Showing 66001 words to 69000 words out of 76752 words
ido daya kafin ta bude dayan idan, Zeena tace "nama fasa aikaki gun Hajjo hada kayanki ki koma gun Binta, can itace zata iya da haukarki."
Fure tace "tuba nake Gimbiya wlh bazan iya zaka gun kowa ba in bake ba."
Hannu ta kara dagawa, da sauri Fure da sake rufe ido, Zeena tasa hannu ta dungure mata kai tai baya, tace "tashi kije can waje cikin rana ki tsaya, nama fahimci duka da hannu batawa kaina lokaci ne."
Fure tace "Haba Gimbiyata, kin manta yau kwananki ne? Ai yanzu zamu fara shirin kwana."
Murmushi Zeena tai tace "kin wanke kanki, me zamu shiryama Ya Junaid yau?"
Fure zatai magana Hajjo ta banko kofa.
Baki a sake Zeena ta kalleta, Hajjo tace "tashi."
Tashi? Wa? Ni?
Hajjo tace "a'a ni."
Zeena tace "meya kawoki dakin sirikinki? Bayan ko gaisheki baizo ba tukun?"
A kufule tace "suruku, kin tashi kin fito mun tafi ko sai na sa an ja ki?"
Zeena fuskarta dauke da mamaki tace "wai ni za'a dauka ko kuwa wata? Na tabbatar kinsan halina da abinda zanyi da wanda bazan ba."
Hajjo tace "yau kuwa dole kiyi abinda nakeso, kin tashi mun tafi ko sai na ci mutuncinki, aure ne na raba ya kawo miki takardarki, ya dau uwarsa da matarsa su koma kauye."
Da fuskarta alamar mamaki ta fara nunawa kafin ta sa dariya tace "lalai Hajjo ni yau Allah yasa lfy kike?"
Kin wuce ko kuwa?"
Gyara zamanta tai ta kalli Fure tace "dubo in Ya Junaid na nan kece mai Hajjo tazo zasu gaisa."
Fure data tsaya a kofa tun zuwa Hajjo tai waje da sauri, Hajjo tace "uban wa yace ina nemanshi? Balle har mu gaisa?"
Zeena bata ce mata komai ba sai kallan gefe ma datai.
******
Binta ce ta gaisheda Sabisu cikin sha'awa ya kalleta yace "Masha Allah kece matar Yariman?"
Binta ta kalli Junaid cikin kunya sannan tai kasa dakai."
Sabisu yace "kai lalai Yarima kayi sa'a na tabbatar da Sarki nadarai da ya kasance mai alfahari da zabinka."
Junaid ne ya kalli Binta wace ganin bai dawo yaci abincin safe ba yasa ta bi bayansa yace "nayi laifi amim afuwa."
Dan kallansa tai ta kasan ido tamai alama da zata wuce, dan wata kunyace ta rufeta datasan akwai babban mutum a can da bazata taso ba.
Junaid yace "Baba tun kafin inyi laifim da za'a dakeni bari naje."
Dariya sosai Sabisu yai yace "waya isa tabaka Yarima? Ko 'yarnan?"
Binta tace "zolayarsa ne wlh."
Da sauri ta mike cikin kunya ta fita.
Dariya Junaid yai, Sabisu cikin sha'awa ya kalleta sannan ya kalleshi.
Junaid ne ya canza yanayin fuskarsa yace "Baba kana tunanin abokin naka zai kai takardar wasikar Gayyatar?"
Sabisu yace "ai inaji yanzu ma ya kai, amma me kake nufi da aika takardar gayyata dakai?"
Junaid yai wani murmushi sannan yace "daga jiya zuwa yau kana tunanin ya isa masarauta nawa?"
Sabisu yace "matsalar dansa ne ba shi din bane, amma shi a lokacin Sarki Zubair in aka aikeshi kai sako kwana daya yakeyi ya je masarauta hudu."
Junaid cikin jinjina yace "masha Allah, to d'an nasa musamai ran daga jiya zuwa yau yaje uku kenan?"
Sabisu yace "eh."
Azi dake bakin kofa yana neman izini ne Junaid yace "shigo."
Nan Azi ya shigo ya gaisheshi, sannan yace "Yarima ance Masarauta biyu na kano da Zazzau sun aiko da sako kyaututuka da taya murnar Murabus din sannan da jinjinama Sarki, wasikar yanzu za'a shiga da ita fada."
Junaid ya kalli Azi yace "Alhamdulila komai na tafiya yanda ya dace."
Kallansu yai yace "bari naje na dawo."
