Showing 99001 words to 102000 words out of 136333 words

Chapter 34 - TANTIRIYA A GIDAN YARI BOOK2 By asma baffa

08 Jul 2024

9536

biya gidan Spark yaci kaniyarsa.







AsmaBaffa
[1/27, 10:32 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI

BOOK 2
~YARAN JAURO~

76-80

Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM

PAGE NAKI NE
Maman Murtala




Mima sai da suka shirya tsaf ba motar shiga a gidan kaf tace yanzu taxi dole zamu shiga sabo da idan nace lallai mota zan Nemo asirinmu zai tonu,fita suka yi suka shiga taxi zuwa gidan Rafeeq,suna zuwa suka ji kida ta window palon suka leka suka hango Malama Ikhram da Ango Rafeeq suna ta Yar rawar su irin ta turawa cike da nishadi,Mima bakin ciki yazo mata wuya tace wai me siyar da maganin gargajiya na mata Allah ya sawwake ta Murda kofar Tare da banko ta ciki,Rafeeq ya juyo ya gansu yace lafiya? Mima ta fisgo Hannun Ikhram tace yau sai kin tafi gidan ubanki ne?,Ikhram Jikin Mima ta fada sannu da zuwa Miman mu, Mima ta fara banbareta daga jikinta amma taki sakin Mima,Rafeeq yace Allah sarki kaunar surukai ta motsa,Mima ta ture Ikhram ta karfin gaske tana zage zage,su Anan sun tsaya suna mata wani Shekeke,Mufee tace aikin banza anzo cin arziki,Ikhram tace sannunku masu arziki Ina abin yake idan aka yi comparing da kudin wani ai talakawa zaku tashi,Ke ki kiyayeni na fiki iskanci wlh ni bazan dauki raini ba,ba wacce ta isa ta takani,mahaifiya dai zan iya mata biyayya amma ba ku ba,ai ko yayyensa ne baku isa ba,masu takama da kudin Uba sai ku bari ku nemi naku tukun,wannan jahilci ne da hauka da kauyenci ko ince gidadanci menene Hakan?

Mima tace to fitsarriya wato ke kunyar Amaryar ma babu,Ikhram tace Ina na ganta dama Banda ita Baku ga irin wa'azin da nake bane ai Kinsan kunya babu,wai Nan kunya kuke nema a wajena Allah sarki ai ban San Inda take ba Dan ni ban taba haduwa da ita ba, Ikhram tana magana tana fari tana jujjuya idanu kamar ta Sha kwaya,Rafeeq shi Kam ya mato sai kallonta yake kamar ya samu tv, Anam tace bari na dakko mana lemo, Ikhram tace Baki isa ba ko kitchen dinki ne ,zata wuce ta fisgota baya,Haly ta taso zata mareta Ikhram tace Inama Allah yasa kin mareni yau Kisha kallon yanda ake Hawa bori da tsakar rana,da na nuna miki baki da hankali.

Dai dai nake da kowa ni ke nifa Aljani ma da zan ganshi in ya zageni sai na rama wlh,ni kizo Ina auren Yayanki kice zaki mareni ai kuwa da anyi ta yau,Mima tace kuzo mu tafi ,Taga masifar Ikhram kamar baza ta kare ba, Yar gidan waye ke sai na binciko tsatson ki cewar Mima,Ikhram bata yi magana ba sabon da ai uwar miji ce,zadai ta kula yaran, ta zauna albarkacin Rafeeq baza ta kulata ba uwa ai uwa ce,Rafeeq yace Mima Ina zaku je ne haka?Mima kamar tayi kuka suka dai fice suka tafi gidan Misam sabo da bankada,lokacin Chika ce kawai taji ana kwankwasa kofa,lekawa tayi ta Yar kafa Taga sune kawai tayi wucewarta taki budewa bugawar duniya taki budewa,sai tace Ina zuwa sai suji shuru,suka sake bugawa tana Jikin kofar tace Ina zuwa amma shuru kake ji sun San Kuma suna gida,Mima tace muje kawai haka suka juya suka tafi gidan Spark, Yana kwance yayi pillow da cinyar Naila tana karanta Masa Abu a waya Mima suka banko kofa ba sallama bare kwankwasawa.

