Showing 9001 words to 12000 words out of 76752 words

Chapter 4 - ZAFIN RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

ayusher   

26 Aug 2024

8563

massalaci suna cewa, kace jiy yaji jiki? Dayan yai dariya yace "nima sai dare naji labari, ai da badan an hana kashe bayi ba inaji yaran nan da sai ya sheka barza'u.

Gaban Azi ne ya fadi ya kallesu da sauri yace "wanene yai laifi?"

Hannunsa da ya rike ya ture yace "ina muka sanshi? Muma labari mukaji."

Da gudu Azi ya juya ya nufi indai yake tunanin samunsa.

Junaid na kishingide ya gaji dajin munsharin dayan, ya mike ya zauna, daga nesa ya hango Azi, cikin tsananin farin ciki, ya ke kallan Azi harya karaso.

Azi idanunsa suka ciciko yace "waye yama wannan wulakanci? Waye wannan......"

Muryarsa ce ta fara rawa saboda karayar zuciya, Junaid ya kalleshi yace "Azi."

Kallansa yai yace "tunda nasan inda kake bari na sanarwa Mai martaba."

Idanu Junaid ya zaro yasa hannu ya jawoshi dan kusa dashi, cikin rada rada yace "karka kuskura, ka wuce ka koma gida gun Binta dan nasan tana nan hankalinta a tashe."

Ni zan taho da zarar ta budeni."

Azi ya kalleshi yace "yanzu Yar....wali kana cikin wannan hali zan tafi gun Binta? Kayi hakuri amma bazan iya barinka ba." Shima cikin rada yai maganar.

Junaid ya kalleshi yace "umarni na baka, ka wuce yanzu ka koma gida, in hankalinka bai kwanta ba nan da kwana goma sai kazo mu tafi."

Azi kam hankalinsa ya tashi, ya kalli Junaid zaiyi magana wannan Bawan yace "ah wai har gari ya fara wayewa."

Junaid ya kallo Azi yace "ka wuce kafin ya mike zaune."

Azi ya juya yana kamar wanda bashida laka a jikinsa.......


********
Binta dukunkune cikin dakin Yarima sai kuka kawai takeyi, Hari tayi lalashi harta gaji, daga baya ma zazzabine ya rufeta, amma duk da haka idanunta bai bar zubar da kwalla ba, saboda jikinta ya gama bata gidansu ya koma ya barta anan.

Cikin kuka tace "mahaifinki ma ya cillar dake ko nemanki baya yi, ga Junaid shima ya yada ke."

Kuka ta kara sakawa.......


*ZAFIN RANA*



*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*


Shafi na Takwas

Zaune take a bakin gado ta dafa kanta wanda yake sara mata, tabbas yaran nan kamarsa daya da Junaid ba idanunta bane yake mata gizo, mikewa tai a hankali ta fito falo.

Bari na tsaye tana ba kuyangun umarni yanda zasu gyara gidan.

Tana ganin Azeema ta fito ta nufi gunta da sauri, Gimbiya lafiya? Da sassafen nan?

Azeema ta kalleta tace "Bari kaini inda yaran nan yake, inada tambaya da zan mai."

Bari cikin mamaki tace "wani yaro?"

Azeema ta kalleta, "yaran jiya?" Bari ta tambaya.
Kai kawai ta daga mata, nan suka shiga cikin daki, bari ta yafa mata wani dogon mayafi, suka fito.

Sum sum sum suke tafiyar saboda basa san wani ya gansu, da yake kuma safiya ce kowa na dakinsa, sai bayi suma kadan daga ciki.

Azi na jingine da ginin hankalinsa a tashe, yana tunanin gaskiya bazai iya tafiya ya barshi cikin wannan halin ba.

Hango mutane biyu sun nufo gun ne yasa ya boye, wucewa sukai, Bari t leka taga dakarun gun basanan, dan dama Azi dazai shiga ne ya aikesu.

Ciki suka shiga da sauri, bari ta kalli Junaid sannan taga wani a gefe, gashi a kwance amma da alama idansa a bude yake, bari tace "kuyi magana bari naje can."

Tana fada ta nufi dayan gun da yake, bawan Allah tambaya nake.

Mikewa yai daga kwancen, ta tare saitin da Azeema take ta fara mai tambayoyin shirme, dayake mutum ne mai san magana ya biye mata yanata bata labari.

