Showing 81001 words to 84000 words out of 136333 words
Itace,za ace Mima ta kashe mijinta ne? Za ace Arham yayi kisa ne? Yusra za ace ta gidan su Mima,ko ace Maman Spark abin kunya ya ganka Spark babarka tayi kisa.
Spark Yana hawaye yace shike nan na daina yawo a gari,Ina zan fita a dinga nuna ni uwata tayi kisa,Mummy ce ta kalle su da kyar, Spark yace Wanda kike fada Jamilu gashi a gabanki ba namiji bane mace ce itace Naila gata Nan Kuma itace matata ita nake aure,a shigar maza kika Santa shi yasa kika kasa gane ta sannan Baku dade ba daga zuwanta kika mata sharri,yanzu gata nan ko zata iya yafe miki oho,kin Sa an bata mata suna,kin Rabata da iyayenta kin kaita gidan yari taci wahala cikin kartan Maza,badan Allah ya kaini ciki ba da shike nan,Mima ce tace haba shi yasa wlh nake ta mata kallon sani,Dan Allah ki yafewa Yar uwata,Naila a ranta tace wlh bazan yafe da wuri ba sai kowa ya roke ni cikinku Allah yasa ta sheka lahira yanda zaku zo neman Alfarma wajena,baya ta juya ta koma tayi zamanta tana kuka.
Arham lallabawa yayi Naila ta tura Masa recording din Mummy duk ya turawa dangi kaf ta Whatsapp,kowa yaji sai ya zaro ido,sai kiran Mima da Spark suke a waya,Misam ya kira Mima yace Mima ashe Kuma haka wani sabon abinunyar ta danno Allah ya tsare gaba Kune da kuka gaskiya,dole kuyi kuka wlh ni dai ta taimaka min karta sheka yanzu Dan aurena ya matso kar ace an daga bikin,Rafeeq Yana gefe Yana cewa Allah ya tashe ta mu dai a samu ayi bikinmu tukun koma me za ayi sai ayi daga baya.
Sai da Mummy ta Fadi gaskiya Kuma sannan kwanaki kadan ta fara Jin sauki sosai kullum sauki samuwa yake,yanzu har abinci take ci,Spark ya daina walwala Sam yasan ko Mummy ta warke karshenta gidan yari amma indai zai dinga Ganinta da sauki,ta samu chance na nemiyar yafiyar ubangiji idan ta shiryu.
Naila kuwa bata nuna ta damu ba sai ma kwantarwa da Spark hankali da take yi.
Suna masaukinsu a kwance,tana jikinsa suna Hira kasa kasa yace Dan Allah Baby zaki iya yafe mata? Naila ta Harare shi tana dariya tace ni din banza ai ko sabo da Kai na yafe mata wlh da zuciya daya amma sabo da Kai,Ina sonka fa ta rainar min Kai na aureka kaddara ta kaini gidan yari badan haka ba baza ta iya kaini can ba,yanzu Baseeru shi dake bai da rabon wahala Kuma da tsawon ransa gashi ya Sha ras da shi,Kuma ni gashi Sila ta sa mun hadu na aure ka,badan haka ba Ina zanga me kudi irinka, ai ni Alkhairi ya zame min amma idan mun koma dole mu koma gaban hukuma a wanke ni fess sannan naje naga su Dan Indo da Goje su tabbatar,yace Inshaallah indai kin yafe ai shike nan,tace na yafe mata har abada sabo da Kai amma karka fadawa dangi har su Mima na yafe so nake suyi darasi pls,yace Inshaallah Yana murna ya rungumeta kamar zai cinyeta Yana sa mata albarka.
