Showing 120001 words to 123000 words out of 136333 words

Chapter 41 - TANTIRIYA A GIDAN YARI BOOK2 By asma baffa

08 Jul 2024

9515

ka dade yau Beb,please wlh ni yau sha'awa nake ji kayi ka kawo kazo muyi romance na rage zafi,Annoor yace Yana Shirin magana ya shide Yana hade hakora ya wani kankame Iman ya kawo,maganin ya fito da shi sabo da takaici ya Watso su kasa ya fara tattake su da kafa Yana masifa,aikin banza aikin wofi babu maganin da suke yi,Wanda bai riga ya take ba Iman ta kwashe su ta jawo locker ta zuba a ciki, tace me ya faru? tsaki ya ja ya shige toilet tare da mako kofar da uban karfi.

Maryam kuwa ta gaji da jiran Annoor ya so ta samu kudi ta shilla kudu wajen matsafa ta tafi can kasar Inyamurai Inda wata kawarta ta mata hanya,a jirgi suka je,suka je har can Arne boka matsafi ya bata kululun wani Abu kamar carbi yace taje Office dinsa ta ajiye abin a kasan kujera Yana zama a kujerar ko sati baza ayi ba zai ce zai aureta direct,amma ko ya aureta bazai iya amfani da ita ba sai wannan tsafin dake jikinsa ya karye,Maryam tace Abu me sauki zanje nasa a karya tsafin amma a fara bani Wanda zai so ni,boka ya cajeta kudi yafi dubu dari uku haka ta bashi suka dawo.

Washe gari Annoor ransa a bace ya shugo asibiti tayi sauri ta riga shi shiga Office din da duster a hannunta" tana goge kujerar" ta saka Masa abin tsafin, ta mike tana Masa sannu da zuwa" ya gasa mata ya zauna,tana ganin ya zauna ta fice da sauri tana murna.





AsmaBaffa
[2/5, 10:44 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI

BOOK 2
~YARAN JAURO~

96-100


Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM


PAGE MA NAKI NE
AIDA MAMAN TASNIM




Tana fita Annoor ya ja wawan tsaki ya zauna,kiran Iman ya gani,wayar ya daga a fusace tace Beb,wane Beb din? Iman tayi murmushi tace wai ba Beb bane,tsaki ya ja tare da kashe wayarsa,Iman tabi wayar da kallo tace a'a to ni me nayi yanzu fa ya bar gidan normal,sake kira tayi yana kallo yaki dagawa,Maryam ya kira yace ta zo,da sauri ta shugo tana rawar jiki dama gata lukuceciya,kujera ya nuna mata tare da furta sit,zama tayi da sauri kallonta ya yayi shi sai yau ma ya kalleta sai yaga ta Masa kyau ta birge shi ma gaba daya,tana zaune bata ce komai ba farin ciki ya kamata tana ta murna,a ranta tace aiki ga me kareka da na tsaya wajen wasu banzayen malaman soro,aiki sai arna wlh.

Iman ce ta sake kira ya danna reject,Iman tace Kai ai nasan Office din wlh bari naje ko ba izininsa me na Masa,bazan iya jira ya dawo ba" ni ba me hakuri bace ,ta shirya tare da saka Jilbab dinta ta kira driver tace kaini Hospital din Annoor.

Maryam kuwa hannunsa ta riko taga bai kwace ba Kuma baiyi masifa ba,ai shike nan ta fara Murza hannunsa tana shafawa,ba uwar da yaji na feeling bare ma ya kawo,tana wasa da hannunsa tace ko baza ka aure ni ba zan baka kaina a haka,burina ni ya cika ko iya haka tana magana a ranta sabo da har yanzu tana Jin tsoronsa,shi fuska ba annuri kawai Ido ya zuba mata,Iman ce tayi knocking amma ba Wanda ya kulata ta turo kofar ta shugo,tana shugowa ta ga Maryam tana Murza hannun Annoor Wanda yake rike da biro da dayan,Juyowa tayi taga Iman tana gani taci gaba tace my love yau she zaka kawo kudin auren namu?