Junaid ne ya kalleta, ya ganeta, itace ta dazun nan.
Shiru tai ta zubamai ido wanda harya fara tsarguwa.

Idanunta sun ciciko suna neman zubar da kwalla, gaba daya jikinta rawa yakeyi, gabanta sai wani irin faduwa yakeyi, a hankali tace "Junaid?"

Kallanta yai zuciyarsa ta fara harbawa, itace kenan? Abinda yazomin a ransa kenan.

Ganin yanda yai da idanunsa ne yasa tace "Junaid?"

Jikinsa ya kalla, ya tuno abinda ya faru dashi jiya a gabanta, kallanta sannan ya wawaiga ya nuna kansa yace " ni?"

Jikinta ne ya saki, ta kalleshi a tsorace tace "Junaid?"

Yace "wai ni?"

Hankalinta ne ta tashi ta kalleshi, idanunta suka zubo da kwalla ba tare data sani ba, shima nashi idanun ne suka fara rauni, daurewa yai ya kalleta yace " wani kike nema Gimbiya?"

Kallansa tai tare da goge hawayen tace " ya sunanka?"

Wali ta fada yana kallanta, kai ra jinjina gaba daya jikinta ya mutu, tai murmushin yake tace " a ina kake?"

Shiru yai yana kallanta itama kallansa take tace " ba a nan garin nake ba, zuwa nai, sannan inada iyaye da kane."

Shiru tai tana kara kallansa, tace zaka iya cire rawaninka? Kasan kanka zan gani."

" kasan kaina?"

Tace "eh."

Yace " Me kikesan gani?" Yai maganar adan raunane.


Kallansa tai tace " ina duba zan fadama, sannan bakai kama da bayi ba, ko daga kalamanka."

Mikewa yai yace " dan Allah Gimbiya ki yafemin, ku barni sa raina, bansan mena aikata ba, yau na fara zuwa gidan sarauta dan Allah ku taimaka ku barni na fita, iyayena na jirana."


Jitai kanta yana kara sarawa, da gaske Junaid ne yake mata gizo a fuskar yaran?
Bari ce ta mata alama da tai sauri, hakan yasa ta kalleshi tace "kayi hakuri in na bata maka."

Harta juya tana neman tafiya yace "wa kike nema?"

Juyowa tai ta kalleshi sannan tai murmushi mai tattare da bege tace "d'ana."

Tana fada ta juy, Bari ga kalli mutumin tace "nagode fa zan duba abinda kacemin."

Ta juya suka fita, suna barin kofar kuwa dakarun na dawowa.

Azi dake tsaye yana kallansu sanda suka fito, shiru yai yana tunani, bari yabi umarnin Junaid ya tabbatar zai kula da kansa harya dawo, juyawa yai ya fita.

Junaid kam tana fita ya runtse idanunsa, gaba daya idanunsa suka kada sosai sukai jaa, dazu yunwa da fitsari sun matseshi amma yanzu sam baima jin yunwar, meyasa kace mata bakai bane? Bayan zata sa a budeka in taji kai waye.

Kai ya girgiza yace sun yadda ni taya zan yarda ta gani a cikin halin tausayi? Bayan ta yarda danta tana rayuwarta yadda ta saba?

*********

Azeema na shig dakinta taga Mai Martaba a zaune a dakin, mamaki ne ya kamata dan ba zuwa yake ba sai dai ya aiko taje, yau lafiya?

Kallanta yai sannan yace "daga ina? Da sassafen nan?"

Zama tai kusa dashi tace "jinai banji dadi shine nai yar tafiya."

Murmushi ya sakar mata sannan ya riko hannunta wanda ya dau sanyi, hannunsa yasa ya rufesh, sannan ya fara hura hannun nata yana murzawa.
Shiru tai ta kuraws kasa ido, sai dayaji hannun yayi dumi sannan ya jawota jikinsa yace "Menene?"

Dagowa tai ta kalleshi tace "wani na gani, kamarsu daya da Junaid."

Kallanta yai jikinsa yai sanyi yace " a ina?"

Tace "jiya yayina Zeena laifi."
Bawa ne kenan?
Tace eh

Da har gabansa ya fadi amma jin haka yasan ba shi bane, balle yasan jiya Azi yazo.

Kwanciya yai a kan gadon sannan ya kwantar da ita kusa dashi, yace "Zaki ganshi insha Allah."
Hawaye ne suka zubo mata, tace "da na dauka gyambon ya tafi, amma yau ganin yaran nan ji nake bazan iya rayuwa ba Junaid ba, Abdulsalam ka taimaka ka nemon Junaid." Kuka ne ya kwace mata.

