Showing 102001 words to 105000 words out of 136333 words
ya Kalli Kaka yace Affa yaji ana son yarsa to ai tarbiyyarka ce Kaine ka fiye yiwa Kubra tarbiyya har tayi yawa,yanzu gashi ta hana nayi aure,Affa yace Allah ya Kara bada zaman lafiya,Baki Abba ya bude yace a'a mu lafiya muke zaune,Affa yace ai ya karo nace Abba yace wannan ma ya isa ni na gode Allah in ba so kake Kuma na hadiye ta ba wanne zaman lafiya kake nema.
Kaka yace to shike nan Hashimu.
Yanzu ai sai na zauna ayi daurin auren Hidaya da ni,Abba yace ba damuwa,zan kira su Naja'e su tattaro suzo sabo da a sheda,in za a kaita Kuma Tani da Goggo sai suzo idan an tsaida rana,Kaka yace Ina tsoron auren Nan na Hidaya karfa Kato ne ya balla mata Kwankwaso,Abba yace a'a irin yaran nan sunfi manya ba abinda zai faru Dan matashi ne fa son kowa da shi,Kaka yace shike nan to.
Hidaya kuwa tana zuwa wajen Umma ta fashe da kuka tace Umma kinji Abba wai auren dole zai min mutum bai ce Yana so na ba,Kubra tace Bai ce Yana sonki ba amma yake ta zuwa kullum Kuma kike fita kina karbo abin hannunsa,kullum raba dare kike waya da shi ko baki San mun sani bane,duk iyayen da basa saka Ido akan yaransu ai sun shiga uku,muna jinki to,har tambayar Aslam kike ko yaushe zaizo,ki sa Aslam a gaba kina Masa hirar Nabeel Ina jinku fa.
Yanzu baki da aboki sai Aslam sabo da Nabeel Yana Aiko shi wajenki,shi yasa muka ce a daura kawai Kinga kin huta,Hidaya tayi mukus tana Jin kunyar kanta tace Amma Umma ai abokina nane,Aboki da namiji bada 'ya'yana ba wlh bari a daura in kinje sai kuci gaba da abotarku,ai Aboki bazai guji abokinsa ba,Hidaya tace gwara ma na tafiyata gidan Aunty Naila tunda ba a so na,Umma tace kamar wani shiri kike da Naila,kina shiga lamarinta ne? Wlh Hidaya ki canja hali hassada ba Inda zata kaiki,ki rasa wacce zaki wa hassada sai Yar uwarki,tunda kika yiwa Yar uwarki uban waye baza ki Masa ba,Hidaya tace ai na daina ni wlh na Dade bana ma Jin Haushinta kawai Nailan ce sai ta dinga nunawa ita ta girmi uban kowa tana wani iskanci,dariya Umma tayi tace Naila ce take iskanci? Bata girmeki ba?
Ai da kadan ta girmeni ni bana so a dinga rainani,Umma tace sannu sarkin girma,in kin San gidanta zaki je ki mata rashin kunya karki je,shi Mohsin ai zuwa kike ki ta yiwa matarsa Aiki,ni kwana biyu ma Banga Beauty tazo gidan Nan ba ko lafiya take oho,bari na tura Aslam da Zarah su gano min lafiyarta,Hidaya tace zance,a'a ba Inda zaki ba gobe zaki tafi Abuja din ba,dama Ku tafi tare da Zarah da Aslam gaba daya,Hidaya tace ni kar a hadani da yara,ke wai a duniya sai son girma wlh tare zaku tafi.
Washe gari Hidaya suka shirya da sassafe Mohsin ya kaisu tasha ya sasu a mota ya biya kudin motar gaba daya sannan ya basu kudin dawowa Dana kashewa,Zarah tace Yaya kaga nama a siya mana muna hanya muna cin abinmu,yaje ya siya musu a can ciki ya kawo musu da yogurt da ruwa yace karfa ku Sha ruwa a hanya da yawa ku fara Jin fitsari suka ce to,Yace ke Hidaya ki kula da su Kuna zuwa tashar ki kira Naila kafin ku karasa zata je can,tace to,mota dama ta cika wata Sharon ta tashi suka tafi.
