Karamin kudi?"

Sarki wanda shi kansa ransa ya baci matuka ya dunkule hannunsa sannan ya dan murmusa yace "me yasa kace haka?"

Junaid yace "A tunanin mutane dayawa Sukai ba wani kudi bane mai daraja sai dai a gun talaka wanda yake neman ci dasha dakyar silay tafi komai daraja a gunsa, kafin a samu wanda baisan darajar sulai daya ba za'a samu talakawan da suka san darajarta ashirin, hakan yasa Silai ta zama kudi mafi daraja a ciki kudi, sannan sai ka hada silai dayawa ne zaka samu kudi mai daraja da kake nema.
Idan har za'a sai sarki to sai a siyeshi a abu mafi daraja wanda talaka da mai kudi sukafi sanin darajarsa."


Yana kaiwa nan yai shiru bai kara tanka komai bs.

Ido Abdulsalam ya zubamai, tabbas koshi bai taba kawo hakan a ransa ba, wannan shi ake kira magana da hikima wanda ake neman Sarki da ita, tabbas dawowar Junaid nan ba karamin matsala zai jawo masa ba nan gaba.

Azeema wacce dadi ya kamata ta kalli Abdulsalam, hannunsa ta kalla dan ta gama saninsa duk wani abu dayake tunani rabi tana ganewa daga kallansa.

Ganin hannunsa a dunkule yasa ta kalli fuskarsa, da sauri ya sake hannunsa sannan ya kalleta cikin nuna tsantssn jin dadinsa yace "Masha Allah! Tabbas wannan shi ake kira magana cikin hikima."


Zeena ce ta kalleshi tace "Mai Martaba ni kaina na tsorata jin Ya Junaid yace silai, sai dai jin bayaninsa yasa na fahimci me yake nufi sannan na fahimci Silai yafi komai daraja kamar yanda Sarki yafi mutanen gari."

Hajjo ce ta sa hannu ta bige Zeena dake gefenta, sannan tace "amsoshi duka sunyi ma'ana kowane da nashi fahimtar."

Azeema ta dau kofin dake gabanta ta kurbi ruwa.

Binta wacce tai shiru tana kallan Junaid wanda ya daure fuska sam ba alamar fara'a a tattare dashi, tabbas Junaid dinta jinin sarauta ne, wanda ita kuma take wacce mahaifinta ma bayaso........

Zeenatu ce ta kalleta ganin yanda take kallan Junsid cikin rauni yasa tace "Binta!"

Kafin ma Binta ta amsa Junaid ya kalli Zeena.

A ranta tace au ashe zaka kalleni, Binta ce ta matso da sauri, Sunkuyowa tai Zeena ta mika mata kofinta tace "dan daurayomin naga kamar kura."

Binta ta kalli Junaid wanda ya dauke kai kamar baisan tana gun ba.
Sai dai gaba daya hankalinsa na kansu, Binta ga amsa tai waje, Azeema ta bita da kallo.

Zubair ne ya kalli Hajjo cikin kunar rai, alams tamai da karya nuna jin haushinsa.

Sarki yai murmushi yace " Junaid kayi tunanin abinda nace ka zaba?"

Junaid yai kasa dakai yace "zan sanar dakai Ranka ya dade."

"Sirri ne kenan?"

Zeena ta tambaya, bai ko kalleta ba sai dai Azeema datace da alama.....




**********
*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍*



Nanma shiru yay yak'i tankawa, yakumak'i kallon kowa.

Binta ta dawo da kofin da zeena tabata ta d'aurayo, rissinawa tayi ta mik'a mata, d'agowar da zatayi suka had'a ido da Junaid, saurin janyewa tayi, shima ya basar.

Azeema da Idonta ke kallon duk motsinsu taji zuciyarta ta k'untata, amma saita had'iye fushinta tamkar babu komai.

Sarki yacigaba da jeho tambayoyinsa ana bashi amsa, Junaid kam tundaga ta farko bai kuma tankawa ba, sai dai tsaf yake nazari akan amsar kowa da motsin kowa.

Bayan taron ya tashi kowa ya nufi sashensa, Azeema taso Junaid yakoma sashenta dan tanason jin miya tanadi zaba bisa ga k'yautar sarki na abinda yakeso.



*****************

Tunda Junaid yadawo daga sashen mai martaba saiya kasa zama, sai safa da marwa yake a falonsa yana cud'anya wasu abubuwa daya danganci masarautar tasu, a yanzu mafita d'ayace dashi, nutsuwa wajen jin sirri da tushen masarautar tasu, haka kawai jikinshi na bashi ba dalilin dazaisa mahaifinsa ya kaishi can gefen gari ba tare da sanin mahaifiyarsa ba.
Ta wannan hanyarne kawai zai samu amsar tambayarsa akan wanene yasa a fiddashi a masarautar zuwa ke6antaccen waje?.