Zuciyarsa gaba daya ta gama karyewa, gaskiya zai kaita inda Junaid yake sai ya fada mata tayi hakuri ta barshi a can tunda umarnin Sarki Zubair ne.

*******

Zeena tana zaune gaban abincin da aka jera mata, kallan Fure tai tace "jeki sa a kawon yaran nan."

Fure cikin mamaki tace "Gimbiya."

Zeena ta zabga mata wata harara, da sauri Fure ta fita, tana zuwa ta sanar dasu sakon Gimbiya nan aka bude Junaid, mamaki ne ya kamashi dan yasan wannan yarinyar bazata bude shi ba, ko Ummansa ce? In itace zai bata hakuri y fada mata.

Fure har ta fara tafiya yace mata yana san shiga kewaye (toilet) ban ta kalli dakawan, sukai kewaye dashi.

Bayan ya gama ne ya tsaya ya kakkade jinkinsa, dan taimama yai yayi sallah a kasa, duk kayan sun baci da kasa,yadan gyara rawanin sa dayai sannan ya fito.

Fure na gaba yana binta a baya, tsayawa yai cak? Dan yanzu ya ganeta itace mai zubamai ruwa jiya, kenan yarinyar nan ce?

Fure ta juyo ta kalleshi tace "muje."

Junaid ya hade fuska yabi bayanta.

Tana zaune haryanzu bata fara cin abincin ba aka shigo dashi, kallansa tai sannan ta fara cin abincinta.

Dayake yunwa yakeji kamshin abinci yasa yunwar ta motsa sosai, Zeena kam cin ahincinta take harta gama sannan ta kalli Fure ta mata alama da a dauke, nan Fure ta sa aka kwashe.

Zeena ta kalleshi tace "fita waje ka tsaya a tsakiyar rana."

Da sauri ya kalleta, tace me? Bazaka iya ba? Ko kafi karfi?

Mikewa yai ya fita waje ya tsaya a tsakiyar rana.

Daga ciki ta wangale kofa tana kallansa, murmushin mugunta tai sannan tace "bani hakuri."

Kallanta yai, Binta! Abinda ya fado masa a rai kenan, ya daure yace "yahkuri."

Dariya tasa tace "haka ake bada hakuri? Ka ban hakuri sosai kace "Gimbiya Zeenatu ki yafemun ki taimaka kiyi hakuri."

Kallanta ya sakeyi tace "kafi karfi?"

Shiru yai kawai baice komai ba, iska tadan furzar tace "karkaga laifina."

Mikewa tai ta fito waje, ruwa ta debo da kanta ta nufo inda yake, ta daga hannu zata zubamai yace " me zai kareki in na fada?"

Da sauri ta kalleshi rai bace tace "mene?"

A hankali yace " kina matsayin Gimbiya bakya tunanin kina kaskantar da kanki gun daga hankalinki akan bayi irin mu?"

Idanunta ne suka fifito saboda bacin rai a zafafe tace "mene?"

Da dan karfi Yace "Gimbiya Zeenatu ki yafemin ki taimaka kiyi hakuri."

Huci kawai take saboda bacin rai, yace "na fada ki barni na koma gida dan Allah."

Kallansa ai tace "gida?"
Tasa dariya tace "na fasa kulleka ma bawana zaka zama zanga me zakayi."

Junaid ya kalleta cikin takaici, yanzu wannan kanwarsa ce? Tunda babansu wa da kani ne? Wani irin tarbiyya aka bata?


***********

Hankalin Hari ya tashi saboda zazzafan zazzabin da Binta keyi, sai amai take shekawa ta kasa cin komai, Hari ta rasa ya zatai, ta bata magani ta zauna kusa da ita tana tausarta akan tasan Junaid bazai taba yadda ita ba.......


Nima nace gaskiya.....lol


*Ayusher Muhd*




*ZAFIN RANA*



*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*


Shafi na Tara


Ran Zeena yakai matuka gun baci da taga yanda ya kalleta.

A zuciya ta ciklar da kwanan data debo ruwa tai ciki rai a bace.
Tana shiga ta hau cillar da abubuwan dake cikin fadar tata.

Tana gamawa, ta wuce ta fito ta kalleshi tace biyoni.