Mikewa yai ya nufi bangaren Binta.
Tana zaune akan kujera ta cika ta batse ya tura kofar tare da dan gyara kafadarsa.
Kauda kanta gefe tai cikin nuna alamar fushi, zama yai kusa da ita sannan yadan bige kafadarta da kafadarsa.
Kara kauda kai tai, turata yai daga inda take ta matsa ya kara turata, mikewa tai zata bai gun, da sauri ya maida ita ta zauna yace "Bintalo na tuba."
Kara hade fuska tai.
"Laaaa har na tuno wata rana, muna zaune a waje ana hira cikin hasken farin wata, wata ta......"
Da sauri ta toshe mai baki tace "Na hakura ya isa ba sai ka fadi me nai ba."
Yana dariya yana kokarin yin magana bakin nasa a rufe.
Dan cizo ya mata a tafin hannun nata, sakeshi tai tana cewa "yaya Allah na hakura."
Yace "inaaa ai sai na karasa."
Batasan sanda ta sake rufe bai baki ba ta daddane shi da jikinta tana girgiza mai kai.
Idanunta yake kallo yana dariya sannan ya daga kai alamar ya daina.
Sakeshi tai tare da cewa "Allah Yaya gaskiya ka gama dani, ka gama sanin komai nawa ina yarinya nasan haka zakai ta zolaya ta."
Dariya yai zai sake magana sukaji ana magana a waje.
Baiwarta ce ta shigo ta sanar da ita sakon Fure.
Junaid ne ya kalleta fuskarshi dauke da mamaki, kallan Binta yai yace "bari na dawo yanzu."
Bangaren Zeena ya nufa, Hadimansa na biye dashi.
Yana kokarin shiga yana Hajjo rike da Hannun Zeena ita kuma tana zaune, ta rike kujera da daya hannun.
Hajjo ko da ganin Junaid bai sa ta bar abinda take ba.
Zeena na ganin Junaid ta warce hannunta da karfi ta nufi kusa da Junaid ta tsaya a bayansa tare da rike rigarsa ta baya.
Hajjo ya kalla alamar karin bayani.
Fuskar Hajjo a turbune tace "ka gaida ni ne?"
Junaid yace "jira nake ki zauna."
Haushi ya kamata tace "ba zama nazo ba tafiya da yar Abdulsalam zanyi tunda bakaga darajar yarsa ba kake neman wulakantashi."
Kallansa Zeena tai cikin rashin fahimtar kalaman Hajjo, Junaid ne ya kalleta yace "babu wulakantace a duniya sai wanda ya wulakanta kansa, sannan duk wanda ya wulakanta mutum da saninsa to lalai cikin dayam biyu ne kodai wanda aka wulakanta baisan kanshi ba ko kuma bashida daraja."
Hajjo ta cika da bacin rai tace "bamu 'yarmu."
Junaid ya kalleta yace "gatanan in zata biki."
Da sauri Zeena tace "Ya Junaid?"
Sannan ta kalli Hajjo tace "ba inda zani."
Junaid Hajjo ta kalla tace "bata takardarta, na tabbatar inka saketa dole ta tafi."
"Takarda?"
Hankali Zeena ne ya tashi tace "Hajjo baki da......"
Kallan da Junaid ya mata ne yasa tai shiru ranta yayi matukar baci.
Junaid yace "wannan kuma banga mai sani inyi abinda banyi niyya ba."
Sannan ya sake kallanta yace "ki huta lafiya."
Ya juya ya fita.
Hajjo kam kiris take jira ta fashe da alama.
*******
Isowar masu aiken sarakunan nan ba karamin hargitsa kwakwalwar Abdulsalam akai ba, yana makale a kasa a lungun gado kamar zautace yana cewa "a'a ba wanda ya isa ya kwacen mulki."
Nace sai mugani ai🙄
*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*
{46}
Gaba daya Azeema banda kwanciya a daki ba abinda takeyi, zazzabin ya barta amma abinda ke zuciyarta ya kasa sakinta, a duk sanda ta tuno abinda ya faru sai taji kwalla na neman kawo mata, ba shakka tasan tama Zubair babban laifi amma inta tuna ta bada kofa anyi amfani da ita ne sannan yanzu hankalinta ya kaimata ai shi Abdulsalam din shine ya kaita gun mai maganin, kenan dama ya gama shirinsa?
Duk sanda ta tuno hakan wani hawaye ne ke zubo mata.
Barira kam ta rasa abinda ke mata dadi, gashi Azeema tace karta sanar da ko Safiyah.
