Showing 129001 words to 132000 words out of 136333 words
ya mutu ta gaji da aure auren Jibson,ko wacce tace ya aureta sai ya aurota shi yasa bai taba sa'ar aure ba ko kadan sai yanzu,Hanan tun tana ladabin dole har ya koma na gaske,Ganin Lubna surukar tace kuje bangarenki mana tunda mun gaisa,lokacin Hanan ta mike suka wuce,suna shiga Lubna tayi dariya tace Anki sharar masallaci anzo ana ta share kasuwa.
Hanan tace ke dai bari Inama wannan abin da nake Mohsin nake wa da iyayensa wlh da bazai sake ni ba,mijina son kowa kin Wanda ya rasa amma ya zanyi na riga na cuci kaina,na yiwa kaina,yanzu Kinga nan ma a haka Alhmdllh komai akwai ci da Sha da komai abincin ma me dadi muke ci,ko Dan uwarsa Ina tauna kashin kaza wlh,sabo da shi babarsa yace dole sai taci dadi tunda da lafiyarta,kullum daga soye soye sai farfesu,Lubna tace to gashi kinyi kiba wlh kin Kara kyau,Hanan tace Madara kullum kayan tea lafiyayyu rabona da su tun Ina gidan Mohsin sai yanzu,Lubna tace to ko fasa fitar zaki yi ne karfa ki fice a nan Mohsin yaki Maida ke Dan wlh yanzu wannan matar tasa ta kankane komai,kiyi dogon nazari tunda Allah yasa Jibson ba matsala ce da shi ta kirki ba ki zamanki,Dan Adam dama tara yake bai cika goma ba,daga ke sai suruka,Hanan tace itama Bata da matsala tare muke aikin komai da ita ba me son jiki bace tayani take yi wlh,Kuma ba sa Ido,kullum sai tayi Masa nasiha da fada ya rikeni Amana,Kinga ma ya siyo min kaya set goma shekaran jiya wai du na Kai a dinka min sabo da ba a yi min lefe ba,yace zai siyo min takalma da jakankuna da mayafai,tafawa suka yi Hanan tace ranar in fada miki na zage mun sha love da dare mutuminki washe gari yaje kasuwa ya dawo sai gashi da kaya wai yaji dadin night din,Lubna tace a Kara dagewa,Hanan tace ba fara sonsa ma fa ni, Lubna ta zaro ido tace da wuri haka? Ya iya love Shima duk da dai nafi son Mohsin amma Shima dai ba laifi
Kuma abinda yasa na Kara sonshi wlh ban sani ba baki ga yanda ya Kai kayan abinci gidan mu ba harda kudin cefane ya bawa babanmu,Kiga fa a yanda aka yi auren nan amma ya iya abin Alkhairi haka in na fita Mohsin bai Mai dani ba wa zan samu kamar sa? Lubna tace shawara gaskiya ki cire fita a gidan nan kiyi zamanki wlh,tace shine Nima nake wannan tunanin ta shiga kitchen ta zubo mata kayan makulashe tana cewa rannan da kannena suka zo Lubna ya basu kudi ya siya musu abubuwa Kuma ya Nemo Napep aka kaisu har gida,Kuma Baba yace idan na sake ya sakeni kar na koma gidansa na nemi gidan wani uban ba dai shi ba,Lubna tace to ki zamanki wlh shawara ce, Hanan tace zanyi biyayya haka na zauna lafiya ya fiye min mutunci ,duk Dan ta zauna sai yabon Jibson take yi Lubna na sake kwantar mata da hankali tayi zamanta.