Junaid bai musa mata ba yabita, bangaren Hajjo tai dashi, tace ya koma ya tsaya cikin rana, ita kuma ta shiga ciki.

Hajjo ta kalleta tace "kinga damar zuwa?"

Zeena ta turo baki tace "Yanzu na tashi."

Hajjo ta tabe baki tace "kardai ki manta anjima zakije gun Yariman Gobir dan mai martaba jiya ya aiko a fada miki."

Kallanta tai tace "Wai meyasa kuke san sai kun aurar dani dole?"

Hajjo ta mata wani kallo tace " kin girma gundin gundin so kike mu saki a gaba muna kallo kamar kawar mu?"

Zeena ta hade fuska tana cewa "ni wlh bana sansa da wani bakinsa kamar na......."
Kallan da Hajjo ta mata ne ya sata tai shiru.

Hajjo tace "baki dai dauko yaran nan daga magarkama bako?"

Kallanta tai a ranta tace ya akai ta sani?

Hajjo ta kalleta tace "kinyi ko?"
Zeena tace "ni ki barni da kaina zan koyamai hankali."

Hajjo tace "ai rashin hakurinki nasan bazaki taba iya barinsa a can ba, wannan rashin hakurin bansan ya zakiyi ba in kakai aure."

Zeena ta juya kai.

Junaid na tsaya cikin rana yunwa kadai ma ta isheshi.

Jin hirar taso da Hajjo bata mata ba yasa ta fito.

Kallansa tai taga yanda ya dan galabaita tace "biyoni."

Nan Junaid ya bita, duk inda taje bata dadewa take fitowa gashi ko ina sai tasashi tsayuwa cikin rana, tun yana daurewa har yunwa ta fara sa kafafunsa dan rawa, rabanshi da abinci tun a gidansu daren shekaranjiya kafin su taho, to gwara a hanya da suka iso Biram sun dan sai gyada sun ci.

Zeenatu ta koma bangarenta, tana zama ana hera mata abincin dare.

Daga waje tana kallan yanda Junaid yake daurewa da alama yunwa ta kusa mai ila.

Kallansa tai sannan ta kalli Fure tace "zuba abinci ki ba wancan."

Fure cikin mamaki tace "eye?"

Zeena ta kalleta, hakan yasa ta yin saurin zubawa, fitowa tai da abincin ta kalleshi tace "gashi."

Junaid ya kalleta sannan ya kalli Zeenatu wacce itama kallansa take, harya kai hannu zai amsa Zeena tace "Fure? Uban wa yace ki zuba abincina ki ba wa wani bawa?"

Fure cikin mamaki ta juyo ta kalli Zeenatu, Kin dawo nan ko sai ranki ya baci?

Fure ta juya da sauri, Junaid ya kalleta, yanzu kam ya gane wani salan wulakanci ne yasata sawa a kawo mai.

Fure na komawa ta amsa ta ajiye sannan ta fara cin nata.

Lomarta uku aka aiko akan taje Yariman Gobir na jiranta.

Ranta ne ya baci wanda ko abincin ma bata iya cigaba da ci ba.

Haka Fure ta tayata ta canza mata kaya, ta mata kwalliya, fuskar nan tata a hade bakin ciki da takaici duk ya isheta.

Tana fitowa tsa hannu ta dau gwaibar dake cikin kwano, ganshi tai a tsaye, kallansa tai tace "biyoni."

Ta kalli Fure tace ku tsaya na dawo.

Mamaki ya kama Fure tace "amma Gimbiya......"

Zeena tai gaba wanda ya hana Fure kara magana.

Junaid yabi bayanta yana tafe a baya tana gaba, juyowa tai ta mikamai gwaibar, ansa yai tare da cewa "na meye?"

Bata kalleshi ba tace "bansan ka mutu min a auramin laifin kasheka."

Haushi yasa bai bata amsa ba, harta dan cigaba da tafiya sai kuma ta tsaya ta juyo tace "ina tunanin abinda zan maka, dan Allah wannan abinda ke yawo akanka sai na saitashi." Ta juya.

Wani kallo ya mata sannan yace "naji ko menene kimin amma dan Allah ki barni na koma gida na bar iyalaina cikin wani hali."

Kamar baza tai magana ba sai jiyai tace " iyalai? Aure gareka?"

Eh harda yara.

Baki ta tabe sannan ta cigaba da tafiyarta, Junaid yace "yaushe zaki sallameni?"

"Ban sani ba, sai sanda ladabinka ya dawo?"