3hrs Kafin su karasa Hidaya ta kira Naila tace sun kusa,ai kuwa Naila ta fito ta samu Spark Yana aiki a Palo da takardu tace Baby su Hidaya sun kusa karasowa,yace zuwa zasu yi baki fada min ba?Naila tace nima da safe Mohsin ya kira ya fada min ban sani ba,yara Kuma su taho a mota ai sai ki fada min a siya musu ticket,Naila tace hidimar tayi yawa shi yasa ma ban fada Maka ba,kudinki ne ko nawa? Naila tace naka ne,ya mike tsaye yace Ina za a dauke su to? ta fada Masa ya karbi number Hidaya yace a sa driver ya dakko su ko kece zaki je? tace ni zanje tana murna yace nasan dama haka zaki ce Yana murmushi,Allah ya yiki da son tuka mota,Naila tace dadi nake ji idan Ina driving in ta yanga ni ga me kudi.
Dariya yayi tace bari na zaba a ciki,sanye take cikin doguwar riga Abaya mayafin ta yafa ta fito da key din mota tace na tafi to,Spark yace a dawo lfy ta fita,har can taje ta riga su zuwa ma tana jiran su karaso.
Sai da ta kusa 1hr a mota tana jiransu sannan suka kira suka ce gasu a tashar sun fito a mota da kayansu,ta bude mota ta fito ta hango su,Zarah tace ga Auntyn ma suka taho wajenta,a mota suka saka jakankunan su sannan Hidaya ta shiga gaba Aslam da Zarah a baya,Naila Mohsin ta kira tace sun sauka gasu suna tare,yace to Alhmdllh,ta kira Umma da Abba duk ta fada musu sun sauka lfy sannan taka mota suka nufi gidanta,su Hidaya sai baza Ido ake,tace Aunty kin more,Naila tace ba yanzu zaki San na more ba sai kinje gidana,suna karasawa gidan suka dinga kallo suna yabawa,Hidaya tace kin caba gaskiya,Naila ta kalleta tace kyaji da shi Hidaya ke baza ki canja hali ba,me nayi Kuma Naila? Wlh ni ba hassada nake miki ba tsakani da Allah na yaba,na gane baida amfani abinda nake yi anyi mana wa'azi naji illar hassada ni wlh na daina Kuma inshaallah Ina neman tsari da ita ma,ki daina ganin ko Ina miki hassada ne,Naila tace Masha Allah anyi hankali.
Jakansu suka dauka suka shiga ciki Naila tace kuyi sallama fa me gidan Yana nan,Hidaya tace to ai ko baki fada ba,sallama suka yi suka shiga,Spark ya amsa da fara'a yace yara sun girma sun zo Abuja da kansu,Aslam yace ko ni sai na kawo kaina,Zara tace Kai Aunty kina Jin dadinki sai na Dade ban koma gida ba,Spark yace da Abba zai bar mana ma Kinga kin huta,tace bazai barni ba Abba Yana so na aure zai min,Dariya suka yi,Hidaya tace Ina Kwana Yaya Spark,yace Ina yini dai ko yunwa kike ji ne,dariya tayi shi bai taba ganin Hidaya tana dariya ba sai yau,sai yaga suna yanayi da Naila,Zara da Aslam Kuma sunfi kama da Naila sosai,bari muyi Sallah mudai cewar Zara,Naila tace to ku kwaso kayan naku,Hidaya tace wai mutum yazo gidanki babu taimako jakar ma baza ki daukar mana ba,Naila tace kawo na daukar miki ta dauki jakar suka haura sama dakin Naila,tace Aslam zo na nuna Maka dakinka,ta kaishi wani dakin daban Hidaya da Zarah dakinsu daban,tace to kuyi wanka kuyi sallah sai kuzo kuci abinci,suka ce to,wurin Spark ta koma.
Mika yayi yace na gaji wlh,ya jawota jikinsa yace Baby na manta ban fada miki ba naje prison wajen Mero Allah sarki ta bani tausayi,Nan take sai Naila ta bata fuska,fushi da kishi ya taso mata,ta daure tace fito da ita zaka yi?
Yace ae ya Bata labarin komai yace wlh Baki gani ba Mero da take Yar bulbul da ita da haskenta duk ta rame tayi duhu ai an dauki alhakinta,Naila tace kace dama kallon Mero kake yi shi yasa ka gane Yar bulbul ce me haske,ba so me ya kawo tausayi,Baki Spark ya bude yace nifa labari na baki ba son Mero nake yi,Dan Allah ka Adana kalamanka wato shine baza ka fada min zaka je ba sai ka tafi ban ma sani ba sabo da son Mero yana ranka,kin San fa komai akan maganar me yasa kike haka? in banje na fitar da ita ba sai yaushe,an zalunceta Kuma uwata fa za a kulle a madadinta,Naila tace a kyale Mummy din mana in yaso ka biya kudi a saki Mero na mene zaka je,farko sanda nice acan ai Rafeeq ka tura da Islam yanzu Mero ka kyasa tana birgeka shine ka tafi can kanwarka ce ko muharramarka,Spark yayi dariya yace wai ke kishi kike da Mero? Allah ya kiyaye nayi kishi kayi ta zuwa idan kullum zaka je kaje,ta mike ta shige kitchen,Spark shi dadi ma yake ji ana kishinsa ko a jikinsa wani ma nishadi yake yi,Naila ta wuce dining tana fushi,yace tace ma a gaishe ki na manta,ke ta fara tambaya,Ashe ma sunanta Khadija,Naila ranta ya Kara baci ko magana bata iya yi ba.
Su Hidaya ne suka fito sunyi wanka tare da canja kaya tace har kunyi sallar? Suka ce ae suka wuce Dining,Zarah harda radawa Naila yau zamu ci abinci a dining,Naila tayi dariya kawai,Hidaya tace an dai dage an koyi abin kirki,Naila tace ya na iya,suna cin abincin Hidaya tace tunda kika iya girki ai kowa ma ya iya, yayi dadi sosai,Naila tace ai nasan dole yayi dadi yarinya.
Spark tashi yayi yace yau ni Amarena sun zo Kuma bana yayin Naila ga Zarah itace Babyna,Zarah ta fara dariya tace mu za a siyawa abin dadi,Spark yace ashe kin gane,Hidaya tace mudai a kaimu yawo Yaya,to ai Kya bari ku huta dai zuwa kwana biyu,wayar Spark ce tayi ringing ya daga Yana bin Steps yace Papa sun bani tausayi a Kai musu shinkafa da wasu abubuwan,Papa yace karka Kai musu komai gwara su dinga zuwa gidajen ku suna ci safi sanin darajar ku data matan ku,Spark yace to shike nan.
Su Haly yau ma haka Mima ta rasa abin dafawa ta sake kantara musu tuwo miyar kuka,su Shahid duk guduwa suka yi neman abinci,Arham Yana gidan ya fito yace Mima me aka dafa Yau ne? Mima tace tuwo,yace yau ma? tace kudin hannuna na cefane ne bai Isa na siya mana shinkafa ko taliya,bana so su kare,Arham yace a fadawa Yaya Misam mana,Mima tace kyale su kawai baza suyi ba duk bakin su Daya,Dan yau ka haife shi ne baka haifi halinsa ba,duk na kirasu da safe Misam sabo da raini ce min Yayi Bai fara fita ba Amarci yake to me zan ce Masa,Spark tace zai kawo bai kawo ba,Rafeeq bashi da shi yanzu sunyi biki Kuma shi baya ajiye kudi hidimar ta Masa yawa,ko na fada ma ba lallai ya kawo ba,Kawai kuyi hakuri mu rungumi tuwon Wanda yaga zai iya zuwa gidajensu yaci yaje in anje a taho min da take away,ni yanzu gaba daya da ka ganni bana cikin hankali na,Arham yace to a cikin Ina kike ke kuwa? Mima tace kasan Allah Arham zan ci mutuncinka ya Ina magana kana raina min hankali.
Bana hayyacina bana cikin nutsuwa,yace amma na ganki a zaune ai sai muga kina kin fige mayafi,kin cire rigar kin fice kin fara tsince tsince a bola shine zamu ce ae tabbas Mima bata cikin hankalinta amma gaki a Palo a zaune kina ta Shan AC gashi kinyi girki ma ai kina cikin hayyaci kuwa.
Arham Babanku yana zirin Gaza an turasu ka duba uban harin da ake kaiwa ance ma ba a San Ina suke ba sun bace a kasar ba a samunsu ba jinsu ba a San halin da suke ciki ba in ban damu ba ya kake so nayi Mima ta fashe da kuka ta jawo dankwalinta tana goge hawayenta,tace wlh duniya ta min zafi tunda spark ya fada min maganar nan shike nan Kuma,Arham farin ciki ya kamashi Mima an fara tuba,yace ki yawaita Sallar dare,tace jiya kwana nayi Ina Sallar dare Ina karatun Qur'ani Ina mikawa Allah kukana,yace to maganar abincin ki fadawa Yan uwanki mata mana su Mummy ai zasu Tara miki kudi,Mima tace ni ban iya tona asirin gidan aure na ba,yanzu duk Gani da samarin 'ya'ya duk suna da shi Kuma ace na fita Ina cewa bamu da abincin kirki a gida mene amfanin Hakan? Ai kamar na burmawa Kaina wuka ne,kowa yayi hakuri a haka ku mike da addua Dan Allah.
Anam ta fito da plate ta gama cin tuwonta tace ba a tashi shiga talauci ba sai da aka sake ni ta wuce kitchen ta fito,Mima tace ki kira su Haly ku fito ku zage ku gyara ko Ina a gidan nan,tace to Anam ta koma ciki suka ki fitowa ga gidan duk yayi dirty,Mima tashi tayi ta same su a bedroom sunci tuwon sun koshi suna danna waya,tace wallahi wallahi idan Baki fito kunyi aiki ba sai naci ubanku a gidan Nan,Dan iskanci sai dai a baku kuci ku kwanta.
Tashi suka yi basa so amma haka suka fito suka fara aikin ga gida Kato wahalar da suka Sha ba karama bace,Mima tace Arham idan 11pm tayi ka rufe mana gida tunda kaga babu masu gadi jiya a bude kuka bar gate fa,yace to zanje gidan Misam tace sai ka dawo,Arham yace Mima na zazzagi matarsa? tace Kai ni yanzu kowa baya gabana Ina da damuwar data Sha kan kowa.
Arham ya boye dariyarsa yasan da a baya ne cewa zata Kaci ubanta,tace na zaci ma gidan Spark zaka je matar tasa tafi hankali da alama,da itace sai nace kace ta soya min doya da kwai ka taho min da ita,yace ai sai asa ta Misam,Mima tace wannan bata da mutunci wannan yarinyar na Santa farin sani idan taji nice ma baza tayi ba,Arham yace a'a baki fahimce ta bane,tace Kai rabu dani duk bazan so su ba gwara Naila,idan ba Naila ce ta soya ba karka kawo min,yace to Mima Yana murmushi yace Mima kina hutawarki abinki duniya sai Kara bude miki take,Juyowa tayi ta biyo shi da gudu,ya fice tace da ka tsaya mana marar kunya.
Gidan Naila ta fara zuwa ya same su dukkansu da kannenta suna kallo a Palo har Spark,ya shiga yace Ashe Baki kika yi Aunty Yana gyara wandonsa da yake sabulewa sabo da Ass down,Spark ya mikawa Hannu suka gaisa yace ba zama nazo yi ba wayarsa ya zaro ya sawa Spark Headphone a kunnensa yace saurari kaji recording nayi Maka, Spark yaji muryar Mima tace yabon Naila duk tafi sauran ace ta soya mata doya,Spark ya sheke da dariya yace wato wasu Ashe kudi da jindadi ne yake sasu suna wasu abubuwan,sabo da Allah mutum bazai nutsu ba sai yaji wahala.