Iman tace auren uwar wa? Ke me zan gani, tasa hannu ta fisge hannun Annoor tace Shegiya mayyar Maza dama irinku ne masu lalata Maza, karya kike wlh Annoor ba abinda zaici da ke,ko aurenki zaiyi wlh nasan to ba lafiya ba,Maryam tayi wata dariya tace kisa Ido ki gani ko dukana zakiyi ne,ke Nan har macece? Iman shake Maryam tayi suka dinga kokawa,Dake Maryam tana zaune ta Mari Maryam har sau biyu ta tuge mata mayafin da dankwali gashinta ya bayyana ba laifi tana da gashi Maryam,da kyar Maryam ta samu ta mike,Kafin ta daidaita Iman ta hankada ta Saman table din Annoor, Maryam ta saki Kara kanta kwam ya bigi Leben Annoor da ya saki Baki Yana kallo, Lebensa zafi ya zaci ma ya fashe,Iman ta haukace Bata ganin kowa Yana ta mata magana bata jinsa ma fridge ta bude ta zaro kwalabar lemon grape wata katuwa da lemon a ciki ta nufi Maryam zata buga mata,Annoor ya riketa,Yana cewa zan mareki Iman me ya kawo ki nan?kwalabar ya kwace Maryam ta fice da gudu ta bar Office din.

Iman tana haki da jijjiga tace wlh idan baka rabu dani ba zan kwashe ka da mari,Ido Annoor ya zaro bai ma San sanda yayi murmushi ba yace ni din zaki mata? tace nawa kake wlh marinka zanyi,ta hau searching Office,ta bude corridor ta dakko tsintsiya,yace kizo ki tafi gida,Iman tace sai na duba Office din nan ko laya aka makala Maka,ni dama Maryam din Nan bana kaunarta bana sonta,bani da makiya kamarta Kuma haka kawai ba abinda ta min kawai na tsaneta ban yarda da ita ba ni" Iman ta hau shara ta durkusa ko Ina tana Searching Yana kallonta yana dariya,Iman ta gano Dan Abu kamar kwallon charbi ta dakko shi tace sai naje naji fatawa a kansa wannan ma ban yarda da shi ba,tana dariya ita kanta wasa ta dauki abin" hand bag dinta ta bude tare da sakawa a ciki ta zuge tace tashi mu tafi gida,Inzo aiki kice in tashi mu tafi,kalau kike kuwa?,Iman tace Dan Allah taso ta marairaice,wata kasala yake ji dama ba uwar da zai iya kawai yazo ne,hannunsa ta rike tace muje to wannan motar sai dai driver ya kawota gida anjima,suna tafiya suka fito Maryam bakin ciki ya kamata ganin ya yarda yabi Matarsa,haushi ya kamata ta leko da kanta kanta kadan tace solobuyo, Dolon miji,Iman ce ta ji ta juya Bata ga kowa ba suka ci gaba da tafiya Maryam ta sake lekowa tace Rakumi da Akalaaa.....tayi wuff ta buya,Iman bata ko juya ba har suka Isa wajen mota ta bude Masa ya shiga ta shiga itama ta zauna driver ya ja suka tafi,tunda suka shiga mota Annoor bai ce komai ba duk yanda suke wasa da Iman yau shuru.

Kwanciya tayi a jikinsa yace a kaini wajen magani ba kalau nake ba,tunda naji Maryam tana birgeni wlh bani da lfy,Iman tun kafin na aureta nayi miki kishiya ki min magani,a yau nasan ba kalau nake ba ni dai,Iman tace ka auri wa? Daga auren mu sati nawa kwata kwata 2weeks kace aure,Iman ta fara hawaye tace ko ka aureta ba abinda zaka iya fa,Annoor yace ji nake idan ban aureta ba ban cika mutum ba,baki Iman ta bude tace a gaban nawa? Iman tace driver kaimu gidan Kawu.