Suna zaune sai ga Jibson ya shugo da Leda,suma ta fito a kansa yayi kyau fiye da kwal da yakewa kansa,Lubna tace ranka ya dade,yace tare da naki sai yau ma za azo Kawa guda,yace me gidan ne nawa baya gari sai da ya dawo,yace Mashaallah a dinga biyayya,Hanan tace sannu da zuwa yace Sweety bayibe(Baby).....ya fada da iskanci wai bazai taba cewa Baby ba sai dai Bayibe...Hanan tace Baby dai yace sai kin haihu sai ki haifi Baby amma yanzu ke a haka katuwa ai sai sai dai Bayibe......Lubna ta dinga dariya,yace wai in tambaye ku suka ce muna ji" Dan Allah a Ina kuka ganni har daya ta kware min? Lubna tace ni na ganka fa naji mata suna ta yabonka ni kuwa nace na gano dai dai da kawata,na nuna mata Kai tace kayi mata,Jibson yace karshen duniya ne yazo dama ance mata zasu dinga Kai kansu wajen mu sai gashi har a kaina a gwadawa duniya,alamomin tashin kiyama har a kaina ya fado,ni Kuma haka Allah yayi ni sai dai mata su dinga zuwa,ni kuwa ban taba turning mace down ba in dai tazo sai na aura wlh ba abinda ya dameni zaka nake da kudina ta wannan barin,amma yanzu Ina fata kar wata tazo Bayibe ta isheni,Hanan harda cewa Ameen Allah ya sa.
Suna zaune yace Yaya Hajiyata yau? Hanan tace lafiya take,yace an mata komai? tace ae yace yawwa,kar ayi min wasa da uwata,Da ran uwata ya baci gwara na mutu na huta indai ta silata ce,Lubna tace wlh Allah ya baka zaka yi karshe me kyau,yace albarkarta ce shi yasa kullum sai rufin asiri,Hanan tunani ta Lula yanda ita suke wasa da kula da iyaye suyi ta bata musu rai sai gashi suna ganin Jibson kamar marar hankali ashe ya fisu hankali,a ranta tace itama zata gyara ta dinga yiwa nata biyayya tun da sauran lokacinta,da yamma mijin Lubna yazo ya dauketa.
Jibson ledar da ya kawo ya bude ya bawa Hanan,dogayen riguna nane kala uku Arabian gown masu kyan gaske tayi godiya,yace da bakya kula da uwata ko slifas bazan siya miki ba,yanzu Kinga a banza zaki dinga cinye kudina,matan gaba masu zuwa a aure su shike nan sai dai suyi hakuri Kuma kin kwace kudin,Hanan a ranta tace dole na dage kuwa.
Jauro kuwa da Amarya a hanya ya siya musu kayan makulashensu,harda Shan maganinsa na Kara kuzarin Maza sabo da yayi Amarya,Amarya Kuma sai kunya take ji,Jauro yace Nima Nan kunyar nake ji karfin hali nake yi Ummu Annoor,kallonsa tayi Yana driving tayi murmushi,yace wannan kunya taki ko budurwar zamani baza tayi ta haka ba,tayi yawa,da budurwar zamani ce" da yanzu ta min kiss yafi ashirin,amma ku sai kuce Kun girma,ku da ya dace kuyi sabo da kune tsohon hannu karki sake Dake Habiba ta miki kafa in ta kwace ni shike Nan,kar ki ganki jajir ba haskenki zan ta kalla ba babu ruwana da shi"sai na tafi wajen Habiba ta bani nishadi,Maman Annoor ta murmusa kawai,yace kamar ba Yar Boko ba ni da nake tunanin ma kafin muje gida kin min kiss yafi goma a kunyace,dariya tayi ba shiri.
Haka suka karasa gidanta Wanda ya gaji da tsaruwa ko Ina kamshi yake,Jauro ya wuce kamar gidansa Yana gaba har bedroom dinta Wanda ya Sha gyara,yace badan aure ba me zai kawo ni nan,sip ta bude ta cirowa Jauro wasu kayan bacci na manya ne riga da wando dogo marasa nauyi sababbi,tace gashi Hubby" Ido Jauro ya zaro yace me kika ce? tace gashi Hubby fa nace harda shagwaba,Jauro yace uhmm yanzu nasan kinyi makaranta,auren me Ilimi yayi a rayuwa,dariya tayi ta shige toilet,tana shiga Jauro ya nuna kansa da yatsa yace ni Hubby yo ai Ina Jin ko Annoor ba a kiransa da wannan suna shi da yake matashi bare Kuma Nabeel da ya auri Yar tatsitsiyar yarinya, Jauro kana shanawa dole na fadawa Hashimu yaji sabon sunana,Yar Innar tasa duk wani yabonta da yake bata taba kiransa da Hubby ba ,sai da ta fito tace kaje kayi wanka,Jauro yayi wanka ya fito suka shirya ya jasu sallah bayan sunyi adduoi suka ci kayan makulashen su harda bawa Amarya a baki.