Ajiyar zuciya ya sauke da addu'ar samun kwarin gwiwa akan samun warwarar cud'ad'd'en al'amari da zuciyarsa ke hangowa gameda abubuwa masu yawan gaske.


*****************

Suna isowa sashenta ta kalli zeena rai 6ace.....

"Hajjo nikam wannan kallon naki tsoro yake ban, nidai nasan banyi wata kato6ara a wannan taronba, banda abin arziki danai."

Hararta Hajjo tayi tana hura hanci, murya a cinkushe tace, "wani lokacin saina ringaji inama bani Na haifi Zubair ba, kwata-kwata k'wak'walwarsa bata ja yanda ya kamata, dolene na nemo malami ya koyar dashi hikimar zance".

Dariya Zeena tayi sosai dukda kallon da hajjo ta watsa Mata bai hanata fad'in "To Hajjo ke da kanki kin kirashi mai kwakwalwar kifi tayaya ko kin d'akko malami masanin hikima kan Yaya zai iya bud'ewa? Da dai kunyarda da shawarata kawai dayafi muku, danni inaji a jikina Yaya bazai mulki masarautar nanb......."

Hannu Hajjo ta kai mata, Zeena tai azamar matsawa da baya. "Nifa umma gaskiya nafad'a, idan baki haifi sairkiba ai kin haifi wadda zata haifa miki sarki, ki zauna kiyi tunani akan hakan?".

"Lallai ashe ba Zubair kawai ne mai kwakwalwar kifiba? Kekam ai saita jakuna, shashasha kawai, idanma barci kike ki farka, babu yanda za'ai jinina ya dunk'ulu dana Azeema".

Baki Zeena ta ta6e ta mike tai hanyar d'akinta da k'unk'uni tana fad'in "Ashe zaki mutu kuwa ayi, Danni koza'a maida masarautarnan birnin sin saboda rikici saina mallaki ya Junaid matsayin mijina uban y'ay'ana, yau na tabbatar shikadai ne ya dace dani dan haka ba wanda ya isa ya hanani mallakarsa."

Hajjo najin k'unk'unin Zeena, amma batajin mitake fad'a, dan haka ta zuba tagumi tana binta da kallo. Takula inhar tayi wasa za'ayi sukuwar irganmun dokuna a masarautar nan batareda ta d'aurama nata sirdi ba. Kai ina ALLAH ya kikaye, koma mizai faru kam sai dai ya faru, sai Zubair yazama *SARKI!*.



hummm to maji magani an binne tsohuwa da ranta😹



***********************

Gaba d'aya zama sashen Azeema bayama Binta dad'i, amma tayi alk'awarin jurewa kodan farin cikin Junaid. Yanzu haka buk'atar ganinsa takeyi, koda bazasuyi maganaba ta gansa tasami nutsuwa, dan talura lallai yamata nisa, ta k'ara fahimtar hakane bisa mizanin fahimtar gayyatar da azeema tamata zuwa taron jiya.

Da farko bata fahimtaba, saida suka dawo ta zauna tayi dogon nazari, ta umarci tabisune saboda a nuna mata iyakarta, murmushin takaici ta saki tana had'iye kukan daya fara taho Mata. Lallai dolene ta sake takunta, dan ta lura mahaifiyar Junaid kishi take da ita. Babbar magana, ina ita ina kishi da matar sarki, mahaifiyar Wanda tafiso aduk fad'in duniyarnan, insha ALLAH cikin ruwan sanyi zatabi matakan da mahaifiyar Junaid zata fahimci ba burinta rabata da d'antaba.


Sam bata iya ko fitowa, daga daki sai takar gida na baya, haka zata zauna tai shiru tana mamakin wannan rayuwa data tsinci kanta a ciki wanda bata taba kawowa ba, ada ta dauka samun inda iyayen Junaid suke shi yafi komai mahimmanci a gareta sai dai yanzu batasan me ke ma ranta ba.
Dan wani sa'in takanji dama bai gansu ba.......
In hakan yazo ranta sai tai saurin yin istigfari tare da fatan Allah ya kauda mata wannan mumunan abin da zuciyarta ke raya mata.

**************
Sai dayai kwana uku bai fita ko ina ba, ya zauna sosai yayi karatu akan abinda yake san fahimta.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login