Suna zuwa suka samu Amaryar Kawu tazo gaida Habiba za a musu nasiha Abba yana nan yazo,Haidar duk suna wurin aiki ba kowa,Rahma suna school su,Kawu Yana ganinsu yace Iman lafiya naga kina kuka? Iman tana kuka tace ba dole ba Kawu tunda Kun zuba mana Ido kunki ku Nemo maganin gashi nan aure zai Kara wai,Abba yace Kai Dan ubanka ko Daya baka gama da ita ba ka tafi neman wata,Kawu yace dama zara ce da Kai na baka 'yata" daga aure shine zaka ce aure zaka Kara,Annoor shuru yayi dan gaba daya baya Jin dadin jikinsa.
Abba yace ni dama ace dadin mace ya sani da sauki mace ai ya dandana yaji ne shi yasa zai karo aure ya Kuma dandana na wata yaji,Jauro ya furta gane min hanya,Maman Annoor dake zaune tare da Habiba ta Kalli Annoor tace baida hankali waye zai daura Masa auren? Marar mutuncin yaro Kai wlh ka bani mamaki ma,Habiba tace ni na taba Jin irin wannan ma sai yau Kai Annoor gaskiya ka bata wayon ka.

Abba yace dama wani me yin kitso ne na kirki aishi daga an ganshi an San ba girma a tare da shi,daga ya daure gashi sai yayi kitso ana ganinsa anga Dan duniya,shi yasa tunda nazo zan daura aure naji gabana na faduwa nace to wannan auren sai abinda Allah yayi,Jauro yace to yanzu ni abinda na fahimta yaron nan maganin musulunci za ayi Masa,Iman Anya kuwa Kuna addua? Iman tana goge hawaye tace ae muna yi har Sallar dare da karatun Qur'ani shine ma watarana in na tashe shi muyi sai yace shi bacci yake ji.
Abba yace wace yarinyar to? wata ce Maryam a asibitin sa take aiki.

Ni ban iya bin malamai ba ku dage da addua da Azkhar cewar Jauro,Iman tace ni wlh ko baza kuje ba sai na Nemo magani Ina kallo na tsaya ayi min kishiya 2weeks da aure ai na fado haba kalleni fa wlh bazan yarda ba,Abba yace harda wallewarki Yar nan?banga laifinki ba.
Annoor zazzabi ya fara ji harda rawar Sanyi yace in ban auri Maryam ba mutuwa zanyi zuciyata zafi take Kawu,suna ganin Abu kamar wasa sai ya zama gaske rawar Sanyi yake sosai,kujerar da suke zaune ya zame ya kwanta Yana cewa a kira min Maryam ko zanji dadi.

Maman Annoor ce tace wannan abin fa ba na wasa bane Aunty Habiba,Iman ta fashe da kuka ta mike ta shiga bedroom tare da fadawa Saman bed tana kuka,Maman Annoor tace lallai ya kamata a Nemo Maryam don wannan wallahi itace ta yi Masa asiri,Annoor ta kalla tace kana da number dinta? Yana rawar Sanyi yace ehh...ya mika musu wayar,Iman ce ta fito da katon bargo ta lulluba Masa ta zauna a gefen kansa" kansa ya Maida Saman cinyarta ya kwanta Yana Nishi a hankali,Jikinsa ya dauki zafi sosai,Kawu yace Iman ku tafi daki ya kwanta,ta mike tare da rike shi ya tashi da kyar da bargon a jikinsa suka shige bedroom dinta na da" Saman bed ya kwanta itama ta kwanta suka shige bargon tare,Rungumeta yayi sosai a jikinsa Yana mata rada a kunne I'm sorry" Nima ban San dalili ba,Iman tana lallaba mijinta tace ko na cire kayan kafin Jin dumin?da sauri yace ae,tashi tayi ta sawa kofar key sannan ta cire kayan jikinta ta shige bargon tare da cire Masa nasa kayan ta rungume shi Kam" sosai shima ya makalkale ta.