Yace sai kace yaki ai Kun bani tsoro Mima bai kamata ki biyewa yara ba da girmanki,kaga karka dameni,Mima zama tayi tace gaya min tsakanin ka da Allah Spark Ina Papan ku? Spark yace tunda kince tsakani da Allah bari na fada miki,Naila tashi tayi ta durkusa tace Ina yini,Mima a lokacin tasan Naila ba karamar me ladabi bace, amsawa tayi da sakin fuska,lemo ta kawo musu da ruwa,sannan ta basu waje,Spark yace Papa yana Gaza kasa ta turasu su taimakawa Palestinian,Hannaye Mima ta dora a Kai tace shike nan kace sun tura su a kashe su,wacce kasa za a biyewa wannan kasar har wata kasar arziki ce da zata tura mutum Abu kuma ya tafi yayi,Arham ne ya fito daga kitchen ashe da yace a basar aci tuwo Nan ya gudo yake ta girke girkensa,Mima tace yaushe ka riga mu barin gidan? Arham yayi murmushi yace tuwo ne kawai naji dadinsa shi yasa Inda kisan na shiga jirgi.

Mima tace banza taci gaba da magana da Spark tace yanzu ba wata hanya da zai dawo ni wlh gwara ya bar aikin Nan,Amma kuka bar mu muka saki baki muna bacci hankali kwance bayan mahaifinku Yana can cikin wani hali,gaba daya Mima ta tashi hankalinta,Spark yace yanzu me kuke so a kawo muku na abincin? Mima tace Kai dalla yi min shuru wa yake ta abinci mijina Yana tsaka me wuya,ni dai duniyar ta min zafi gaba daya,Arham tashi yayi ya karo karfin AC yace yanzu dai dole kiji sanyin duniya,Mima tashi tayi tace Dan ubanka wai ni sa'arka ce? Ko kakarka ce ni,ta rike Arham tare da mamake Masa Kai,Arham Yana dariya yace kar dai Kiga Ina kama da Papa ki zaci shine ki bari ya dawo sai kuyi soyayyar ku.

Naila tana fitowa Taga duk sun shanye lemon akan kwana biyu kawai da basu samu me dadi ba,kitchen ta shiga tana dariya tace bari nayi tsokana ta fito tace ko a kawo muku tea? Haly tace da Madara Dan Allah,taje ta hado musu lafiyayyen tea kowacce ta kawo mata a katon cup har Mummy,Anam tace bread Dan Allah,taje ta kawo musu tace ko a soya muku kwai da chips? da sauri suka ce ei,Spark yace ba sunci tuwon su ba a gida Yana hararar Naila,Naila Bata San horo ake musu ba,taje duk ta soyo ta kawo,Mima tace Allah sarki ta Rafeeq kuwa da ta dinga bala'i tafi 30mnt sai kace me aljanu,Haly tace ni na taba ganin jaraba irin wannan daga magana,Anam tace gwara ita sai da muka tsokaneta waccen marar mutuncin wlh kin budewa tayi ma Sam,Spark Yana jinsu yace ato in baku gode Ni'imar Allah ba ai Kwa gode Azabarsa.

Suna zaune gidan Naila kamar kar su tafi dadi ko Ina Kal Kal Yana kamshi ga girke girke sai kawo musu take,minti kadan ta kawo wani abin,Arham Yana ta dariya yace sabo da rashin hakuri wai kwana biyu kawai shine suka koma kamar mayu,Mima har dare tana Jimamin mijinta hankalinta a tashe,Spark ya kwanta a doguwar kujera ya kira Naila dake kitchen Baby....na'am ta amsa zo ki min tausa,Mima tace kaifa Dan iska ne a gaban namu ga kannenka,yace matata ce fa Mima ba Karuwa na kawo ba,nifa babu me zuwa ya takura min a gidana in baza ku iya Gani ba ku tashi,yanzu Spark gobe ma tuwo yara zasu ci? Spark yace ku jika gero ku Kai markade mana ayi musu Koko,Mima tace Koko fa? Yace to za a siyo wake sai ku dinga hadawa da kosai,Wannan madarar da sugar da ka kawo ai sunyi kadan Kuma bama Shan Madara Yar awo,Mima da ita fa ake Albishir da alawar Madara mudai muna so cewar Arham,Mima tace kaga Arham idan Ina magana kana sa min Baki kana bani amsa sai na taka maka wuya wlh,yace sai kace zakara za a yanka,Mikewa Mima tayi tace bar nan wajen ko na hada kanka da bango.