A hankali tace Bado Yana bukatar Hallare,Ido ya zaro yace wannan son Hallaren naki kuwa na lafiya ne? Yau how many times muka yi karfa na koma Baseeru da Mummy,Naila tace Kuma wlh ba ciki bane ko ni Ina mamaki naje a asibitin sun min test sunce ba shi bane,naso ace shine na Maka surprise,yace Allah ya baki tace Ameen inyi nakuda ta in haihu,Spark yayi dariya yace ke Nakudar ma birge ki take yi? Naila tace sosai na dinga wash...ahhh Spark....bayana...kuguna...harda yin goho a Saman bed tace sai Da ya fado aji Inya Inya,ace Namiji ta haifa ko mace,Spark ya kama dariya yace haka fa kika yi a first night sai gashi kinfi kowa raki,Naila tace banda haihuwa,Kai yaro guda wasa ne Allah ya bani mace,yace masu Albarka dai,tace ko namiji ne ma Allah ya amfana Ina laifi,Allah yasa ya gado hallarenka matarsa ta kwashi dadi,Naila harda rawa da Kai ana Jin dadi sai Shoky ahhh....Spark dai Yana ta dariya Yana latsa waya,kwanciya tayi a jikinsa tana mika,wayarsa ya ajiye yace idan na kamaki Allah sai kin gudu yau,Naila harda adungure a Saman bed ai haka nake so yeee ai ni sai yanzu na balaga ashe,da ban balaga ba,sai dariya take ba Spark da gaske kullum Naila Kara fetsarewa take a bed,wani abin da take har mamaki yake.
Nabeel ne ya tsiri zuwa gaida Abba duk bayan kwana biyu sai yaje,Abba ya gaji ganin yau ma ance yazo inji Nabeel,Abba fitowa yayi yace Kai idan kana da manufa ka fito ka fada sai kace Kaine Jauro sai sintiri kake,nema kake lallai sai kayi Aboki dani Kuma bazan zama abokinka,yau naji yaro Dan Albarka kullum sai kazo wajena na gaji,bana sonka da aboki ni karka ganni wani saurayi saurayi da shekaru na,Nabeel dariya yayi kyakyawa ne sosai,Abba yace yau dinma gaisuwar ce? Nabeel yace ae Kuma yarinya zaka turo min ta karbi sako,Abba yace ai Ina da yaro Aslam me yasa baza kace yaro ba sai kace yarinya,Nabeel yace to a turo Aslam din duk Daya ne,Abba ya shiga ya turo Aslam,Aslam Yana fitowa ya gaida Nabeel Wanda kofar motarsa a bude take ya fito da manyan Ledoji shake da kayan ciye ciye yace Auntynka zaka bawa, yace wacce a ciki? Nabeel yace Yar Kwaila dai gata nan wata kamar tana na manta sunanta,Aslam yace Zarah kenan yace ba ita ba ai na San Zarah yarinya ce sosai,yace Aunty Hidaya? yace yawwa ae ita,Aslam yace Kai kace mata Kwaila sai na fada mata,Nabeel yayi dariya a ransa yace yaro yayi gadon Ubansa,a fili yace to fada mata mana tsoronta nake yi,kace ta cinye idan ba haka ba Ina dawowa naji ance bata ci ba sai na balla ta,Aslam yace a nawa? Yaro da wayon tsiya,yace sa kudi yace dubu daya sai na Maka CID,yace yawwa yaro ya bashi 2k yace idan bata ci ba ka fada min,yace bani number waya zan saci wayar Abba na kiraka,Nabeel ya rubuta number dinsa ya bashi sannan ya tafi.
Annoor kuwa tunda akace an tsaida ranar aure duk ya rude da shirye shirye wata Daya aka sa tal,Habiba ta fara gyara Amarya sosai tana zuwa wajen gyara,sosai suke shiri,yayin da Maryam tana ji tace wlh baza ta sabu ba,Kauyen Maman su ta shirya ta tafi,tana zuwa ta samu Yan uwanta na wajen uwa tace Dan Allah wajen gagararren malamai zaku raka ni,miji na samu zan aura naga yanzu Yana min Wala Wala zai gudu,mutanen kauye da masifar son ayi aure ko za a mutu,wata Dausiyya matar aure ta raka tace akwai Malam Musa aikinsa kamar Yankan wuka wlh,idan zai yuwu zai fada miki daret (direct).
Suna zuwa suka same shi a zaure ya dawo kenan daga Kasuwar kauye ya siyo kayan taushe,Yace a'a Dausiyya kece tafe? tace Malam Yar uwata na kawo maka,yace mashaallah to ta shugo,Maryam anci wanka ita ga Yar birni ta shiga cikin zauren ta zauna,Dausiyya ta tsaya a waje sabo da sirri.