Inta gaji da kwanciyar ta mike tai tasbihi da hailala.
*******
Gaba daya shi kadai ne a cikin tangamemen kilisarsa yana zaune a lungu hankalinsa a tashe.
Jakadiya ce ta sake shigowa tace "Takawa ana jiranka a fada."
Abdulsalam ya kalleta hankalinsa a tashe, sannan yace "to."
Da kyar ya daure hadimansa suka shigo suka tayashi shiryawa.
Junaid yana zaune falan Binta amma gaba daya hankalinsa nakan Azi akan ya dawo ya sanar dashi ko Sarki ya shiga fada.
Binta ce ta fito daga daki ta kalleshi tace "Yaya!"
Kallanta yai yace "zuwan zakiyi?"
Tace "tunda kai bazaka ba gwara ni naje, dan Allah yaya kazo muje Allah Umma batada lfy."
Yanda ya kalleta tasan bazashi ba, fuska ta hade tace "shikenan."
Ta fita, murmushi yai tare da kara jiran Azi.
Binta ko minti biyar da fita batai ba Azi ya dawo.
Junaid na ganinshi ya mike yace "ya?"
Azi yace ya fito daga sashensa.
Nan Junaid yace muje.
Tare suka fito hadiman sa suka bi bayansa suna tafe ya kalla Azi yace "Zeena fa? Tabi Hajjon?"
Yace "a'a tana bangarenta."
Su Waziri fa?
Sun iso yarima.
Junaid ya jinjina kai sannan yace "Zubair fa?"
Haddashi?
Junaid yadan kalleshi kadan yace "haddashi."
Nan Azi ya amsa aike sannan ya juya.
Junaid fada ya wuce daga nan kai tsaye.
A fada kuwa Sarki na zaune bayan ya amsa gaisuwa ne, kallan Waziri yai wanda kansa ke kasa, ya kalli Shamaki shima kansa na kasa, ya kuma kalli Galadima.
Daurewa yai yace "banyi tsammanin taran gaggawa haka ba, Allah yasa komai dai lafiya."
Turaki cikin mamaki yace "Ranka ya dade ai mu sako aka iso mana dashi akan kana neman nemanmu a fada."
Nan kowa ya amsa da hakan ne, Sarki yai shiru kenan Junaid ne? Uban me yake nema dashi?
Zagi ne ya sanar da isowar Wakilan da aka turo, Sarki ya basu izini cikin dakewa, duk da yanda gabansa ke faduwa.
Suna shigowa Zagi ya sanar da isowar Junaid.
Ba Sarki ba hatta su Waziri sai da gabansu ya fadi.
Junaid ne ya shigo cikin isa da takamarsa, ya gaida sarki sannan ya zauna.
Wakilai suka kalli Junaid sannan suka kalli Sarki, wakilin sarkin kano ne yace "wannan sako ne daga mai martaba sarkin Kano, tabbas yana kara jinjina maka yace mu tafin masa da ranar yin nadin shi da kansa zaizo."
Sarkin Zazzau ma abu daya ya fada, ajiye kayan kyautar da suka kawoma Junaid sukai sannan suka gaisheshi.
Gaba daya Abdulsalam ya kara rikicewa kafafunsa kawai yake matsewa ta cikin kayansa.
Junaid ya amsa tare da yin godiya, sai da suka fita, Turaki yace "ai Sarki wannan lamari kowa yana bashi mamaki, duk da muma ba san murabus dinka muke ba amma in muka tuna namijin kokarin dakai gun yanke wannan hukunci sai musan bakuda bakin magana."
Nan kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa, Abdulsalam ji yake kamar ya saki wani ihu a gun da yake.
Junaid ne ya kalleshi cikin mamaki yace "Takawa ina tafe ina fatan Allah yasa ba abinda kake shirin fada yasa ka taramu ba?"
Abdulsalam ya kalleshi me yake shirin yi?
Zubair ne ya shigo ya zauna, Turaki yace "Mai Martaba badai....?"
Sai yai shiru suna kallan Juna.
Wale yace "Takawa bai kamata ayi abu cikin gaggawa ba."
Junaid yace "sosai ma kuwa, komai ayishi a hankali, dan Allah ka janye alkawarin nan naka na yau zaka ajiye mulkin nan."
Bai san sanda ya bude baki ba, Waziri cikin tsoron Junaid ya kalli Sarki anya wannan zai barsu suma kuwa?
Turaki yace "au yau? Indai Alkawari yai ba yanda zamuyi."