Junaid baisan sanda yace "mene?" Cikin sautin dayai maganar ne yasata juyowa a fusace tace "me kace?"

Shiru yai sai kallanta dayai, ranta ya kara baci tace "me kace?"

Yace "bance komai ba gimbiya."

Juya wa tai rai bace ta cigaba da tafiya.

Wani hadaden ginin ne a gun, anmai kwalliya sosai, tsayawa tai ta kalleshi sannan tace "bude kofar."

Da sauri ya haura ya bude ta shiga ciki, yana neman rufe musu kofar tace "shigo."

Nan ya shiga sannan yaja kofar ya rufe.


***********


Zaune take a gabansa tace "Takawa ka aika a kirani?"

Kallanta yai sannan ya mike zaune, hannu yasa ya riko hannunta ya dagota daga gun da take sannan ya wuce da ita cikin turakarsa.

Kofa ya rufe sannan ya dawo kan gado ya zauna, kallansa tai tanasan magana sai dai yanda taga yanayinsa yasata yin shiru.

Zama yai a kusa da ita yace "Azeema!"

A hankali ta juyo saitinsa yanda ya kira sunantane yasa ta kasa amsawa.

Kallanta yai yacw "nasan Azeema da rashin hakuri, rashin yafiya, daukar fansa, rashin barin wani yai nasara a kanta."

Murmushi tai tace "shaidar dakamin kenan? Duk ba shaidar arziki?"

Yace "Sai dai macece wacce tasan kanta, bata shiga hakkin wani, bat taka na kasa da ita, bata yin abinda zai jawo mata zagi gun mutane."

Dariya tai tace "to naji menene ke faruwa?"

Shiru yai tare da kura mata ido, tace "menene? Kasan halina banda hakuri ko na jira ne."

Dariya yadanyi kadan sannan ya mike tsaye da sauri yace "dama fada miki zanyi jibi ki shirya zamu wani guri dake, sai dai mu biyu zamuyi tafiyar sai dakaru guda uku."

Kallansa tai cikin mamaki tace "ina zamu haka da sai a boye zamu?" Yace "in mun je kya gani sai dai wannan karan duk rashin hakurinki dole ki hakura sai munje can."

Murmushi tai tace "ya na iya? Na hakura."

***********
Ga duk mai bukatar siyan littafin nan ya tuntubi 07084161619.
**********



Zama tai daga inda aka tanada dominta, yarima na zaune ya kalli Junaid yace "dan bamu guri ko?"

Junaid ya juya zai fita, Zeenatu tace "ni nace ya tsaya."

Cikin mamaki Yarima yace "kinsan gobe zan koma ina bukatar muyi sallama ne."

Muyi sallamar a haka dan ni wlh bacci ma nakeji.

Shiru yai yana kallanta, murmushin rainin hankali ta saki, Junaid ya fahimci amfani take sanyi dashi hakan yasa ya juya kawai zai fita.

Jiyai tace "ina zaka?"

Junaid ya juyo yana kallanta, Yarima Sulaiman ya hade fuska sosai, balle dayaga Junaid ya kalleta ido cikin ido, kallanta yai yace "meye tsakaninki dsshi? Dan ba bawan dazai kalli Uwar gijiyarsa ido cikin ido."

Junaid ya kalleshi yace "Tuba nake Yarima amma ina da aure."

Ya juya y fita rai a bace, mexaiyi da wannan? Wallahi ko aura masa ita akai sai san yanda zaiyi ya gudu daga gunta.

Binta ce ta fadomai, gwaibar hannunsa ya kalla,yai ajiyar zuciya anya binta taci abinci ma kuwa? Jiyai gaba daya kansa ya rike, ko ya gudu daga nan tunda ba mai kallansa.

Kafin ka fita kofar masarautar ma an kamoks.

Dole ya lalabata inta fito tabashi damar tafiya.

A ciki kuwa Sulaiman ne ya kalli Zeena yace "wai Gimbiya meke damunki? Sai yaushe ne zaki tsaya muyi magana ta fahimta?"

Kallansa tai tace "kafi kowa sanin bana sanka to akan me zaka damu da sai ka aureni? Akwai yan mata a gidan mu ka zabi wacce kake so ka aura amma bani ba."

Cikin mamaki ya kalleta yace "saboda yaran can?"

Dama dalilin tahowa dashi datai kenan dan ya korar mata wannan cingan din.

Kasa tai da kanta batace komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login