Maryam bayan sun gaisa tace Malam wani nake so kamar na mutu Malam amma yaki so na wata yake so gashi har an sa bikinsa an kusa ma,Malam gashi da kudi ga kyau Inda kasan shi yayi kansa wlh,Malam komai da ake so a wajen namiji ya hada,amma yaki so na,Malam yace Kash me yasa baki zo da wuri ba ai da tuni ma kina gidansa idan da rabo ma an samu.
Yanzu bari a fara dubawa aga ta yanda za a bullowa aikin,Kasarsa ya jawo a faranti ya fara Zane Zane,sai da ya dauki lokaci sannan yace babu alheri a auren ku,kece kike sonsa amma shi baya sonki ko kadan, dai dai da digo baya sonki,gashi Nan zuciyarsa babu hasken sonki a ciki duhu dundum,Maryam tace to ya za ayi a kulla kaunar ya dawo Yana so na? Malam Musa yace aurensa fa babu fashi sai anyi shi ko me zaki Masa,Maryam tace to a haukatar da Iman din mana,Malam yace babu Hali babu hauka a kaddararta,duk Kuma Wanda zaki je sai dai ya miki karya yaci kudinki sannan ni bana haukatar da mutum bana kisa Kuma,Abu daya zan iya miki idan anyi auren kar ya kusance ta,Maryam tace yawwa tace Hakan ma yayi,Malam yace indai ya sake ta kwance Mazagi ma'ana tazuge to shike nan sai ya kawo,Maryam harda dariya tace haka yayi ni Kuma zan San yanda nayi ya Soni,Malam yace idan ta tabashi sai ya kawo kawai,Maryam tace wlh yayi min,nawa zan bayar yace wannan karamin aiki ne ki Bada sadaka kawai,ta bashi dubu goma,Malam ya haukace yace zaki ga aiki,ya Saba da mutanen kauye Dari biyar dubu daya akan wannan wani sai yayi kisan Kai.
Maryam tana fitowa tace an gama Dausiyya gaskiya ya hadu Malamin Nan,suka tafa tace ai zaki ga aiki wlh,a ranar Maryam ta koma gida birni,Malam yace sati biyu yayi yawa Amarya tana tarewa bazai iya komai ba.
Masu Sharhi Ina godiya,Baby Ak Ina godiya sosai.
Arewa book
AsmaBaffa1
TikTok
AsmaBaffa
AsmaBaffa
[1/24, 5:46 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
BOOK 2
~YARAN JAURO~
61-65
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM
Page naki ne
'Yar Gold
Ango Misam har da cewa ku sani a gaba na fara tozali da Amarya ta farin gani,sanyin raina, gidan iyayen suka fara shiga aka gaisa da su Spark da dukkan matasan Misam ko kunya yana gaba,Suna fitowa suka nufi makwafta Inda Amarya Chikar gayu take,irin kyan da tayi ba a magana, sai kida suke ji Dj ya bar musu kayan kidan ya tafi su suke saka abinsu,Naila ita ba rawa take ba wata ce me kula da kidan, Yan mata ana ta fitsara,Beauty ta shige cikin yan gidan yarinsu sai chashewa suke a compound duk iri daya suke yi kowacce rawa da sunanta, kawai sabo da an daura aure suke ta faman rawa.
Yau Amarya ta tsaya tana kallo kawai duk rawarta taki yi yau, Naila har ta hango nata hannu ta daga Masa,yayi dariya, Naila tace yau na karbi Chika ni tunda ta kasa mu bara muyi, tasowa tayi tana rawa a hankali da rangaji da cup a hannunta cike da fresh yo har ta isa gaban Spark Wanda ganin abinda take ya ja gefe Yana mata video, Rafeeq yace baza kuci lokacinku kuci namu ba fa ato,mutane suna dariya Arham wajen Amarya ya nufa shi yana rawar yace Naila ma tayi bare mu,duk lalacewa irin ta Naila a rawa ta iya yinta yau,dariya ake tayi,Misam ya jawo Arham baya yace matarka ce wai da kake rawa kana tafiya wajenta ,ana ta yiwa Chika tsiya yau taki yin rawa,kujera ta jawowa Ango ya zauna durkusawa tayi a gabansa tare da dora kanta a Saman cinyarsa.