Naila ya sawa abinda Mima tace a kunne,Naila tayi dariya tace bari na yi mata,yace to zanje na dawo sai na tafi da shi,Yaya bani Aron motarka,key ya jefa Masa yace ka hau wannan itace ba a Hawa sosai so nake ma a kunna ta tayi aiki,ficewa yayi sai gidan Misam,Yana kwankwasawa Misam ya bude,yace wai Kaine dama? yace nine mana,yace ya gida Ya Mima?tana nan lafiya,yace good.
Chika ce ta fito tana bulbula kamshi yanda gidanta ke zuba kamshi ko ina haka take kamshi,sanye take da maroon Less yaji dinkin fitted gown an mata hula me kamar gogoro ta Dora abarta,tace Arham wai Kaine ma? yace nine da yamman nan Amarya irin wannan wanka dole ki hana Yayana fita,Chika ta furta kaga laifina,yanzu Shahid ya tafi shi da kaninsa Yama kuke ce Masa? Junior? tace ae shi yace uhm sun kyauta.
Chika Misam yace Queen dakko min laptop Dina,Arham bakinsa ya rufe Yana dariya yace wato ita Queen ce uhm iyayi,kitchen ta shiga ta kawowa Arham kayan ci da Sha yace bari muci girkin Amarya Muji idan baiyi ba mu fara neman aure mu karo wata,Misam yace waye zaiyi auren? Ka shiga hankalinka ko daya ban gama cinyewa ba,Arham yace to ya kaima ka daina wankan da ruwan sanyin? ta hana Misam ya furta,Arham yace kudai Kun shiga uku to kaima tana gaishe ka? yace wajibi ne da asuba zata durkusa tace My king Ina Kwana ka tashi lafiya,amma fa bana baki ba yaro a aikace,Arham harda yin kasa da Murya yace Allah? yace cafeni take yi chaf Dan uwarka munafuki ni yaro ne ance Maka da zaka zo kana min tambayoyi,Arham yayi dariya yace da alama taka bata yi kuka ba,ta Rafeeq dai tayi sanda naje ma da kyar take tafiya,wlh idan ka kallar min mata sai naci uwarka dama abinda ke kawo ku kenan,Arham shuru yayi yayi yaci gaba da cin abincinsa.
Chika ta laptop din ta kawo Masa ta jona Masa a charge ta kawo Masa ita gefensa ta tsaya a gabansa tana murmushi tana Masa magana da Ido,dariya suke Arham Bai San me suke cewa ba da Ido da gira,Gemunsa chika ta shiga shafawa Yana kallon fuskarta Yana murmushi hakoransa masu kyau suka bayyana,har wani daga mata gira yake tana ta shafawa ta rike gemun gefen tafin hannunta Dake Saman lips ya shiga yiwa kiss,suna nishadi,a gefensa ta zauna kafadarta tana gugan tasa kanta ta Dora a kafadarsa suna magana kasa kasa,ba Wanda zai iya ji,Chika rada Masa take Sucking din Nan ashe matsiyacin dadi gare shi a dinga min kullum kullum.
Arham bai San me suke cewa ba,yace Kai idan banyi aure bama ai ni wani banza ne,sai dai ayi wacce za ayi bari Papa ya dawo,Kai Yaya Dan Allah ku daina baligi ne ni sai kusa na kasa bacci yau ina zamana lafiya Ina lallaba kaina,karku lalatani gaskiya ku gidanku ba dama Azo a tafi lafiya sai kunyi abin fada,Chika jikinta ta janye tace au Ashe yaro Yana Nan,Arham yace wlh ba yaro bane tunda na girmeki ke kanwata ce.
Misam yace kayi ka gama ka tafi gida kayi fitsari ka kwanta,yace ai na gama a juye min namana a Leda,Chika ta shiga kitchen ta zubo Masa wani da yawa ya juye na kwanon yace na gode Aunty,Misam yace kudi ya irgo ya bashi zasu Kai 10k yace karka dawo gobe baza mu bude kofa ba,tunda ka biya cin hanci ai an gama na gode ya karba ya fice.
Gidan Naila ya koma har ta gama soya Masa