Junaid ya kalli Abdulsalam sannan ya kalli Zubair wanda ya kumbura fam.
Abdulsalam idanunsa ne suka canza kala, ya daure ya kallesu yanzu kam yasan bashida wata mafita, inba so yake komai ya fito ba, an gama daureshi ta ko ina.
Wale ne yace "da alama Sarki sauri yake ya baka mulki a matsayinka na sirikinsa kuma dansa, yafisan yai jika yana gefe."
Dariya sukai dukansu wanda dariyar ta kasance kamar arsashi ne ya dira a zuciyarsa.
Zubair ya kalla wanda ya gama bata rai, Junaid ya kalla wanda ya kalleshi shima.
Mamaki me ya kamashi dayaji yace "to Mai Martaba."
Kafin ya fara tunanin me zaiyi kawai yaga ya taso yazo inda yake ya tsuguna, ya dukufo kusa da kunnensa.
Yace "idan har baka sauka ba a wannan lokacin yanzu kuma, duk abinda ya biyo baya a wannan lokacin karkaga laifin kowa sai naka, ga danka ga fadawan ka nan, kowa yaga mumunan halinka da kake boyewa a cikin fara'arka, sannan kar ka manta ina da shaidar laifukanka, kana batamin rai komai xai tarwatse a gun nan."
Murmushi yai bayan ya dago ya daga kai alamar to sannan ya juya ya zauna.
Waziri dasu Shamaki ba shakka tsananin tsoron Junaid ya gama kamasu.
Sarki ya daure yai gyaran murya, da kyar ya samu ya daidaita muryar sa dake rawa yace "abu dai da kukaji haka yake, ina faran zaku bani hadin kai, nima na samu na huta, dama can asalin mulkin nan na shi ne, na rikemai ne saboda mahaifinsa ne wato yayana ya sani, sai dai yanzu Junaid ya girma yayi aure, na tabbatar ku kanku yanzu kunsan Junaid ya cancanci kujerarsa."
Zubair kara habaka yai, cikin bacin rai matuka.
Sukam yan fada kowa ya gamsu da maganar Abdulsalam.
Yau zan ajiye mulkin nan, a wannan lokacin ina fatan xaku ba shi hadin kai, na tabbatar xai yi abinda ni da mahaifinsa bamuyi ba."
Wale yai dan murmushi yace "tabbas Takawa samun irinka a duniya sai an tona."
Junaid ya rusuna sosai yace "Ina godiya Takawa, na gode daka zabeni sama da jininka, wannan hallarci naka tabbas abin dubawa ne."
Kallan Shamaki yai yace "a dako sandar mulki a da kamai, inyaso ragowar abin Sarauta sai ranar da za'ai nadin sai a bashi."
Nan Shamaki ya juya ya fita, Waziri ya kalli Sarki wanda yasan Allah ne kadai yasan halin da yake ciki a wannan lokacin.
********
Haka Binta ta zauna sai dataga Azeema taci abinci sosai, sannan sukafara hira sama sama duk da rabin hira Binta ce ke bata labarin tasowarsu da abubuwan daya faru a shekarun.
Azeema nata murmushin jin dadi tare da kunyar abinda ta aikata.
*********
Hajjo dake zauna cikin bacin rai ta kalli Ramlatu tace "ya kike ganin zanyi in kamo yarinyarcan?"
Ramlatu tace "ai Gimbiya ce in ta dage a abu ba mai hanata."
Hajjo a kufule tace "duk ni na barta haka yanzu ga abinda take neman jawomin ai."
Sanar da isowar Jakadiya da akai ne yasa Hajjo cikin mamaki ta kalli kofa.
Jakadiya cikin haki da alama gudu tai ta shigo ta zube a gabanta tace "Hajjo Hajjo."
Hajjo ta kalleta rai a bace tace "meye kuma?"
Jakadiya tace "Sarki ya ajiye mulkinsa."
Mene? Ta tambaya cikin rashin fahimta.
Jakadiya tace "an dako sandar mulki yanzu an shiga da ita fada, bansan meke faruwa ba."
Hajjo tace "yauwa Abdulsalam gwara kaga Zubair mulkin kafin wacen mara mutuncin ya aikata mana tsiya, ashe shi yasa aka kira Zubair dazu?"
Cikin wata dariyar farin ciki ta tambayi Ramlatu.
Dariya sosai Hajjo take cikin jin dadi tana jin jina kai, Ramlatu sai kara wasa mata kai take.
🙊tab😝
****
Ayusher🏌🏻♀️
*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*
{47}
Hajjo cikin tsananin murna ta mike ta fito daga sasshenta Ramlatu na bi mata baya cikin tsananin farin ciki.
Daga dan nesa kadan taga kamar Zeena da tata tawagar, baki ta tabe tace "naga bakin ki yanzu mai zaice."
Hajjo tai gaba ba tare da ta kara ko kallan Zeena ba, Zeena wacce yanzu taji abinda ke faruwa ta taso dan san ganin Hajjo da halin da take ciki ta tsaya daga inda take, fuskarta dauke da mamaki, dan bata taba tunanin ganin Hajjo haka ba.
Kallan Fure tai tace "da alama Hajjo lafiyanta kalau, mu koma tun kafin wani abu ya faru muna waje."
Nan Fure ta amsa dato, haka suka juya Zeenatu na tafe da tsananin mamakin abubuwa biyu, na farko murabus din da gaba daya bata taba tunani ba, sannan da ganin Hajjo hankali a kwance.
Hajjo tana tsakiyar masarauta inda tafiya kadan ne zai hadasu da Fada sukaji masu kirari da busa sun fara, sam duk yanda masu kirari Ke magana bataji saboda tsabar zumudi.
Ramlatu wacce yanzu kunnanta sukaji Junaid akema kirarin, yasa a tsorace ta matso kusa da Hajjo.
Hajjo ta tsaya ganin yanda tadan tare gefen tafiyarta kadan.
Hajjo tace "ya akai?"
Ramlatu a tsorace tace "Hajjo ina tunanin mu koma daga nan."
Mu koma ina? Ai dole muje godiya, Ramlatu a tsorace take kallanta sannan tace "tuba nake Hajjo amma dakin danji me masu kirarin nan suke cewa."
Kallan banza ta mata sannan tace "ina nake da lokacin jin wannan shirman, me suke cewa?"
Ramlatu dai tai shiru kafin tace "mu koma mu kira Yarima Zubair din yazo da kansa."
Hajjo tai shiru kafin tace "bai kamata muje godiyar ba?"
Ramlatu tace "eh gwara mu jirashi."
Shiru tai kafin tace "to."
Juyawa tai suka koma, fuskarnan tata wasai da farinciki, kallan hanya tai tace "waccen yar rainin hankalin ta juya ne?"
Ramlatu da batama jita ba tana tunanin yanda zata zame ta gudu, Hajjo ta kalleta tace "me kike tunani?"
Ramlatu tace "inaji tsabar murna ce tasa kaina ciwo ina tunanin komawa bangarena kafin Yariman ya dawo."
Hajjo tace "shikenan."
Nan tai wuf ta gudu da hadimanta, Hajjo tana tafe tana farin ciki, daga sama sama taji kamar sun kira Junaid, sai kuma taji Zubair.
Baki ta tabe tace "wato yayan Junaid? Ni da sunbi ta tawa ko sunanansa basa kiraba."
Tasa kafa zata shiga bangarenta taga Hadimanta ragowar data bari sun hada kai suna magana, suna ganinta sukai shiru.
Wucewa ciki tai ta zauna.
Batafi minti goma da zama ba sai ka bawan Zubair wanda yafi kusanci dashi ya nemi izini ya shigo.
Hajjo cikin zumudi tace "Aram ya akai? Ina Ranka ya dade din?"
Kallanta yai yace "Hajjo! ki taimaka ki aika a kira Yarima kafin wani abu ya sameshi."
Me zai sameshi? Ta tambaya cikin mamaki.
Aram yace "Hajjo gaba daya ba wanda yake bi takan Yarima murna kawai suke taya Junaid ba wands ya damu da halin da yake ciki, gashi ba damar ya taso kar a dauka bakin ciki yake."
Bakin ciki? Ta tambaya hankali a tashe.
Yace "bakiji Sarki ya ba Junaid mulkin na?"
A zabure ta mike tsaye tace "yaba Yarima me?"
Aram yace "yanzu kam ai kowa yasan abinda ke faruwa, tunda gashi anata busa ana kirarin ana sanarwa."
Gaba daya hankalinta ne ya tashi tace "inji wa? Inki ubanwa yace ya isa ya ba Junaid mulki ba Zubair ba?"
Hajjo gaba daya ta rikice hankalinta a tashe take magana........
*****
Zeena sai sintiri take a sashenta kafin ta kalli Fure tace "hankalina ya kasa kwanciya Fure dubomin Binta."
Nan Fure tai waje, bata dade ba ta dawo tace "tana bangaren Gimbiya Azeema."
Zeena tace "tashi muje gun