Misam yace zan sawa Amarya Albarka ya dafa kanta sau uku yace Allah ya miki albarka,aka saki shewa,Spark Yana Shan fresh yo dinsa da Naila ta bashi,Chika mayafinta ta bude a gabansa ya dinga mata liki Yana ta shigewa mayafinta kawai rapa yake farkewa ta Yan dubu dubu Yana liki,ya sake balle wata ya watsa sama,Yana ta uban liki yace sai Kun rike ni in ba haka ba yau sai dai jari ya karye ,ya zaro wata su Arham suka rike shi,yace ku barni,uhm uhm Yaya suka ce,dariya ake ta yi yace to na gama ya watsa last sama 'Yan mata suna ta tsincewa ,Chika taje ta juyewa Beauty kudin tace shirya min abina,ta dawo suna ta pics,Naila tace wlh nima sai ka min liki har rawa nayi,Spark yace kwantar da hankalinki bari su gama,sun shiga duka anyi pics iri iri da videos,Spark ya ja kujerar Ango ya zauna Naila ta tsaya a gabansa aka sa mata kida,dollars Spark ya balle shi baya ma lika mata a jikinta kafarta ya duka kamar Yana gyara mata takalmi ya dinga farfar da kudin,Mohsin sai dauka yake Yana dariya shi kanshi sai yau ya taba ganin Naila tayi rawa,Ana ta dauka Naila sai dariya take tana rufe fuska sabo da bata rawa, harda yiwa Chika gwalo,Misam ta kalla tana Yar rawarta ta Masa gwalo,dariya sukeyi yanda Naila take musu gwalo ko Ina sai ta juya tayi musu gwalo,Arham Yana gefe yana ta rawarsa, Kamal Yana ta dauka shima sai da Naila ta dafa Spark tace na gaji sannan ya tsaya da likin,Su Chika suka kwashe mata kudinta itama.
Abinci kuwa fried rice ta Sha hadi da quarter din kaza ga lemo ga ruwa shi aka rabawa duk wani Wanda yaje daurin auren,su Abba kuwa Naila ce ta Kai musu nasu suka gaisa ta dawo,ko mayafi basa sawa,Spark yace shi bai yarda ba sai ta sa mayafi,haka ta dakko ta yafa karami,Mohsin ya makale can gefe shi da Beauty suna ta hira cike da nishadi,yace kina iya cin abincin kuwa? tace Naila tana min girki na,yace kin huta,abincinsa ta bude tana bashi a baki,Jauro su sun cinye nasu,Abba yace Mohsin ya fito mu tafi, Jauro yace kyale shi ya gama Dan Allah,Abba yace Yar Inna yau Sakwara take min bana so ta huce,Jauro yace wai baza muje zancen bane Abba yace gobe sai muje Inshaallah amma ai kawai zuwa zamuyi a matsayin ba zance muka je ba sai an daura auren sai ta San da Kai aka daura,yawwa dan gari haka nake nufi cewar Jauro,iyakaci idan an daura taga nine mijin ta fara Dan hawayen gulma tana shagwaba ni..ni..nii...Habiba kawata ce faaaa...Jauro harda gwadawa, Abba yace Kai Kam ka tabe Jauro harda komawa dan Daudu?,kana nemafa kayi a asara a rayuwa wanne irin Abune sai surukina ya ganka ka kunyata mu.
Arham anga yan mata sai faman baza Ido yake yace Yaya Spark Nima na zaba? In kana da kudinka zabi mana,ba Wanda zai sake aure yanzu a gidanmu sai Nan da 4yrs uban waye zai rike muku matan,Arham yace wai na fara soyayyar Nima,sanda kake yi shawara kake dani duk kwailayen da kake kulawa,yaro ka nemi kudin tukun,Arham yace Ina da Uba Allah yasa ba maraya bane ni,Misam ne ya kira Naila yace ba wani Palo Wanda ba mutane kin gane ai ki turo min Amarya zan fada mata wata magana,Naila tace babu sun kulle dakunan su sun tafi gidan bikin,Misam yace to anji jeki tunda ke Baki iya hada harkar Lada ba,dariya tayi tace ae sai da suka yi sallar La'asar sannan suka wuce Kano,Shaheed yace Naila ta fito su tafi,Rafeeq ya matsu shi ya ganshi a Kano ma,Naila,Beauty har wasu matan kaf Yan gidan yari an tafi wajen Malama,Chika aka bari da kawayenta Yan Kd ba damar zuwa.
7pm suka dira a masaukinsu can hotel,mata kuwa suka yi gidan Malama,Yahuza Donation ya kwaso karuwai da masu kida wai sun zo Masa murna zai aurar da Yar uwarsa,suna ta tambada a kofar gidan Yahuza,kida ne na gasken gasken kamar zai fasa layin,kidan ko baka so sai kayi nishadi,Su Naila suna zuwa suka ce ai mu bi sahu kawai,Amarya taci kwalliya cikin fitted gown na Bride material wani blue an zuba mata make up,tana zaune ana ta cashewa a gabanta,ya zata yi ance dole a gabanta za ayi,Naila ta kira Spark tace ai ku taho a Nan ake biki ku taho da kudin liki,yace hmm na gaji ni bacci zanyi,Naila ta dame shi ni wlh sai kazo.
Arham su dama ko masaukin basu je gidan Amaryar suka taho sai suka iske Inda ake badala,kowa ya rike baki gidan su Malama guda,Arham yace lallai a Nan ake biki,duk fitsarar su sai da suka tsaya kallo yanda Yan mata balagaggu ke barin mazaunai da kirji,Kuma tare da Maza,Stella ta jawo Amarya dai dai lokacin angwaye sun zo,Ikhram tace tun kafin a daura bazan iya jurewa ba dole na chashe,tana farawa aka dauki shewa da guda aka bata fili,Naila tace Ango ga ranarka kace zaka chashe,Rafeeq yace anya bazan iya ba yana dariya,ba irin rawata bace, Malama kida ya mata yawa ba ruwanta da kowa,Rafeeq tazo ta jawo ciki tace idan baza ka iya ba just watch ta juya Masa duwaisiyya tana girgizawa,Misam da sauran suka dinga dariya,Misam yace akwai abin ai dole kiyi,Ango ya fara zuba ruwan kudi Yana liki, Ku bani tamburan Ikhram harda tamke baki,akan yana liki ga rawa ana Masa yaga kaya.
Su Naila suka shugo suma suna ta liki,masu kidan karuwai suka Kara dagewa,suna cewa mu yau a nan zamu kwana,yau kwana nan,anyi liki sosai,Yan gidan yari suma sajewa suka yi da karuwan,sai wurin 1am,Spark Yana zuwa yaga abinda ake ya ja Naila mota suka zauna ciki suna tsotse tsotse,sai da angwaye zasu tafi masauki Kamal yazo yace Madam a bar mana mota,Naila fitowa tayi ta barsu suka tafi ita Kuma ta koma ciki,Amare nan ma masu kwana tattarawa suka yi suka koma kusa da gidan Yahuza Donation wani gida me kyau da Dan fadinsa ya Sha tiles matar yare ce me shegen tsafta,da aurenta ma da Mijinta shima yare,four rooms ne agidan da Parlo.
Naila suka baje a gidan,Beauty tace Naila banci abinci ba fa tun safe,Naila tace ke na gaji ki fadawa Amarya,Ikhram tace me zata ci a dafa mata yanzu,tace taliya da manja da yaji,Naila tace kullum dan masifa taliya,wata ce a kawayen Ikhram ta siyo taliya,tace naje gida na karbo mana,Ikhram tasan halin su Asabe tace a'a shafa'atu ga kudi siyo mata.
Naila tace a dafa Dani,Ikhram tace wlh Baku isa ba ga Abinci za a kawo mana wa za a barwa shi, Shafa'atu ta karbi kudi ta siyo taje dakin Ikhram ta dakko yaji ta soya manja a gas dinta sannan ta dafa taliyar ta kawo,Beauty ta ja gefe da taliya guda a dafe tana ci kadan ta rage,Naila tace naci wannan tace a'a da safe zan dumamata,Ikhram tace ki bata taci da safe a dafa miki wata wannan masifar cikin naki ke tab,Beauty tace yarinya rai dai