Maman Annoor ce ta kira Maryam ta zaci Annoor ne tunda da wayarsa ta kira,da sauri ta daga tare da furta my love,Maman Annoor tace ba shi bane Mamansa ce,da sauri Maryam tace Ina yini Mama? wai a dole ita ta gari ce,Maman Annoor ta furta Annoor yace Yana sonki shi aurenki zaiyi,gashi bamu sanki ba ko zaki iya zuwa mu ganki sai muyi miki wasu Yan tambayoyi, Maryam taji zancen aure tace to yaushe kuke son ganina? Yau ma in da hali ai akwai lokaci" okay to bari nazo,tace yawwa gidan Kawunsu ai kin San gidan tunda a karkashinsa kike aiki,Maryam da sauri tace to,Bayan sun gama wayar,Abba ya Kalli Jauro ya tabe baki yace baka iya soyayya ba Jauro Amarya guda tayi abin Azo a Gani maimakon kace ban mu kashe sai ka tsaya sekeke da Kai kamar bishiyar dabino,Habiba dariya ta dinga yi tace ku dai wlh baza ku girma ba,Hashimu Allah ya shirye ka,Abba yace Allah ya shiryeni wlh tunda ba Yar Wanda na lalata,Kuma gani da iyalina muna zaune lafiya har fada nake nema muyi ma ai kuwa ba karamin shiryayye bane ni,Maman Annoor tayi dariya tana dauke fuskarta sabo da Jauro ya kafe ta da Ido kamar wani maye.

Jauro ya dawo tsakiyar matansa ya zauna Habiba a gefe Amarya a gefe,ya Kalli Habiba yace black beauty, ya Kalli Amarya Sadaka yalla wace ne zata kwace ni,Habiba tace na bar mata wlh har sati daya kwana,Abba yace ai baki birge ba Nan har kyauta kika yi Habiba,ke da zaki ce Jauro na barka kayi wata uku a dakin Amarya sai kice sati daya kacal sabo da dama ku gidanku Habiba gadon rowa kuka yi wlh,madarar shanu bakwa iya kyautarta,sanda kike tallan fura wacce irin tsada ce baki ba,ana ganinki da kwaryar nono har nunaki ake da baki ga uwar tsada can.

Jauro yace karka takurawa matata Kai Yar Innar taka mene bata yi ba,Abba ya gyara zamansa yace Yar Inna ta hau dokin zuciya fushi take dani kwana da kwanaki taki sakkowa,abin ya dameni Kuma Ina Jin Mohsin zan fadawa yazo ya tare min fadan nan,muna zaman mu lafiya na takalowa kaina yanzu gashi Yar Inna ta juya min baya,Jauro ya dinga dariya yace Allah ya Kara,idan ance Maka Dolo kaji haushi,Abba yace ka taba ji nace naji haushi in an ce min Dolo? Ni bana Jin haushi Wanda ya fada shine a wahale bakinsa ke aiki.

Maman Annoor kunyar Habiba take ji duk ta kasa magana,Abba yace to Habiba uwargida Kinga hukuncin Allah,haka Allah ya tsara kiyi hakuri da abinda aka miki,ba wai mun Kara aure bane Dan aci mutuncinki ba,Jauro yace ban gane mun Kara aure ba? Na Kara aure dai Kai Ina ruwanka a ciki ,wai Hashimu ko da Kai zamu shiga dakin Amarya ne? Abba mikewa yayi yace a'a Allah baka hakuri tunda baka gane hausar ba,ni na shiga dakin matar wani Allah ya tsare min,Jauro yace to zauna mana a karasa Abba yace a'a,Habiba tace Dan Allah ka zauna a kashe wutar Annoor tukun,da kyar Abba ya zauna,Abba baya fushi ba a fada da shi,yace ai ni Yar Inna yau Alala take mana,idan banci akan lokaci ba akwai kura,dama kadan take jira fushi take yi.

Ba a dade ba sai ga Maryam tayi Sallama cikin katon Hijab dinta har kasa,tayi shigar Kamala,ta shugo ta zube a kasa tana ladabi ta durkusa ta gaida su da ladabi,suka amsa,Habiba tace kece Maryam din? Maryam tana kasa da Kai ta dago fuskarta tace nice,Maman Annoor ce ta Mike da sauri tana nuna Maryam da yatsa tare da kiran sunanta tace Maryam kece? Maryam tace kin sanni ne? tace kece dai baki gane ni ba,Ina mahaifinki? tace Yana US Bai dawo ba,Maman Annoor tace to ai ke shirme kike yi Annoor din Yayanki ne Ubanku daya da shi,babu aure a tsakaninku idan baki yarda ba kira mahaifinki yanzu kice waye Annoor.