Bayan sun gama kowa ya koshi zama suka yi suna hira sabo da abincin ya narke yabi jiki,Jauro mikewa yayi tare da zama a Saman gadon Yana addua,zama tayi itama sannan suka kwanta gaba daya tare da shigewa bargo,Jauro ya fara soyewa da Amaryarsa gwanin birgewa haka suka tsunduma a wata duniyar ta musamman,Jauro Jarumi ya jiyar da Amarya dadi ya jefa ta a farin cikin da ta dade bata samu ba.
Yahuza donation ya fito daga gidan giya a make Yana tafiya Yana tangadi bai kula ba ya hau Saman kwalta wata karuwar mota tazo ta make shi nan take ya fashe a titin ko shurawa baiyi ba yace ga garinku Nan,mutane suka cika a wajen dake popular ne kowa yasan shi sai jimami akeyi aka dauki gawarsa da Yan sanda bayan an gama duk abinda ya kamata aka kawowa iyalansa,Iyalansa Asabe sai kuka da ihu,yaransa ma haka,Asabe tana kuka tace wlh nasan matukar mutum yaki jin tsoron Allah ya tuba karshe wani a kan aikin banzar zai mutu,gashi Nan ance daga mashaya ya fito,anyi anyi ya daina yaki gashi mutum Yana ta abu bai san Kwanansa ya kare ba a duniya,shi yasa ake so mu dinga tuna Allah da mutuwa tana iya riskar mutum a kowanne hali,babu batun sai da cuta.
Amarya tana kasa tana ta birgima ana bata hakuri tana cewa yaranmu nake ji Asabe yaran mu,duk da haka shi din katanga ne a tare damu,komai lalacewar me gida to me gidane wlh kawai muyi Masa addua Allah me yafiya ne zai iya yafe Masa,Asabe tace amma ba haka aka so ba ka mutu a wannan hali,waya suka dauka suka dinga kiran danginsu da danginsa na birni dana kauye.
Ikhram tana zaune tayi wanka kenan suka kirata,tayi mamakin ganin kiran Asabe dagawa tayi taji Asabe tana kuka tana cewa Ikhram ki taho Uncle dinki ya rasu yanzu aka kawo gawarsa mota ta make shi...kit ta kashe wayar,Ikhram ta fara Innalillahi wa innailayhirrajun tace duk abinda ka min uncle Allah ka sheda na yafe Masa,Allah gadona da ya cinye kaf na yafe Masa har abada Allah ka Masa Rahma.
Kuka ta fara ta kira Rafeeq Yana Office Spark ya saka shi gaba da masifa sai ya karasa aikinsa,Spark Yana zaune a Office din Rafeeq wai dole sai ya gama Yana Nan Yana jira.
Waya ya daga ta fada Masa,Shima salati ya saki yace Allah yaji kansa bari nazo,Spark yace waye? Sirikina nane ya rasu Yahuza Donation,Spark yace Wanda yace baza a daura aure ba? Yace ae cousin din Ikhram,yace Allah sarki Allah yaji kansa yace Ameen,yanzu me zaka Bada sadaka wlh ko gidan kansu basu da shi,Spark ya Kalli Rafeeq yace nawa ne a accnt dinka? ai ka sani,sai dai idan Joint Dina da Sa yara zan siyar sai a hada a samu a siya musu gida su zauna a basu jari,Spark yace ka daina wani zancen siyar da joint kudin tallafi na kamfanin nan ai sun taru da yawa a eba a ciki ayi musu komai,Yace to mun gode,wai yaushe za a kaishi? yace kaima kasan yau ne tunda rana ce,yanzu tafiya zaka yi kenan? Yace bata bakinka kake yi ma ai zuwa zanyi na dauki Yar dagwai dagwai ta kafata kafarta in na kaita sai na kama hotel a can kullum naje har ayi 3days sai mu taho gida,Spark yayi dariya yace na gaisheka mazan fama,Ina zan iya barinta haka da yamma na dauki abata mu tafi masauki muyi bacci na kwashi aikin dare da safe na kawota,Spark yayi dariya yace Kai Namiji,Rafeeq yace Namiji ai sai Misam idan ba Chika tayi ciki,Spark kamar shine me cikin harda kakarin amai ohhhh uhhhh....Rafeeq Yana dariya yace wlh da gaske nake wai tsinken pt ta siyo ya bada positive,suka tafi asibiti akace ciki ne 4weeks kenan da samunsa,Chika tana nan da ciki ana amarci da ciki,Kai kuwa Spark ko gado kayi ne na mummynka har yanzu 6mnths shuru shuru kullum Naila sumul,Spark yace Amarcina nake ci dama ni nafi son haka amma yanzu Ina so ta samu cikin sai abinda Allah yayi,Rafeeq yace Allah ya kawo,Misam za ayi Baby ko mace ko namiji sai wani iyayi yake wai shi namiji ne,Spark yace ah yayi gaskiya ya je da zafinsa Kai.