Mima tace ku tashi mu tafi,Spark yace ku tsaya driver ya kaiku,Mima taji Haushi gidansa kayan dadi su yaki siya musu tace bar mu ai taxi muka shugo mu koma a ciki,yace to ku gaida da gida,Arham yace Nidai a dinga girki Dani a nan dan Allah yau Ina gidan nan gobe kwanona na gidan Rafeeq jibi kwano na Yana gidan Misam.

Spark yace kowa yaci na gidansu,Banda gidana idan hakane to sai dai ka dauki gida daya ka dinga zuwa kana ci,ni nan banda gidana nifa babu me takura min Ina so in sake a dinga kallona,Arham yace kuyi kiss dinku da rungumemeniyar ku bazan kalle ku ba,ai gwara na baka kudin Abinci kullum kaje ka siya,yace yawwa tura min,plate biyu kullum nawa,yace to Hakan ma yayi.
Sai da ya bar gidan yaje gidan Rafeeq,Rafeeq Yana zaune Ikhram tana Saman cinyarsa ya shugo taki tashi Kuma,Arham yace ana ta Shan chaji ne? Rafeeq ya mika Masa hannu suka gaisa yace dan Allah ya kaji dumi da muka gaisa?,Arham yana dariya yace a naji zafi zauu,Rafeeq ya nuna kan Ikhram da yatsa wacce tace Arham barka da zuwa yace yawwa,Mikewa zata yi Rafeeq ya rike ta,tana shagwaba tace pls...,sakinta yayi ta tashi tare da wucewa kitchen,Arham ya leka Rafeeq yace mu gani Hallare tana aiki,Dariya Rafeeq yayi harda wani bajewa zaman ma ya wani bubbuda kafa ya kwanta tare da nutsewa a cikin kujera,ga Hallare a mike ko a jikinsa,Arham yace nan zaman angwaye ne haka? Rafeeq ba tare da yayi magana yace hutawa na barta tana yi na bata wahala Kai shege ne ni,na bata kuka ranar da Sai ga sabon Ladabi da sanyin Safiya,yanzu ko fuska na bata sai anji dalilin fushina,Wayyo Ina ganin gata,Arham yace uhm Allah ya baku ku Kuwa,Rafeeq yace sanda Ina Gwauro da ruwan Sanyi nake wanka yanzu kuwa tace ban isa ba ta hana,Arham yace ka yarda Kuma yace wane ubana ba dole ba.

Arham yace hmm ni ba macen da ta isa ta sani ko ta hanani,Rafeeq yace tab ni kuwa gani,girki Dan ubanka a jera min hadaddun flask ana ci mana,Ina sani nace na koshi,a dinga lallabani Kaci pls My Heart,ba sai naji Kuma na koma shagwababbe ba ahh sai shagwaba ana Lilita ni,Arham Yana ta dariya yace yanzu duk a 2days aka yi haka? Ana amarci da wasa ne Malam babu lokacin banza a amarci every single minute,second a ciki Jin dadi ake tunda mun gaisa tashi kafin Dan Allah,Ikhram ce ta fito dauke da abinci tace Ango na biyu....mene ne haka? Waye Ango na biyu nine na farko nine na biyu kar na sake ji Bada ni ba wasan kanin miji a gidana Ina wlh ban so,tsakani da Allah ya fada,tace to kayi hakuri bazan a sake ba,farin ciki ya kama Rafeeq yace Kai Malama ce wannan ta gasken ni gani har tsoron fushina akeyi yi.
Arham bai dade ba ya tafi gida yace gobe Kuma sai naje gidan Misam na Gani.