Maryam gigicewa tayi ta rude ta dakko wayarta a jaka tare da kiran Mahaifinta a waya,bayan sun gaisa tace Daddy wai dama kana da Da Annoor? Daddy yace Ina Annoor din? Dan Allah hadani da shi ya girma sosai Ina da pictures dinsa mahaifiyarsa ta tura min ta Whatsapp,Allah sarki ai ubanku Daya Maryam Yayanki ne shine Dana na farko,na zalunci mahaifiyarsa na zalunce shi,Allah yasa mahaifiyarsa ta yafe min,na nemi yafiyarta,yanzu shi kawai ya rage min, inshaallah next week zan zo Nigeria ki kaini Inda yake.

Maryam tuni ta fara kuka tana hawaye ta durkushe a wajen tace Dan Allah ku kira Annoor zan tonawa kaina asiri,wlh ban san Dan uwana bane na jini,ban sani ba na cutar da shi,shi yasa aka ce in Allah bai baka Abu ba karka sake kace Kai ta dole sai ka same shi.
Habiba tashi tayi taje ta dinga knocking tuni sunyi bacci har Iman din,da kyar Iman ta farka tace Ina zuwa,kayanta ta Maida jikinta tare da bude kofarta tace Umma,Habiba tace taso Annoor ku fito" tana fadar haka ta juya,Iman tashinsa tayi da kyar ya tashi ya zauna kayan ma sai da ta tayashi ya saka sabo sangarta,tace muje Umma suna kira,yace Allah yasa sun Nemo Maryam din na ganta,hannun sa Iman ta kama ta gartsa Masa cizo,ya saki Kara suka fito Yana yarfe hannu.

Yana fitowa yaga Maryam a zaune tana sharbar kuka,Abba yace Iman ku zauna,zama suka yi,baka Jin komai sai sautun kukan Maryam,tace dan Allah Annoor ku yafe min,na cutar da ku nasa kunyi Zina Bada saninku ba,tana kuka tana basu labarin yanda akayi duk ta kaisu hotel har Annoor yayi amfani da Iman basa cikin hayyacinsu,sannan ta Fadi duk irin asirin data dinga musu,tace wannan na karshe shine na sa Masa a kasan kujera ya zauna,Iman ta jawo Jakarta ta zaro Dan kwallon abin kamar carbi ta nunawa Maryam tace shine wannan? Maryam tace shi...shi....shine,Annoor yaji komai amma kala bazai iya cewa ba,tsafi Yana jikinsa,Iman tashi tayi ta rufe Maryam da duka da cizo da yakushi,Maryam tana kuka,Abba yace kyaleta Iman ko me zaki yi baza ki iya ramawa ba,cuta ce ta cutar da ku,amma wannan yarinya ke dai lokacin Jima'in cikinki tare babanki yayi da shedan lokaci guda suka aiwatar da shedan,Jauro yace tambadaddiya ba duk yanda aka yi a nono ta tsotso.
Cabdi cewar Habiba sai ki je ki karya tsafin naki ko,Maryam ta mike ta fice da gudu tana kuka,motarta ta shiga a lokacin ta wuce kauye wajen Malamin da yayiwa Annoor tsafin hanashi mu'amular aure,tana zuwa taci sa'a Yana Nan,tace Malam ka taimakeni Wanda na baka aiki a kansa kayi min Dan uwana nane na jini ubanmu daya,Malam yace na baki shawara ai tun farko kika dage.

Maryam tace da me yasa baka fada min Dan uwana bane tunda Kuna duba ai sai ka sani,Malam yace Allah ne yasan gaibu,Maryam tana harararsa tace ku dai makaryata,Yace ke ki shiga hankalinki badan Ina Tausayin yaron ba wlh bazan karya ba,sai na kassara rayuwarki,shuru Maryam tayi tace nawa zan biya yace dubu Hamsim,haka ta bashi akan ya karya aikin,wani garin magani ya bata yace kije ki zuba garin Nan na magani a hannunki ki kira sunansa sau uku sannan ki bushe garin yabi iska shike nan,Maryam tace zan iya yi a Nan garin? Yace ko a Ina ma,ta karba ta fito ta shiga motarta sai da tayi Nisa da garin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login