Rafeeq tashi yayi suka fito yace nima gida zan wuce na gaji so nake muje aikin hajji ma da Naila da Chika,Rafeeq yace ni shine za a ware ni ba komai,yace alkawarin Chika ne Sanda akayi bikinmu tayi kokari nace zan biya mata,Rafeeq yace okay to Allah ya kaimu,Spark yace kafi kowa cin kudina duk ka isheni haba, Rafeeq yace yanzu ma Ina jiran na taimakon kamfanin za ayi sadaka,Dan Allah kuzo da su Misam da su Arham,Spark yace zamu zo gaisuwa ayiwa Malamar Yan iska gaisuwa,dariya Rafeeq yayi ya shiga motarsa ya wuce gida.
Yana zuwa ya samu matar tasa har ta shirya tana jiransa da akwatinta,Yana shugowa ta rungume shi tana hawaye,yace sai hakuri Muma duk lokaci muke jira yana bata baki,yace bari na shirya,tare zamu tafi? Yace ae mana" murna tayi sosai taje ta tayashi ya shirya ta zuba Masa kayansa da duk wani abin bukata sannan suka kulle gidansu ya kira Arham yazo ya dauki motarsa ya kaisu Airport, suka wuce shi Kuma ya tafi da motar abinsa yace banza ta Fadi zan more mota,a motar ya wuce gidan Misam,Yana zuwa ya samu Chika a kwance tana hutawa tana kallon film,Sallamarsa ta amsa tace nayi fushi sai yau,murmushi yayi Yana gyara agogonsa me tsada ya zauna yace Ina yini ta amsa tare da tambayar ya su Mima? Suna nan lafiya,ta furta sannu dan saurayi,me zaka ci? yace abin dadi mana Ina yayan? ya fita" yawwa Arham na aikeka mana,yace Ina? Dan Allah kasar calaba zaka siyo min wacce masu ciki suke ci,Arham yayi dariya yace irin taku kenan kice Misam shi har ya jefa one goal,gaskiya an bar Spark da Chaskarar kwallo har yanzu Kuma ya kasa jefawa Allah ya kiyaye shi da zama Mummy,Chika tace ni ance Maka ciki ne Dani to,shine mana Aunty tun yaushe kuma an gamu,Chika tace dan Allah tafi ka siyo min kafin ka dawo na hada ma abincin,ni yau bana Jin yunwa abin dadi kawai zaki hada min Inci,Yana fita bai dade ba ya siyo mata ya kawo,ta kawo Masa su fruits salat ya sha hadi,ta kawo Masa wata samosa me dadi taji hadi ga nama a soye,ya zauna Yana cin abinsa hankali kwance.
Suna ta hira da Chika,Chika tace wai Arham kai baka da budurwa ne? Yace Ina maraya wa zai min aure ni,in kayi budurwa ai kana da kudi har yanzu fa ci da ni ake ko kaina bana iya ciyarwa ta ya zan zauna Ina budurwa tace kudin anko bani da Sisi,tace Data Ina fama da tawa bada ni ba,Chika tana dariya tace haba Arham Ina ganinka babban yaro,yace uhm in munga hadaddiya sai dai nace Allah ya azurta mu amma bazan tare ta ba.