Washe gari Spark Kano ya wuce Gidan yari akan maganar fidda Mero,Ma'aikan ya samu har Office din Ogan suka Masa Iso,bayan ya shiga ya zauna suka gaisa Sosai,ya Masa magana akan Mero da duk abinda Mummy tayi mata,yace me sauki ne wannan amma baza mu fitar da ita ba yanzu dole sai an Kai kotu idan kotu ta saurari komai za mu shigo da ita Mummy dinka sannan a fitar da Mero,yace ni yanzu bazan iya Kai uwata Kara kotu ba gaskiya,yace ai dama ba Kai zaka yi ba,Inda Mummy ta Bada cin hanci suka kawo Mero nan su zasu dawo su tura su kotu dama abinda ya kamata sunyi kenan suka karbi kudi,sai kayi hakuri dole haka zaka jajirce amma wani taimako da zanyi ni zan kaiwa kotu case din ya koma can sai su kaiwa Mummy takadar sammaci shike nan,Spark yace na gode ya bashi kudi ya fito.

Yana fitowa ya tambayi na bangaren ziyara ya kwatanta musu Mero suka ce gaskiya su basu San wata Mero ba sai dai Khadija wacce yake tambaya,Spark bai San ta da Khadija ba yace a kira min ita na ganta ko itace,ba ranar ziyara bace amma sabo da kudi da gudu suka Nemo Khadija,tana ciki Allah sarki Mero duk tayi duhu ta lalace sabo da Bata da gata,Fitowa tayi Taga Spark Mero ta washe Dan karamin bakinta tace Ina Kwana,Kallonta Spark yayi ta bashi tausayi shi da ya San Mero Yar dumimi da ita me haske, da sakin fuska ya amsa yace ya ciki din? Mero ta fara dariya tace da dadi,yace da dadi naga kin rame,Mero tace abinda yasa tunani nake da dare ban San matsayi na ba a gidan nan ba,ba fa a yanke min hukunci ba, duk zaman da nake a banza nake yinsa,shine ya dameni,amma komai Ina ci ni,ga Ummata son kudi ya mata yawa sau Daya fa suka zo min wai kudin mota tsada Kuma fa a Kano ne Dan kawai suna kauye,Baffa na Kuma Umma ta mallake shi sai abinda taga dama tsoronta yake ji,Spark yace Allah ya kyauta,tace Ameen Ina matarka? Spark an tambayi Naila harda sosa Kai yace tana Nan lafiya,yanzu me kike bukata? Mero tace a yanke min hukunci kawai shi ya dameni,ni wahalar rayuwa bata dameni ba ko wacce iri ce na Saba da ita zan jure,yace to ki daina tunani za'a fitar Dake kwana nan Inshaallah,Mero tace a jinkirta Dan Allah ba yanzu ba,yace sabo da me uban me kike yi a ciki? Mero tace wani ne nake ganinsa a TikTok sanda Ina gida,kawai sai na ganshi a nan,dariya ta ba Spark yace idan ba shine ba fa? Mero tace shine ma,to ta ya zaki hadu da shi Yana bangaren maza ke kina bangaren mata? Mero tace tab baka san tsiyar da nake hadawa bane a gidan nan,amma bari saura kadan,Spark yace to yanzu sai yaushe zaki gama? Mero tace wata Daya,kyale Mummy Kaci gaba da ganin abarka ni na gano arzikina a nan,Spark Yana jinjina shiriritar Mero yace to kudi zan baki ko me kike so a kawo miki? Mero tace bani kudin kayi tafiyarka zan ji da kaina,Spark ya bude mata asusu a cikin ya sa mata 50k yace gashi nan ki dinga karba,idan baki fito ba sun kare zan tura wasu ga number dina na bawa ma'aikata in kina bukatar wani abu ki kira,Mero tace na gode Allah ya Kara budi,suka rabu ta koma ciki ya sallami ma'aikatan da kyautar kudi ya wuce abinsa.

Hanan gajiya tayi da zaman gidan miji take nema Ido rufe wai so take yi tayi auren kisan wuta ta fito ta koma gidan Mohsin,wani Dan babban mutum kawarta ta fada mata tace wani Dolo Dolo ne ta aure shi kawai tana tarewa sati daya ta Masa tijara dole ya saketa,aurensa uku duk baya dace fita suke yi kuma ko wacce tace tana sonsa sai ya gode miki Kuma ya aureki,in kika ce sakeni sai ya dankara miki saki yace ai itace tace na sake ta,idan kika je kika ce Hamza aureni sai yace to, Kuma wlh sai ya aure ki,Yana samun kudi Kuma a kasuwa yake shagon wani,Allah ya Masa baiwa duk abinda ya taba sai an samu kudi,Hanan tace kice Lubna wannan ai yayi wlh,tace Kuma zai Kai 40yrs Kuma gashi da tsabta da gayu ke baza kice Dolo bane,Ki samu kiyi gyaran jiki,Hanan tace ai na siyo supplements dina gasu Nan dana kiba da na haske ai fasowa zanyi gari kwana nan,yawwa idan kika yi kyau sosai dama ke ba mummuna ba har gidansu zan Kaiki,bashi da iyaye sai kakarsa kawai a gidan itama Kuma bangarenta daban,tafawa suka yi tace to sai na kiraki a waya,kina zuwa kice Hamza dama sonka nake aure ni,zai aureki.

Kakan Naila ne yazo Kano gidan yarsa Yar Inna,Abba suruki yazo sai zumudi akeyi,har kasa ya durkusa ya gaida shi,yace Affa an zo lafiya yace lafiya Alhmdllh,Abba yace lallai kamatuddini tudan haka Nima surukaina suke durkusa min su gaishe ni,sai yanzu na tabbatar da bin na gaba bin Allah da bana yi Maka waye zai min nima,Affa ya Kalli Hashimu kawai yace Hashimu ya yaran? Suna Nan lafiya kalau,ya wajen su Naila? Sumul suke dazu ma ta kirani,itama Hidaya tayi miji Inshaallah saura kwana hudu za a daura auren kaninsa zance kawai a hada a daura da Ita Hidayan daga baya sai ta tare mene amfanin jiran,Affa yace Mashaallah dama naga ta wani girma,Abba yace yaran ne ba irin na da ba,Yar Inna a gida ta fara Al'ada amma su Hidaya tuni muke ta asarar kudin auduga,Zarah ma tunda naga nono ya fito mata nace shike nan Kuma yanzu zata fara daukan Albashi duk wata sai an Bada na pad,Kaka yace Allah ya kyauta ai ni Hidaya ma na kawowa magani ta Sha Yana sawa a danyi Kumari ayi bulbul,Abba yace Yar jakar Uba ni ta gado,Affa yace a'a ba Kai bane wlh zata cika Dan Bata girma ba,to tunda kasan zata cika me yasa ka kawo magani,kaka yasan halin Hashimu sai ya bar zancen,yace Nidai kira min Hidaya.

Bayan an kira Hidaya ya bata magunguna yace gasu Nan yanda nace ki Sha haka zaki yi na Sanyi ne,Hidaya ta karba tace na gode,Abba yace a fada Mata gaskiya ke Hidaya ranar asabar zan daura miki aure Inshaallah,Hidaya tace Abba aure Kuma da wa? Abba yace da Wanda yake sonki tunda kina karbar kayansa kina cinyewa ai shike nan kina sonsa,Hidaya tace Abba Bai taba cewa fa Yana so na ba,yace to ya fada miki I love you din a gidanki,kunyi candy me zakiyi in Yana ra'ayin karatu ya saki da kansa,Hidaya ta fara kuka tace Dan wlh ba Naila bace da Naila ce baza a mata haka ba,an fi son Naila dani,ita kudin samari nawa ta ci,Abba yace kafin bikin dai ki shirya gobe ki tafi gidan Naila Dan wlh kika sake aka daura ba Inda zai barki kije kiyi kwanaki,ko sati kiyi acan idan an daura ma kina can tunda ba yanzu za a kaiki ba,ni na yaba da hankalinsa na bashi.

Kaka yace kayi daidai Hashimu bai dace a dinga barin Yan mata haka ba a gidan iyaye,Hidaya juyawa tayi wajen Umman su,Abba yace ko kin fada Mata a banza bakin mu daya,idan nayi magana da yawun Kubra nayi idan Kubra tayi magana da yawuna tayi,Kaka ya washe baki yaji ana son yarsa Kubra,Kubra yarsa tayi dace bata da wata matsala,Abba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login