Showing 135001 words to 136333 words out of 136333 words
Kai dan Zafi ne,Allah Yana kallonka cutata da kayi,Dariya ta kama Nabeel ita Hidaya sai da aka yi abin bakinta ya bude take ya cakaki ba ji ba gani,dama mugunta Goggo ta shirya min sabo da basa kaunata Naila suke,shi yasa suka turoka kazo da Baba Ibejinkaaaa....sai kuka ihun bayan hari sai da aka gama take kuka,Nabeel dariya duk ta kama shi da kyar yake danne ta.
Iman kuwa yau yini tayi a wahala bata San an Kai Amaryar Nabeel bama tana faman jinya,dare nayi Kuma Annoor yace bazai iya hakura ba shi mutuwa zaiyi sai ya Kara yi,suka dinga daru da fada,ta kira Umma Habiba a waya tana kuka tace Annoor ne zai kashe ni Dan Allah kuzo ku taimaka min,Habiba tana ji tace ya mikawa Annoor wayar,ya karba ya fita a hayyacinsa ma,Habiba tana ta Masa fada Kai Annoor ba haka ake ba fa,hakuri akeyi sai taji sauki ta warke kayi hakuri kaji,to kawai yake iya furtawa,suna gama wayar yace da Iman ni nace ki sa min magani? Iman Baki na rawa tace ai ai ai...ni taimakonka nayi ban San abin haka yake ba,nufarta yayi ta mike da ihu wayyo...tayi tsalle gefe ga ko Ina ya kulle,Iman tayi rokon tayi magiya tayi kukan amma Annoor bai ji bai gani,sai da ya sake yi,Kuma ya Dade bai kawo ba,a haka ma kokari yayi ya kawo wai,Iman ta mike taza bude kofa ta gudu yace wlh ba Inda zakije Nan yini Nan kwana,tace ba sai ka kashe ni ka huta ba,dariya yayi cikin nishadi yace I'm sorry wlh bazan iya hakura ba ni anjima ma zan iya Kari muje na gasaki na miki Allura ki samu relief kafin asuba.
Iman zubewa tayi a kasa tana birgima tana kururuwar neman agaji,gogan kuwa a wani nutse yake ko a jikinsa,waya ta sake dauka ta kira Kawu tana rusa kuka,sai da Kawu ya tsorata ta fada Masa tace Kawu ya kulleni a daki wlh ba fita ba shiga sai Abu daya yake zai kasheni,maganin nan na Abban su Hidaya na bashi wlh ban San Yana yi ba,Kawu yace ke Dan ubanki wanne karanbani ne ya kaiki,Iman tace Dan Allah a kawo min agaji ko da ambulance a taho Kawu kwana na zai kare.
Kawu yaji tsoro ya taho a tamanin shi da Amaryarsa,tun daga Palo suke Jin kukan Iman,shi kuwa Yana gefen bed Yana latsa wayarsa cikin nutsuwa Yana Jin dadin duniya,shi bai taba Jin dadin duniya ba sai yau.
Knocking aka yi a kofar yace waye? ubanka ne cewar Maman Annoor,baza ka bude kofar ba,yace to yanzu mutum da Iyalinsa sai a dinga Masa katsalandan,Jauro da lallashi yace Annoor bude kaji nawan,Annoor yace ni gaskiya ba a yi min adalci tun yaushe nayi aure Kuma daga na samu lafiya shike nan sai a sani a gaba,Kawu yace wannan ma ai lalura ce Annoor ka bari a samo Maka magani,yace ni nafi so na a haka a barni a haka,to bude kofar a samu a kular Maka da Iman din,da kyar ya bude Iman ta fice da sauri jiki na rawa tana dingishi,tace ku tafi dani wlh kuka barni shike nan sai gawata,Iman Jauro ya kalla duk ta firgice kamar mahaukaciya,a mota suka sata suka tafi da ita,Annoor yace wlh za a San an tafi min da mata,kuje ba Inda zanje zan gani waye da power.
Ni dama tunda Mama ta shugo mana dangi ta auri Kawu nasan ta dinga takura min kenan.
Maman Annoor dai gidanta ta wuce da Iman,Iman a mota tace Kai Tausayinsa nake ji gaskiya a Maida ni in da kwana na a gaba na tashi,Dan Allah ku Maida ni,Jauro Ido ya zaro waje yace a Maida ke? Iman tace ni gaskiya a Maida ni Tausayinsa nake ji yayi min Allura,Jauro yayi reverse ba tare da yace komai ba,Maman Annoor zata yi magana yace rabu da su a maidata,ai dai tace a maidata to a kaita Allah ya tsare,Iman tace Likita ne ya min Allura dama Yana yi min,Jauro af ai an gama kwantar da hankalinki Iman ai munyi shishigi,Iman ba kunya tace ei dama cewa nayi ai a gidan a iya gidan za a taimaka min ba a tafi dani ba,Jauro yace madallaaaaa....ya Maida Iman har gidan Annoor ya fito yace muje na rakaki Inda na dakko ki tace to,suka tafi da Jauro,tsabar takaici Maman Annoor bata fito a mota ba.
Har bedroom suka shiga,Jauro yaga Annoor a zaune yayi tagumi yace ga matarka tace a dawo da ita tausayinka take ji,Likita ne Kai kana da Allura a gafarce mu,Jauro ya juya ya fice yace ka sa key dinka,Annoor murmushi yayi ya rungume Iman,tace kaga dai tausayinka naji nima ka tausaya min yace ya zama dole tawan,da na kulla tsiya da Kinga tashin hankali da kin zauna,Iman tace a'a bazan zauna bama muyi wanka kayi min Allura na samu sauki.
Kawu Yana driving yace yau naji kunyar da ban taba ji ba,daga yau ban sake wannan shishigi shi yasa Hashimu ya fada min yace ko an kawo Kara a irin wannan nayi kamar banji ba naki ji gashi naji kunya.
Maman Annoor tace amma da ta hakura an gyarata taji sauki shi Kuma an samu makarin maganin tunda akwai,Jauro yace tace Yana da Allura fa rabu da su.
GIDAN YARI
Khadija wacce aka fi sani da Mero da gudu ta fito daga wani daki wuf ta afka wani dakin na kusa da Wanda ta fito a ciki,tana shiga ta dauki wani karfenta dogo me nauyi da kauri kamar Yar sanda,Wanda a gidan yarin ta tsinci abinta
Tana zuwa ta samu Jikin bango daidai wata kusurwar dakin Inda wajen yake a tsage taci gaba cusa Karfenta tana dukan wajen tana bulawa lallai sai tayi kofa,tana ta marmaso kasar gini tana ta fama kamar wata yajuju wa majuju tana ta aikin fasa gini,Matashin Dake cikin dakin ta baya Yana kwance Yana baccinsa yaji abinda aka Saba yi kullum ta bayan dakinsa dake VIP, tashi yayi zaune Yana tsaki.
Dan bakinsa karami ya bude yace waye? Mero tana jinsa tace nice kawarka,yace kawar ubanwa? taka ta bashi amsa,ransa ya baci,kyakyawan matashi ne na gaske fari ne amma ba fari karr ba sai Dan Karen kyau,Kana ganinsa kasan bai saba da wahala ba,gashinsa me yawa ya shafa ya dauki wayarsa me tsada dake ringing,yace hello...Abbu...gobara...ta cinye gidan du?...Muryar Mero yaji tace amma dai bata ci mutum ba ko? shareta yayi yaci gaba da wayarsa yace Subhannallah duka yanzu gidanmu ya Kone Abbu? Mero ce ta fashe da kuka daga baya tace shike nan gidan surukaina ya Kone munyi gobara,ta daina bula ginin ta fito tana kuka bilhakki da gaskiya,kowa ya tare Mero me ya faru? gidan su saurayina nane ya Kone gobara aka yi mana,sun zaci gobarar ma da gaske a gidansu aka yi ta.
Mutane suka cika dakin su Mero ana ta zuwar mata jaje,Mata sai tururuwa suke yi,Khadija Ashe haka aka yi muku gobara,tace wallahi abin ba kyau gida hadadde an ware min part dina guda za a kaini can in anyi aure amma ba rabo ya Kone yanzu sai an gina wani,labari ya cika ko Ina anyiwa Khadija gobara a gidan aurenta,Dake tayi mugun suna shi yasa kowa yaji labari,shi Kuma matashin da aka yiwa gobarar ma ba Wanda ya fadawa to bama ya kula kowa a gidan,dama dama ma su Malam Jilani Yana zuwa wajen su.
Mero tsabar jaraba har su Skola sun Santa su Goje sabo da tsayawa take a Jikin katangar Maza tayi ta surutu tana basu labari,idan Allah ya kawo wani zai wuce yaji kadan, da tunanin su Goje ma Aljana ce a wajen take fitowa tunda basa ganin kowa sai dai suji maganganu" Kuma sabo da tsayin katangar da kaurinta bama a Jin me mutum ke fada sai anyi da gaske.
End of book 2
Mu hadu a book 3
Babu hutu Kuma sabo da anyi tsaye tsaye sosai
AsmaBaffa