Yau da yamma za a Kai Hidaya gidan miji,tun safe take kuka tunda gari ya waye take kuka,wajen Azahar Abba ya shugo gidan,Kubra tace wai yarinyar nan har yanzu taki hakura sai kuka take anyi lallashin anyi taki hakura,Abba yace rabu da ita idan ta fara ciwon Kai taji wuya ta daina ko shi Angon ai zai lallashe ta da Hallare lafiyayya rabu da ita Dan Allah karku sake cewa tayi shuru,Kubra ta dinga dariya tace kaima dai Naila ta koya Maka wlh,yace ni ta gado na Dade da sanin ana kiranta Hallare ke ma kin sani ke da yarenki zaki dinga wani gulma,Kubra tayi murmushi,wajen su Goggo Abba yaje,Goggo da Tani sun dawo,Yana shiga suka gaisa yace barkanku da zuwa,suka ce yawwa yace Amma zaku je ku gano Naila suka ce Inshaallah zamu je mu gano ta.
6pm su Haidar suka zo daukan Amarya a motoci ,kawayen Hidaya kamar yayi sun Sha anko,kawayen Kubra da danginsu na kauye,Amarya wacce ta Sha gyara taci kuka ta gaji ta shirya cikin wani Leshi white and Golden dan gaske da Naila ta dinka mata gown ce hadaddiya daga baya har kasa take ja,da kyar ta tsaida kukan aka mata Yar make up sama sama sannan aka tafi kaita dakin miji,Abba ya riga ya mata nasiha tun jiya shi yasa yau ba a tsaya ba.
Habiba da tawagarta suna nan suna jiran Amarya Ango Kuma Yana gida a sama bedroom dinsa ya fito ta corridor din baya Yana hango motoci an bude gate Yana Jin dadi Yana kallo ta samansa.
Amarya aka fito da ita Haidar ya kira a waya ya daga yace ka ganni a sama Ina Kallo ya ka gane min Amarya ta? Haidar Yana dariya yace Amarya fa ta karo wulakanci irin kyau haka wlh ban ganeta ba,yace ni dama nasan haka zata dawo sai taji wukar yanka balangu ma tukun,Haidar Yana ta dariya yace ni kuwa yar Kunkumar tawa munyi fada dama kawu bai sonta na tsine mata na koreta,dariya suka yi masu kai Amarya tuni suka yi ciki da Amarya,su Habiba suka sauke su hannu bibiyu da karramawa,Nabeela da Rahma suna can gidan Amarya su suka gyara komai na gidan,sai da suka yi sallar Isha sannan suka tafi da Amarya hadadden gidanta,su Goggo suna ganin gida suka dinga cewa lallai Hidaya ma anyi dace,shi dai Hashimu Allah ya Cece shi,Hidaya tana ta kuka an Rabata da iyayenta,tunda taga an fara watsewa ba kowa sai Goggo da Tani ta rike Goggo tana rusa kuka ni a Maida ni gidanmu....wayyoo....Umma ta....Abbanaaaaa....Goggo ta fisge jikinta suka fice a bar Hidaya tana ta faman kuka,Wanda zasu zauna ma a wajenta duk Goggo taje kowa ya tafi tunda baza ta yiwa mutane shuru ba,suka kira Ango Goggo tace kaje yanzu mu Kam mun tafi tana nan tana ta rusa uban kuka wala'allah Kai ka iya lallashinta ta yarda,yace to bari naje,lokacin wanka yake niyyar yi ya fasa ya kira Haidar yazo ya kaishi can.
Goggo tace Naila kuwa tafi dadin sha'ani wlh muka kaita cikin Jin dadi ba kuka ba komai har muna ganin laifinta ashe gwara ita wannan jarabar kuka haka,Kuma yau dai ba kyaleta zaiyi ba,Tani tace Ina fa zai barta ai in zata tsage bazai barta ba sai dai idan suma take,Ina Tausayin Hidaya yarinya ce sosai,Wannan yaran da kike gani ki kiyaye su cewar Goggo.
AsmaBaffa
[2/8, 8:18 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI
BOOK2
~YARAN JAURO~
106-110
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA